MIN QALB 19

Advertisement

 

*_MQ 19_*

 

 

 

*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*

 

*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*

 

Advertisements

*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*

 

*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*๐Ÿ’†๐Ÿพโ€โ™€๏ธ๐Ÿ™Ž๐Ÿฝโ€โ™€๏ธ

 

*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaษ—a ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*๐Ÿ‘ฏ๐Ÿฝโ€โ™€๏ธ๐Ÿ‘ฏ๐Ÿฝโ€โ™€๏ธ

 

*karki xama ‘yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*

*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*

 

*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*

 

Advertisements

*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*

 

*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*๐Ÿคž๐Ÿพ๐Ÿคž๐Ÿพ๐Ÿคž๐Ÿพ๐Ÿคž๐Ÿพ

 

 

 

**********

Doguwar tafiya tayi har zuwa sashensu tana Jin tsananin azabar radadin da hannunta keyi ta daure ta iso tana rintse ido cikin uwar azaba ga zufa sai karyo Mata yake shiyasa tana isowa tun a Palo ta zube Kan kujera tana kallon hannun da harya Fara kumbura

Sanin anty zarah na dayar palon tareda baquwarta yasa ta sulala tayi dakinta ta kwanta Dan kada ta dagawa anty zarah din hankali saidai ita kadai tasan uwar azabar datake ciki shiyasama takira usi

Yana daga wayar sai alokacin taji hawaye sun ciko idanuwanta sai Kuma takasa mgn ta kashe wayar ta ajiye tana gani yanata Kira takasa dauka sbd karta daga Masa hankali kawai.

 

 

Duk yanda take tunanin zata iya riqe ciwon takasa sbd sosaine tasamu gocewar qashin hannun sai kumbura yakeyi har takai tafara kasa motsasa sbd tsamin daya dauko.

 

Har dare tana dakin Taki fitowa sai bayan magrib baquwar anty zarah ta tafi

Itama anty zaran dakinta ta nufa sai datayi sallar magrib da ishai tukuna ta fito palon saidai rashin ganin amatu a palon yasa ko zama batayiba ta nufi dakinta.

 

A kwance ta taddata Idanuwanta a rufe tanajin anty zarah din ta tashi zaune tana rintse ido alamar ciwo

Nan anty zarah din ta qarasa bakin gadon da sauri tana dafa Hannun me azabar Bata saniba

Wani irin zabura Amatu tayi cikin tsananin radadin dataji tana tana cewa”

 

Anty hannuna ya karye.

 

Da sauri anty zarah ta kalli hannun batasan lokacin data zaro ido ba ganin ya kumbure sul a rude tace”

 

Amatu meye wannan nake gani?

Garin Yaya hakan yasame ki??

 

Sai alokacin hawayenta suka gangaro tace”

 

Anty wannan me son Dr din ce ta tureni na Fadi a hannun…..

 

Mene??””anty zarah tafada da qarfi tana maida kallonta Kan cikin Amatun da har lokacin Bata cire cikonba tace”

 

Ta ture ki batada hankaline bataga Abinda ke jikinki bane ko so hauka ne Bari nakira Dr yanxun Nan yazo

Ita Kuma Nuratun I will deal with her later wannan ai ganganci ne.

 

Dr najin Abinda yafaru hankalinsa ya tashi gashi wani mahimmin meeting sukeyi sbd gobe shida wasu manyan likitocin asibitinsu zasuyi tafiya zuwa china gurin wani program na sati biyu.

 

Tunda zarah takirasa tafada Masa hankalinsa ya rabu biyu

Meeting din kawai suke Amma Rabin hankalinsa na gidan sanyi daya dayakeji aransa shine SALMAN yananan yadawo kwararren likitan qashi ne yasan basa buqatar zuwa koina.

