MIN QALB 16

Advertisement

 

MQ 16_*

 

Zaune take gaban madubin dakin daya zama Mata tana kallon fuskarta datayi haske sosai tareda duka fatar jikinta har wani qyallin samun hutu da kayan gyara masu tsada da mutunci zuwa qirjinta daya ciko shima yayi daram dam  sabanin dah banbancinsa da shafe idan tasaka brazier ne push up.

 

Mayarda kallonta tayi Kan cikinta tana miqewa tsaye ta Dan matse rigarta tana shafa cikin sai tasamu kanta da sakin murmushi karon farko datai shaawar dama ace cikin gasken ne da ita da zaiyi mata kyau Kuma da duk wahala da dawainiyar anty zarah baza taje a banxa ba,

 

Dan sake dafe cikin tayi tana cewa”

Advertisements

 

To idan ace cikin gske ne to waye zai zama babansa?

 

Dr??

 

Girgiza Kai tayi tana cewa”

 

Ummen sa bazata Bari ba.

 

Amma dai duk da haka shine zaifi iya bawa babyna kulawa Amma dai kamanninsa kuwa anty zarah nakeson ya dauko sak sai Kuma……

 

Shiru tayi takasa qarasawa

Advertisements

 

Daga bayanta taji ance’ sai Kuma me maman bby?

 

Juyowa tayi tana kallon ZARAH din kafin ta juya ta qurawa cikinta ido ta cikin madubin ahankali tace’

 

Sai Kuma inason ya dauko hancin MD.

 

Zarah dake qoqarin zama bakin gado tsayawa tayi ta kalli amatun tana karban zancen a baibai saidai kawai tasan duk irin shirme shirmen Amatun sai kawai tasaki murmushi tana janye Amatun daga gaban madubi tana cewa”

 

Zoki zauna zaki gaji da tsayuwa gashi yau zamuje scanning anjima kadan

MD nake jira ya kirani na sanar Masa zamu fita nayita Kira baya dauka tun safe bayan fitarsa.

 

Ki qyalesa anty zarah mu tafiyarmu kawai tunda Dr na can Yana jiranmu a asibitin tun dazu yake Kira bamu fitoba.

 

Bazaki gane bane Amatu dokar MD ce baya barina fita Babu wani babban dalili me qarfi sbd shi mutum ne me buqatar sirrintacciyar rayuwa Mara hayaniya shiyasa bayason ko iyalinsa ace kowa ya sansu a haka dai zance MD mutum ne me tsananin kishi.

 

Dibar zancen na anty zarah tayi ta watsar da baki tana cewa”

 

Anty zarah to nidai gskia muje karki tsaya jira tunda yaga Kiran naki fa na tabbata,

Kuma nidai bazan Bari Dr yayita jiraba tunda Modibbo da Andi sunsan da zancen fitar muje kawai Dan Allah.

 

Miqewa anty zarah tayi tana nufar qofa tana cewa’

 

Amatun 6acin ran MD ba kyau bazan iya take dokarsaba

Zan iya fita yanxu wani Abu yafaru wlh bazan iya daukar fushinsaba kiyi hkr Bari nasake gwada kiransa kozai dauka….

 

Takaici yasa Amatun dafe ciki ta durqushe tana cewa”

 

Wayyo Allah anty zarah cikina marata ciwo sosai

Dan Allah anty ki taimakeni kada cikina ya samu matsala Ina sonsa banason ya zube…..

 

Da gudu anty zarah ta dawo tana Kiran sunanta cikin tashin hankali tana riqota

Ita kuwa Amatu sai wani murqususu takeyi tana sako hawayen qarya tana Daman cewa”

 

Anty ki taimakeni banaso cikina ya zube.

 

Tsabar tashin hankali da firgici tareda tausayin Amatun me tsanani ZARAH batasan lokacin data fashe da kuka ba tana kamota jikinta tana qoqarin muqar da ita tana kwalawa hafsatu Kira Dan tazo su kamata suyi asibiti.

 

Kamata sukayi suka saka mota a gigice anty zarah ta yafo gyalen jallabiyar dake jikinta ta fada motar ta jasu suka fice tana cewa hafsatu”

 

Hafsatu maza Yi sauri ki Kira Dr khalil ki sanar Masa Abinda yake faruwa gamunan zuwa.

