MIN QALB 17

Advertisement

 

MQ 17_*

_Mg_

 

 

Ana qoqarin turata motar Yan sandan ta hangosa tareda mutane Yana waya har lokacin kamalarsa na sake fita dabam acikinsu batasan lokacin data washe baki ba tana cewa”

 

Anty zarah bazan Bari kije station ba da mutuncinki,

Advertisements

Fizge hannunta tayi daga hannun ‘yar sandar mace ta maraice da fuska kamar zatayi kuka tace”

 

Officer madam Dena riqeni da qarfi cikine Dani Kuma….

 

Kallonta anty zarah tayi duk da tsananin baqin ciki da kunyar datake ciki Bata fatan Abinda zai samu Amatun sbd cikin jikinta

Zatai Magana idonta ya sauka kan MD dasuke qarasowa daf dasu zasu shiga mall din

Wani mummunan tashin hankali ya shigeta tai saurin fadawa motar Dan kada ya ganta bazataso mutuncinsa ya zube agurin ba da zarar angano ita matarsa ce

Barema sanin dokarsa da Abinda yafi tsana shine iyalinsa suzo budadden gurinda za’a Gama ganesu kamar wasu marasa daraja.

 

Amatu na ganin haka ta ‘dan daga murya tace”

 

Ku bamu damar Kiran wani daga gida

Advertisements

Sbd daga babban gida muka fito wato ZABEERAS.

 

Cak ta ‘dan tsaya bai juyoba saidata qara Kiran sunan zabeeras din tana sake Dan daga murya sbd ganin ya tsaya

Kai tsaye ya juyo idanuwansa suka sauka kanta a bakin motar ‘yan sandan Babu alamar kunya ko Jin nauyi atare da ita

Kai kawai ya dauke zai tafiyarsa saikuma ya tsaya cak sbd kamar matarsa ya hango cikin motar

Saiya kasa juyowa tsawon seconds kafin ya juyo cikin nutsuwa ya kalli cikin motar

Zarah dince kuwa a zaune tana sunkuyar da kanta

 take wani irin dacin Rai me mugun tsanani ya rufesa Amma idanba Wanda yasansa ba bazai iya ganewaba

Rintse idanuwansa yayi dasuka sauya atake yana controlling nutsuwarsa ta sakan hudu kafin ya budesu ya sauke Kan managern gurin cikin muryarsa me taushi da nutsuwa yace”

 

Meyake faruwa anan?

 

Bayani tsaf manager ya koro Masa Yana qarawa da cewar”

 

Ranka ya Dade wannan itace asalin wadda tayi satar inaga ita waccan me ajewa ce wato shugabarta Kuma………

 

Hannu ya dagawa managern Yana qara controlling fushinsa da idan yasakesa agurin fasa gurin zaiyi gaba daya Dan bazai iya daukar fushinsaba.

 

Yana daga wayarsa dake ringing yace”

 

Ku sakesu suje

Abar zancen daganan

Zanyi handling komai da kaina.

 

Okay ranka ya Dade angama

Officer ku sakesu su tafi

Ke hajiya fito

Allah ya taimakeku MD yasa baki ku wuce karku sake zuwa Nan sbd next time bazaku samu wannan damarba ta kubuta Dan munsan yanda muke dealing da qananun barayi irinku..

 

Zuwa lokacin kuka anty zarah keyi sbd maganganun dayake jefa musu dakuma sanin yau taqare Mata tsakaninta da MD Dan ita kawai ke iya hango _rage_ din dake fuskarsa gasu tafito bada izininsa ba,

Takai dare a waje ga wani irin bacin suna da aka ja Masa Danma ba’a gano ita matarsa bace.

 

Daqyar take Jan qafa jikinta na mugun rawa ga hawayen datake sosai ta nufi mota Amatu na binta jikinta a macen itama sbd ganin halinda anty zarah din ke ciki Wanda Bata taba ganinta acikinsaba.

 

Suna shiga mota daqyar anty zarah din ta iya tayarwa suka bar gurin Babu me iya ko dogon motsi a motar har suka Isa Kuma har lokacin hawayen anty zarah Basu tsayaba.

 

Suna barin gurin ya daga wayarsa daketa ringin Kai tsaye yace”

 

Dr duk Abinda kakeyi ka tabbatarda matarka tabar gidana acikin Daren Nan.