 

Sai guraren 8:40 suka fito gashi Kuma yanada wani Wanda yayiwa alqawarin ganinsa idan yafito hakanan yakoma office dinsa

Koda ya Isa office din mutumin na kiransa Nan suka Fara mgnar dazasuyi ahankali yanayi Yana shafa qirjinsa da numfashinsa ke Dan sauyawa tun safe yakejin hakan Kuma yasan alamace ta ciwonsa zai iya tashi ko wane lokaci Amma meeting din yasa baisamu damar amfani da inhaler gashi idan yataso duka Dole saidai oxygen Wanda duk lokacinda aka saka Masa oxygen rayuwarsa tana cikin mugun hadari ne sbd oxygen din nabawa lungs dinsa matsala sbd dama can basuda qarfi lungs din tun haihuwarsa shiyasa shida likitocinsa sunriga sunkai qarshe akan karya taba Bari ciwonsa natashi gaba daya harya tafi qarfin inhaler ta riqesa.

 

 

Qoqarin Kama numfashinsa dake son qwace Masa yakeyi Yana dagawa mutumin Kai sbd Magana tafara son gabatarda ya dago daqyar ya kallesa Yana dannewa yace Masa yaje zai nemesa idan yadawo daga tafiya zasuyi Magana.

 

Mutumin na fita ya dafe qirjinsa cikin tsananin azabar rashin fitar numfashi idanuwansa sunyi jajir jijiyoyin kansa sunfito sosai

Hannunsa na rawa ya jawo drawer office din nasa ya Fara laluba baiji inhaler dinsa ba,

Firfito da duka kayan ciki yayi Yana watsowa cikin sauri da tsananin azabar dayake ciki baiganta ba gashi yafara loosing control din kansa sbd idanuwansa sun Fara gani dishi dishi

Da sauri ya miqe ya dauki wayarsa da keys din motarsa ya fito Yana riqeda kurkinsa ya nufi motarsa ya fada Yana tayarwa yafito asibiti saidai abin yaci qarfinsa gaba daya zuwa lokacin sbd numfashinsa daya dawo gaba daya bakinsa tuni motar tafara qwace Masa.

 

 

Daga government house yafito daga wani guntun meeting dayayi da deputy governor akan investing dasuke sonyi a sabon ZABEERA LTD dinsa dake Bangkok,

Shida malam Umar ne a motar shike tukasa

Gaba daya hankalinsa nakan wayarsa dayake duba tarin misscalls din da akaita Masa Wanda duk yawanci daga  mutanen hurdarsa ne sai sauran daga family wainda yasan dukansu bazai wuce buqatar kudi daga garesaba Wanda Sam shi ko mamakinsu baida lokacin tsayawa yayi

Misscal din zarah guda hudu ne ya kalla numbernta dayayi saving da ZB wato zarah zabeera,

Sam Bata gajiya da Kira ita duk da tasan bako yaushe yake dagawa Amma Sam taqi sabawa da hakan

Wasu mutanen suke aikata Abinda zai 6ata ransu,

Abinda tasani ya koya a rayuwarsa shine kayi rayuwa akan mizanin dazai baka nutsuwa da ease

Baya tunanin har abada zai iya jefawa ko Kai kansa ga Abinda zai baqanta ransa ya Bata Masa Rai yayi iya qunci da baqin cikin dazaiyi tun Yanada quciya Dan haka wannan babin na damuwa akan alamarinda wani zaisaka ya Dade da wucewa agurinsa

 

 

MD ga wannan kamar motar Dr khalil ce Kuma kamar dai ba lafiya ba Dan…..

 

Bai qarasa yayi saurin over taking motar Dr din sbd wani junction dazata nufa ta buga.

 

MD din ne da kansa yafito ya nufi motar Yana budewa idanuwan Khalil din na qoqarin rufewa da zafin nama ya fizgosa daga cikin motar tareda taimakon malam Umar suka kamasa zuwa motarsa da kansa ya qara sanyin AC din motar tareda fitowa cikin sauri ya zagaya ya bude gaba cikin sauri yabude can qarqashin sit din driver saigashi yaciro inhaler da sauri ya zagayo ya dago Kan Khalil din Yana shaqa Masa Amma Ina Sam ko Shiga batayi sbd numfashinsa ya tsaya gaba daya.

