MIJIN AMMINA NE SILA 49-50

Advertisement

 

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

Written by NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER’S📚✍

page-49_50

a hankali ya mirgina sai ya zama na tana kasan sa yayinda yayi mata rumfa da faffadar kafadar sa, ido cikin ido yake duban ta haka itama …..tsawon mintuna 15 suka dauka ba tare da sun ko kyafta idon su ba. ita tayi karfin halin janye idanunta yayinda yanayinta ya canza lokaci guda…  mirginawa gefe yayi cikin Damuwa  yace 

Advertisements

“menene wiffy?”

“Ammina!” tace idanun ta na ciko da kwalla.

“ina take?” yace yana goge mata hawayen da ya fara sauka kan kyakyyawar fuskarta.

“Ta…tana gidan Shettima”

 “waye Shettima?” ya tambayeta.

Wani abu mai daci ta hadiya tace “Mijin Ammina”

dan zaro ido yayi yace “shine kike kiran sunan shi”?

Advertisements

murmushi mai ciwo tayi kana tace “a haka nayi masa adalci dana kira asalin sunanshi”…

cikin daurewan kai yace “decent one ban fahimci abinda kike nufi ba, i thought mijin ammi ne, he deserve some respect from you”….

kuka mai matukar ciwo ta fashe da shi jikinta har wani rawa yake, take hankalinsa ya tashi domin sam kwakwalwarta baya bukatar damuwa da duk wani tashin hankali, cikin lallashi ya dora ta a kirjin sa yace “it’s ok decent one, mu bar maganar nan yanzu, za mu yi ta wani lokacin”

luf tayi a kirjin sa tana sauke karfaffar ajiyar zuciya. “mu tafi gida dan Allah” yaji saukar muryar ta.

“zamu tafi cikin satin nan kinji” jinjina masa tayi tana kara zagaye shi da hannunta hadi da kara rungumar sa, domin haka kawai taji ya kwanta mata a rai, wanda bata san dalili ba, amma tana ji a jikin ta cewa shi din na daban ne…. bangaren Aaban kuwa ba haka yaso ba, yaso su dan kara kwanaki a garin shi da decent one din shi ko dan su kara samun fahimtar juna, amma tun da ta bukaci su tafi dolensa su tafi domin yafi bukatar farincikin ta fiye da komai……

*NIGERIA*

a hankali suke taka matattakalan benen jirgin, hannuwan su cikin na juna, sanye Abrar take da pakistan red color da mayafinsa, hannuwanta awarwaro ne masu kalar ja, kunnenta sanye da fashion din dan kunne mai dan tsayi baki masu stone, kafarta na sanye da black shoe mai dan tsini amma ba sosai ba,… duk da ita ba fara bace amma sosai tayi kyau domin kayan sun karbi jikin ta kwarai, Aaban kuwa sanye yake da pencil jeans baki da jan riga da aka rubuta “MY WOMAN”  da  manyan aruffa, kansa akwai P-cap yayinda fuskarsa ke rufe da glass da ya yi matukar karban fuskar sa, kafarsa kuwa sanye take da takalmi sau ciki baki, agogon zallan azurfa ne ke kwance kan lafiyayyan farar fatar sa, sun yi matuk’ar haduwa sun kuma dace kwarai da junan su…

kasancewar bai sanar da cewa gida cewa yau zasu dawo ba, ya sanya babu wanda ya zo tarban su, taxi ya tsayar suka nufi gida… Abrar kuwa jikinta ne ya yi sanyi sosai domin bata san ya halin yan gidan su yake ba, shine Mahaifiyarsa za ta karbeta amatsayin suruka? da kuma tunanin ammi da dai sauran tunani sune suka haifar mata da sanyi jiki….

Kura mata ido ya yi sonta mai zafin gaske da matsananci tausayin ta na ratsa shi,  ko dai dai da second daya baya son ganin damuwa shimfud’e kan kyakyyawar fuskarta hakan yasa shi cewa janyota jikinsa “bana son ganin damuwar ki, please ki daina tunani kinji?” ya fada idanunsa kafe kanta…

“toh na daina” ta fada hawaye ya zubo kan fuskarta, kamo fuskarta yayi cikin lallausan tafin hannunsa ba tare da ya ko kalli driver ba ya fito da harshensa ya shiga lashe hawayen fuskarta… shiru tayi tana kallonsa yayinda take jin wani son sa na ratsa jininta, shi din na daban ne, haka komai nasa ma special ne, murmushi ta sakar masa tana kokarin daidaita yanayinta, duk dan ta kwantar masa da hankali domin ya cancanci fiyeda haka, hannun sa ta zame daga fuskar ta ta kwantar da kanta kan kafadar sa tana sauke ajiyar zuciya…

bayan sun isa bakin tangamemmen gate din mansion din su, ya bawa driver umarnin tsayawa, fitowa ya fara yi kana ya riko hannunta ya fito da ita, sallaman driver yayi, bai ko karbi canji ba, driver godiya ya dinga zubawa wanda har sun shiga ta karamin gate di’n suna jiyo godiyar sa… mai gadi ne ya fara ganinsu nan ya gaishesu cikin girmamawa, haka ma sauran ma’aikatan sukar gaishen su, Abrar har kunya amsawa take domin dukkanin su sun girme mata…

a dan sace take bin mansion di’n da kallon tana kuma mamakin girma da haduwarsa, suna daf da shiga cikin main parlour din ya janyota jikinsa yace “decent one relax, ki kwantar da hankali everthing will be fine ok”.

