MIJIN AMMINA NE SILA 29-30

Advertisement

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

(A heart touching story)
written by Noor Eemaan
page29-30
cikin madaukakin mamaki mummy tace “Aabaan Hanan kun san tane?” amma sam hankalinsu baya tare da ita musamman Aabaan daya ke jinshi cikin farinciki mara iyaka adalilin ganin Abrar, tabass baya ko tantama decent ce  tsaya agabansa, agabansa ma cikin gidansu, duk da ta kara girma akan da, amma ko yana magagin bacci baze taba manta fuskartaba, dama all this while itace? amma ya kasa gane ta…

kusan lokaci daya suka karasa gabanta shi da Hanan, beyi tunanin abunda ze faru ba, beyi tunanin cewa akan be dace ba, shi dai burinsa kawai yasa ta a kirjinsa ko ze ji saukin ciwon sonta hadi da radadin rasata dayayi abaya…
 cikin zafin nama ya manna ta a kirjinsa, yayinda ya lumshe ido  yana jin saukin radaddin sonta a kirjinsa, cikin muryansa dake son bayyana rauninsa yace 
“where have you been decent one? i so much miss you please stay with me ok?”
 Abrar kuwa shiru tayi ta lafe akirjinsa sai faman raba idanu kawai take, kukan Hanan ne yadawo dashi nutsuwarsa, tace
 “bestie Abrar daman kece? meyasamiki, yasake taba ki ne?  dan Allah ki gayamin Abrar”… Abrar kara shigar da kanta jikin Aaban take hadi da boye fuskarta, kukan hanan ne ya karu domin ta fahimci ciwon Abrar yafi na da tunda har ta kasa ganeta…
cikin mamaki su mummy ke bin Aaban da kallon domin basu taba tunanin cewa ze iya wanna rudewar akan mace ba, macen ma mara cikakken lafiya, cikin wani sabon rudewan mummy tace “ba magana nake muku ba, nace kun santa ne!!!” mum ta kara fada  a tsawace
sai lokacin Hanan tace “mummy Abrar ce fa, Abrar kawata damuka hadu a cyprus”
cikin sake daure kai mummy tace “ban gane ba, daman tana da tabin hankali ne?”
kuka Hanan tasa tace “mummy ba tabin hankali bane, my bestie is not insane matsananci damuwa hadi da firgici ne ya haddasa mata wanna halin datake ciki yanzu haka”…
mummy zata sake magana daddy yace “mummynsu duk ku zauna mu tattauna wanna maganar a nutse domin nima kaina ya daure, saboda ina mata kallon sani, kallon Aaban dake rugunme da Abrar har yanzu idanunsa alumshe daddy yayi,  murmushi  yayi dashi kadai yasan ma’anar yasa kana yace abokina zo ku zauna muyi magana”
sai lokacin yabude idanunsa dasuka sanja launin, yayinda yake jin zafin ciwonta, meyasa duk haduwarsu baya taba ganinta cikin yanayi mai kyau, yakuma fahimci wasu abubuwan daga maganganun Hanan, a hankali ya rabata da kirjinsa ya riko hannunta, saurin sake shigewa jikinsa tayi, be hanata ba, ya tafi da ita ahaka tana gefen kirjinsa kan kujera suka zauna yayinda ta shiga boye fuskarta tamkar me jin tsoron kada akamata. 
Hanan kasa hakuri tayi tace “yanzu bestie na baki gane ni ba, nice fa Hanan”
Aaban kallon Hanan yayi yana cike da mamakin yanda har Hanan ta santa har haka, Abrar kuwa tsura mata ido tayi kana ta fashe da dariya hadi da dukan Aabaan tana masa alaman ya kalli Hanan, cikin rashin jin dadi halin datake ciki ya kama hannun datake dukansa dashi ya matse cikin nasa hannun kana ya dora hannunsa kan lips dinsa alamun tayi shiru, kallonshi tayi sai kuma tayi shiru kamar wacce ta fahimci maganarsa…
gyaran murya daddy yayi yace ” Mummynsu idan na fahimce ki, wanna Abrar itace kikeso Abokina ya aura ko? shin baki taba haduwa da ita bane?”
cikin mamakin da be gama sakin mummy ba tace “daddynsu haka maganar take, domin Aaban ya shiga mayuwanci hali abaya akan son wata patient daya ce ya hadu da ita, saide yace mun ya ganta ahalin na  mara kyau domin an mata fyade ya sinceta, nikuma nace masa da raina dai bazan bari wacce bata tare da mutuncinta ta shigo cikin zuri’a ta ba, na kuma ce masa kawar Hanan Abrar ze aura, domin na yaba da nutsuwarta duk da cewa ban taba haduwa da ita azahiri ba… Ajiyar zuciya ta saki kana ta cigaba da cewa; sai dai yanzu na kasa gane komai, domin naji Hanan tace kawarta ce Abrar, ga Aaban daya nuna shima yasanta,  gashi naji kaima kace kana mata kallon sani, daddynsu am totally confused na kasa gane komai”… 
jinjina kai daddy yayi yace “abokina zaka iya mana bayanin inda kasanta?” 
kallon Abrar yayi hadi da cewa “itace wacce na gaya wa mum inaso… nan ya sake bada labarin abunda ya faru adaren daya fara haduwa da Abrar din
“ikon Allah”  daddy yace yana girmama girman al’amarin, “idan na fahimce ku, wanna yarinyar kawar Hanan ce, wacce kikeso Abokina  ya aura, wanda baki san cewa itace dai shi abokin nawa ke baki labarin cewa ita yakeso ba,,,, nima kuma nasanta domin aranar dana je taron yaye dalibai dinsu a cyprus na hadu da ita, domin Hanan ta gabatar min da ita amatsayin kawarta, sedai ranar lafiya lau na ganta tsabanin yau, ko hanan zaki iya bamu labarin yadda akayi take wanna halin yanzu…
hawaye hanan tashare zata yi magana kenan mummy tayi saurin cewa “daddynsu wacce bayani zata yi kuma ? bayan ga abu afili, yarinya kawai taje ta zubar da mutuncin ta atiti za’a raina mana hankali, nafada zan sake maimaitawa bazan hada jini da mara kamun kai ba, sannan zata bar gidan domin bazan iya zama da ita ba, domin ada nazata mai nutsuwa ce, shiyasa na ce ita Aabaan ze aura idan kuma bata bar gidanan, toh ban yarda ko Hanan tace zata kula da ita ba, wanda yadauko ta ya cigaba da dawainiyya da ita domin idan tafara haukan ba iyawa zamuyi da ita ba” 
“kai mummy bafa mahaukaciya bace, sannan Abrar kamilalliya ce kaddara ce ta fada mata…
“ke dalla can rufemin baki, sakarya kawai”  mummy na gama fadin haka ta bar wajen fuuuu, yayinda amal da itama sai yanzu ta gane kan zancen tabi bayan mummy.
Abrar kuwa abun tausayi ta shige jikin Aabaan saboda fadan da mummy keyi, Aaban idanunsa na lumshe duk be ji dadin yanda mummy ta aibata decent one din shi ba, amma ba yanda ya iya uwa ce dolensa yayi hakuri.
daddy daya bi mummy da kallo ya girgiza kansa domin yasan halin matarsa kwarai, shiyasa be dakatar da ita ba. “Abokina ka kara hakuri,  mummynku zata sauko with time,   indai ta nine ina baka goyon bayan aurenta, Allah ya kuma bata lafiya” 
sai alokacin ya bude idanunsa yace “nagode dad” hadi da sakar masa murmushi, shima dad mayar masa yayi da martani kana ya mike ya nufi part dinsa…
kura wa Abrar madaidaitan sexy eyes dinsa yayi, take kuwa  idanunsa ya gano masa rigar daya  sanya mata asibiti, sai ya sake kallon hannunta yaga diamond ring din daya sanya mata a hannu, dafe kai  yayi cikin takaicin kansa na kasa ganeta da yayi tsayin wanna lokacin sai yau…
Hanan data kura musu ido tana kallonsu ta share hawaye, tabass ba yanda Allah baya ikonsa, ace tasan Abrar amma ashe  yayanta na faman nemanta, mikewa tayi ta nufi wajensu tace
 “ya Aaban kayi hakuri in sha Allah everthing will be alright, sannan wallahi ban taba sanin cewa ita kakeso ba da tuni nasada ku da ita, domin itace wanna kawar tawa a cyprus, ina maka murna  samun kamilan mace kamar Abrar, ina kuma goyon bayan ka aureta, domin ta cancanci farinciki arayuwa, she deserve it ya Aaban”… tana gama fadin haka ta ruga dakinta da gudu tana kukan tausayin Abrar…
da kallon Abrar tabi hanan yayinda ta kyakyalle da dariya, sai kuma ta mike zumbur ta dauko teddy data gani kan kujera ta rungume, sai kuma ta dauko remote dake  kan centre table ta rosa shi da tiles, sai tasa kuka hadi da dago teddynta ta kura masa ido tace 
“sai na kasheka, saina kashe ka shettima! tafada tana dukan teddy tamkar shettima ne agabanta, gaban Aaban ta dawo tace zaka bani wuka in kashe shi ko?”…
kwalla ne suka ciko masa idanu amma bayajin ze iya bari su zubo, gaban babban plasma taje ta shiga dukkan shi da dukkanin karfinta, tasowa yayi yakamo hannunta, tirjewa take tana nuna masa dinning table, fahimtar abunda take nufi yasa shi nufar wajen zaunar da ita yayi kana ya dauki plate hadi da serving spoon ya zuba mata jollof rice daya sha kayan lambu ya kuma wadatu da naman kaza spoon yasa mata, amma ko kallon cokalin ba ta yi ba, tasa hannunta biyu ta fara ci, ci  take sosai tamkar bata taba cin abunci ba, kallon so da burgewan yanda take cin abunci yake mata domin ko kadan beji  haushi hakan ba, tana gama ci yasiyaya mata juice a glass cup tana kai bakinta ta firzo shi gaba daya sai kan  farar rigarshi gaba daya ta bata rigar, sai ta kwabe fuska tana nuna masa ruwan faro shima zuba mata yayi awani glass cup ta kuwa shanye shi tas tana lashe baki hadi da sakin gyatsa, murmushi da be shirya ba ya tsubuce masa kana yasa tattausan hannunsa ya dauke shinkafan daya makale gefen cute lips dinta.
“Amal matukar ina raye babu wanda mad girl din babu yayanku, domin ina zan kai wanna abun kunyar?”
“mummy relax ki kwantar da hankali, nima ina bayanki wallahi,  tayaya ya Aabaan the hole classic guy ya kare da low class irinta, low class dinma mahaukaciya, na tsaneta ma ni mummy, na kuma san ya Aaban na matukar son ganin farincikin ki beze taba iya auranta ba tunda kin nuna bakya so”…
“daya fiye masa kuwa, domin matukar yayi kokarin auranta babu ni babu shi”… mummy tafada cikin matsananci bacin rai.
bangaren ammi kuwa har yanzu tana rufe adakinta, sai dai kullum alhaji shettima ya yi saurin tura mata abinci ya sake rufe dakin, tun tana gaya masa maganganu har ta dawo yi masa magiya akan ya bude mata taje neman yarta, amma ko kulata bayayi haka ze yi ficewarsa, ta rame sosai kullum bata da  tunanin sai na yarta Abrar, bangaren alhaji shettima kuwa har yanzu ya baza mutanen sa nema masa Abrar domin acewar sa be koshi da ita ba, a gurbataciyyar tunaninsa yace matukar ya ganta, guest house din shi  da ba kowa yasan dashi ba ze kaita, sannan ya cigaba da saduwa da ita har ta saba ta zama tashi domin kullum da matsananciyar sha’awarta yake kwana yake tashi…..
much love my beautiful people Alkhairin Allah ya kai muku duk inda kuke.❤
SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌
NOOR EEMAAN CE✍

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like