KIBIYAR AJALI 8

Advertisement

 

_*BABI NA: 8_*

 

 

_*Wattpad:missxoxo00_*

 

 

            ***

 

Advertisements

“Hannu malama Mardiyya.”

 

“Yauwa Dije gwara da Allah ya had’a ni dake yanzu. Me ya sa bakya zuwa makaranta kwana biyu, na bincika ance min kina nan lafiya lau kawai ganin dama ne baki zo na.”

 

Na tafa hannaye ina dariya,

 

“Malama tawa!”

 

Maganar tawa ta fito cike da sauki dan ina son matar nan saboda tana sona.

 

“Ina jinki gaya min meke faruwa?”

Advertisements

 

“Babu komai wallahi, mantawa nayi ma da makarantar.”

 

“Innalillahi! Dije daman baki saka son zuwa makarantar nan a zuciyar ki ba?”

 

Na zaro ido waje,

 

“Kai! Malama ai bazan iya sata a zuciya ta ba, kinga girman makarantar kuwa?”

 

Ta girgiza kai,

 

“Ni ba haka nake nufi ba, ina nufin kiji kina son zuwa koyan karatu a cikin ranki. Haba Khadija ya za’a yi kina girma amman baki dena wasu abubuwan na shirme ba? Yanzu ina zaki je?”

 

“Oho, ni daga wajan kallon wasan kauraye nake.”

 

Ta girgiza kai tare da gyara jakarta a kafadarta. Kallo na tayi sosai sannan tace.

 

“Muje ki nuna min gidan ku”

 

Babu musu na amsa mata muka tafi muna hirar mu har muka hadu da malam Auwal zai tafi gidan liman, yana kallan mu amman yaki kula mu itama malama Mardiyya bata yi masa magana ba har muka wuce. Da sallama a baki na muka shiga ciki, Gajiyalle tana tankaden garin dawa da zata yi tuwo. Taki amsa min tayi tunanin ni kadai ce, sai da taji muryar malama Mardiyya cikin sallamarta da dole ne duk wanda yake cikin gidan ya jiyo.

 

“Sannuki da zuwa bakuwa, shigo mana.”

 

Gajiyalle ta fada tana janyo tabarmar dake bayan ta, naje na karba ina ta faman rawar kafa saboda malama tazo gidan mu. Malama Mardiyya ta zauna tana bin gidan mu da kallo ta ko ina, muryar Gaji ta katse mata tunanin ta inda tace mata.

 

“Ina wuni?”

 

“Lafiya lau, ya gidan?”

 

“Ƙalau muke, sai dai ban wanyeki ba.”

 

Gajiyalle tayi maganar tana ajiye rariyar da take tankade da ita sai kallon malama take yi kamar wacce aka kafewa idanuwa a kanta.

 

“Allah sarki daman ba zaki sanni ba gaskiya. Ni malama ce a wannan makarantar da aka bude. Kwana biyu naga Dije bata zuwa, shine na hadu da ita a hanya nace dan Allah ta kawo ni gidan su.”

 

Tunda Gajiyalle taji tace malamar mu ce shikenan ta sauya fuska tayi kicin-kicin da fuska da alama bata so hakan ba. Malama Mardiyya ta ce na zauna na samu guri a bayan ta na zauna dan ban san me zata fada mata ba, kar naje Gajiyallen ta kawo min naushi.

 

“Maman Khadija dan Allah me yasa baki tursasata akan zuwa makaranta? Gashi duk tayi wani yarbatsai kamar wata marar mafadi. Dube ta ɗan Allah kamar ba mace ba sai tsami take, ilimi fa yana da dadi Maman Dije, dan Allah kiyi kokari ki canza ta. Ni ban zo dan na gyara miki wani abun ba, amman dan Allah kisa ido akan ta koda wajan kula da ibada ne, ace kamar Dije amman bata san meye sallah ba bare tayi? Muna so muga an samu manya a cikin kauyan nan, amman burin mu ba zai cika ba sai da taimakon ku iyaye, musamman ku mata.”

