MIN QALB 26

Advertisement

 

26_*

Zaune suke a Palo itada anty zarah anty zarah na Mata fira Dan sakata nishadi ganin duk tazama so serious Wanda Sam kowa yasan ba halinta bane tafi sabawa da hayaniya shiyasa duk inda take to hayaniya na gurin.,

 

Ana bude qofar palon atare dukkaninsu suka kalla qofar shigowar kowacce fuskarta daukeda murmushin yiwa Dr khalil din maraba Musamman Amatun da murmushinta na yau ya banbanta Dana kullum sbd yau sauran zuciyar Khalil takeson qarasa sacewa sbd ta zamo Tata ita kadai shiyasa yau komai nasa na musamman ne agareta saidai sabanin ganin fuskar Dr khalil zabeera a cikin idanuwan MAHMOUD ZABEERA idanuwanta suka sauka murmushinta me sanyi da tsada akan fuskarsa yafara sauka gabanta yayi mummunan faduwa ta hadiye sauran murmushinta fuskarta na sauya cikeda mamaki da fargaba da sanyin jiki..

 

Tsayawa yayi kallonsu fuskar na bayyanarda mamakinsa daba’a cika ganewaba ganin yanda dukkansu suka waiwayo suka zuba Masa Ido kowacce fuskarta daukeda murmushin daya mugun daukar hankalinsa da sakashi wasi wasin mamakinsu musamman Amatu datafi bayyanarda murmushinta da dukkanin farin cikinta dabai taba ganiba,

Advertisements

Ganin Ahankali Amatu ta dauke idanuwanta dake cikin nasa tana kallon bayansa murmushinta da farin cikinta fiyeda na farko Yana dawowa yasashi dawowa MD dinsa ya sauke boyayyan numfashinda Babu Wanda yaji ya Fara takowa ahankali idanuwansa na sauyawa cikin wani boyayyan yanayin dayake ciki sbd sai alokacin ya fahimci Khalil ne keda wannan murmushi da farin cikin,

 

Zama yayi Kan couch din dakinsa Yana rintse idanuwansa tareda yamutsa kansa yanajin wani irin zafi na ratsa dukkanin jikinsa

Take kuwa zufa ya kakkaryo Masa Tako ina bayan ga kukan AC Nan yanaji yasan a kunne yake….

 

Zarah ya tuno da itama taketa washe baki tana murmushi to idan ita waccar tayi Dan Yana sunan  mijinta to itafa???

 

Jin kansa ya dauki zafi Yana neman saukewa zarah laifin sai kawai ya miqe ya fada toilet yayo wanka yayi clearing mind dinsa ya shirya cikin kayan bacci ya dauki laptop yafara wani aiki Yana basar da tunanin komai da kowama.

 

 

 

Dr khalil kuwa duk yanda yake tunanin Amatu takai cikin ransa sai yanzu yake gane ta wuce Nan sbd wannan murmushin datake jifarsa dashi yagama hargitsa Masa Kai da tunani.,

Advertisements

 

Zama yayi bayan sungama gaisawa da zarah ta wuce tabasu guri ya juyo suna fuskantar juna Yana kallonta cikin kulawa yace”

 

Hw are you AMATULLAH???

 

Zuba Masa idanuwanta tayi har lokacin murmushinta bai daina fitaba tace”

 

Nayi fushi ka koma na barwa Nuratu.

 

Wani irin Dadi yaji ya kamasa me sanyi cikin nutsuwarsa yace”

 

Kishi kikeyi ita tafara tarbona???

 

Harara ta sakar Masa tana cewa”

 

Zanyi maka kuka idan kasakemin maganarta.

 

Kallonta yayi Yana cewa”

 

Ok tom yanzu duk wannan adon sbd zandawo akayisa?

