MIJIN AMMINA NE SILA 23-24

Advertisement

 ✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

written by noor Eemaan

wattpad@NoorEemaan

page 23-24

daidai ta saitin aaban ta wuce saidai sam bai lura ba domin hankalinsa naga wayarsa sai data yi gaba sannan ya juyo asakamakon wani kamshi daya bugesa gashi yanayin bugun zuciyarsa ya sanja amma ko gefen fuskarta bai gani ba domin ita ma kanta na kasa ne….

Advertisements

bayan ya gano inda hanan take, suka yi hirarsu da bai wuce minti goma ba wanda yawanci hirar hanan ke yinsa kana ya mike dan tafiya sai lokaci hanan ta marairaice tace “ya aaban please kabari bestie na tazo ku gaisa tare muke”

“a’a hanan i have to go zan yi missing jirgi”  ya fada bayan ya bata wani kyakyawan jaka da alama shopping yayi mata babu yanda ta iya, hugging dinshi tayi kana suna ki sallama cikin kaunar juna, zama tayi tana sauraren zuwan  abrar….

cikin sauri abrar ta taho domin tasan hanan na jiranta, kamar yanda suka wuce juna dazu haka ma wanna karon, sai dai saurin da abrar kiyi yasa ta dan bugesa batare da tasani ba, cak ta tsaya yayinda zuciyarta ya bada ras! manyan idonta ta zaro batare da tajuyo ba tace

 “am sorry please”

aaban shima kasa motsi yayi datayi magana jiyayi kamar yasan wanna muryan “amma a ina?” ya tambayi kansa juyowa yayi yaga har tayi nisa still bai ga  face dinta ba, kafada ya daga irin i dont care dinan  ya fita…

tun daga nesa hanan ke zabga mata harara domin taso kwarai su gaisa da aaban, kunshe dariyarta abrar keyi tace “afuwan bestie hanan”

bata rai hanan tayi tace “ba wani nan gashi kin ja ya tafi baku gaisa”

“ba komai ai zamu gaisa wata rana tun da ana tare” da haka ta lallaba hanan…

Advertisements

haka rayuwa ta cigaba da juya musu da dadi da akasin haka domin matukar ciwon hanan ya tashi tofah basu da sauran kwanciyar hankali, bangaren mummy kuwa alhaji abdur-rauf ya kan zo yayi kwana biyu ya koma, hakan yasa bata yi masa maganar ba amma tasa aranta matukar yazo hutu mai tsayi zata tuntube shi da maganar auren aaban din  kasancewar harkokin kasuwancinsa sun fi yawa a kuwait.

“BAYAN SHEKARU UKU”

wanda yayi daidai da gama karatun su abrar acikin wadannan shekaru abubuwa da dama sun faru ciki har da zuwan hanan sau biyu nigeria, yayinda abrar taki zuwa domin tsoron abinda alhaji shettima zai mata, hanan tayi tayi da ita tabi ta zuwa gidansu taki yanzu dasuke dab da komawa nigeria ciwonta yafi tashi akai akai domin firgice da take kasancewa aciki kullum.

ayau zasu yi taron yaye dalibai, duk wani  dalibi daka gani fuskarsa dauke da farinciki amma, banda abrar dake cikin fargaba hadi da matsananci tsoro…

wurin taron yayi matukar haduwa ga iyaye, malamai hadi dalibai ta ko ina, hanan bakinta yaki rufuwa adalilin ganin daddyn ta cikin iyaye azaune domin bata yi tsamanin zai samu zuwa ba, taron yahadu domin suna gabatar da komai cikin ilimine da sanin ya kamata daga karshe aka kira wanda ya zo na daya a gaba dayan makarantar domin a bashi kyautar karamawarsa, wanda ya kasance dan asalin cyprus din ne, tabass da abrar bata cikin halin damuwa da ita ce zata zo ta daya saboda kwazonta domin har malamai na yabonta, fitowa saurayi yayi cikin murna yayinda iyayensa suka fito aka basu gift din suka yi hoto gwanin burgewa, sai mai gabatar ya kara cewa wacce tazo ta biyu itace “ABRAR SAJEED”….

