MIN QALB 18

Advertisement

 

*_MQ 18_*

_Mg_

 

 

 

Koda anty zarah tace yazauna suyi breakfast tare baiso karya Mata qwarin gwiwaba amma Dole yace Mata MD yariga yafice tun dazu so karma su jirasa suyi abinsu shima bai tsayaba sbd yau umme tace taredashi zatayi breakfast ya fice ya nufi can tun kafin rashin zuwansa ya shafi Amatu Dan Babu ranarda Bata tsinewa ranar data Fara haduwa da amatun.

 

Advertisements

Shiru anty zarah din tayi a sanyaye Jin MD baya gidan ya fice.

 

Dafa hannunta dake zuba chips Amatu tayi tana murmushi tace”

 

Anty karki damu zai hakura inshallah,

Nice nayi laifin Kuma nice zan gyara

Inshallah Allah saina sa Rabin ranki ya yafe Miki Dan haka ki daina damuwa Amatu zatai Miki handling komai.

 

Qasa tayi da murya Yana cewa”

 

Saina Fara sashi yasan dawa yakeyi kafin Nan,

Shine jiya haddasa Dr ya durqusa agabansa Yana wani daddaure fuska Yana Shan qamshi to zaisan yasa Dr da anty zarah damuwa indai nice Amatu saiya sani.

Advertisements

 

Me kike cewa Amahh.

 

Cika baki tayi da chips da kwai tana cewa”

 

Bance komaiba anty zarah

Zauna kici abincinki karki Hana kanki abinci sbd soyayya.

 

Zama tayi tana murmushi tace”

 

Amah samun Wanda kakeso yanada Dadi hardai idan shima Yana sinks,

Kinga kamar ke da Dr.

 

Tea ta kwankwada tana cewa”

 

Yanxu ni da Dr son juna muke??

 

Eh Mana gashinan a fili Muna gani musamman Dr bayada damuwa sai Taki,

Farin cikinki da walwalarki sune nasa

Kina gani yanda baya iya dauke Ido a kanki koyaushe kece first priority dinsa.

 

To ni anty banajin wainnan abubuwan da Kika fada nadai San acikin maza banida kamar su uku shi da kawu da usi,

Yanda kakejin usi hakan nakejin Dr zan iya komai Dan farin cikinsa da kula dashi.

 

Bakyajin faduwar gaba duk lokacinda Kika jiyo muryarsa kafin ya iso gareki??

 

Sake cika bakinta da soyayyan qwai tayi tana cewa”

 

Banaji Amma Kinga Rabin ranki Dana jiyo ko qamshin turaran Nan Masa me qarfi gabana faduwa yake sbd masifarsa.

 

Tsit anty zarah tayi tana kallonta kafin tasaki murmushi tana cewa”

 

Shikenan karki damu zankoya Miki yanda zakiso Dr matuqa kamar yanda yake sonki.

 

Anty zarah inason nazama wacce zata bawa Dr farin ciki da dukkanin wata soyayya..

 

Bazaki iya basa farin ciki ba sai kin basa dukkanin zuciyarki da soyayyarki.

 

Zanbasa sbd shine kadai a duniya cikin maza ya cancanci zuciyata

Koda zuciyata batasan meye so ba zanbada ita saiya koyar da ita da kansa.

 

Taso bawa maganganun amatu nutsuwa Amma ta watsar sbd Amatun kanta batasan abubuwan datake fadaba Dan haka ba amfanin nazarinsu.

 

 

Suna Gama cin abincin Palo suka dawo anty zarah ta zauna tana waya da ummanta ita Kuma Amatu dakinta Takoma Dan watsa ruwa.

 

Wanka tayi ta sanya riga da skirt na atampa coffee kala ta tsaya gaban madubi Yana duba kanta tana sauke ajiyar zuciya sbd ganin Masha Allah yanxu ita da kanta sha’awar kanta takeyi sbd mulmulewa da jikinta yayi da hutu da kayan gyara jiki da fata.

 

 

Akan cikinta dake shafe kamar bashi yake daukar uban kayan Dadi da abincin datake zuba Masa ba ta shafa ahankali tana gyara tsayuwa

Hakanan kawai yanxu tsananin son cikinta ya shigeta duk da tasan ana Magana ne akan Abinda Babu kwata kwata saidai ita zancen yashigeta musamman idan tayi tunanin ganin babyn a hannunta tana Masa Wasa Yana murmushi irin na Dr.

 

Dankwalin kayan jikinta ta zare tareda nadawa ta saka cikin rigarta daidai cikinta saita saki rigarta cikin yataso ya zauna daidai tareda qarawa tsayinta kyau sai tayi kamar sabuwar amarya me qaramin ciki

Batasan lokacinda tasaki murmushi ba tana shafa cikin saiga anty zarah tashiga tana cewa”

 

Amatu baki gama Shirin bane gurin Modibbo zamuje gaisuwa tunda kikazo bakije kin gaishesaba hakama umme sune fa iyayen mijinki….

 

Tsayawa tayi da maganar lokacinda idonta ya sauka kan ‘dan matashin cikin na jikin Amatun take dukkanin farin ciki da Jin Dadinta ya fito fili ta qaraso da sauri tana cewa”

 

Kinga Amatu yanxu cikinki yafito sbd kinsaka riga da skirt dogayen rigunan Nan boye cikin sukeyi gaba daya..

 

Kallonta Amatu keyi tana murmushin ganin yanda ganin fitowar cikin kawai yasaka anty zarah wannan farin cikin to ranar da aka haifesa fa ta daukesa a hannunta.

 

Anty zarah Inshallah kema zaki dauki ciki ki haifi ‘yayan kanki Dana Rabin ranki.

 

Allah yasa Amatu

Sbd babbar adduata a yanxu shine samun haihuwa tareda MD sbd haihuwa ce kawai zanyi na tabbatarda MD ZABEERA yazama nawa,nasamu muhalli acikin zuciyarsa da rayuwarsa.

 

 

Gyale coffee ta yafa akanta suka fito zuwa sashen Modibbo,

 

Kamar Wasa saigasu sun ‘dan jima agurinsa sbd yanda Amatun ta zage tana basa labarin qanxon kurege na aurensu da Dr daya sake tambayarta,

 

Hakanan sai ta ‘dan shiga ransa sbd Jin yanda sukayi gwagwarmaya itada mahaifiyata baba Jamila.

 

 

Daganan sashen umme suka nufa Kai tsaye Amatu nata sake bude idanuwanta da zabeera din koina kallo takeyi cikin burgewa tana sake tantance asalin girma da wadatar Zabeera din.

 

 

Kwankwasa qatuwar qofar shiga palon umme sukayi

Tsawon mintuna hudu kafin me aikinta tazo ta bude musu suka shigo Amatu na santin kallon qayataccen palon da qamshi tareda sanyin AC suka cikasa.

 

Zama zukayi jiran saukowarta saidai shiru shiru Bata saukoba Nan Zarah da aka Kira tayi baquwa ta tafi tabar Amatu na zaman jira.

 

Saidata shafe awa kusan biyu a zaune kafin ummen ta fito cikin shigar alfarma tana waya Kuma dagaji da Dr take wayar sbd yanda take amsawa da Dan sauran haushinsa dabai Gama sakinta ba

Saidata shigo tsakiyar palon ta lurada  Amatu dake zaune tana kallo tana Kira ruwan lemu da aka kawo Mata hankalinta kwance Dan wuce guri da volume bai ishetaba ta dauko remote taqara tana shigaba da kallonta remote din a hannunta sai murmushin Abinda take kalla takeyi.

 

 

Ko sallama da Khalil din batayi ba a wayar ta kashe tana cewa”

 

Uban waye zaune har cikin palona?

 

Juyowa Amatu tayi tana aje cup din hannunta da murmushi Kan fuskarta tace”

 

Haj Mama nice Amatu matar khalil nasan zuwa yanzu kinmantani.

 

Cikin quluwa ta daka Mata tsawa tana cewa”

 

Uwar matar khalil din ce ba matarsa ba

Zoki fice kafin nasa kiyi nadamar zuwa Nan.

 

Matsowa Amatu tayi da sauri gabanta tana cewa”

 

Umme Dan Allah kiyi hkr da Abinda yafaru ba laifina bane bakuma laifin Dr bane qaddarane Kuma nidai na karba qaddarar nan da hannu biyu ta zama matar Dr wlh inaso…..

 

Ganin tafara loosing patience dinta batason tayiwa Amatun komai yanzu sbd tanadin datai Mata tukuna shiyasata fixgota a wulaqance ta jeho ta waje daidai isowar Nuratu  wajen ta tareta daga faduwar dazatai saidata dago taga Amatu ce aikuwa ta saketa amatun tayi muguwar faduwa akan hannunta na dama take ta samu kurdewar qashi tasaki wani razanannen ihu tana qoqarin tashi Amma takasa dafawa sbd azaba take wani zufa ya karyo Mata ta kalli Nuratu a masife tace”

 

Ita waccan data jeho ni nasan dalilinta kekuwa da kikaimin haka meye naki dalilin??

 

Dalilina shine cikin jikinki””tafada cikin tsananin tsana da takaicin ganin cikin jikin Amatun.

 

Miqewa tayi da qyar tana dafe hannun cikin azaba tace”

 

To ke meye ruwanki da cikina kokuwa kema cikin ‘yan koren uwar Mijina ce sbd dai bakida alama da ‘yan zabeera daga Ina malama???

 

Baqin ciki maganar Amatun tai Mata tana sake quluwa tace”

 

Ni ba matsiyaciya bace kamar ki wadda Babu Wanda yakeda tabbacin ba karuwa bace Khalil ya fada tarkonta ta auresa sbd kudi

Wama yakeda tabbacin wannan cikin nasane Kona wani qa……..

 

Wani gigitaccen Mari ya sauka akan fuskar Nuratun dayasa gefen bakinta ‘dan fashewa

Ta dago da sauri tace”

 

Ni Kika Mara???

 

Zuciya data gama ciyota kukan kura tayi tai Kan Amatun zata mareta aka riqe hannunta ta bayanta ta fizge zata Kuma Yi Kan Amatun ya sake riqe hannunta tareda zagayo gabanta kyakkyawar fuskarsa ta jinin zabeera tana fidda sheqi

Tace”

 

SALMAN????

 

Sakeni,

wlh saina koyawa wannan mummunar karuwar hankali..

 

Saukar wani Marin ne a fuskarta yasata qarasa zaucewa tana qwacewa tace”

 

Wlh yau sainaga ubanda ya tsaya wannan tinkiyar…

 

Sakinta Salman din yayi tareda kallon Amatu da mamakinta yagama kashesa yana cewa”

 

Lallai Nima zanso ganin Wanda take dashi daya Bata wannan qwarin gwiwar me ban mamaki da burgewa

Ina buqatar saninsa Dan basa jinjinawa ta musamman.

 

Kallonsa Amatu tayi ganin Yana qarawa wutar masifar fetur tace”

 

Amatu itace tsayayyiyar kanta Bata buqatar tsayawar wani gurin nunawa  kowa matsayinsa,

 

Ki zauna ki nanatawa tosashiyar qwaqwalwarki ni Amatu nariga Masha gabanki

Idan har akwai Amatu har abada Dr khalil zabeera bazai taba kallonki ba

Kai da kake Dan uwanta saika taimaka Mata gurin fahimtar hakan

Amatu ba tsarar yinki bace.

 

Tana Gama fadar hakan ta wuce Yana shafa cikinta Dan qara qular da Nuratun

Cikin mugun baqin ciki da takaici nuratu ta juya a zuciye tabar gurin tana fidda huci kamar zuciyarta zata tarwatse idanuwanta har wani cikowa da hawayen baqin ciki suke

Dama can Kuma halinta ce saurin fusata.

 

 

The great ORTHOPEDIC Dr Salman zabeera kuwa gabaki daya Amatu tagama basa mamaki lokaci daya da burgesa sbd sanin darajar kanta datayi takuma nuna batareda tsoro ba,

Koma wacece Amatu shi tagama burgesa shiyasa yakasa dauke Ido daga kanta harta bace.

##Mamuh#

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 40

Advertisement  ##Mamuh#*_MQ 40_*  Kasa daukarta bacci yayi Kuma ko juye juye takasa tadaiyi lamo cikin lullubin duvet tana…

MIN QALB 23

Advertisement   *_MQ 23_*   *_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN…

MIN QALB 11

Advertisement  _*MIN QALB 11*_ _mamuhgee_ Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins…

MIN QALB 37

Advertisement   MQ 37_*     *_kina da burin koyon sana’a wadda zaki yita daga gida a sauqaqe_*…

MIN QALB 26

Advertisement   26_* Zaune suke a Palo itada anty zarah anty zarah na Mata fira Dan sakata nishadi…

MIN QALB 44

Advertisement   ****** Zama tayi a palon zuciyarta na wani irin tiririn takaici da baqin cikinsu su dukan…