 

Kashe wayarsa yayi Yana Gama fadar hakan kafin yajuyo ya kalli P.A dinsa yace”

 

Faruk handle this for now

Gida zanje gobe zaka bani details din yanda akayi.

 

Juyawa yayi Kai tsaye ya nufi motarsa ya fada tareda janta da kansa yabar gurin sai alokacin suka fahimci da matsala sbd yanda yaja motar yabar gurin.

 

 

Suna shiga Palo tayi saurin Shan gaban anty zarah tareda zubewa qasa da qarfi Kan gwiwoyinta tana sunkuyar dakai cikin tsananin nadama tace”

 

Anty zarah kalmar hakurina bazata canza komaiba gameda tozarcin Dana janyo Miki yau din

Dan Allah anty zarah kiyi hkr wallahi bantaba Jin kunya da takaicin halinaba sai ayau,

 wlh sbd ke yau naji na tsani wannan halin nawa Dan Allah anty zarah kiyi hkr wlh banyi Dan tozarta…..

 

Saukar wani lafiyayyan Mari taji a fuskarta Wanda yasata qarasa zubewa zaune tana taba fuskarta amatuqar gigice ta dago a zuciye zatai Magana idonta ya sauka cikin nasa idanun dasuka kada sukai jajir….

 

Da sauri zarah ta zube qasa itama zatai Magana ya daga Mata hannu batareda ya kalletaba yace”

 

For first time ayau naji nayi takaicin amincewa da aurenki,

Hw cud you zarah,

Bakisan mutuncin kanki da Wanda ya ajiyeki bane dazaki fita in the first place batareda izini ba

Ever this stupid being came here nasan zaayi haka wata Rana sbd wannan ba mace bane she is just a shame,

Sata rayuwarta ne

Shi aka reneta dashi sbd Abinda tasani shine kawai sata da yawo cikin maza with no shame,

A hausance banma san sunan dazan kirataba sbd idanma ankirata da abin kunya an Bata sunan mutunci

Amma ke this is the last thing I expected from you…

 

Banason hayaniya I prefer rayuwata ni kadai yafi nutsuwa da kwanciyan hankali so please ku duka just park ur things kubar Nan

Ni kadai nakeson zama anan just I think kowannenmu need a break…….

 

 

Wani irin kuka Mai taba zuciya anty zarah tasaki tana qoqarin basa hkr ya juyawarsa zai haye sama Amatu ta miqe da saurin Tasha gabansa tareda sake zubewa tana tsiyayo hawaye masu tsananin ‘dacin kalaman daya furta akanta saidai komai ‘dacinsu zata hade bazata Bari laifinta ya lalata auren anty zarah ba kodan yanda tasan shine rayuwar anty zarah din.

 

Akaro na farko a rayuwarta datake qwallan cin zarafi da akai Mata sabanin da ko ajikinta Dan ko damuwa batayi barema ada Babu Wanda ya Isa ya tsareta ya iya fada Mata haka Bata saka an Masa zanen yorbawa a fuskar ba.

 

Sabbin hawaye suka gangaro Kan fuskarta ta bude baki muryarta a matuqar sanyaye tace”

 

Dan Allah kayi hakuri anty zarah batada lai…

 

Ko kallon inda take baiyiba ya wuce tayi saurin rarrafawa zatasha gabansa  cikin tsananin 6acin Rai ya daga qafa zai wuce da ita aka saka hannuwa biyu aka tare qafar

Ya tsaya cak kallon Dr daya riqe qafar tasa cikin tsananin mamaki da sabon takaici.

 

Dr daya jima tsaye Yana sauraran duk Abinda MD din ya fada suna dukan zuciyarsa duka me tsananin daya karya gwarin gwiwarsa.

 

Baice komaiba sai kawai ya sauke gwiwoyinsa qasa gaban MD din tareda sunkuyar da Kai cikin tsananin rauni da damuwa me nauyi murya a sanyaye yace”

 

MAHMOUD karka hukunta zarah akan laifin amatu na roqeka da sunan Allah,

Itama Amatu Ina roqonka daka yafe Mata Koda  hakan zai zama alfarmar qarshe dazakamin arayuwata to Dan Allah ka yafe Mata ba laifinta bane laifina ne Dana kasa bar Mata duk Abinda yakamata nabar Mata……

 

What???Khalil Kama San waye wannan yarinyar kuwa?

Tun farko bansan me kagani na hankali atareda wannan yarinyarba harka iya sabawa iyayenka ka aureta,

And now kana durqushe a gabana duk sbd ita

Khalil Kama ganin daidaine hakan?