jitayi kanta ya dau wani dummm domin bata yi tunanin tayi wani abun arziki  da har zata zo ta biyu ba, sai lokacin naga kyawun da abrar ta kara da girma kirarta ta  cola cola ya kara fitowa, brown skin dinta yasake kyau da kyalli ataikace komai nata ya sanja, yanayin jikinta na tafiya da ne da shekarunta, kasanewar yanzu ta shiga shekaru sha tara a aduniya.

 asanyaye take tafiya domin har zuciyarta bata ji dadin rashin ganin ammi ba, take mutuwar abbinta ya dawo mata sabo hawaye sun ciko idanunta amma bata basu daman zuba ba, tafi ne ke tashi raf raf ta ko ina a wajen domin nutsuwar ya burge mutane da dama domin kallo daya zaka mata kasan cewa ita din mai nutsuwa ce, cikin sauri hanan ta turawa daddyn ta text msg tace

“daddy please ka taya kawata ansar kyautarta iyayenta basu zo dan Allah”

daddy najin shigowar sako ya duba kana ya kalli hanan dake nesa dashi, jinjina masa kai tayi alamun tabattarwa ba musu ya mike ya nufi wajen,… abrar na shirin sa hannu ta karbi gift taga hannu daddy shima, murmushi kawai tasakar masa domin ta gane shi saboda hanan ta nuna mata shi dazu bayan an musu hoto, suka koma wajen zamansu sai  aka kira hanan amatsayin ta uku still daddy ne yasake mikewa domin karban na hanan sai mutane suka yi tunanin su duka biyun  yayyan sa ne…

bayan taro ya tashi abrar tayi wa daddy godiya sosai “kada ki damu kema yata ce” daddy ta bata amsar hakan, daddy bai jima ba ya koma kuwait…

 bayan sati daya su abrar suka  fara shirin komawa nigeria yayinda fargabanta na kara daduwa, hanan ce mai tausarta washegari suka yi sallama da cyprus hadi da linda da itama zata koma a ranar har mutsanyar number sukayi da hanan kana suka nufi filin jirgi…

basu jima a filin jirgin ba suka lula sararin samaniya bayan wasu awannin suka  dira a nigeria, tausarta hanan tasake yi  hadi da kwantar mata da hankali takuma yi mata alkawarin zuwa gidan washegari domin tayi magana da ammi kila ta fahimta wanna karon, da wanna  hankalinta ya dan kwanta sallama suka yi,  taxi abrar ta shiga ta bar airport din….

 bayan an zo kofar gidan nasu tasauka hadi da biyan driver hakkinsa, trolley dinta ta rike yayinda take bin gidan da kallo, gidan na nan yanda yake saidai an kara kawata shi fiye da na baya, ajiyar zuciya mai dauke da abubuwa da dama ta saki kana ta turo dan karamin gate ta shige, mai gadi na ganinta ya mike domin karban trolley dinta, ta hanashi hadi da yi masa godiya ta nufi cikin gidan, tana  daf da zuwa kofar da zai sadata da falo taga alhaji ya fito… 

dam! dam!! gabanta ya fadi har wani sama da kasa kirjinta yake, alhaji shettima kuwa baki ya saki yana kallon abrar kamar wani sauna, ganin irin girma, kyau, da cikar halittan data kara  jiyayi wata muguwar sha’awarta daya tara ta karu fiye da  tunanin mai tunanin, yayinda fuskarsa ke cike da annushuwa, gefe da gefensa ya kalla kana ya tari  gabanta yana cewa “abrar daddy’s girl, my sweet baby kin ga girman da kika kara kuwa? ya kamata ki more rayuwarki ki bani dama na cigaba daka inda na tsaya ni kuma na miki alkawarin baki k ababben more rayuwar ko meye shi kuwa, domin ni mai iya baki kudi ne daga naira dubu daya-daya har million dari, matukar kin amince kada ki damu da ammin ki bazata sani ba…”

jitayi kanta ya fara juyawa, kamar zata bashi amsa sai kuma tayi gaba, tana shirin bude kofar ta shiga taji yace ” yau dole in kwashi garabasa, yau zan more jikinki, ki shirya ina zuwa gareki zumana”… ya fada cikin dariya kana ya hau motarsa ya bar gidan…

cak abrar ta tsaya tana bi motar da kallo yayinda gabanta ya yawaita faduwa daidaita fuskarta tayi kana ta bude kofar ta shige… ammi dake bakin kofar tun dazu tabar wajen domin ta dade tana kallon alhaji shettima dake wa abrar magana sai dai batajin abunda yake cewa daman bata ji tashin motarsa ba yasa ta leka…

cikin zazzakar muryanta tayi sallama kana ta zauna kusa da ammi  dake zaune asanyaye tace, “nayi kewarki ammi” abrar ta fada tana kallonta, “nima nayi kewarki diyata”  ammi ta fada tana shafa kanta.

“ammi bakizo wurin taron mu ba?” abrar ta tambaya tana kallon ta.

“nazo zuwa abrar naji jikina ba dadi amma na nemi number hanan kawarki awayata in miki bayani narasa” jinjina kai abrar tayi alamun gamsuwa…

“jeki kiyi wanka ki dawo na hada miki abunci “

“toh”  tace cikin jindadi domin taga ammi ta dan sauko daga fushin datake yi da ita, tana kuma fatan ammi ta dawo mata kamarda….

 bayan tayi shiga dakin taga shi tsaf tsaf dashi ta kuma san wanna aikin amminta ne, duk da tana fushi amma tana gyara mata daki “babu kamar uwa aduniya ta aiyana aranta”

bayan tayi wanka ta fito ta dan tsakuri abunci, sai ta dawo falon ta zauna kusa da kafar ammi dake zaune kan kujera, katon plasma falon ta kurawa ido, azahiri zaka dauka kallon take amma ina duniyar tunanin ta fada duk abunda  alhaji shettima ya fada mata sai dawowa brain dinta yake take kan ta ya hausuna sai ta shiga kyalkyale dariya sosai har da bubbuga kafa akasa, kallonta ammi tayi cikin mamaki sai kuma ta kalli tv taga ko abun dariya ake, sai taga akasin haka domin wani fim din yaki ake a mbc action kara dawo da kallonta tayi wajen abrar tace “abrar?” shiru ba amsa sai dariyarta daya cigiba da tashi, adan tsawace tace “abrar!!!!”  hadi da dan bubbuga kafadunta, dif dariyar ta dauke  sai kuma ta sa kuka sosai, cikin tsoro da mamaki ammi tace

 “abrar lafiyarki kalau kuwa? Gayamin meyake damunki?”

“cikin kuka tace “ammi sai na kashe shi idan ya sake taba mutuncina” ta fada tana dunkule hannunta…

“wake nan” ammi ta fada cikin rawar murya.

“Dariya da kuka ta saki lokaci tace  “MIJIN AMMINA”…

gaban ammi ne yafadi take abubuwan da abrar ta fada mata shekarun baya suka shiga dawo mata, amma sam bata son amincewa da hakan duk da zuciyarta na son gasgata hakan…

pillows din kan kujera ta shiga cille dasu kana ta cigaba da magana cikin fitar hayyaci da alama yau ciwon ya matso sosai “ammina sai na kashe shi, da hannuna zan maka shi akotu, kigaya wa shettima kada ya kara taba muntuncina”… ta kai karshe cikin kuka- kuka dariya-dariya…

Matsananci tsoro daya ninka na dazu ya dirar wa ammi,  “addu’a ta shiga tofah mata takai kusan minti ashirin kana tayi shiru alamun bacci ya dauke ta…

shiru ammi tayi gaba daya ta rasa tunanin daya dace tayi, take kuma ganin data yiwa alhaji shettima dazu da abrar dazata shigo ya dawo mata dafe kanta tayi tace “innalillahi wa innah ilaihi raju’un ” sake kallon abrar tayi sai ta dauketa ta mayar da ita dakinta kana ta fito asanyaye…

da misalin karfe goma abrar ta farka garau da ita, wanda ammi tazo dakin ganin ko ta farka yafi sau a kirga, toilet ta fada tayi wanka hadi da alwala, lotion ts shafa ta  murza deodorant a hammatan kana ta bude wardrobe dinta inners ta dauko farare kana ta shiga duba kayan dazata sa…

take idanunta suka kan kayan nan ta aaban ya sanya mata asibiti, cire shi tayi domin tana son rigar duk da cewa batasan ya aka yi tasamu rigar ba…

bayan ta sanya ta zura hijab, daidaita sahunta tayi ta fuskanci gabas ta shiga rama sallollinta, bayan ta iddar tayi addu’ointa musamman kan Allah ya ganar da ammi yakuma tsareta da sharrin alhaji shettima, kwanciya tayi kan sallaya babu jimawa taji shigowar ammi “kin tashi?”

“eh ammi” 

“ga tea kisha” ba musu ta karba ta shanye

“muji kici abinci ko” ammi ta fada.

“a’a ammi na koshi, bacci zan yi” jinjina kai ammi tayi alamun “toh” tana son yiwa abrar tambayoyi sai kuma fasa tabar wa gobe dasafe sai suyi maganar…

har ammi ta bude kofar  taji abrar tace “ammi sai da safe”

“Allah ya kaimu” ta fada tana barin dakin

da kallon tabi ammi, sai kuma ta mike ta shige toilet tayi brush domin ta riga ta saba da hakan idan zata yi bacci kan sallayan ta dawo ta kwanta babu jimawa wani bacci yasake daukarta.

sai karfe shadaya alhaji shettima yadawo gida, azaune ya tarar da ammi akan gado ta fada cikin wasi’wasi, sallama yayi kamar mutumin arziki ammi ta amsa, da murmushi afuskarsa ya karosa yace “hajiyata kiyi hakuri, na biya ta wajen wanna abokin kasuwancina ne alhaji sa’id shiyasa nayi dare”

murmushi ammi ta kakaro tace “bakomai alhaji”

“bari nayi wanka amma kafin nan bari na baki maganin warware gajiyen nan domin nasan yau diyata ta dawo kinyi dawainiyya da ita sosai yafada yanufi firgji ya dauko exotic hadi da glass cup

 

da kallon mamaki ammi ke binshi, ita fa kanta ya fara kullewa meyasa sai in abrar ta dawo daga cyprus yake bata maganin nan??? ta aiyana aranta…

“gashi hajiya sha ki kwanta ki huta”

“alhaji nifa banason maganin nan yawan bacci yake sani wallahi.

“ai shiyasa ban siyi irin wancen ba, wanna bashi da karfi da asuba zaki ma tashi kiyi sallah” ya zagba karya…

ammi bata kara cewa komai ba ta karbi maganin tazuba abaki, sai ta sa cup din lemon bakin ta, ganin hakan yasa alhaji shettima shigewa toilet cikin murna…

ammi na ganin shigarsa toilet ta dawo da maganin cikin glass cup din daman bata sha ba, yana harshenta yau sotake tagani idan bata sha maganin nan ba me zai faru? cikin locker ta bude ta dire cup din ahankali, to koma ta kwanta alhaji shettima bai jima ba ya fito yana  tsane ruwan jikinsa, jallabiya yasa ya fetsa body spray domin alhaji shettima badai son kamshi ba, lockern nan da ammi ta boye glass cup aciki ya nufa, gaban ammi ne ya bada dam! cikin sauri tace “alhaji mikake nema ne”?

dakatawa yayi daga bude locker’n yace “yar karamar wayata nan ta kasuwanci nan na ajiye ta” 

gabanta ne yasakewa faduwa tace “alhaji ai wayar nan tana falo domin nama so in kawoshi nan dakin na mantaba” ammi ta fada tana fatan kada ya bude…

“anya wayarta wa ce?” yafada cikin mamaki yana nufar falon

 

cikin sauri ammi ta bude locker’n ta nufi toilet, zubarwa tayi kana tayi flushing da ruwa da fito ta ajiye cup din kan saman locker’n

tana ajiyewa yana shigowa yace “anya ba wani abu kika gani ba hajiya? domin na duba ko ina afalon baya nan” ya fada yana bude lockern take kuwa ya fito da wayarsa

rufe ido ammi tayi tamkar mai bacci, tana ta sake sake aranta, fatan ta kada abunda abrar ke fada ya zama gaskiya…

“BAYAN AWA BIYU”

alhaji shettima ya kalli ammi yaga tana ta sharar bacci, murmushi yayi ya mike hadi da nufar dakin abrar,,, ammi da idonta biyu ta mike…

yana bude kofar kuwa yaga ta bude kwancen take kan sallaya har yanzu, sai dai sam ya manta  bai rufe da key ba saboda halin zumudin dayake ciki

cikin matsananci mamaki ammi dake biya dashi ta dafe bakinta tana kokarin rike kukan dake neman kufce mata…

cikin bacci taji ana yi mata yan abubuwa, afirgice ta farka ganin alhaji shettima yasa ta mike zumbur tana ja da baya yayinda hawaye suka wanke mata fuska cikin kuka tace”wallahi koda zan mutu yau bazaka sake cin galaba a kaina ba bakin azzulumi”

“hhhh my sweet baby, naki wasa ne  kinsan shekara nawa na dauka ina matse sha’awarki dake damuna? toh kisani yau kota halin kaka sai na kusance ki sai na sake  lasar zumarki”….

“karya kake mugu azzulumi”… tafada wani kukan na kufce mata,  nufarta yayi gadan -ganda yayinda ya zame wandonsa, hadi da danne abrar kan gado ya rufe mata baki da hannunsa, take Allah ya bata sa’a ta rarumo bed side lamp ta buga masa akai da karfi, wani uban kara ya sake hadi mirginawa ya fada kan gado cikin fitar hayyaci hanan ta duro a kan gado ta nufi kofa wanda yayi daidai da shigowar ammi… kallon kallo ammi da abrar suka yiwa juna yayinda yayinda hawaye ke zuba idanunsu, juyawa abrar tayi ta ga alhaji shettima na kokarin tashi wani mugun gudu tasa ta bar wajen…

cikin dauriya alhaji ya tashi domin ya cin mata, saboda bayaso ko kadan  asirinsa ya tonu, yana fitowa kuwa yaga ammi ajikin kofa tsaye  bata ko kifta idanu da alama suman tsaye tayi, jiyayi wani mugun faduwar gaba da bai taba riskan kanshi aciki ba ya saukar masa ga wani uban gumi daya fara tsatsafo masa cikin tashin hankali ya fara….

tana fitowa haraban gidan ta cigaba da gudu tana waiwaya baya domin har wani gizo yake mata yana biye da ita a baya ganin gate  a rufe tana kuma ganin kamar kafin ta bude ya cimmata, hakan yasa ta nufi lada dake gefen gate din, bata ko tunanin  komai burinta kawai ta tsira daga kaidin alhaji shettima, cikin sauri sauri ta fara haye kan ladan tana zuwa karshe taga nisan dake tsakanin saman inda take da kasa akwai nisa sosai, hawaye masu matukar zafi suka zubo mata kana ta rufe idanunta ta duro kasa…

tana dira a kasa tasaki wani mugun kara domin jitayi kafarta ya lankwashe ya bada wani sauti kas kas karass da alama karyewa tayi, still bata damu ba ta cigaba da gudu cikin fitar hayyaci,  gudu take awanna uban dare baka jin motsin komai sai haushin karnuka, duk da uban zugin da kafarta keyi amma sam bata damu, kwata kwata batasan inda take  jifa karfa ta ba…

a nutse yake driving yayinda ya kunna  kira’ar sheik abdulbasit yana bi cikin muryansa mai dadin amo,  baya ko tsoron daren domin inda sa  sabo ya saba da night duty shiyasa baya ko jin tsoron hanyar, ji yayi motar ta tsaya cak! lumshe gajiyayun idanunsa yayi kana ya budesu ahankali, shi dai yasan motar bata da matsalan komai domin last week ya fara hawanta, murza key yayi yaga motar bata tashi ba, kawai sai ya fito, bude motar yayi yadan yi tabe tabensa kana ya sauke karfe daya rike murfin yana kokarin rufe motar yaji an yi masa wata runguma da mugun karfi, jiyayi kirjinsa ya bada dam! wani yanayi na ratsa shi “ka… kataimake ni kada ya sake samun galaba akaina domin idan hakan ya faru zan mutu!!!”  tana gaman fadin hakan jikinta yasaki, ganin tana kokarin kaiwa kasa yasashi juyawa cikin zafin nama ya manna ta akirjinsa…..

(arayuwa wata  kaddarar  baya taba faruwa sai da wata kaddaran inma mai kyau ko akasin haka, toh hakan ke faruwa arayuwar abrar,  kudai cigaba da bina dan  jin yanda abun zai kasance, sannan yau nadan yi typing da yawa ku karanta rabi yau  ko bar rabi wa gobe😝 saboda ba lallai inyi posting ba).

kutayani share dan Allah da mazonsa

SHARE✔

COMMENT✔

VOTE✔

EDIT❌❌

NOOR ✍

https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like