 

Shiru Amatu tayi daga kukan qaryan datakeyi jikinta na yin sanyi da yanda anty zarah ta daga hankalinta sai hawaye takeyi tana Mata sannu Amma Babu yanda ta iyane itama sbd Dr yace Mata komai zatayi ta tabbatarda sunxo asibitin sbd yabasu scanning din daya shirya Dan ita din idan basuxo asibitin ba to tabbas wani likita ummensa zatasa akawo har zabeera din Dan kawai ayi komai yafito fili

A bangare daya Kuma ga USI da shima zasu hadu duk a asibitin shiyasa tayi hakan,

 

Ahankali ta kamo hannun anty zarah din bayan har sun iso asibiti Khalil ya karbeta sun shige yayi duk yanda zaiyi ya hado scanning din aka kwantar da ita office dinsa tareda ‘yan magungunan vitamins sai alokacin hankalin zarah yadawo jikinta ganin Amatun tadawo daidai ciwon ya daina.

 

tana kallon anty zarah din bayan ta riqe hannunta ganin har lokacin da sauran damuwa a fuskarta itama cikin sanyin murya furta”

 

Nagode anty zarah,

Nagode da matsayin da Kika bani na qanwa tamkar wadda kuka fito ciki daya,

Anty zarah wlh kece mutum ta uku da Kika taba qaunata tsakani da Allah ba qyamata ko wulaqantawa Dan haka kinada babban matsayi a zuciyata da har abada bazan mantaki ba.

 

Kasa cewa komai anty zarah tayi sbd har lokacin Bata Gama fitowa cikin shock din halinda Amatun tashigaba

Dan wato da ace wani Abu yasamu cikin bazata taba yafewa kanta ba.

 

Shigowar Dr da USI a bayansa yasata miqewa zaune da sauri tana washe dukkanin haqoranta cikin tsananin farin ciki takira sunansa tana qoqarin saukowa gadon Dr khalil yayi Mata gyara murya Yana kallonta

Take ta kallesa tana dawowa nutsuwarta saita waske ta hanyar cewa”

 

Anty zarah ga qanina usman.

 

Kallonta anty zarah tayi irin da gasken Nan kike?

 

Daga Mata Kai tayi murnarta na sake bayyanuwa ta jawo Usman din gaban anty zarah tana cewa”

 

Usi ka gaida anty zarah.

 

Da sauri cikin girmamawa yace”

 

Anty mun wuni lafiya?

Ya gida Yakuma qoqari?

Mungode sosai sosai fa anty

Allah ya saka Miki da alheri

Ya biya Miki buqatunki na alkairi.

 

 

Murmushi anty zarah tayi tana kallon yanda jikinsa har mazari yakeyi gurin gaidata Yana fiddo dukkanin girmamawar dayake ji akanta sbd duk yanda take qaunar Amatunsa tafada Masa shiyasa shima tun baigantaba yake Jin qaunar halayenta da ganin girmanta.

 

Kallon Amatu dake cikin dokin ganin usman din tayi tana cewa”

 

Amatu me Kika fada Masa yaketa wannan addua haka?

Usman karka ji komai ba komai Amatu tamkar qanwar da kuka fito ciki daya nake jinta

Saidai kayi Mata nasiha ko zataji Amatu Bata zama kurum kodan halin datake ciki gashi yauma sbd tasa damuwar fitowa Dole yasa akaso samun matsala har muka qare kwance a asibiti.

 

Anty zarah ki ringa doketa kokuma ki Fara hanata kayan Dadi zata dawo hankalinta.

 

Dariya sosai anty zarah tareda Dr suka saki harda ita Amatun tana kaiwa usi mugun duka a baya tace”

 

Ni zakayiwa baqin ciki usi?

Zakasan dawa kayi sai nasa kawu ya aura maka qanwar maman junior data maqale maka.

 

Cab wannan ai koni tafi iya sanin yanda ake sanfewa Dan wlh koke duk qwarewarki saita sanfeki

Kisa ranarda aka kawota ta sanfe Dan cinikin iyami da kawu kejin yanzu yafara zamowa sahun masu abun Kai kawu ya kwana ya debewa auren albarka.

 

Dariya suka saki gaba dayansu hadda anty zarah da batasan meye sanfewarba dagasu sai Dr ne kawai suka sani shima sbd yayi bincike sosai akansu ne Kuma sun zauna dashi su kawu da USI din Basu boye Masa komaiba gameba rayuwarsu sbd sunriga sun daukesa kamar jininsu.