 

Rintse idanu Dr yayi a sanyaye Yace”

 

Abinda nasani yanxu arayuwata shine indai sbd itane zanyi har Abinda yafi durqusawa sbd tsirar Mata da mutuncinta,

Kai Dan uwanane mafi kusanci agareni Wanda kalmomin batanci mafi Muni suka fito daga bakinka kan macen danafi so da qaunar Kare martabarta shiyasa na durqusa gaban nake neman afuwarka sbd ita,

 

Cikin sake kunnasa da Khalil din yayi da maganganunsa hakanan kawai yaji mugun zafinsu

Yau Khalil ne ke fadar kariya da martabarta

Rintse ido yayi suna qara rinewa ya kalleta

Sautin kukanta na fita ahankali sbd maganganun Dr sungama sanyata cikin nadama me tsanani

Take zafin zuciyarsa yafara loosing control ya juya zai wuce Khalil ya miqe tareda Shan gabansa yace”

 

MD matuqar haryanxu matsayina na Nan a zuciyarka da rayuwarka inason ka tabashi biyu kabani nida Amatu sbd wlh ni itace tawa rayuwar,

Zakaimin alqawarin yafe Mata tareda Bata mutunci amatsayinta tawa,

Idan bakayi Dan ni ba kayi kodan jinina dayake jikinta Wanda yake shima naka jinin,

MD Ina fatan zakamin wannan alfarma ko bayan idona.

 

 

Kasa kallon Khalil din yayi sbd baqin ciki da takaicin duk akan mace ya zare haka macen ma ba kamar matan mutunci ba haryana kirarin idan yana qaunarsa saiya qaunaceta

Ra’besa kawai yayi ya haye sama tun kafin shida Khalil din ta 6aci akan yarinyar.

 

 

Bayansa Khalil yabi da kallon harya shige kafin ya saki numfashi a sanyaye tareda juyowa ahankali ya zauna gefen amatu dake kuka qasa qasa takasa ko motsi.

 

Kallon zarah dake nata kukan yayi zaiyi mgn ta miqe tabar gurin tayi dakinta ta rufo sbd itama kukan takeso tayi sosai ko nauyin zuciyarta zai ragu.

 

Cikin sanyin jiki ya maido da kallonsa Kan amatu yafara lallashinta Yana Mata nasiha hartayi shiru da kansa ya dauko ruwa a fridge yabata Tasha ya rakata har dakinta kafin ya wuce zuwa nasa part din jiki da zuciyarsa amatuqar sanyaye.

 

Sallolinta tayi ta zame ta kwanta Kan dadduma a inda tayi sallar yau ba Maganar cin Dadi

Amma datayi awanni a kwance taga bacci ba zuwa zaiyiba sbd yunwa hakanan ta miqe ta fito taje kicin taci fruits dinta da yoghurts ta qoshi tazo ta kwanta tunanin Dr na dawo Mata bangare daya Kuma damuwar da anty zarah take ciki.

 

 

Washe gari tunda safe Dr khalil yazo sbd yasan shikenan MD zai Fara rashin ‘dan zaman dayakeyi a gidan fita tinda safe dawowa sai dare qarshema yasan zai iya tafiya yabar qasar yakoma wata qasa sai yaga dama ya dawo.

 

MD na ganinsa ya kallesa Yana watsar da tunanin abubuwan jiya din sbd shi ba mutum ne me aje hargitsi cikin kansa ba Sam ko maganar batason a tayar sbd kar asashi cuwon Kai.

 

Kallonsa Dr khalil yayi Yana qaqalo murmushi yace”

 

Good morning MD ZABEERA.

 

‘dan kallonsa MD din yayi Yana maida kallonsa Kan agogon hannunsa cikin miskilanci yace”

 

Morning Dr khalil zabeera.

 

Murmushi Khalil din yayi Yana cewa”

 

Sorry MD.

 

Kallonsa ya ‘danyi kafin yaci gaba da duba wayarsa.

 

Bai kamata nama Magana irin yanda nayi maka a jiyan kayi hkr.

 

Karka damu I can’t even recall Abinda yafaru a jiyan.

 

Numfashi Khalil ya sauke Yana gyara tsayuwa kafin yace”

 

Amma akan Amatu inakan duk Abinda nafada Dan haka Ina riqon alfarmarka sbd abin dake cikinta please kabata damar dazan gyarata kodan ‘yayana su samu uwa ta gari.