 

Kasa mgana yayi yafito idanuwansa na sauya ya karbi mukulli hannun malam Umar ya zagaya ya figi motar cikin mugun speed din dayasa Mutanen gurin watsewa da sauri sbd gudun tsautsayi shikuma Mal Umar yashiga motar Dr din yaja yabi bayansu.

 

 

Zabeera ya nufa Kai tsaye

Securities suna hango motarsa da yanayin da yake tahowar cikin speed yasasu saurin wangale Masa makeken gate din da mutum uku ne ke iya rufesa

Yana isowa yashige gate din Yana qara gudun motarsa yabi bangaren dama inda tacan gefen hanyar zuwa part din Khalil din yake.

 

Yanayin parking bakin part dinsa yafito ya nufi wata qatuwar flower vase dake bakin qofar shiga palonsa inda anan yasan Khalil din na aje keys dinsa.

 

Ya a budewa da bedroom dinsa ya nufa Kai tsaye sbd yasan inda allurar take

Tun daga cikin dakin ya hadota yadawo motar Yana shiga ya daga hannun Khalil din ya soka Masa tareda dannata da sauri ruwan suka shige jikinsa take yayi wani irin yunquri tareda Jan numfashi me qarfi da qara kafin jikinsa yakoma yasaki.

 

Sai alokacin MAHMOUD ya sauke ajiyar zuciya Yana ‘dan dafe goshinsa tareda lumshe fararen idanuwansa dasuka sauya kala.,

 

A duniya idan akwai mutum daya dazai iya sadaukarwa Koda rayuwarsace to shine Khalil,

Khalil ne kawai weakness dinsa a duniyar Nan sbd shikadai ne yake shiga tashin hankali akansa aduk lokacinda yaga ciwonsa yatashi sbd hakan na razana jarumtarsa Dan Khalil shine mutum na qarshe dayake baya iya tunanin ma rasawa,

A rayuwarsa he has only two dear ones,

Na farko mahaifiyarsa da har yanzu take cikin qasan ransa daya kasa cire kewarta,

Sai na biyun shine khlail,Wanda bayada wani Dan uwa dayake gani amatsayin jininsa kamarsa.

Tsananin mataki da kulawar daya daukarwa ciwon Khalil din yasa dukkanin motocinsa da office dinsa yanada ajiyayyar inhaler dayake ajewa sbd Khalil din Dan Koda ta kwana irin haka.

 

 

Ahankali yaji an dafa hannunsa

Saida yaqara rinste idanuwansa yasaki qaramin numfashi kafin yabudesu akan hannunsa da khalil din ya dafa a wahalce.

 

Kallon fuskarsa Khalil yayi tareda sakin wani wahalallen numfashi ganin duk duniya idanba ubangiji daya halacci MAHMOUD din ba Babu me iya gane kowane yanayi na MAHMOUD da Abinda yake ciki sbd fuskarsa Bata taba nunawa,farin ciki ko akasin hakan.

 

Kallonsa yayi da jajirtaccin idanuwansa cikin nutsuwa yace”

 

Koma me kake tunanin kanayi zaifi idan kadawo kanka,

You know this is stupidity right??

Menene amfanin aiki da gwagwarmayar idan Babu lafiya you better come back to your damn senses.

 

Girgiza Masa Kai Khalil yayi tareda qoqarin fitowa motar Amma bazai iyaba sbd jikinsa ba qwari Dole MAHMOUD din yakamasa suka fito yakaisa har cikin bedroom dinsa kafin yayi amfani da wayar khalil din yayiwa umme txt akan bayajin Dadi.

 

Harzai juya ya fice Khalil din ya riqo hannunsa Saida ya fidda numfashi ahankali na marasa lafiya kafin ahankali ya furta”

 

Thank you.

 

If you want to thank me be careful about your health,

Next time idan kayi Wasa irin haka yafaru ka shirya rabuwa Dani sbd i can’t take this stupidity,

U’re unbelievable Khalil

Kana likita Amma Kaine kake Wasa da lafiyarka har kake tunanin yin tukin mota cikin wancan yanayin,

Menene cikin kanka dayafi kula da lafiyarka mahimmanci????

 

Amatu.

 

Tsit MAHMOUD yayi sbd Jin zancen na Khalil a bazata.

 

Kallonsa yayi cikin zallar mamakin irin like seriously??

 

Lumshe ido yayi Yana sake maimata sunan Amatun a gajiye

Yadora da fadin”

 

MAHMOUD wallahi Amatu itace tunanin kulawa da ita yafimin lafiyata,

Acikin yanayin danake ciki Babu Abinda nake tunanin cimmawa kamar na iso gida gareta sbd tana cikin halin buqatata akusa,

Banajin yanayina kawai Abinda nakeso na iso gida alokacin.

 

Zame hannunsa MD yayi tareda miqewa Yana qoqarin barin gurin sbd idan baiyi nesa da Khalil ba tsaf zaisa a binciko Masa the best psychiatrist Dr taduba Masa shi.

 

Tashi zaune Khalil din yayi cikin dasasshiyar murya yace”

 

Amatu amanata ce idan kana qaunar ‘dan uwanka zaka kulamin da ita aduk lokacin da bana kusa

Shine kawai Abinda nake roqanka a matsayin alfarma ta har iya rayuwa.

 

Cak ya tsaya tareda kasa juyowa zuciyarsa na juya Abinda Khalil din yafada Wanda yasashi Jin wani iri saidai kawai ya wuce batareda ya juyoba Kuma baice kala ba ya ficewarsa daidai isowarsu umme tareda Nuratu da tuni hankalinta yayi mugun tashi Jin Khalil dinta bayajin Dadi.

 

 

 

Zaune zarah take a Palo tana jiran isowar Khalil din sbd tayita kira daga bayan nan wayarsa a kashe

Allah ma yasa Amatun tasamu bacci ya ‘dan dauketa.

 

Yana shigowa ta dauka Khalil dinne tayi saurin miqewa zatai Magana saitaga MAHMOUD ne fuskarsa daukeda wani yanayi na kasala da sauri ta qaraso gabansa tana cewa”

 

Sannu da dawowaยฟ

 

Kallonta yayi tareda kallon agogon dake palon yasake maido da idanuwansa kanta yayi Mata kallon minti biyu cif ahankali ya daga Mata Kai alamar amsawa cikin sautinsa me sanyi yace”

 

Haryanxu kina zaune a Palo

Akwai matsala ne?

 

Kallonsa tayi wani irin sanyin Dadi na kwaranya cikin zuciyarta harsaida murmushinta ya bayyana ta kalli cikin idanuwansa ya dauke Kai sbd Sam bayason ana kallon cikin idanunsa ahankali tace”

 

Dr nake jira nakirasa tuntuni yanzu Kuma wayarsa akashe

Amatu ce ba lafiya taji ciwo sosai a hannunta…..

 

Cak ya tsaya daga tafiyar dayakeyi batareda ya juyoba saikuma ya tafiyarsa Yana cewa'”

 

Shima bayajin Dadi bazaiso damuwa ba yanzu shima Kuma gobe tunda safe zaiyi tafiya so just handle her situation for him.

 

Wucewa yayi yabarta tsaye dafe da goshin tunanin mafita da abin Yi.

 

Ganin Amatun tasamu bacci haka ta lallaba itama taje ta shirya tayi dakin MD din saidai duk Rabin hankalinta na qasa gurin Amatu.

 

 

 

Dr Khalil kuwa asubar farko lafiya kalau yatashi da qarfinsa kamar baisamu attack din ba ajiyan,

Qarfe Bakwai na safe jirginsu zaitashi Dan haka qarfe shida da rabi yafito a shirye driver din umme zai kaisa airport

Yaso ganin Amatu Amma yasan lokacin Basu tashi ba hakanan ya hakura ya wuce bayan yayiwa zarah text tareda transfer din kudi masu kauri na kulada duk Abinda amatun ke so kafin sati biyun yadawo,

Hakama bai wuceba Saida yayi Magana da Salman akan zaije yaduba Amatu yasan matsalarta da Abinda za’ayi Mata.

 

 

 

 

Tun qarfe hudun asuba ta tashi tayita juye juyen azaba tun tana daurewa harta kasa tafara hawayen azaba tana juye juye Dan haka Koda gari ya waye anty zarah tashigo tuni idanuwanta da fuskarta sungama kunburewa sbd kukan azaba aikuwa tana ganin anty zarah din ta sake sabon kuka

Da sauri zarah ta rungumeta tana rarrashinta da Mata sannu kamar zatayi kuka.

 

Hannun har wani qyallin kumburi yakeyi shiya qara daga hankalin zarah ta kamota suka fito Palo tana cewa”

 

Dr yayi tafiya Bari nafadawa MD zamuje asibiti.

 

Tana qoqarin juyawa saiga qwanqwasa qofar Salman tareda usi bayansa Wanda Dr khalil ya roqesa akan yadaukosa aje dashi yaduba Amatu sbd tun jiyan data kirasa taqi Magana hankalinsa yake atashe.

 

Aikuwa amatu na ganinsa tasaki sabon kuka

Da gudunsa yayo gurinta hankalinsa a mugun tashe Yana cewa”

 

Amatu??

 

Zama yayi kusa da ita Yana kallon hannunta sai kawai yaji shima idanuwansa sun ciko da hawaye kamar mace saigasu suna gangarowa.

 

 

Dr salman zabeera sai suka basa dariya ya zauna Yana duba hannun Yana cewa”

 

Zarah kina ganin mutuniyarki tasa oga Usman kuka saikace ba namiji ba,

Usman dama jarumtar taka a baki take kenan.

 

Matsa hannun nata yayi da qarfi take tasaki wani razanannen ihu tana damqe hannun dataji akusa da hannunta dake Kan hannun kujera

 

Shikuma da saukowarsa kenan basusan dashiba ba yazo wucewa yaji an damqe hannunsa ya tsaya cak batareda ya juyoba sbd ko bai juyoba yasan itace sbd zafin ciwo ta riqesa batareda tasani ba

Saidai Kuma samun kansa yayi da tsayawa batareda ya qwace hannunba  yana gane radadin datake ji ta hanyar yanda ta mugun matse hannunsa.

##mamuh#

 

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 21

Advertisement   MQ 21_*  *_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA…

MIN QALB 24

Advertisement   MQ 24_*       Tafiya sukeyi ahankali cikin motarsa Babu me Magana sai sanyin AC…

MIN QALB 1 (mamuhgee)

Advertisement  *_MIN QALB_* _Mamuhgee_ 1 Bismillahir-rahamanir Raheem. Qoqarin durqusawa takeyi ta dauki busashen biredin dataga wani yaro yazo…

MIN QALB 49

Advertisement   #*_MQ 49_*       *_THE FLAVORLAND BY ACEEY_* Ina maโ€™abotan son ingataccen yaji, Different Flavors…

MIN QALB 45

Advertisement   MQ 45_*    Sai Bayan sallar asuba jirginsu ya sauka Nigeria ta dayake ta Kira USI…

MIN QALB 6

Advertisement  *_MIN QALB 6_* Wani ‘dan murmushin mamaki haj Maryam tasaki tana miqewa tsaye bayan ta ajiye qaramin…