 

Gajiyalle tasa kafarta ta buga a kasa tare da kankance idanuwa tana mai nuna malama Mardiyya da yatsa tare da cewa.

 

“Ke! Dakata min da wannan surutun naki haba, cacacaca kamar wata mai rubabban baki. Yo haka ne mana kinzo sai barin zance kike kamar wadda aka budewa makogwaro. A hayye na naye yau na ga ikon Allah, kizo har gida na kice zaki tsara min yacce zan dinga yin rayuwa ta? To ko hi mai gidan be isa ba ballantana wata ke fankan fayau. Dije kuma ai gaki gata nan sai ki maida ita yadda kike so kinji uwata? Ki tashi ki bar min gida kafin na dakko tabarya na ragargaji kanki walle.”

 

Da sauri naga malama ta tashi tana rataya jaka, ta kuma kallon Gajiyalle cike da takaici sannan ta wuce ta bar gidan. Nima juyawa nayi da nufin na bi bayan malama naji ta riko min riga ba zato kawai ta wanke min fuska da mari tana kuma dukana.

 

“Shegiyar yarinya kawai, bari na kashe ki na huta da janyo min magana da kike yawan yi. Saboda rahin mutunci irin naki sai kije ki dinga taho min da mutane, wato zuwa kike kina min hirri a waje ko? To walle talle ko babanki bai isa ya dinga yi min surutu a gari ba.”

 

Ta dinga duka na malama Mardiyya na ji amman ta kasa dawowa saboda kar taje bayan ta tafi ta barni cikin wata fitinar tunda ba tare zamu zauna da ita ba. Ranar nasha wahala a gurin ta, nayi wankin kayanta da wanke-wanke da shara ta hanani fita ko ina sai da aka yi magariba sannan na gudu da ta shiga bandaki.

 

Washe gari tun da sassafe na tafi gidan Sahura nayi layin karbar sadakar koko da liman yasa a dinga bayarwa. Na karba nasha daga can kuma na yi wucewa ta makaranta duk da cewa babu kowa haka na samu guri na kwanta har wani baccin ya yi gaba da ni ban sani ba. Hananiyar mutane ita ce ta sani farkawa naga har an fara taruwa, na tashi ina ta faman zaro ido karaf miƙa hada idanuwa da malam Auwal yana rike da bulala ya ce min.

 

“Nan ina ne?”

 

“Aji.”

 

“Shi ne kika zo kina ta yiwa mutane munshari kamar kina kan gado?” Na yatsina fuska ban kula shi ba.

 

Mtsww ya ja tsaki ya bar gurin ya zauna akan kujerar malamai yana ta bude littattafai har aka gama zuwa. Ya dakko rigester yana kiran sunaye, yana zuwa kan sunana ya dinga tsaki saboda ganin fashin da nake yi a ciki yafi na kowa yawa, kamar ba zai kira ni ba sai kuma ya ci gaba da kiran ragowar mazan.

 

“Maude Nalami…?” Ya amsa.

_“Present Sir..”_

 

“Yahaya Liti…?” Shima ya amsa.

_“Present Sir..”_

 

“Khadija Baffa…?” Ina sosa cikin kunne na ina amsawa.

 

_“Na’am..! Gani..!! Nazo..!!! Sa farazen…!!!!”_

 

Malam Auwal ya sanya kasan biron hannunsa cikin baki yana taunawa da hakori saboda takaicin da na bashi. Ya hura iska daga bakinsa yana sake matse ido kamar wani mai jin ciwon kai, ya dago yana kallo na cike da tsantsar tsana wacce na rasa dalilin da yasa yake min ita.

 

“Baki da kunya Khadija, amman zan gyara miki zama a cikin ajin nan wa wuya kawai.”

 

Yaci gaba da kiran sunaye jefi-jefi yana jan tsaki, ni dai tunda ya kira suna na ban sake kula shi ba, ana haka sai ga shi malama Mardiyya ta aiko cewar naje office na same ta, na tashi na fita tun kafin ma ya bani izinin tafiya. Ina zuwa ta taso tace muje ni dai ban tambaye ta ko ina zamu ba dan duk inda zata kai ni bin ta zanyi shi yasa ma ban tambaya d’in ba. Kai tsaye muka tafi gidan mai gari, bayan sun gaisa da matan sa dama mai gari ya riga ya sanar da su zuwan ta tayi mishi bayani tun jiya cewar zata zo da ni.