 

Gaba daya MD din ya dago ya kallesa wannan karon tareda ‘dan lumshe fararen idanuwansa yasaki wani sahirtaccen numfashi kafin yace”

 

I hope you know wat u’re doing.

 

Motarsa ya fada tareda cewa”

 

Mu yini lfy Dr.

 

Murmushi Khalil yayi Yana cewa”

 

Zan dauki wannan amatsayin amincewa da roqona thank you.

 

Ciki ya qarasa gurinsu sbd Suma yanason mgn dasu musamman zarah bayason tasamu matsala da Amatu akan wannan alamarin sbd ita kadaice yasan Amatu is safe a gurinta.

 

Cikin sa’a kuwa Zarah din na dining tana qoqarin jera breakfast tayi ‘dan adonta duk da ba walwala sosai a fuskarta duk sbd taqara bawa MD hakuri.

 

Cikin sakin fuska yakira sunanta

Ta juyo tana yaqen Dole suka gaisa

 

Suna cikin mgn saiga Amatu ta fito jiyo muryarsa

A sidade ta qaraso tana kallon fuskar zarah a raunane.

 

Ganin yanda tayi din sai anty zarah din taji rashin Dadi ta saki ‘dan guntun murmushi tana cewa”

 

Amatu Zo

Kinci abinci jiya da daddare kuwa?da maganinki ma kinsha??

 

Wani sabon girma da qaunar anty zarah dinne suka rufeta batasan lokacinda ta qarasa gurinta da sauri ba ta rungumeta tareda sakin wani siririn kuka tana cewa”

 

Anty zarah Dan Allah ki yafemun wlh nayi nadama me tsanani akan Abinda na ja miki.

 

Karki damu Amatu qaddarane Kuma yariga ya wuce tunda kince bazaki sake ba.

 

Zama tayi gefen anty zarah din ta share hawayenta tana sunkuyar da Kai tace”

 

Anty zarah kunyarki nakeji haryanxu sbd tun yanxu nafara saka Miki da Abu Mara kyau akan alkairi da qaunar da kike mini,

 

Ayau naji gida nakeson komawa inda nafito,

Cikin mutanenda nafito,

Cikin rayuwar damuka saba da qanqancin da muka Saba dauka sbd nafara gane ban cancanci zama cikin mutane masu mutunci da daraja kamarku ba,

 

Anty zarah daukar abin wani yazama tamkar qaddaratace sbd saimun dauki abin wani muke iya ciyar da cikinmu abinci wata Rana,

Rayuwa da mutanen cikintane suke tilastamu ga aikata wasu laifukan wata Rana,

 

Nida usi muntaso cikin bola muka rayu acikinta mukayi wayo,

Acikin bola muka Fara sanin yanda zamuyi fafutuka mu gudanar da rayuwarmu,

 

Bayan Tasha shine gurin kwananmu

Shine muhallinmu a lokacin,

Tun munada shekarun da bamu Gama sanin bambamcin jinsuba aka lalatawa usi rayuwa ta hanyar Masa fyade,

Fyaden da shine sanadin farko na qarin tabarbarewar rayuwarmu,

Alokacin mukasan ba tausayi atareda mutanen cikin duniya,

Munkoyi data Danmu ci mu tsira mu rayu,

 

Anty zarah bamu qara fuskantar qasqancin halin rayuwa da mutanen cikintaba sai alokacin da nida USI aka kamamu a gaban idonsa aka yaga tsumman sutura dake jikina za’ayi mini fyade Wanda yayi sanadin haduwarmu da mutum na farko daya Fara yima kallon muma ‘yayane Kuma mutane ‘yan Adam,

 

Kawu ya gabatar Mana da sabuwar rayuwar almajiranci wadda nayita acikin maza da siffar maza ta hanyar rayuwa usman namin aski,

Munyi almajiranci na wahala Wanda yasamu baqin jini acikin almajirai Yan uwanmu,

Munyi kukan sarari munyi na fili saidai bamuda tudun dafawa har Saida rayuwar wahala da garari ta aure mu kafin kawu yasake kallonmu da idanuwansa na rahama da jin qai ya zamo uba garemu,

Ya bamu uwa me qaunarmu tamkar ‘yayanta iyami,

 

Mezamu ce arayuwar Nan bayan wahala da rayuwar garari a jininmu take shiyasa ko a gidan kawu tsanani da Matsin rayuwa be qare Mana,

 

Muna kwana da yunwa mutashi da ita Kuma muyi rayuwarmu,

Munshiga masifu iri iri da rayuwa ta jefamu aciki saidai Babu wani mahaluki ‘daya daya taba kallonmu da zuciya me kyau

Kowa nada buri Mara kyau akanmu Wanda ya dangantamu da irin wannan rayuwar da ake qyamarmu sbd ita,

Rayuwa ta zabar Mana gwagwarmayar samun Abinda zamucu kota halin Yaya alokacinda ‘yaya kamarmu suke makaranta suna karatu shin anty zarah bawa shi yake zabarwa kansa qaddarane??