“ok pure heart” ta fada tana sakar masa murmushin karfin hali, shima martani ya mayar mata domin sosai yake son sunan da ta rada masa.

“Assalama alaykum”

sallamar sa tare da na Abrar ne ya karade falon, sai dai nata ba da karfi tayi ba, amsawa mummy ta yi kasancewar ita kadai ce a falon yayinda fuskar Mummy ke dauke da murmushin ganin danta mafi soyuwa a ranta, a hankali Abrar ta nufi inda Mummy take domin ba sai an gaya mata ba, wanna kyakyyawar matar dake zaune mahaifiyar pure heart din ta ce, dai dai gabanta ta durkusa cikin ladabi da girmamawa surukar ta tace 

” Mummy ina wuni, mun same ku lafiya?”

fuskar Mummy a dan sake tace “lafiya lou, ya jikin ki?”

“Alhamdulillah Mum” ta amsa still kanta na kasa, dafe kanta Mummy tayi tace “Allah ya kara sauki”

da “ameen” ta amsa  har ma da Aaban daya tunkaro in da suke, domin kwarai ya ji dadin yanda Mummy ta amsa gaisuwar ta, a sake yana kuma da yakinin cewa wata rana zata sake da ita ta kuma so ta amatsayin MATAR DAN TA….

gefen Mummy  ya zauna ya gaishe ta, cikin kaunar dan ta tace “welcome home son, Allah ya yi maka albarka”

 da “Ameen” ya amsa yana sumbatar hannunta, Abrar da kanta ke kasa ruwan hawaye ya ciko idon ta saboda tuno da Ammin ta, Aaban na shirin tambayar ina Hanan? suka ji sallamar ta cikin murna tace “ya Aaban saukar yaushe?” cikin sauri Abrar ta dago kanta jin muryar aminiyar ta, kawa daya tamkar da dubu, cikin muryar mamaki hadi matsananci farinciki mara misaltuwa tace “bestie Hanan?” ta fada tana kallon Aaban alamun neman karin bayani, kashe mata ido yayi kana ya motsa labbansa yace “SUPRISE” cikin sauri ta nufi Hanan yayin da itama Hanan ta taho da gudo ta na  fadin “bestieee” ta ja harafin E d’in da tsayi.

Rungume juna suka yi yayinda Abrar ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, sun jima sosai suna kukan domin ko ba’a fada ba, Hanan yar’uwar pure heart ce, amma ta ya ya ta kasa gane hakan? duk da basa wani kama amma jini daya ba wasa ba…

“Allah na gode maka bestie na ta warke”

Hanan tace cikin murna.

“nayi kewar ki my masifatu” Abrar tace cikin kuka da mai hade da murmushi tuno rayuwar su ta baya, Bangaren Hanan ma dariya tayi mai hade da hawaye.

 Aaban har ma da Mummy ido suka kura musu, yayinda Aaban  ke jin ba dadi jin saukar sautin kukan  ta a kunnen sa, bangaren Mummy kuwa wani tausayi Abrar ne ke kokarin ratsa zuciyarta…. 

Ganin basu da niyyar daina kukan musamman Abrar yasa Mummy ta kalle su tace

“toh ya isa hakan nan ku karaso ku zauna”

Sai a lokacin Abrar ta tuna cewa ba su kadai bane a falon, saurin share fuskarta ta yi, yayinda Hanan ta riko hannunta suka karasa in da su Mummy ke zaune…

Kallonta mummy ke yi a fakaice tana kokarin karantar halaiyen ta, Abrar kuwa ganin Mummy zaune a wurin ya hana ta sakewa, fahimtar hakan yasa Mummy cewa

“son ya kamata ku je ku huta hakan nan, kafin Daddy’n ku ya dawo sai ku sauko ku gaisa”.

ba musu ya mike yana satar kallon Abrar alamun ta mike, sai dai kanta na kasa bata ma san yana yi ba, har ya yi gaba tana zaune, ita kam kunya take ji, ta ya ya zata mike ta bishi alhalin ga Mummy zaune tana kallonsu, fahimtar cewa kunya take ji yasa Mummy cewa 

“Abrar tashi ki bishi mana”

sosai kunya ya kamata, hannu Hanan ta damke a hankali tace “bestie tashi ki raka ni wallahi ina jin kunyar Mummy”

dariyar mugunta Hanan ta fashe da shi tana shirin yin magana Abrar ta sa hannu ta rufe mata kana ta ja ta suka fara tafiya, domin tsaf tasan Hanan zata iya kunya ta ta a gaban Mummy…

da kallon Mummy ta bi Abrar, tabbas ta hango nutsuwa a tare da ita, amma bazata yi saurin yarda cewa wanna shine halin ta na asali ba, har sai an kwana biyu idan ma tana da hali mara kyau, zai bayyana kansa ne….

har side din Aaban Hanan ta raka ta, ganin Hanan na shirin juyawa yasa tace “haba mana bestie ki zo mu shiga tare” Abrar ta fada fuska a marairaice…

“ku ji min iyayi da gulma, wai mu shiga tare, salon in shiga kina ja min Allah ya isa a ranki na shiga hakkin ku” Hanan tace a zolaye tana dariya.

“ke Hanan uwar sharri” Abrar tace tana zaro idanun ta.

dariya hanan tayi tace “eh naji, zan dawo anjima in ji ta yadda kika kamo da son yayana, ko dan kin ga farin fata ne” Hanan tace cikin wasa tana barin wajen da gudu.

da kallon Abrar ta bita yayinda fuskarta ke dauke da murmushin, sai da ta bace wa ganinta kana ta shige part din nasu… tana shiga ta gan shi zaune kan gado yana kokarin cire takalminsa, a hankali ta karaso inda yake hadi ta durkusawa gaban sa ta shiga cire masa takalmin, hannunsa ya cire ya kafe ta da ido sonta na ratsa jinin jikinsa, saukar muryar ta yaji cikin shagwaba tace “pure heart daman kai brother din bestie na ne baka gayamin ba” ta karasa tana turo dan karamin bakinta. 

har ta gama cire takalmin bai bata amsa ba, sai data gama cire takalmin ya daga ta kan cinyar sa ya dora ta, yayinda ya kafe ta da idanunsa mai sata nutsuwa yace “suprise na shirya yi miki shiyasa ban sanar dake ba, ko hakan bai bada sugar ba? yace yana dage girar sa.

murmushi tayi, haba shiyasa ya samu kyakkyawar  muhalli a zuciyarta ashe shi din yayan Hanan din ta ce…

“I love you” tace a kunyace

saurin kallonta yayi yace”repeat again please wifffy”

cikin kunya tayi saurin rungumar sa tace “I love youuuuuu” ta karasa tana jan U din.

wani mugun shaukin son ta ne ya dirar masa fuskarta ya kamo cikin tafin hannunsa yace “I so much love with all of my heart, you re my life, my heart beat, my everthing decent one” ya fada yana sumbatar hannunta.

kallonsa tayi, kallon so da burgewa, iska mai sanyi ya hure mata a fuska, yayinda kamshin minti din bakinsa ya daki hancinta, hakan yasa ta lumshe manyan kyakyyawan idanunta.

“am all yours decent one, ki rage kallona”

kunya ce ta kamata ta shigar da kanta a kirjin shi tana dariya, tashi yayi da ita a jikinsa ya kaita har bakin toilet yace 

“ki shiga kiyi wanka ina zuwa”… yana gama fadin haka ya bar wajen, wankan tayi ta fito cikin sanda, ganin baya dakin yasa tayi saurin shafa lotion a brown skin dinta, kaya ta gani akan gadon, atamfa super holland mai kalan yellow da touches din farare ajiki, sosai kayan suka burgeta domin atamfar bashi da color masu yawa, dinkin riga da zani ne, sai dai ta kasa daura zanin kasancewar bata taba yin kaya mai zani ba, atakaice ma bata sa atamfa sosai, tana cikin kiciniyar daura zanin ya shigo, kura mata ido yayi yana yaba yanda kayan yayi matukar amsar ta, murmushi yayi ganin yadda take fama da daura zani, tunkarota ya shiga yi, sai a lokacin ta ganshi, shagwaba fuska tayi tace

 “pure heart na kasa”…. 

bai ce komai ba ya tsaya daga bayanta ya kamo bakin zanin ya shiga daura mata, sai da ya tabattar zanin ya dauru kana ya juyo da ita gaba daya suna fuskantar juna, “so cute wifffy” yace yana bin jikinta da kallon.

murmushi ta sakar masa tace “thank you and you look handsome too” domin sai yanzu ta lura da ya canza kayan jikinsa da alama shima wankan yayi”…

” muje mu ci abinci, kuma Daddy ya dawo yace yana bukatar ganin mu down stairs”.

“toh” tace tana jin gabanta ya bada dam! data rasa dalilin hakan, sai dai bata bari ya gane hakan ba, hannunta ya riko suka fito….

share✔

 

      comment✔

              vote ✔

 

                 edit❌

Noor Eemaan ce✍

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like