 

Mayafi ta gyara sannan ta dakko wani zani a cikin wata bakar leda ta miko min wai na cire kayan jikina na daura shi, nayi kamar yadda tace daga nan tace muje bandaki. Na shiga ita kuma ta dibo ruwa cikin bokiti ta kai bandakin, ta kuma dibar wani ta kai sannan ta dakko soso da sabulu ta shigo tace na cire zanin nawa na cire. Allah sarki malama Mardiyya mace mai mutunci mai kyauta da yin alkairi fisabilillahi. Sai da tayi min sabi uku harda goge faso duk da cewa bai fita ba amman an rage ba laifi.

 

Na daura zanin muka fito wata iska naji tana shiga cikin jikina mai matukar dadi da ratsa zuciya, na dinga jina tamkar a cikin furanni masu launi nake. Ta shafa min mai sannan ta ciro uniform da sabon pant na saka ta kuma shafa min huda da kwalli, tun a gidan su Baraka wato amaryar mai gari suke ta yi min tsiya, ni kuma ina ta dashe baki saboda farin cikin yadda nake jin na sauya gabaki d’aya.

 

“Ko kefa Khadija, kinga yadda kika yi kyau kuwa? Dan ma dai ba ayi kitso ba, amman soon shima zan yi aiki a wannan gashin naki.”

 

Malama Mardiyya tayi maganar tana nuna min wasu kaya a ledar da ta zo da ita, tace min idan an tashi daga makaranta nazo wajan Baraka na karba, riga da skirt ne na atamfa, sai dai daga gani ansa saboda ba sabo bane amman masu kyau ne tunda da kyansu har yanzu. Ta kama hannu na muka fito, mutane tun a hanya suke kallo na suna yi min tsiya, a haka muka karasa makaranta ta kai ni har cikin ajin mu, a lokacin daman period ta kusa fita mu shiga ta malam Auwal. Yan ajin mu baki bude suka kalle ni suna mamakin gani na a haka, sai kowa ya fara matsa min kusa dashi wai nazo na zauna ni kuma sai yatsina fuska nake yi, dan ji nake nafi kowa kyau a duniyar nan.

 

“Dije!”

 

“Na’am malam Habu.”

 

“Kinga yadda kikai kyau kuwa? Masha Allah, kai Allah ya sakawa malama Mardiyya da alkairi tayi kokari.”

 

Ina hura hanci na tafi karshen ajin na zauna sai faman bude ido nake yi. Malam Habu yana hada littattafansa yana cewa.

 

“Dama zaki ci gaba da tsafta da kinfi haka mutunci Dije.”

 

Ban kula shi ba ji dai dan magana ma a wannan lokacin wahala take yi min.

 

Malam Auwal ya shigo daman shine last period, ya dinga bin yan ajin da alama da alamar akwai abin da yake nema, na dora kai na akan benci dan bana son ma yaga fuskata bare yace nayi kyau bana son yabon shi.

 

“Ina Uwande da Dijeh?”

 

Ya tambaya yana kallon yan ajin.

 

“Ga Dije nan, Uwande kuma tun dazu ta tambayi malam Habu zata fitsari har yanzu bata dawo ba.”

 

“Guduwa tayi yau ma kenan?” Ya tambaya.

 

“Eh malam tallen wake da hinkafa ta tafi.”

 

“Okay! Ina Dijen ita kuma?”

 

“Malam gata nan ta boye?” Suka hada baki wajan bashi amsa.

 

“Ke Khadija! Ke! Ba magana nake miki ba ne?”

 

Kamar irin a film d’in nan idan za’a nuna star, haka na dago a hankali cike da yanga har na tashi gabaki d’aya. Da ya kalle ni sai da ya murza idanuwa alamar ko yana ganin gizo, saboda dazu ya san na fita kamar yadda ya sanni, amman yanzu ya dawo ya ganni fes kamar ba Dije Oganniya ba. Bakinsa a hangame yana shafa d’an siririn gemunsa ya lashi lebansa tare da cewa.

 

“Zo nan.”

 

Nayi tamkar banji ba sai da ya sake cewa.

 

“Baki ji ba ne?”

 

“Naji, kafa tace take ciwo.”

 

“Yanzu ta fara yi miki?”

 

“A’a tunda zamu dawo nida malama Mardiyya.”

 

Jinjina kai ya yi tare da kallon Siyama da Habi yace.

 

“Kuje ku riko hannun ta ku kawo min ita nan.”

 

Haushi ya kuma kamani, wannan malamin jarababbene uban masifa, Hege! Suka riko ni kawai na fara dingishi kamar wata gurguwa har suka kai ni inda nake zama idan shine a ajin. Ya shiga shafar gemo yana kallo na kasa kasa kamar wani marar gaskiya, sai kawai cewa ya yi.

 

“Kin ganki kuwa? Amman dai ba ke ki kayi wankan ba ko?”

 

Ban san lokacin da na daga masa kai ba alamar ‘eh’ sai kuma haushin kai na ya kama ni.

 

“Haba ni dai naga alama, toh Allah yasa dai a dore da tsabtar. Yanzu dai ga ki kamar mutum yanzu.”

 

“Kutmelesi! Da ni aljana ce ko me?”

 

Harar da ya watsa min itace ta tunatar dani a yadda na yi masa maganar, nayi saurin sanya hannu na toshe baki na ina muzurai.

 

Ci gaba da koyar damu ya yi jefi-jefi yana kallo na tare da yi min tambayoyi amman duk babu wasu kwararan amsoshi, a haka har ya kammala mana aka kada karaurawar tashi.

 

Ana tashi daga boko mun mimmike zamu tafi gidah Malam Auwal ya dakatar damu ta hanyar biga bencin gaban sa,

 

 “Kowa ya zauna..”

 

Kowa ya zauna ban dani, Saboda ni yanzu bakin kasuwa nake son zuwa wajen Habibalo mai awara. Yanzu i war haka ta gama suya zata bayar da burbushin awara sadaka,

 

 “Khadija Baffa samu waje Ki zauna, Kin tsaya gandar-dar a tsaye uwa sanda.”

 

 “Malam sauri nake yasin. Me zamu maka ne bayan an tahi?”

 

 “Uban.. Zaki zauna ko sai na lakada miki duka.”

 

Baki na na cuno gaba, Gwara ya casa ni akan ya hanani zuwa wajen Habi mai awara.

 

 “Ke ba zaki zauna..”

 

 “Jaraba gad’ar maza. Aikin banza.”

 

Na fada a hankali ina mai sake kafewa a tsaye, Tsumangiya ya d’akko sai dake ni, Sai ga malama Mardiyya ta shigo da littattafai fal a hannun ta.

 

 “Ah’ah Khadija mai kike a tsaye?”

 

 “Ko ba Malam bane zai daka ni? An fa tahi Malama, walle sauri nake akwai inda zani, Amma ya hana mu ko me zamu masa.”

 

 “Zauna kinji? Karatun arabi Za’a fara muku yanzu. Kuma kullum hakan ce zata kasance da yardar Allah. Zan raba muku littattafai da Qur’ani, Malam Auwal zai fara yi muku nasa b’angaren kafin na shigo nayi muku iya matan kina ji?”

 

Kada kai nayi badan naso ba . Na koma na zauna kawai Saboda ganin mutuncin ta. Tana min magana ne a hankali kullum, Sam bata fada. Shiyasa take birge ni. Ba dan inason na zama kamar irin na gidan radiyo da talabijin ba da nazama Malama nima irin Malama Mardiyya.

 

Fita tayi bayan ta babbamu komai, Malam Auwal ya tsaya akan mu yana muzurai, Ni walle gemun sa irin na bunsurun Gajiyalle shi yake ban daria. Na sheke da dariya ina tafa hannaye,

 

 “Ke Wai baki da hankali ne?”

 

 “Walle dariya kake ban Malam.”

 

 “Okay ga mahaukaci yana magana ko.?”

 

 “Aa walle ba haka bane..”

 

Na fada ina gimtse dariya ta. Dogon tsaki yaja,

 

 “Ballagaza kawai..”

 

Rubutu yayi a allo, Ya juyo yana kallon mu.

 

 “Kafin mu fara komai, Zan dinga kiran sunayen ku a rajista shima, Wanda yazo ya amsa da ‘Labbaika Ya Sayyadi..’ Ba kamar na boko da zaku amsa da present sir ba ko sir. Kunaji? Fahimtun?”

 

Muka daga kai muna tafa hannuwa, Cikin nutsuwa ya fara koya mana karatun arabi. Walle da dadi, Sai na samu kai na cikin nutsuwa, Haka ya gama koya mana ya fita, Malama Mardiyya ta shigo, Ta fara koya mana nata bangaren. Ta bamu biskin da ruwan ledar fiya wata.

 

Ta kokkoya mana yadda zamuyi alwala da sallah. Ta k’ark’are mana da,

 

“Sai bayani na gaba akan”

 

1-Jinin Haila.

2-Jinin Nifasi.

3-Jinin Istihadha.

      

“Ku saurare ni da kyau, Domin duk kankantar mace wataran uwa ce. Yauwa Jinin Haila: Sassan da bayani zai gudana akai sune: A-Ma’anar Haila.B-Alamomin Jinin Haila.C-Muddan kwanukan Haila.D-Shekarun Haila.E- (karancin kwanukan tsarki.F-Rabe-raben Haila.G-Abubuwan da suka Haramta ko karhanta ga mai Haila da kuma ababen da suke mustahabbi gareta.H-Yadda ake wankan Haila.I-Hukunce-hukuncen Haila,

 

          “A-Ma’anar Haila:Jinin Haila shine jini wanda yake fita daga mahaifar mace kowane wata na wasu kwanuka. (B-Alamomin jinin Haila:Jinin Haila ja ne wani lokaci yakan sauya zuwa bakii ko ya yi jajur,kuma yana da tunkuza wajen fitowa da kuma zafi,

          “C-Muddan kwanukan Haila:Mafi karancin kwanukan Haila kwana ukku/biyu ne saboda haka idan ya kasance kasa da kwanaki ukku/biyu ne to ba Haila bane, Amma ance akwai mai zuwa rana d’aya tal. haka nan wadannan kwanaki ukku dole su kasance biye da juna,mafi yawan kwanukan Haila kwana goma ne.

          “D-Shekarun Haila:Jinin Haila yana farawa ne da cikar ‘ya mace shekara tara saboda haka duk jinin da yarinya karama za ta gani ya fito mata kafin ta cika shekaru tara,to ba Haila ba ne,ko da kuwa yana da siffofi hailar.Haka nan jinin da mace ta gani bayan shekarun daina Haila –Shekarun daina Haila shekaru sittin ne ga wadda take Bakuraishiya,in kuma wadda ba ita ba bane daga sauran kabilu shekaru hamsin ne – Wato dai shekarun soma Haila shine shekara tara,abinda ake nufi da shekara tara anan shine lokacin da yarinya ta cika shekara tara cif-cif wato ba mujarradin shigar ta shekara tara ba a’a sai ta cika shekara tara din cif-cif,haka nan ita ma wadda ta kai shekarun daina Hailar sai ta cika shekaru hamsin cif-cif ba mujarradin shigar ta shekaru hamsin ba.

          “E-k’arancin kwanukan tsarki:Mafi karancin kwanuka tsarki wato tsakanin wannan Haila da wannan Haila kwanaki goma ne,saboda haka zai iya yiwuwa mace ta iya yin jinin Haila sau biyu a wata amma fa da sharadin a samu tazaran kwana goma tsakanin Haila ta farko da kuma Haila ta biyu.Amma mafi yawan kwanukan tsarki to shi bai da iyaka wato a ce kwana kaza ne.

          “F-Rabe-raben Haila:Mai Haila imma ta kasance wadda take ma’abuciyar al’ada ko kuma wadda take ba ma’abuciyar al’ada ba,wadda take ma’abuciyar al’ada itace wadda ta maimaita Haila sau biyu kuma biye da juna haka nan kuma ya kasance an samu dacewa a lokacin da kuma adadin kwanakin,ko kuma ya kasance a samu dacewa a cikin lokutan ka kai ko kuma a adadin kwanakin ka kai,to da wannan ne mace za ta zama ma’abuciyar al’ada mai lokaci tsayayye ko ma’abuciyar al’ada mai adadi tsayayye ko kuma ma’abuciyar al’adi mai lokaci da kuma adadi tsayayye.Ita kuma wadda take ba ma’abuciyar al’ada ba ta kasu zuwa kashi ukku wato imma ta kasance yanzu ta fara wato ba ta taba ganin hailar ba ko sauya kaya,ko kuma ta zamo wadda al’adarta ba tsayayya ba wato tana rawa,ko kuma ta zamo ta manta al’adarta,ita ma wannan wato wadda ta manta al’adarta ta kasu gida ukku ko dai ya kasance ta manta lokacin Hailar ta ko kuma ta manta adadin kwanakin Hailar ta ko kuma da adadin kwanakin da kuma lokacin duk ta manta.To duka bayanai sanka-sanka na wadannan rabe-raben Haila ana iya komawa ga littafan Fiqhu misali littafin Zubda ko Tahrirul wasila na Imam Khumaini.

          “G-Abubuwan da suka haramta da kuma karhanta ga mai Haila:Daga cikin ababen da suka haramta a gareta akwai yin Sallah,Azumi, [dawafi,Iitikafi da kuma dukkan ababen da suka haramta ga mai janaba kamar taba sunan Allah da na Annabawa da kuma Aimma na Ahlul bayt ko kuma zama cikin masallaci.Haka nan haramun ne ga mijinta saduwa da ita.Wasu kuma daga cikin abubuwan da suke aikata su makruhi ne gareta akwai karatun Alkur’ani mai girma ma’ana daukar Alkur’ani Hizb sittin, Anan zan dakata sai zuwa zama na gaba idan Allah ya kai mu gobe. “

 

“Wallahi haka kawai na samu kai na da son acigaba da karatun nan, Domin tun ba yau ba. Yalwajin Innarajo na gayamin tafara jini. Billahil lazi na dauka jinin yankewa ne wai ahe sunan sa jinin al’ada. Hi’iyasa Uwande tace Innar ta tace data fara jini ta gaya mata? “Na kada kai ina jijjiga kafata.

 

“Akwai masu tambaya? Wanda bai gane komai ba ya tambaye ni kunga dai yan maza sun fita.”

 

Duk mu kai shiru, Malama Mardiyya ta sake cewa,

 

 “Toh Allah ya kai mu acikin satin nan ni zan fara muku tambayoyi. kwa iya tafiya, Shikenan an tashi.”

 

 

__

_Asubah ta gari masoyan Dije, Ku shirya tsaf Dijangalar ku fa an kusa wayewa, Kada ku manta har yanzu muna kan shimfidar book dinne ne. Ko kun manta da yadda yazo muku a dandano😉? Na gayshe da yan comment box 1, Gaisuwar ku ga dije na zuwa kunne na, Ana gayamin sosai, Na kusa wantsalowa nima cikin box din a dama dani, Amma kafin sannan Nabila shehu, Maryam Saminu suleiman, (Islaha/Rip maryam) , Daughter billy, Da sauran wanda ban anbata ba. 🤲🏻Dije na godia kwarai😘🥰❤️  Na gaishe ku, Gaisuwa mai kima tare da fatan alkhairi ga masoyan Dijengala dama zafafa books gaba d’aya.. OneLove😘❤️_

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 13

Advertisement                   _13//KASBTSTW_     *BRITISH ENG LEARNING CENTRE*   Idanuwa na shiga zarewa a lokacin da…

KIBIYAR AJALI 31-32

Advertisement  _*KIBIYAR AJALI…..!!!!*_ _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_            🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA…