MIN QALB 25

Advertisement

 

MQ 25*_

 

 

Saurin dauke idanuwanta tayi tana juyar da kanta zuwa wani gefen tana cigaba da dariyarta ta firar dasukeyi da Salman Wanda shima ya lura da yanayinda Amatun tashiga sai ya basar kamar yanda itama ta basar suka fito suna cigaba da zancensu.

 

Gurin MD din ya nufa ya bude Masa mota ya fito Yana gaidashi tareda fada Masa saqon Dr khalil daya basa sbd yakasa samun wayoyin MD din duka.

 

Advertisements

Itadai gaba tayi tashigewarta ko Palo Bata tsayaba sbd sanin ciki sukayo

Anty zarah ce ta tsaya tai Masa sannu da zuwa ganin Salman yasata itama wucewa sbd yanda ya amsa kamar bazai amsa ba karya kwafsa Mata gaban Salman din itama bedroom dinta ta wuce Kai tsaye sbd dukkaninsu suna buqatar wankene kawai Dan ko yunwa basa ji Dan Babu  kalar cimar dasuke buqata wadda Salman be siya musu ba Wanda kusan hakan yasa tafarajin qaiqayin ciwon Abinda rayuwarta take ciki na rashin kulawa daga kowa musamman mijinta Wanda shine yakamata ace ya jiyar da ita dadi da nushadin rayuwa amma Bata samu hakan daga kowa ba sai yanzu sanadin Wanda batamasan meye ake Kira gata da arziki ba a rayuwa gashi ta sanadinta suna nishadantuwa da rayuwarsu da Basu San komaiba sai bin umarni da oda.

 

 

Wanka tayo ta shirya cikin kayan baccinta ta sanya dogon hijab tayi sallah tana idarwa taje ta dauko yoghurts a fridge ta zuba cikin cup ta qara Masa madarar gari sosai ta juya sosai tadawo daki tana Sha tana daukarwa Dr khalil hotunan lallenta tana tura Masa saigashi yakira.

 

Daukar wayar tayi tana murmushi qasa qasa tace”

 

Kai Dr baka shanye rada ba.

 

Wani siririn numfashi ya sauke Wanda yasata aje spoon din hannunta  cikin kulawa tace”

 

Advertisements

Yadai???

Lafiya najika kamar kana bacci?

 

Murmushi me sauti yasako Mata Yana gyara kwanciyarsa da lullubinsa yace”

 

Lafiya kalau kawai sanyin garin Nan ne yafara tabani tun satin daya gabata  garin qasar ta daina shafamin lafiya Amma ai alhmdlh tunda gobe zamu dawo.

 

Ajiyar zuciya ta sauke tana cigaba da Shan yoghurts din tace”

 

To Meyesa zaka zauna harka Dade haka a inda baya shafa maka lfy???

Gwara da gobe zaka dawo da yau saina daga maka hankali kabaro.

 

Murmushin qarfin hali yayi Yana cewa”

 

Gobe idan nadawo me Kika ajemin?

 

Wani juyi tayi tareda kifewa kan carpet tace”

 

Saika dawo zaka gani.

 

Fira sukeyi ahankali sbd yanayin yanda yakejin jikin nasa sbd sanyi ya shigesa sosai Wanda yafara yiwa lafiyarsa barazana Dan yanaji ciwonsa yafara tashi ahankali.

 

 

 

****Miqewa Nuratu zabeera tayi daga zaunen datake a cikin restaurant din blue fox tana juya envelope din data karba tana sakin wani irin qyayataccen murmushi tace”

 

Manager kayimin Abinda zai juya rayuwata nasamu Abinda nakeso kaima kasamu wadda kakeso,

Wannan taimakon naka yabani farin cikin danayi shekaru bansamu ba sbd Dr khalil zabeera shine farin cikina,burina dakuma zuciyata…

 

Kallonta yayi tareda miqewa tsaye yace”

 

Ina fatar zan mallaki Amatu kamar yanda kikaimin alqawari??

 

Karka damu idan ka iya takunka zakayi amfani da damarka ka sameta daga lokacinda aka watsota daga rayuwar farin cikina da zabeera ma gabaki daya.

 

Barin gurin tayi tana sake riqe envelope din farin cikinta na qaruwa ta nufi motarta tashiga ta rufe..

 

Bayan ta zauna cikin motar kallon envelope din tayi tana cewa”

 

AMATULLAH K SALEH wannan shine asalinki tun kina Yar bolarki har zuwa yanzu,

 rayuwar alfaharinki tazo qarshe,

Kinyi kutse a tsakanin masoyanda ba’a iya rabawa sbd son danakewa khalil hankalinkima bazai daukaba bare ki iya rabamu,

Kina alfahari da kanki dakuma gatan da Kika samu daga Khalil, Modibbo da Andi ma gaba daya

Zan ruguza rayuwarki gabaki daya sai nasaka kowa ya tsaneki fiyeda yanda tunaninki zai dauka,

Ki shirya komawa rayuwar sata da dauke dauken da Kika fito bayan kinyi shari’a da familyn ZABEERA na Bata sunan da kikaso yimusu.

 

Cikin handbag dinta ta sakashi ta ajiye jekar gefenta tareda tayarda motar tabar gurin cikin mugun speed Dan amatse take data Isa zabeera sbd so takeyi kafin Dr khalil zabeera ya iso an dade da korar Amatun daga rayuwarsu,

 

Agogon motar ta kalla taga qarfe biyar  ta yamma takusa gashi guraren yamma jirginsu Khalil ake sakaran zai sauka,gudu taqarawa motarta tana kallon titi.

 

 

 

 

***Cikin riga da skirt na lace maroon tayi adonta tareda daura dankwalin lace din ta sanya Yan kunne marasa tsawo sosai kalli agogo tana zama bakin gado da wayarta a hannu tana daukar hoto tace”

 

Kowane lokaci yanzu Salman yace Dr zasu iya saukowa Meyesa yau nakejin wani iri cikin raina kamar inajin kunyarsa ne kokuwa wani abin daban.

 

Shiru tayi gabanta na ‘dan faduwa taji duk batajin sukuni ta miqe tana ajiye wayarta gefen gadon ta miqe tareda fitowa zuwa Palo gurin anty zarah ko zata debe Mata yanayin da fira.

 

 

Tana fitowa anty zarah na fitowa daga nata bedroom din sanye da doguwar Turkish abaya red itama tayi kyau sosai sai qamshi takeyi kamar Amatun sai abin yabasu Daria kusan atare suka saki dariyar Zarah na cewa”

 

 

Wannan da kishiyoyi muke bansan wa mijin zai Fara kalla ba sbd kalar duk jajaye ne Kuma kalar ja idan ba mantawa nayiba tana cikin kalar da MD ke tsananin so sbd ance kalar kayan mahaifiyarsa kenan kafin ta rasu sbd sarautar da mahaifinta yataba Yi.

 

Kallonta Amatu tayi tanayin shiru cikin tunanin kalamanta aranta tace”

 

Anty zarah Allah yasa kada ‘yan Amin na kusa su karba Miki zancenki sbd ita Magana ana fadarta ne da fatar ‘yan Amin su amsa shiyasa ake cewa kafada alkhairi ko Kayi shiru.

 

Wucewa gaba anty zarah din tayi Amatu naci gaba da binta da kallo zuciyarta na sake shiga fargaba saita kuma komawa daki zata zauna kenan saiga Kiran wayar Salman da sauri ta dauka Dan dama shi zata Kira ya debe Mata kewar tunaninta..

 

Salman ka……

 

Muryan Dr khalil taji yace”

 

AMATULLAH.

 

Wani irin sanyi da farin ciki taji ya kwaranya cikin ranta batasan lokacinda tasaki wani irin qaya taccen murmushi ba tana furta” Alhamdulillah ya Allah.

 

Har cikin ransa yaji dadin hakan ya kashe wayar tareda miqawa Salman batareda yace komaiba suka kamo hanyar gida.

 

 

Koda suka iso gida a gurin ummensa ya sauka Dan itama a matse take da ganin Dan nata musamman sbd kwanakin wata sabuwar qauna da kewar danta ke kamata shiyasa itama a matse take da taga abinta Nan aka hau hidimarsa kayan abinci da snacks kala kala anyi Masa taredasu fruits dasu fura duk dai wasu kayan marmarin kewar gida anyi Masa Nan yaci abinci tareda ita da Haj maryam da salman da Nuratu wadda koda ta iso gida kusan ataredasu Khalil din ta shigo Dan motarsu na gaba kafin Tata

Ganinsa yasa takasa riqe farin cikinta da zumudinta tama manta da Abinda tadawo dashi Nan ta zauna cikinsu anacin abincin tana faman kula da duk motsinsa da Abinda yake so iyayensu kuwa sai washe baki sukeyi sbd dama shine burinsu hada Khalil din da Nuratu.

 

Bai bar gurin umme ba sai magriba ya wuce gurin Modibbo acan sukai sallah taredashi da salman da MD ma Wanda ya shigo ana magribar.

 

Bayan sungama sallah anan suka zauna tareda Modibbo Yana tambayar MD Amatu sbd duk yau da jiya Bata Zo ta gaidashiba kamar yanda ta Saba shiru MD din yayi Yana Dan sauke Kai yace”

 

Inshallah duk suna lfy sbd Nima na kwana biyu bana zama gobe ma insha Allah Nima zanyi tafiya zuwa Germany.

 

Allah ya taimaka ya tsare yabada sa’a Kuma.

 

Amin dukkaninsu sukace suna qoqarin miqewa cikin sautinsa me saka nutsuwa yace”

 

Khalilu matarka Ina saka ran a lissafi saura wata uku haihuwarta ko???

 

Tsit sukayi dukkaninsu su ukun

Take zufa tafara Dan tsatsafowa Khalil din MD kuwa fararen idanuwansa ya zuba Masa Yana jiran jin amsar da Khalil din zai bada sbd shidai wadda ake maganar cikin akanta tana zaune gidansa Amma baitaba ganin ciki a jikinta ba gashi ana maganar saura wata uku haihuwa.

 

Dan gyara murya Khalil yayi cikin girmamawa yace”

 

Inshallah haka ake saka Rai saidai cikin yazo da tangarda ne sbd rashin girmansa ya bayyana cikin baida lfy inasaka ran ma gobe zanje da ita asibiti musake dubawa.

 

 

Cikin watanni da dama baa fada baida lfy ba sai yanxu?

 

Sarqewa Dr khalil din yayi Yana Dan gyara murya yace”

 

Ayi mini afuwa Modibbo nayi kuskuren rashin sanarwar.

 

Shikenan ba damuwa kuje Allah ya Bata lfy.

 

Amin”Khalil din yace suka miqe suka fito tare suna tafiya zuwa hanyar sashensu dayake direction guda.

 

Tafiya sukeyi su biyu Banda salman daya wuce ya nufi motarsa yafita zabeera ahankali kowannensu shiru Babu me mgn dama sun Saba haka suke koyaushe idan suna tare saisun jima shiru kafin su Fara mgn Wanda MD ne me wannan halayyar shikuma Dr khalil Yana girmama kowane irin Hali da MD ya zabawa kansa da rayuwarsa.

 

Tsayawa yayi ahankali batareda ya juyo ya kalli khalil dinba yace”

 

Bansan wane mataki ka dauki wannan alamarin ba Amma ya kamata kasan kana saka kanka cikin hadari along with her.. ‘dan shiru yayi kafin ya juyo ya kalli khalil din cikin wani irin yanayi yace”

 

Atleast kayi tunanin Hali da Abinda zata fuskanta kafin kasata a irin wannan tight spot din sbd yanxu ku duka Kuna situation dinda only God can help so kafin komai ya fita hannunka kasan Abinda kakeyi ka dawo daidai,the truth doesn’t cost anything but a lie could cost you everything.

 

Kallonsa Khalil yayi tareda sauke ajiyar zuciya cikin damuwa yace”

 

Bansaniba ko kasan Abinda nake qoqarin boyewa Amma bazaka iya fahimtar dalilina nayin hakan ba sbd komai yazone alokacinda banyi tsammaninsaba Babu mafita bayan wadda na dauka a wancan lokacin da yanzu ma..

 

Denying the truth doesn’t change the fact cewa ka dauki hanya Mara bullewa,

Ka zauna kayi tunani zaka samu wata mafitar wannan batayi ba.

 

Yana Gama fadar haka ya wuce gaba batareda ya juyoba yayi hanyar sashensa.

 

Shiru Dr khalil zabeera yayi yana tunanin maganganun MAHMOUD din wainda suka sakashi zurfin tunanin sbd tabbas qaryarsu takusa qarewa wadda idan bai nemo mfitaba asiri ya tonu to daga Ummensa har Amatu dashima suna cikin matsalarne,

Babban burinsa daya dawo dashi shine maganar auren Amatun tukuna sbd duk wasu kayayakin aure na akwati ya siyosu yazo dasu saitin akwatinsa cif ya hado kayan aurensa Wanda ko gidan bai kawosu ba daga airport gidansu kawu suka Fara ajiyesu kafin su qaraso gida.

 

 

Ajiyar zuciya ya sauke kafin shima yabi Bayan MD din zuwa ganin Amatu da tun Yana gurin umme take kiransa yaqi dauka sbd kada farin cikin ummen ya gushe.

##Mamuh#

 

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 6

Advertisement  *_MIN QALB 6_* Wani ‘dan murmushin mamaki haj Maryam tasaki tana miqewa tsaye bayan ta ajiye qaramin…

MIN QALB 36

Advertisement  MQ 36_*  Umme da kanta tabata abinci abaki taci tana qara jinjina zancen Dr Fatima data fada…

MIN QALB 35

Advertisement   MQ 35_*   Godia kawu yasake kafin ya sake gyara zama bayan fitar MD yace”  …

MIN QALB 37

Advertisement   MQ 37_*     *_kina da burin koyon sana’a wadda zaki yita daga gida a sauqaqe_*…

MIN QALB 44

Advertisement   ****** Zama tayi a palon zuciyarta na wani irin tiririn takaici da baqin cikinsu su dukan…

MIN QALB 9

Advertisement  *_MIN QALB 9_* _mamuhgee_ Gabaki ‘daya hankalinsa nakan fuskar amatu da ita Kuma hankalinta nakan usi da…