KIBIYAR AJALI 9

Advertisement

 

    *9*

 

*WASHE-GARI:*

 

      *Ko da* na tashi daga bacci na fito tsakar gida, Buta na dauka na dibi ruwa na shiga bandaki. Ina fitowa nayi alwala yadda zan iya naje na bubbuga sallah ta wacce ban san iya adadin raka’o’in da nayi ba, na fito na bar gidan, daman tun jiya da uniform dina na yini kuma na kwana dashi, hakan yasa ina karbo sadakar koko na nayi makaranta hankali kwance.

 

Yau kam ban kwanta ba wajan bishiyoyin dake cikin makarantar na nufa, na kad’o mangwaro na zauna nasha abata babu ko wankewa amman ban damu ba. Har aka fara zuwa sannan na koma cikin yan ajin mu. Malama Mardiyya na zuwa ni ta fara nema, aikuwa ta ganni kamar yar jakuna, ba zaka taba cewa sabbabin uniform bane a jiki na duba da yadda suka ci uwar dauda. Ta kalle ni bayan ta rike habar ta tana cewa.

Advertisements

 

“Yanzu Khadija kayan makarantar ne kika mai da su haka? Amman dai baki cire su ba tunda kika saka su ko?”

 

“Wallahi malama ban cire ba, yo ji nayi anata yabo ana fadin nayi kyau hi yasa naki cewa sai nan da sati biyu.”

 

“Innalillahi wa’ina ilaihir rajiun, Khadija ban san ranar da zaki nutsu ba wallahi. Mu je zan gan ki.”

 

Jiki na na rawa na bi bayanta, Bata yi min magana ba har muka karasa gidajen malamai mata dake unguwar yangayu wato yankin mai gari. Dakin ta muka shiga, Sai tashin k’amshi yake kasan cewar an basu guraran zama, amman duk da ita bata zama saboda tana da aure kuma mijin ta be yarda ta dinga kwana ba, Yasa ta gyara shi saboda ta dinga hutawa kafin ta tafi can. Wata leda ta dakko min ta bani.

 

“Kaya ne. Karki bu’de sai kinje gidah. Yanzu dai ga sabulu da soso zakiyi wanka. Kafin nan zan wanke miki kai yau.”

 

“Kai! Yauma wankan zan yi?…. Malama kiyi hak’uri. Yasin sauri nake zanje wajen Habi. Nagode Allah ya biya ki.”

Advertisements

 

“Zaki zauna ko sai na dake ki tukun na?”

 

Zama nayi, Ina raba idanuwa. Malama tafita ta dora ruwa a risho irin na gidan su Nafisan kansila. Yayi zafi ta kira ni ta wanke min kai na sau ba adadi. Tun yana fitar da wasu abubuwa har ya dena ya dawo farin kumfa. Ta bani sabulu da soso tace na yo wanka a bandaki, Hohoho bandaki sekace dakin matar sarki, Ya hya siminti, Na dirje jikina Sau bakwai kamar yadda ta taba yi min. Kana ta miko min burishi irin na Mudikalle da Makilis nan ma tace na wanke baki na sau uku.

 

Inayi tana matsamin wani har na gama. Walle sai naji kamar ba ni ba. Anya kuwa ni ce? Iska kuwa kota ina ratsa ni take gwanin hya’awa. Ta min kitso guda shida ta shafamin man kai. Tabani sabuwar riga doguwa da takauni ta fesamin turare. Bansan sanda hawaye suka fara zubo min ba.

 

 “Malama! Nagode, Allah ya sa miki da alkhairi. Harda takauni, Kaya kawa na amaryar birni? Dama ke kika haife ni, Nagode kwarai malama.”

 

Malama Mardiyya ta jijjiga kai tana murmushi,

 

 “Meye kuma takauni Khadija?”

 

 “Takauni na k’afa da ake sawa..”

 

 “Au takalmi..? Hahahaha! Takalmi ake cewa. Kidena gode min kinji ko? Allah ya bani ikon cigaba da temaka miki kinji Khadija. Allah ya baki miji nagari Aamin.”

 

 “Aamin Malama.”

 

Hinkafa da qundun kaza (shinkafa da wake a kauye) ta zuba min, Yasha mayi na k’uli da yaji. Naci nai dam na gyatse. Ta sake koyamin alwala nayo nayi sallah. Raina fyes. Jikina sai tashin K’amshi yake. Na jima a gidan malama kafin na tafi gidan mu. Tamin gargadin kar na soma bawa Gajiyalle komai rintsi nace mata Malama zata gayawa mai gari inde ta k’wace. Hakan kuwa akai ina komawa gida na boye a akurkin kajin daya lalace na daki na. Raina fyes na kwanta bacci ya kwahe ni.

 

Saboda tsabar iskar da take ratsani yasa baccin nawa ya yi dadi harda mafarkai masu ban sha’awa. Ana ta kiraye-kirayen sallar karfe d’aya na farka ina sakin hamma. Na fito tsakar gida ina kalle-kalle na hango Mudi yana cin kwadon zogale. Zuwa nayi na dauki buta ya yin da ya bini da kallo gani na cikin doguwar riga da be sani a ciki ba, gashi dama babu dankwali da kan nawa garin bacci ne ya zame ni kuma saboda nishad’i yasa naki tsayawa na daura, na wuce ina zuba kamshin turaren da malama ta fesa min dan har lokacin be fita ba. Duk da cewa ya gama ci amman sai yaki tashi daga gurin har sai da na fito a lokacin ne Gajiyalle ta fito daga cikin dakin ta kawai ta bini da ido tana hura hanci.

 

“Daman dan bantan ubanki kina cikin gidan nan ban sani ba, har waccan munafukar malamar taku ta aiko wai kije makaranta tana jiranki nace kin fita yawan shaidancinki? Uhmmm zoki gaya min wane dan iskan ne ya bataki harda baki kayan sawa.”

 

Na ajiye butar tare da cuno baki ina kifta idanuwa kamar me shirin yin kuka, sannan ta kuma rike kugu tana girgiza jiki tace.

 

“Ahh! Har da su kitso Dije? Ehhh lallai abin naki ya shahara, zaki bude baki ki gaya min ko sai na ragarkajeki sannan?”

 

“Toh ba malama Mardiyya ta bani ba, kuma ta wanke min kai na tasa min turare tace kullum a haka take son ta ganni ina wanka.”

 

Na karasa fada ina sosa ido na guda daya. Gajiyalle ta dinga tafa hannaye tana sallallami tace.

 

“Na shiga uku karfa matar nan ta jefaki hanyar halaka azo ana cewa bana kula dake. Aikuwa bari malam yazo sai na gaya mihi dan ba zai yiwu kizo ki janyo mana abin kunya ba la’ananniya kawai mai bakar aniya.”

 

“Haba Gaji, kina ganin yarinya tayi kyau amman ki dinga aibata ta haka, shegiya Dije ahe dai kina da hegen kyau, aradu baki ganki ba kamar wata Fati Muhammed (Muhammad).”

 

Harara Gajiyalle ta watsawa Mudukalle da yake ta sakin murmushi wanda shi kadai yasan ko na menene yake yi. Ni dai ban yi magana ba na koma cikin inda nake na dauki dankwalin na daura tare da dakko mayafi na wanda ko daga nesa ka hango shi a kuguna kasan cewa ni ce na doso. Naje zan fita daga gidan Mudi ya biyo ni a baya da sauri ya tsare kofar fita yana cewa.

 

“Yar gari, ki gaya min gaskiyar wanda yake baki wadannan abubuwan, na yi miki alkawarin zan dora daga inda ya tsaya.”

 

Cikin rashin fahimtar inda maganar sa ta nufa nace dashi.

 

“Wane abubuwa nake samowa?”

 

“Shegiya karki rai na min hankali ma, wane saurayin kikai yake tabe ki yana baki kudi gashi har kin fara sanya kayan yan birni?”

 

“Cab! Bafa namiji ne ya bani ba, malamar mu ce ta yi min duk wannan abin, kuma bari kaji na gaya maka harda wasu kayan ma suna daki na ajiye su, bazan saka ba sai da sallah.”

 

Mudukalle ya kuma dashare baki tare da kallo na yana kanna ido, muryar Baffa ita ce san Mudi saurin matsawa daga kusa dani. Nayi saurin zuwa gurin Baffan ina juyawa tare da ware hannuwa alamar ya ganni da kyau. Ya rike baki yana kuma bina da kallon mamaki, ina ta dariya dan nasan zai ji dadin gani na a cikin wannan yanayin.

 

“Ummina kece haka?”

 

“Ni ce nan Baffa, ya ka ganni?”

 

“Kamar Ummina a cikin radio ko talabijin.”

 

“Hahahah Baffa har na zama ta cikin radio?”

 

“Eh mana Ummina, nan gaba kadan idan kika dage da karatu zaki ganki a ciki. Wane dan albarkan ne ya baki kayan nan Ummina?”

 

Na kamo hannunsa nasa a kai na kafin na zare dankwalin nan kitso na ya bayyana na kara da cewa.

 

“Baffa malamar mu ce ta gyara min kuma tayi min kitson, ya yi kyau ko Baffa na?”

 

“Allahu Akubar, ubangiji ya saka mata da alkairi, na gode mata sosai….”

 

Sai kawai naga yana goge hawaye da alama mahaifiyata ya tuna, yasan da rana nan kamar haka zai dinga gani na cikin tsabta da kwalliya. Mutuwa mai raba da da uwa, ta raba miji da mata a duk lokacin da Allah ya tsara mata.

 

“Yanzu ina zaki je.?”

 

“Baffa zanje nemo abin da zanci.”

 

“Ikon Allah, ba tayi girki bane Gajin?”

 

“Baffa kasan fa Gajiyalle ba bani take yi ba, dama idan nayi mata talla ne take bani da dadin rai. Amman yanzu tunda na dena ta dena bani ka sani dai Baffa.”

 

Yaja numfashi tare da zura hannu cikin aljihu ya zaro kudin, naira saba’in ne ya miko min hamsin yace naje na siyo alala gwangwani uku. Na karba duk da nasan su kadai ne dashi hakan besa na bar mishi ashirin din nan ba sai da na karbe na hada sannan na fita ina murna. A hanyata ta zuwa ne naga ashe ba’a tashi daga makaranta ba, ni tunda malama Mardiyya ta bani kaya tace naje na boye ban koma ba, dan haka sai na tura kudi na cikin dankwali sannan na ciro mayafi na daga kuguna sai na yafa na shiga cikin ajin mu.

 

Murna ta kamani ganin malama Mardiyya ce a ciki, naje gurin ta da sauri ina washe baki wai ni naga uwa ta. ‘Eh’ mana uwa tunda itace take share min kuka na.

 

“Ke kuwa Khadija ina kika shiga daga cewa ki kai kaya gida shikenan bake ba labarin ki, kuma har Aminu na aika gidan ku aka ce bakya nan.”

 

“Walle malama mantawa nayi har zan dawo makaranta. Ina zuwa gida bacci nayi he yanzu zanje siyan alala kawai naji ana ta karatu hi ne na higo nace bari a gama dani.”

 

“Lallai kin kyauta tunda har kinyi tunanin zuwa a karasa karatu dake. Toh yau idan an tashi kin koma gida ki samu ruwa ki wanke kayan makarantarki kinji ko?”

 

Kada kai nayi tare da zuwa na zauna, ta ci gaba da tambayar matan da suka fara al’ada a cikin mu, wadan su suka tashi ta tambayi yadda suka yi lokacin da suka ganshi, Bara’atu tace ta gayawa Innar su tace ta dena sallah kuma yau kimanin wata biyu kenan bata sallah, ma’ana ta zarce da rashin yin sallah tun da Innar ta ba ta yi mata bayinin cewar har sai ya dauke ba. Malama Mardiyya ta dafe kanta ta kasa dagowa tsawon lokaci.

 

“Yanzu Bara’atu tsawon wattani biyu bakya sallah?”

 

“Eh wallahi malama.”

 

“Toh naji, daga yau duk wacce ta kuma ganin jinin al’ada toh kar tayi sallah har sai lokacin da taga jinin ya dauke. Sannan sai tayi wanka, ba wai wanka na sabulu da soso ba a’a na tsarki. Wankan haila, da na janaba da na biki da sauransu duk daya ne, babu wani bambanci sai a niyya. Ga yadda siffar wankan janaba nan take kamar yadda ya zo a hadisin Ummuna Aisha (r.a): An karbo hadisi daga Aisha (r.a) ta ce: ((Manzon Allah (ﷺ) ya kasance idan zai yi wanka na janaba, yana farawa da wanke hannayensa, sannan sai ya zuba ruwa da damansa a bisa hagunsa, sai ya wanke farjinsa, sannan ya yi alwala. Sannan ya kama ruwa sai ya shigar da yatsunsa a cikin asalin gashin kanshi, sai ya zuba ruwa a kanshi sau uku, sai ya game jikinsa da ruwa, sannan ya wanke kafafunshi)). Bukhary da Muslim, lafazin Muslim ne.

 

“A takaici wannan hadisin na ko yarda mu yadda ake yin wankan tsarki ne, imma (janaba, haila, biki, Wankan Juma’a da sauransu). Yara idan kun tashi za ku fara ne da wanke hannayen, sannan ku yi tsarki da hannun hagu tare da wanke duk inda najasa ta ta6a, sannan sai ku yi alwala kamar yadda aka saba yi idan za a yi sallah, sannan sai ku wanke gashin kanku tare da cuccudawa, ku sanya yatsunku har zuwa kasan gashin sau uku, sannan sai ku game jikinki da ruwa. Babbar manufar dai shi ne ya kasance ruwa ya isa kowani lungu da sako na jiki, don haka duk inda aka ga ruwa be isa ba, sai a isar da shi. Kun fahimta?”

 

Nayi saurin cewa.

 

“Eh to, wani gurin dai sai an sake gaya mana.”

 

“Toh shikenan duk wacce ta fara ko take yi tazo ta same ni ta gaya min kunji?”

 

Duk muka hada baki wajan cewa.

 

“Eh…!”

 

Daga nan ta ci gaba da sanar damu yadda zamu dinga tsabtace jikin mu har aka tashi gabaki d’aya. Muna cikin fitowa daga aji ni da su Siyama muka hadu da malam Auwal na bishi da kallon sama da kasa, yasha kananun kaya farar t-shirt da dogon wanda jah ya yi kyau sai dai ji nake na fishi hakan yasa na kuma gyara mayafi na.

 

“Zonan Khadija.” Ya kira ni.

 

“Gani malam, amman kayi sauri saboda wallahi yunwa nake ji.”

 

“Haka dai. Daga ina kike ci ina zaki ci.”

 

Yai maganar yana jajjan gemunsa.

 

“Yooo ai lafiya ce ta iheni ba dan haka ba ai bazan ci ba, kai ma malam wallahi da zaka dinga rage ciki kana cin abinci da he kafi haka kauri.” Sai ya share maganar ta hanyar cewa.

 

“Ina uniform dinki?”

 

“Suna gida malama tace sai na wanke zan saka.”

 

“Toh karki sake zuwa mana da kayan kida.”

 

Na yatsina fuska alamun banji ba bazan dena ba, shi sai kace makarantar shi duk yabi ya takurawa yan makarantar kowa tsoransa take ji. Na turo baki ina zaro kudi na daga inda na boye ina cewa.

 

“Malam in rafi?”

 

“A’a zo muje wajan mashin dina zan baki abu.”

 

Ya yi gaba ba tare da ya saurare ni ba, na harari bayan nasa ina bin shi.

 

Bude mashin din ya yi ya dakko wata bakar leda a kulle ya miko min tare da cewa.

 

“Idan kinje gida kici.”

 

Tunda ya ambaci naci nasan cewa kyautar tawa ce.

 

“Malam na gode Allah ya himaka albarka.”

 

Ya yi murmushi banji ya amsa a fili ba amman ina tunanin ya amsa a cikin ransa. Ai banma bari naje gida ba, kawai na samu guri na bude ledar, naci karo da gassashiyar kaza. Wayyo Allah an jima ba’a hadu ba, na gyara zama na tare da janyo ledar na shiga ci hankali kwance, abin da ya bani mamaki shine da naji ina son ragewa Baffa koda kuwa zan iya cinyewa, naji na rage na kulle na tafi ina tsallen dadi tare da yiwa malam Auwal addu’a….

 

.

______________________

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA’ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

 

To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.

 

        Ina ma’abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

 

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

 

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana’arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

 

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 29

Advertisement   *29….*      _*KIBIYAR AJALI…..!_* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_                  🏹🥰😍   Advertisements…