KIBIYAR AJALI 6

Advertisement

 

BABI NA: 6_*

     _*TUNA BAYA…!_*

 ****Malam Basheer (Bashari) Inuwa na Alkali, Shine cikakken sunan mahafi na, Kuma karkarar Durbun itace tushen su, Anan aka haifi kaka na marigayi Malam Inuwa na Alkali, ance aminin marigayi alkali ne, Mutumi na farko a karkarar mu daya je birni yayo karatu ya zama alkali. Mahaifi na Malam Bashari shi kadai ne ‘da awajen iyayen sa, Baffan mu yace sauran yan uwan sa da anhaife su suke

rasuwa, Shi kadai ne awajen iyayen sa. Mahaifiyar sa fulanin karkarar Gandar ce. Gaba da baya mahaifi na bashi da yan uwa, Domin mahaifiyar shi dama kafin rasuwar ta irin fulanin tashin nan ne. Toh bayan ta auri kakana ma’ana mahaifin Baba na sai yan uwanta suka tashi daga karkarar Durbun suka koma wani k’auyen.

 

Mahaifin sa kuwa dama ya manyan ta, Bai da wasu sauran yan uwa, Sai kanwar baban sa, Ita kadai ce tayi ragowa tana can cikin kauyen nan wajajen rijiyar badamasi, Kuma ta manyanta ko gani bata yi sosai.

Advertisements

 

Baffan mu yace ya hadu da Umma ta ne a birnin, Acan gefen gari suke. Yace hakika Umma ta tafuto daga tsatson babban gida, Domin gida ne na malaman addinin musulunci, Domin har makarantar islamiyya suke da ita a kofar gidan. Ba dai masu arziki bane, Amma suna da wadatar zuci. Yayan mamana yana da makarantar allo ta almajirai. Shi dai Baffa na abunda ya kai shi birni alokacin neman kudi yaje, Ya fara sana’ar wankau, Daga nan ya dena ya koma sana’ar gini. Inda yake leburanci yana debewa ma’aikatan dake gini ‘kasa da kuma ruwa. A rijiyar gidan su Umman mu yake debo ruwa, Kasancewar akwai samari a layin, Sai ya zamto Baffan mu ya fara wanke takalma (shoe shiner) Yakan wanke musu takalman su ya kuma goge musu har da dinke wa. Har Allah ya hada jinin su da Yayan Ummah ta, Suka fara abota. Ta sanadiyyar yayan umma ta, Baffa yasan Umma. Inda suka fara zumunci na yaya da kanwa, Domin abotar su da yayan umma ta ta kara kulluwa sun zama aminai.

 

Umma ta tafara boko har aji biyar, Bata gama ba suka fara soyayya da Baffa na. Baffa ya nemi auren ta aka bashi. Ya kasance Baffa yace da yazowa da yan uwa da yan karkarar nan maganar auren sa sai suka soki zancen, Kan ya za’ai ya auro yar boko? Bayan ba bokon yai ba? Kuma yar birni masu abun kunya. Baffa ya toshe kunnuwan sa da surutan mutane yai biris da zancen su. Ya auro Umma na suka dawo nan Durbun da zama. Baffa yace sam bata kyamace shi ba ba kuma ta kyamaci yan kauyen nan ba. Suka zauna cikin lumana da kaunar juna, Kafin ta haife ni ta haifi har jarirai uku duk suka rasu, D’aya kuma bai zo da rai ba. Sai daga baya Allah ya azurta ta da samun ciki na, Baffa yace tasha wahalar ciki na, Domin Sai da suka yita zuwa birni a asibiti ana kara mata jini. Allah yasa ta haife ni lapia. Kuma tunda ta haife ni, Shikenan tayi sallama da lapiar ta, Yau tana Lapia gobe tana gadon asibiti. Ina shekara shida Allah ya mata rasuwa..

 

Malama Mardiyya ta zare tagumin da tayi tana matsar hawaye, Nima hawayen nake. Na Kasa cigaba Sai da Malama Mardiyya ta sake tambayata cewar,

 

 “Kiyi hak’uri Khadija, Allah ya jikan Umman ki da rahama, Allah ya dubi maraicin ki ya baki miji nagari. Yanzu yan uwan mahaifiyar ki suna ina? Shin ba sunan halin da kike ciki bane? Ko dama can mahaifin ki nada wata matar?”

 

Saurin girgiza kai nayi, Na fyato kakkaurar majina na katse da wani kara a gefen kafar Malama Mardiyya kafin na cigaba da cewa,

 

 “Yan uwan Umma ta na can birni, Kuma duk maza ne Ita kadai ce mace a dakin su, Bayan tayi aure Baffa yace iyayen ta sun rasu daga baya kafin a haife ni. Amma su hudu ne a wajen iyayen su, Maza uku, Mace d’aya, Ita kenan. Akwai Kawu Hashim, Kawu Kabiru, Da Kawu Isma’el, Sai ita Umma ta mai suna Jamila. Sun taba zuwa su duka ukun da wata sallah, Suka bani kudi da yawa da kaya, Lokacin Baffa na ya auro Gajiyalle walle ta kwace komai. Kinsan fa Baffa na tsoron ta yake wallahi, “Yan uwan mahaifiya ta gaba ki dayan su ba wuri d’aya suke zaune ba, kowanne yana wani gari shi da iyalin sa, Shi Kawu Isma’el shi kadai ne a birni inda kuka zo, Sai Kawu Hashim shi yana garin legas, Sai Kawu Kabiru Shi kuma yana garin Jos. Duk kanin su kowanne a tare yake da iyalin sa, Kowanne da irin aikin sa, Domin Kawu Hashim shi malamin makaranta ne bangaren arabi a jami’ar Legas. Sai Kawu Kabiru shi ma babban malamin sunnah ne yana kuma da makarantar kansa a garin na Jos,

Advertisements

 

“Sai Kawu Isma’el shi yana Birni. Kuma Baffa yace min babban dan kasuwa ne shi da ake ji da shi a birnin. Wallahi da suna kula da ni fushi sukai daga baya. Sunce Baffa ya bar musu ni yaki. Kuma yazo ya auro Gajiyalle da wayo na sunzo ta musu rashin mutinci har ta juyewa kawu Isma’el ruwan randa a kayan sa. Shine tun daga lokacin ba su sake zuwa ba. Amman nace idan na zama babba walle sai naje birni wajen kawunni na..”

 

Malama Mardiyya ta kada kai kafin ta sake cewa,

 

 “Yaushe aka auro Gajiyallen?..”

 

Na bude baki zan bata amsa, Sai ga Malam Auwal akan mu yana zare idanu,

 

 “Ke tashi kije aji..”

 

 “Zatazo Malam afuwan. Magana muke yi mai matuk’ar muhimmanci, Kuma nima free period ce dani. Amana hak’uri.”

 

Kada kai yayi ya koma Aji, Ni kuma dadi ya mamaye min kriji jin ance bazan koma ajin ba sai anjima. Dama duk dan zaman da nayi acan ya gundure ni, Takashi na sai ciwo yake. Cike da farin ciki na cigaba da cewa Malama Mardiyya,

 

“Bayan rasuwar mahafiya ta, Na zauna a hannun Kanwar kakana ta wajen uba. Wadda nace miki tana can b’angaren rijiyar badamasi? To na zauna acan na tsawon shekara d’aya. Daga nan yan karkarar nan suka damu Baffan mu da maganar ya kara aure, Ya kasa samun wadda zai aura, Shine aka hada shi da Gaji sunanta Salamatu. Amman fa ta taba aure, Wai auren tane ya mutu, Kuma mijin yana nan wallahi kwanaki ma ya auro wata yar kasan layin mu. Wurin gidan su Tsalha…”

 

Malama Mardiyya ta kada kai tana bi na da kallo, Na sakuto hanci na na goge a rigata kafin na cigaba da cewa,

 

 “Toh sai baffan mu ya auro ta, Daku na uku ne a gidan mu, D’aya dakin babu komai cikin sa, Bayan ya auro ta sai tace wai kar ya dakko yar sa dan ba zata rike ni ba, Awajen Baba Ladingo naji( Kanwar Kakana.) Dakyar dai Baffa ya dakko ni ya dawo dani gidan, Shine itama ta karbo dan ta a gidan tsohon mijin ta. Tazo dashi gidan, Ya girme mini sosai, Sunan sa Mudi. Tunda tazo gidan mu ta gaje gidan, Dakuna ukun dake gidan mu biyu suka zama mallakin ta, D’aya nata , D’aya na Mudi. D’aya kuma na baffan mu. Harabar gidan kuma ta mai da rabin sa turke ta zuba dabbobin ta. D’aya dakin kuma dakin girki ne na abinci. Dake babba ne sai ta raba shi biyu d’aya ta zuba kajin ta da zabbin ta da sauran abubuwan kiwon ta. Rabin dakin kuma aciki nake Kwana da taburma ta,

 

“Tunda Baffa ya auro Gajiyalle na shiga kuncin rayuwa, Gaba d’aya bansan farin ciki ba, Kankanuwa ta dani anman damuwa ta mun yawa, Ta kassara Baffa na sam bashi da jarin kansa, Duk yan kadarorin sa ta cinye. Tanata bunkasa harkar kiwon ta Shi kuma yana kara talaucewa, Har takai ta kawo gonar sa guda d’aya ce tai ragowa, Itace yake samu yai noma mu samu na abinci… Wannan shine takaitaccen tarihi na malama!”

 

Malama Mardiyya taja doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai cike da damuwa,

 

 “SubhanAllah! Lalle Khadija kina ganin jarabawar rayuwa kala kala. Shysa tun sanda na ganki nake kokonton anya a hannun mahaifiyar ki kike? Ubangiji Allah ya shiga cikin lamuran ki Khadija. Babu komai Kowa da irin tasa jarabawar kinji? Da’din ta na gaba, In Allah ya yarda kuwa, Zaki tuno munyi zancen nan. Kina zuwa Islamiyya kuwa?”

 

Nai saurin kada kai alamun a’ah! Nan ma kai ta sake girgiza cike da tausayi murya na rawa ta sake cemin,

 

 “Kenan baki iya karatun addini ba Khadija?”

 

 “Ban iya ba Malama, Har sallah dik banayi Malama. Makarantar allon garin nan maza ne kawai keyi. Islamiyyar kuma can alfindi masu kudi ke kai yayayen su suyi. Toh yanzu nema mai gari yace zaku dinga koya mana ko Malama?”

 

 “Insha Allahu kuwa! Da yardar Allah zamu koya muku. Kisa a ranki kuma zaki iya Khadija. Da yardar Allah kanki zai waye da komai. Duk abunda baki gane ba ki rika tambaya ta kinji! Ki kuma dauke ni tamkar yayar ki. Kinji ko?”

 

“Eh Malama. Nagode Allah ya saka da alkhairi..”

 

“Amin.. Muje na raka ki ajin kinji? Cikin satin nan kuma zan baki uniform kyauta da takalmi, Da kayan wanka. Kinji?”

 

 “Nagode Malama.”

 

Bayanin asambuli ta min, Dama sauran abubuwan da suka shafi harkar rubutu, Sannan ta riko hannu na, Ta raka ni har aj. Malam auwal ya zabga min harara nima na rama harda karin gatsine gatsine.

 

“Wallahi karkaryaki zan yi dan bana daukar rai ni. Kizo nan kuma ki zauna ta yadda in kinyi ba dai-dai ba in zaneki.”

 

Ya yi maganar yana nuna min gaba, na kalli karshen ajin naga babu kowa kuma Uwande tana gurin tana siyar da yajin masau, can nake son na zauna amman mutumin nan yana neman ya kwafsa min. Na rike kuguna ina cizon leban kasa tamkar wace take shirin yin dambe.

 

“Ina jin dai baki ji abin da nace miki ba ko? Khadija ki shiga hankalinki kar kisa musa kafar wando daya da ke, zo ki zauna nan gurin.”

 

Ganin yadda ya kafe sai akan dole sai na zauna a gaba yasa naje na zauna ba dan zuciya ta na so ba. Yaci gaba da koyar damu gaba daya bana fahimtar abin da yake cewa, dan tunani na da hankali na duk suna gurin Uwande dake sai da kayan kwalam da makulashe.

 

“Ke Khadija tashi ki karanto min abinda na koyar daku yanzu.” Na dafe kirji ina zaro idanuwa nace,

 

“Ni kuma malam! Na shiga uku ni Dije yo me naji kana koyarwa?”

 

Da alama yaji matukar haushi duba da yadda ya tsuke fuska yana min kallon tsana dan ina da tabbacin na rashin son zamana a ajin ne. Ya sake canza min guri ya maida ni kusa da kujerar da yake zama idan ya gama zazzagawa cikin ajin, saboda wai tsokanar na kusa dani da nake yi shine ya hanani sauraran bayanansa. Yaci gaba da nanata mana A to Z, sauran yara suna fada dai dai sabanin ni da wasu da muke fadin. Ah be ch dh eh af gh.. Shec ai de ke al af-af, daga wadannan harrufan duk bana iya fada dai dai, amman daga O zuwa karshe duk ina iya furtawa yadda suke.

 

“Very good Siyama, zan baki kyauta don yau kinfi kowa kokari zoki karba.” Ya kira Siyama ya mika mata alayoyi da biskit.

 

“Malam nima fa nayi da karfi.” Nayi magana hankali na a tashe ganin an bada kyauta.

 

“Rufe min wannan kazamin bakin naki, kinyi da karfi kina wani Ah be. Sai ki bari idan kin iya cewa A b sai asan kin yi koda a hankali ne.” Da zumudi nace.

 

“Da gaske idan nayi dai dai gobe zaka bani nima?” Ya fara hada littattafansa yana cewa….

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 31-32

Advertisement  _*KIBIYAR AJALI…..!!!!*_ _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_            🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA…

KIBIYAR AJALI 11

Advertisement                  *11*         *Ranar* wata sanyayyar asabar da damina, Muka tashi da babban tashin…