 

Ta Dan saci kallon Dr da ita yake kallo shima zuciyarsa na samun nutsuwa da yanda yake ganinsu cikin nishadi zuciyarsa na sake samun nutsuwa

Ta juya ta harari usi tareda take Masa qafa da qarfi har Saida ya zabura tayi saurin dafesa Dan kada anty zarah tagane qasa qasa tace”

 

A gaban Dr baban babyn nawa kake tayarda maganar qwarewata a sata ka  shirya kwanciya a asibitin Nan Dan saina fasa maka baki da haqora idan anty zarah ta fita.

 

Kallon Dr yayi da Ido Yana cewa”

 

Ka ceceni matarka zata fasa bakina Wai.

 

Kamar zaiyi Magana sai ya fasa Yana sakar Mata murmushi sbd idanun data zuba Masa tana jiran jin Abinda zai ce ta mayarda rigimar kansa.

 

Ikon Allah anty zarah tayita kallo a tsakaninsu sunata raha da nishadinsu cikin tsananin qaunar junansu ga Dr da tuni dama yazama ‘daya daga cikinsu gabanta harsu iyami aka Kira da kawu a wayar Dr Nan aka Dora wata sabuwar hayaniyar sbd labarin fadanda kawu yayi dasu maman basiru ya dauko motar yan sanda biyu aka kwashe gidan kaf harda alhaji mande daya iya shigar sani infika.

 

Dariya sukeyi sosai musamman da iyami ke fadawa Amatu kawunta ya zabure yanzu tunda yaga ya ‘dan tsayu hakama insfector Garba na Nan Yana bibiyar kawun akan maganar aurenta.

 

Nishadi sosai suke saka anty zarah tayi zugum tana kallonsu suna burgeta hakanan taji inama acikinsu take itama data samu farin ciki kamarsu,

Abu daya tasani shine Koda take cikin wadata ta taso cikin tun tana gidansu Basu San wani Abu Wai sakewa cikin nishadi kayi rayuwarka ba,

Tun a gida sun Saba bin umarni ne kawai da oda suka sani

Iyayensu basa jansu ajiki Wai da sunan tarbiya da kadasu lalace

Shiyasa yawancinsu Basu wani cikin walwala saidai kawai suyi rayuwa cikin daular Amma Babu wani walwala saigashi wainnan bayin Allan sunada duk wani nishadi da walwala suna rayuwarsu hankali kwance,

Tabbas shi nishadi da farin ciki ba siyansa akeyiba Allah ne yake baka

Gashi ayau duk da tarin daular datake ciki rayuwar wainnan talakawan tana burgeta harma tanajin inama acikinsu take.

 

Anan sukai kusan Rabin yinin sai yamma suka fito gabaki dayansa tana Jin kewar usi dasu kawu tun Usin be tafi Amma hakanan suka rabu shida Dr suke tafi a motar Dr sbd yakaisa gida itakuma suka tafi a motar anty zarah da hafsatu.

 

Suna tafe suna tana kallon titi cikin nishadi sbd tunda tashiga zabeera tsawon wata biyu sai yau tafito,

Gskia dai ma Ashe wani lokacin masu kudin rayuwar takura kawai sukeyi kullum a killace Wai sbd kar mutane su dameka,

Ita Sam batason akoma gidan yanzu yawo takeso tadan sakata ta Wala.

 

Qaramin tsoki taja a fili Wanda yasa anty zarah kallonta tana cewa”

 

Yaya dai Amatu?

 

Bata fuska tayi tana yamutsawa tace”

 

Anty zarah Dan Allah muje blue fox na taba yin aiki acan

Muje kibiya madam dinmu kudi yau da kanta zata wanke min Kai da qafafu tasan Nima bayan ta koreni aiki nayi gaba ba bataba.

 

Murmushi tayi tana cewa”

 

Amatu ba dama.

 

A blue fox wani shaqiyanci ta dinga yiwa madam bell din tana cewa ga Abinda da Abinda takeso

Haka dai suka ringa yimata Abinda tace sbd ganin wadda sukazo tareda ita din she’s from zabeeras.

 

Gyaran Kai akai musu itada anty zarah din tareda kyan qafa da gyaran fuska take suka koma tamkar wasu amare musamman amatun da Bata taba irin wannan gyaran ba take suka hau wani irin sheqi.

 

Daga nan restaurant din blue fox din ta matsawa anty zarah suka shiga Nan tayi odar kayan dadin dataci harta Bar saura sbd sunfi qarfin cikinta suka fito nanma matsawa anty zarah  tayi suka nufi wani qatoton shopping mall datace tanada kwadayin son shigarsa.

 

Suna shiga mall din me hawa biyu batasan lokacin data saki tsallen murna ba tana rarraba idanu cikin gurin farin cikinta a bayyane.

 

Sama suka hau gurin kayan babies antyn na cewa kayan baby kawai zasu siya

 Nan anty zarah tadan zaba kayan babies suka sauko Amatun nata zare Ido tarasa abin dauka sbd duk kayan Dadi da maqulashen dake gurin akwaisa a gida hakama sutura Bata buqata sbd Dr kusan kullum cikin kawo Mata su yake hakama anty zarah

Idan turarukane duk tanadasu a gidan hakama takalma,

Ita Kam da a dah ne tazo wannan gurin da saita sace kusan kayan dubu dark saidai suje station

Amma ko yanxu ba damuwa Dan saita yiwa Dr tsarabar dazai ringa tunata.

 

Wani tsadadden agogon Rolex tagani Yana qyalli take ta hango kyanda zaiyi a hannun Dr

tasaki murmushi tana kallon anty zarah dake qoqarin Ciro card dinta tabayar gurin payment ta faki idanuwansu ta zaresa tareda sakawa cikin aljihun doguwar English gown din dake jikinta tana waskewa tahau ‘yan juye juye tana latsa wayar anty zarah dake hannunta.

 

Suna Gama payment din suka fito har zasu shiga mota aka tsayar dasu da sauri ana cewa su dawo ciki anason ganinsu.

 

Tsayawa anty zarah tayi tana kallonsu cikin mamaki kafin ta kalli time har anfara Kiran sallar magrib tace”

 

Lafiya?

Sauri mukeyi munyi dare fa.

 

Dayan ne me sanyeda suit kamar ma shine babbnsu yace”

 

Haj wani Abu mukeson kugani da idanuwanku kafin muyi mgn please.

 

Qaramin tsoki tasaki tana cewa”

 

Amatu ku jira a mota Ina zuwa.

 

Aa hajiya da ita zakuzo duka muke buqatar ganinku.

 

Ba musu suka koma ciki har office din managern gurin suka zauna take aka kunna musu Abinda footage na CCTV camera

Mutuwar zaune anty zarah tayi cikin mamaki da kunya

Amatun ma cikeda kunyar anty zarah ta dago ta kalleta kafin tayiwa manager kallon takaici

Bataji kunyarsa ba ko kadan ita anty zarah ce kawai abin Jin nauyinta itama dandai na farkone datayi a gabanta.

 

Bude baki anty zarah tayi Yana Mata nauyi zatayi Magana kenan saiga Yan sandan da aka Kira mota guda har sun iso Nan take aka gargadosu zuwa mota anty zarah tsabar rudewa da tashin hankali ko magana ma takasa Yi.

Wata baqar Mercedes-Benz beymach30745 2020 ce tashigo harabar gurin tayi parking

Tareda wasu motoci guda biyu manya na asalin me mall din dasukazo Dan duba gurin zai siye tareda estate din dake bayan mall din.

 saidaya dauki lokaci Yana qarasa wayar dayakeyi kafin yafito

Lokacin su alhaji bayo din yafito tareda P.A dinsa dukkanin ma’aikatan gurin sunyo gurinsa suna Masa barka da zuwa hakama ganin MD ZABEERA taredashi yasasu qara bada girmamawa suna Masa barka da zuwa barema daman sunji shine zai siye gurin.

##mamuh#

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 15

Advertisement   MIN QALB 15_* _mamuhgee_     Jin idanuwa ajikinsa yasashi ‘dan dagowa ya kalli inda suke…

MIN QALB 11

Advertisement  _*MIN QALB 11*_ _mamuhgee_ Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins…

MIN QALB 10

Advertisement  _*MIN QALB 11*_ _mamuhgee_ Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins…

MIN QALB 17

Advertisement   MQ 17_* _Mg_     Ana qoqarin turata motar Yan sandan ta hangosa tareda mutane Yana…

MIN QALB 9

Advertisement  *_MIN QALB 9_* _mamuhgee_ Gabaki ‘daya hankalinsa nakan fuskar amatu da ita Kuma hankalinta nakan usi da…

MIN QALB 26

Advertisement   26_* Zaune suke a Palo itada anty zarah anty zarah na Mata fira Dan sakata nishadi…