To Meyesa baki shafamin Dan lipstick dinnan naku danaga ana sakawaba Nuratu tasaka ita……

 

Miqewa tayi a fusace tayi dakinta Yana kiranta ko waiwayosa batayiba tana shiga gaban mudubi ta wuce Kai tsaye

Ta dauki janbaki hot red tashafa a bakinta tana kallon madubin saikuma taga tayi kyau saita dauki turare taqara fesawa tadawo palon tana kallon yanayin dayake kallonta fuskarsa na bayyanarda farin ciki sosai sai taji farin ciki yakamata sbd ganin ta kyautata Masa shiyasama take nuna kishin Nuratu sbd ganin hakan na sanyasa farin ciki.

 

Cake din datayi da fruit drink dominsa taje ta dauko takawo Masa Nan suka Fara fira cikin nutsuwarsa yake cin cake din duk da a qoshe yake Amma sbd itace tayi da kanta yakeci cikin alfahari.

 

Sai guraren qarfe goma yabar part din ta rakosa har waje kafin tadawo ciki ta wuce dakinta tanajin farin ciki kamar bazata iya bacci ba yau din.

 

 

Washe gari ataredasu Dr khalil din yayi breakfast kafin suka fita tare harda Dr Salman daya Fara aiki asibitin Dr khalil kafin ya kammala shirye shiryen sa danshi ba anan qasar yakeson aikiba.

 

Gidansu kawu suka Fara zuwa tunda ta Isa gidan kowa ke Mata wani irin kallon burgewa suna tayata murna Wanda yasata sakin baki tana kallonsu cikin mamaki.

 

bakin dakin iyami tagan akwatina a jere tsaf su maman junior sai washe baki sukeyi suna budewa iyami ma yau bakin Nan har kunne sai annashuwarta takeyi tana sake bubbudewa su maman junior kayan suna gani suna shewa.

 

tsayawa tayi tana kallonsu cikeda mamaki kafin ta juyo ta kalli su Dr khalil dasuka tsaya qofar shigowa suna Magana da kawu Wanda shima yau harda saka babbar rigar farar shadda wadda itama Dr khalil ne ya dinko mishi su kusan kala bakwai.

 

Sake juyowa tayi gurinsu iyami da suke Mata barka da zuwa Maman junior kuwa rawa tahau Yi tana janyota tana waqarsu ta yarbawa tana cewa”

 

Amatunmu tasamu mijinda zai Bata farin ciki da suna me girma na mutunci.

 

Kallon rashin fahimta tayi Mata gabanta na mummunan faduwa ta qwace da sauri zatayi Magana iyami datasan Abinda zata iya fada tayi saurin cewa”

 

Kayan Dr khalil ne jiya da daddare aka kawo.

 

Kallon iyamin tayi da sauri tareda juyawa ta kalli inda suke Magana da kawu Yana Dan sato kallon inda suke Dan yaga reaction dinta..

Wani irin farin ciki Mara misaltuwa ya shigeta da sauri ta rungume maman junior tana cewa”

 

Alhamdulillah ya Allah.

 

Dariyar farin ciki iyami ta sake tana sake sakawa Khalil din albarka sbd duk iya bincike kawu yayi akansa Kuma sun Dade da yaba nutsuwarsa da halayensa sbd a wannan zamanin basu taba haduwa da yaro me nutsuwa ba kamar Khalil din,

Shiyasa Babu wani dogon janye janye na al’adu kawu yabasa auren Amatun kawai waliyan Khalil din yake jira idan sun daidaice da khalil din sbd Khalil ya sanar dashi akwai Yar hayaniya a zuriar tasu idan ta lafa zasu zo idan Kuma akasin hakan ne ya amince asamu waliyai a daura musu aure.

 

Zama tayi gefen iyami ta bude kayan tsaf taga abinta tana sake Jin inama gobene ranar auren ayi kowama ya huta.

 

Ciki su Dr khalil din suka qaraso suka gaida iyami tareda gaisawa da sauran mutanen gidan suka koma waje suna jiran Amatun tagama ganin kayan su fito.

 

 

Kusan awa biyu ta Bata kafin ta fito suka wuce asibiti inda ya ajiyeta a office dinsa suka Shiga meeting tayi zamanta tareda miqewa a kujerarsa tana game a wayarsa daya barmata wadda kyakkyawan hotonta yake shimfide lock screen dinsa na ummensa Kuma a main screen dinsa sai hakan yasaka jikinta yin sanyi sbd a rayuwar Khalil yanzu duk Wanda yasansa yasan itada ummensa sune sanyin zuciyarsa da idaniyarsa Amma Kuma gashi Sam ko inuwa daya basa zama a taqaicema ummen Babu Wanda ta tsana a rayuwa kamarta ita Kuma Babu wadda take ganin ta rainawa wayo kamarta

sai kawai taji Bata girmama soyayyar Dr khalil dinba.

 

Sai qarfe uku suka baro asibiti sai kawai suka wuce gurin cin abinci a 5star daganan ma gurin shopping suka wuce sai gab da magrib suka shigo zabeera

Kai tsaye sashen ummensa ya nufa tana ganin sunyi parking bakin flat din tayi saurin kallonsa shima ita ya kalla Yana cewa”

 

Inason ganin Mata biyu masu mahimmanci gareni sun zama daya wannan shine babban fatana,

Amatu please kiyi hkr da duk Abinda umme ke Miki ki Bata dama kigani tanada zuciya me kyau,

Abinda nasani shine duk Abinda nakeso ummina na sonshi bare ke datasan Ina Miki tsaftatacciyar so Wanda bazan iya dainawaba

Dan haka nasan zata soki wata Rana ko Ina Raye ko bana Raye nasan wata Rana saita soki kamar yanda takesona,so please AMATULLAH ki qaunaceta ki kulamin da ita I promise you wata Rana zata daina tsangwamanki zata qaunaceki kamar yanda take qaunata.

 

Wani irin sanyi jikinta yayi sosai saitaji kunyarsa ta kamata ta dago a sanyaye ta kallesa ya da yayi saitaji kamar Bata girmama soyayyarsa ba tunda takasa girmama mahaifiyarsa.,

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali cikin sanyi tace”

 

Inshallah Zan kiyaye zancenka daga yanxu zanyi iya qoqarina gurin kyautata Mata.

 

Numfashi ya sauke ahankali yace”

Thank you AMATULLAH.

 

Fitowa sukayi suka nufi ciki Yana gaba tana gefensa jiki a sanyaye take tafiyar sbd yanayinsa duk ya Gama sanyayata ga wani irin damuwa daya shigeta ga faduwar gaban yanda zasuyi da ummen Amma koma menene tayi alqawarin jurewa sbd shi.

 

A palon farko dasuka shigo take qoqarin zama ya tsaya tareda juyowa ya kalleta yana girgiza Mata Kai tareda cewa”

 

Follow me.

 

Falonta na qurya suka nufa Wanda dagashi sai bedroom dinta Yana gaba tana bayansa.

 

Zaune take tana kallon wani Shirin girke girken larabawa da akeyi a mazzika taji shigowarsa tareda sallamarsa ta juyo fuskarta daukeda murmushin dake bayyanarda girman son datakewa Dan nata sai idanuwanta suka sauka akan wadda ke bayansa ta hadiye sauran murmushinta fuskarta na sauyawa zuwa bacin Rai da fushin ganinta ta tsuke fuska sosai tana dauke Kai daga bakin qofar.

 

Tsayawa Amatu tayi daga Inda take tana sauke Kai ganin irin kallon qyama da tsanar da ummen ke Yi Mata,

 

Qarasowa yayi gefen ummen ya zauna Yana kallon fuskarta data canza yaji ransa yaqara jagulewa ya sauke wani irin numfashi Mara Dadi Yana dafa hannun ummen cikin kulawa da sanyin jiki tareda sautin daya sakasu kallonsa duk su duka biyun yace”

 

Umme Meyesa Zaki dauki halayyar daba naki ba¿

Shin Amatu tanada wani banbanci ne da sauran mutane da Kika zabi qyamarta ita kadai?

Umme Amatu matar dazan aurace sbd Ina sonta da dukkanin zuciyata

Shin umme kodan son datakewa dan naki bazaki qaunacetaba kodan hakan?

 

Girgiza Kai tayi tana danne 6acin ranta ta kallesa tace”

 

Khalil kadaina cewa tana sonka wannan bayan kudi duk duniya Babu yaren datake ganewa,

Wannan Babu wani buri a rayuwarsu Bayan samun kudi ta ko wane halin Yaya,

Kudine kawai agabanta ta yanda zata iya yin komai akan kudi ciki ina fada maka harda mutuncinta zata iya siyarwa akan kudi,

Wlh khalil kaima sbd kudinka take sonka da bakada kudi bazata taba sonkaba

Irin wannan matar kakeson nabari ka aura Khalil???

 

Dagowa yayi ya kalli Inda Amatun ke tsaye cikin wani irin yanayi na damuwa ya sauke ajiyar zuciya tareda cewa”

 

Zo AMATULLAH,

Zo Nan kusada umme.

 

Kallon ummen tayi taga ko kallon inda take Bata qaunar Yi sbd qiyayya ta tako ahankali tazo gefensa ta zauna ahankali Kan carpet din dake gurin tana sauke kai maganganun ummen na sake jujjuyawa cikin kanta.

 

Numfashi ya Kuma saukewa cikin wani irin yanayi na damuwarsa dake bayyane wadda tasa dukansu su biyun kallonsa yasake riqo hannun ummen cikin sanyin murya yace”

 

Ummen banfara son AMATULLAH ba Sai danasan asalin wacece ita,

Nafara sonta ne bayan nasan batada kowa aduniya,

Banfara sonta ba saidanasan a bola ta tashi acan tayi wayo ta koyi gwagwarmayar rayuwa,

Banfara tsananin sonta ba saidanasan irin wahalalliyar rayuwar datayi amatsayin almajiri Mara yanci Wanda ta rayu cikinsu amatsayin namiji bayan tana matsayin mace,

Amatu bakowa mace face yarinyarda wasu bayin Allah suka taimaka suka daukesu Bayan sungama wahalalliyar rayuwa acikin bola da mataccin gidaje da shagunan daba’a gamaba,

Babu Wanda yataba kallonsu da idon Rahama,

Babu Wanda yataba duba yanayin shekaru da jinsinta amatsayin mace ya taimakesu,

Sun kwana da yunwa suntashi da ita,

Sunyi sata dan suci suyi rayuwa,

Maza da yawa sunyi yunqurin lalata rayuwarsu da sunan taimakawa shin umme Wanda yake ciki irin wannan qaddarar Dan yayi sata dan yaci ya Hana kansa Zina illa ne dahar za’a gujesa??????

 

Umme wallahi tallahi ina tsananin son AMATULLAH da dukkanin zuciyata bansan ta Yaya zanyi Miki bayani ki qaunaci Amatu ba,

Na shirya auren AMATULLAH na zamo gatanta itada zuriarta Wanda Babu wani Abu dazai sauya niyata akan hakan,

 

Shin umme kintaba zaunawa kinyi tunanin irin tarin Lada da farin cikin dazaki samu aduk lokacinda Kika kawo murmushi da farin ciki a rayuwar marayu?

Umme tarin ladace me yawa wadda zata iya gyara Miki ko wanke kurakurenki Kuma yabaki nutsuwar zuciya da ruhi….

 

Zuwa lokacin Amatu kuka takeyi sosai sbd Bata taba sanin khalil yasan asalinta ba daduk halinda suka Shiga arayuwa Kuma ahakan yake sonta tabbas yagama bawa rayuwarta girgizar data sauya zuciyarta akansa gabaki daya.

 

Umme ma hawaye takeyi sosai tsananin so da qaunar danta na ratsata…

 

Ahankali ya zamo qasa ya durqusa gabanta tareda riqo hannuwanta idanuwansa dasukai laushi na kallonta a karye yace”

 

Umme ayau gani na durqusa a gabanki Ina roqonki daki ajiye dukkanin wani burin rayuwa ko komawa Allah kodan samun nustuwar zuciya,

Umme Ina roqonki da ki qaunaci Amatu ki da zuciya daya sbd bazan iya ganinku acikin halinda kuke cikiba,

Umme……

 

Bata Bari ya qarasa ba tayi saurin dagosa tana rungumesa hawayenta na qara tsiyayowa tace”

 

Nayi maka alqawari Khalil wlh Babu wani al’amarin duniya dazan sake Bari na 6ata akansa,

Idan dai Amatu ce Kuma wlh na amince maka bazan qara qintaba idan har na tabbatarda har zuciyarta itama take sonka….

 

Rungumeta yayi da sauri Yana cewa”

 

Thank you ya umme.

 

Share Mata hawayenta yafarayi tareda juyowa ya kalli Amatu dake kuka sosai ahankali tanajin Sam Bata cancanci soyayyar khalil ba,

Zuciyarta batayi Mata adalci ba son wani ‘da namiji a zuciyarta Wanda ba khalil ba…

 

Ahankali yakamo hannunta ya dawo da ita gefen umme dake kallonta cikin wani irin sabon yanayi ya zaunar da ita ahankali yace”

 

Amatu ga amanar ummi na ki kular min da ita amatsayinki na matar ‘danta.

 

Dago jajayen idanuwanta tayi ta kallesa kafin ta kalli ummen ta daga Kai ahankali takasa cewa komai sai binsa takeyi da Ido zuciyarta na karban zazzafan baqon yanayi akansa  Wanda ta tabbatarda sone me zafi.

 

Murmushi umme tasaki ahankali tareda kallon Amatun tana nuna Mata gefenta tace”

 

Kimin alqawarin zaki so shi fiyeda yanda yake sonki??

 

Murmushinsa me nutsuwa ya saki Yana kawar da zancen da cewa”

 

Umme wannan son Kaine zakice ta Soni fiyeda yanda nake sonta sbd bazata iya Sona yanda nake sontaba nawa me girma ne.

 

Murmushi sukayi Banda Amatu dake Jin wani babban al’amari me girma atareda ita hakanan taji gabaki daya nutsuwarta na barinta.

 

 

Haj maryam da Nuratu dasuka jima Bakin qofar palon suna jin dukkanin Abinda yafaru baqin ciki me girma yarufe zukatansu da idanuwansu musamman nuratu data gama zaucewa a fusace ta juya tana qoqarin sakin ihun baqin ciki da zuciyarta dake neman tarwatsewa da gudu Haj maryam tabi bayanta tana cewa”

 

Yau tunda Kika juyamin baya Aisha akan danki kowa ya shirya tashin hankalin dazai biyo daren Nan Dan wlh yau sai takardun asalin Amatu sun kwana a hannun Modibbo da Andi.

##mamuh#

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 11

Advertisement  _*MIN QALB 11*_ _mamuhgee_ Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins…

MIN QALB 18

Advertisement   *_MQ 18_* _Mg_       Koda anty zarah tace yazauna suyi breakfast tare baiso karya…

MIN QALB 39

Advertisement   MQ 39_*     Direct wani kebantaccen guri suka nufa daga bayan joint din inda aka…

MIN QALB 36

Advertisement  MQ 36_*  Umme da kanta tabata abinci abaki taci tana qara jinjina zancen Dr Fatima data fada…

MIN QALB 42

Advertisement   MQ 42_*     Da lakabe anty zarah takai kanta cikin daki sbd dishi dishi da…

MIN QALB 46-47

Advertisement   MQ 46/47_*     _INA MASU SHA’AWA DA QAUNAR KARANTA LITTAFIN DAZAI SANYASU CIKIN NISHADI DA…