 

A tsawon shekarun ban bantaba Jin nadamar daukar abin waniba sai a jiya Dana jawa macen data Soni tsakaninta da Allah batareda ta hada komai daniba,

 

Anty zarah a shirye nake Dana bar Nan sbd zamana anan masifa zai janyo Miki ba alhe…….

 

Rungumeta anty zarah tayi da sauri Yana sakin sheshekar kukan datakeyi na tausayin Amatun da usman tareda su kawu dasuka taimakesu bayan Suma taimakon suke nema.

 

Tabbas Amatu sbd Allah nakesonki tun ranar da kikazo Nan,

Kinmin laifi Amma ban riqeki a raiba sbd sanin ajizanci irin na ‘dan Adam,

A da Ina zaune dake amatsayin matar Dr dakuma Amana da aka bani Amma daga yanxu zan zauna dakene amatsayin qanwa da muka fito ciki ‘daya.

 

Zamewa Amatun tayi da sauri tana share hawayenta ta saki qaramar dariya tanason kawar da kukan anty zarah din tace”

 

Anty da gaske?

 

‘daga Mata Kai tayi tana share hawayenta itama.

 

Anty zarah karfa wata Rana kice aa alqawari kikamin munzama kamar ciki daya muka fiyo.

 

Dariya antyn tayi har lokacin hawayenta Basu Gama tsayawaba tace”

 

Amatu nayi alqawari ba canzawa

Amma kema kinsan kinyi alqawari zakiban babynki idan kin haihu”” tafada cikin tsokanar Amatun.

 

Da sauri ta kalla Dr dayayi mutuwar zaune da tsananin so,qauna, tausayi tareda ganin girman Amatun

Ta dafe cikinta tana cewa”

 

Dr kaji anty zarah Wai zamu Bata babyn.

 

Yana kallonta cikin tsananin shauqi yace”

 

Idan har kin amince zaki Bata ni Kuma idan har nine dadynsa nayi alqawari da hannuna zanbatashi.

 

Murmushi yasaki tana shafa cikinta ahankali tace”

 

Inama inada cikin wlh Dana baki anty zarah.

 

Qasa yayi da murya daidai kunnenta yace”

 

Karki damu watanni kadan ne yarage mufita wannan dilemma din zamu bawa antynki da MD baby.

 

Kallonsa tayi da sauri tana boye dariyarta Dan batasan yajitaba ganin yakasa daina murmushi yasata miqewa da sauri tayi hanyar dining tana cewa”

 

Anty zarah mijinki yagama ci muzo muyi namu party din a dining Dan wlh har yunwar jiya saina fanshe abuta.

 

Murmushi sukeyi suna Mamakinta ganin tabbas Bata aje al’amarin duniya a ranta sbd karta wahalar da kanta a banza sbd me gatane ke tsayawa kuka da damuwa Dan a lallashesa suda basuda ko daya sunyi futo na fito da kuka da damuwa tareda abin kunya Sam baya damunsu.

##Mamuh#

 

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 22

Advertisement   *_MQ 22_*   *_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN…

MIN QALB 26

Advertisement   26_* Zaune suke a Palo itada anty zarah anty zarah na Mata fira Dan sakata nishadi…

MIN QALB 35

Advertisement   MQ 35_*   Godia kawu yasake kafin ya sake gyara zama bayan fitar MD yace”  …

MIN QALB 45

Advertisement   MQ 45_*    Sai Bayan sallar asuba jirginsu ya sauka Nigeria ta dayake ta Kira USI…

MIN QALB 49

Advertisement   #*_MQ 49_*       *_THE FLAVORLAND BY ACEEY_* Ina ma’abotan son ingataccen yaji, Different Flavors…

MIN QALB 10

Advertisement  _*MIN QALB 11*_ _mamuhgee_ Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins…