MIN QALB 34

Advertisement

 

MQ 34_*

 

 

 

 

 

Fuska kawu ya sake bayan isowar MD yace”

 

Advertisements

MAHMOUD sannu da qoqari mungode sosai Allah yasaka yayi muku albarka duk ku duka Allah yaji qan Khalilu yayi Masa rahama tareda albarkar Abinda yabari a baya.

 

Amin kowannensu yace jiki a sanyaye kafin umme ta Dora da fadin”

 

MAHMOUD kayi Magana da kawu Dan Allah yabar Amatu harta haihu tukuna ayi maganar tafiyarta.

 

Miqawa zarah takardar dake hannunsa Wanda Fatima tabayar kafin ya kallesu cikin rashin son Jan dogon zance yace”

 

Kutafi zamuyi mgn da kawun Zan wuto da ita idan angama.

 

Kallonsa umme tayi tana miqa dukkanin yardarta akan cika maganarsa na zai dawo da Amatun zabeera idan sun barta.

Advertisements

 

Ahankali ya gyada Kai Yana Dan rufe Ido.

 

Kallon Amatun umme tayi jiki a matuqar mace tace”

 

Ina jiran dawowarki Amatu.

 

Gyada Mata Kai tayi tana murmushin Bata qwarin gwiwa kafin ta kalli anty zarah da ita tayi wani iri tace”

 

Anty ZARAH saki fuskan Mana saikace Rabin ranki ne akace za’a tafi dashi.

 

Guntun murmushi anty zarah din tasake tana Dan hararar Amatun tace”

 

Kina tunanin MAHMOUD zai barni yatafi wani gurin bayan tafiye tafiyensa?

Kece dai abin jimamin sbd ba’a shiga Zabeera family a fita saidai mutuwa””taqarasa tana dariyar Amatun qasa qasa.

 

Tafiya sukai suka bar Amatun taredasu iyami dasu kawun Nan kawun da MAHMOUD suka kebe sukai magana sai gashi sun wuce a motar Salman sun barta tareda MAHMOUD din

Batareda yayi Mata kallo biyu ba ya nufi motarsa bayan yace suje.

 

Drivernsa ita yafara budewa mota tashiga kafin ya zagaya ya budewa MD din yashiga ya rufe yafada motar shima ya tayar sukabar gurin.

 

Jinginar da kanta tayi baya tareda lumshe ido ta sauke numfashi ahankali sbd imperial majesty dinsa daya gaurayu da AC dakuma qamshin motar saiyake Bata nutsuwa sbd dadinsa.

 

Shikuma wayarsace datai ringing ya dauka yafara waya cikin nutsuwa a harshen turancin dayasata Dan bude Ido kadan ta saci kallonsa sbd ya tuno Mata da Dr khalil dinta idan Yana turanci zaunawa takeyi ta zubawa bakinsa Ido cikin burgewa da son koya sbd abin na matuqar burgeta tana sha’awar zama Yar gayun Yar Boko me zuba turanci Wanda tasan da Dr na Nan da yanzu tafara karatu Inshallah.

 

Ajiyar zuciya ta sauke afili Wanda yasashi Dan waiwayowa kadan ya kalli gefenta kafin yaci gaba da wayarsa.

 

Har bakin qofar palonsu motar ta tsaya direban yafito da sauri ya zagayo ya bude Mata batareda ta juyo ta kallesaba tace”

 

Nagode””ta fice ta shige palon tana sauke numfashi sbd atakure take cikin motar ko dogon motsi bakada ikon Yi kamar an takura Masa ne shiyasa ko matarsa zarah wata ran basa kwana tare sbd yawan juye juyenta da motsi Wanda ke hanasa bacci ko kadan hakan Kuma na saka Rabin kansa ciwo.

 

A palon ta tararda anty salamatu na qoqarin ajiye abincinda tafito dashi daga kicin akan dinning itada shafa’atu me aikinta.

 

Wecewa tayi dakinta Kai tsaye tayi wanka da ruwan dumi sosai kafin ta fito ta sanya jallabiya tayi sallar magriba da akayi suna hanya tayiwa mijinta addua sosai cikin farin ciki da walwala take sbd cikin jikinta ya dawo da duk wani farin ciki datake tunanin ta rasa Dan kuwa Dr khalil dinta Jin take kaman yadawo sbd tasamu Abu mafi soyuwa daga garesa.

 

Shafa cikin tayi bayan ta miqe ta zauna bakin gado ahankali ta tuno da cikin qaryarsu Wanda shauqin abin alokacin yayita shigarsu itada Dr Ashe ita kadai zata qarar da zuwan ranar,

Idan namiji na Haifa baida sunan daya wuce na mahaifinsa inshallah.

 

Wayartace tayi ringing ta juya ta kalla screen din wayar taga sunan USI

Tasaki murmushi me Fadi tana daukar wayar kusan atare sukace”

 

Lallaima.

 

Dariya suka saki lokaci daya Jin bakinsu yazo daya tace”

 

Allah USI nakusa gayawa kawu ya yafewa Yan can Kai,

Yanzu duk yinin yau sai yanzu kake kirana.

 

Dadina dake masifa ko numfashi bazaki Bari mutum ya saukeba,

Yaya jikin to?

Nayi waya dasu kawu yace ansallameki sunkoma gida.

 

Eh da magribar Nan nadawo.

 

Amah nayi Magana da kawu akan Zaki koma gida sbd zaifi Mana sauki harzuwa lokacin haihuwarki tunda ko haihuwa Kikai bana sakaran zasu karba Abinda aka Haifa din saiyayi wayo sosai kokuma idan Zaki koma makaranta

Dagani har kawu Amatu karatu yanzu mukeson kiyi.

 

Numfashi ta sauke tareda gyara zamanta tace”

 

USI Nima naso komawa gidan saidai Kuma yanada wuya su Bari nabar Nan din shiyasama kawai nabari Bayan haihuwar saina koma gida tunda koba komai Ina haihuwa na fita takaba ba sauran dalilin zamana anan din Amma dai kawu yace zaizo gobe zasuyi Magana dasu Modibbon idan sun Bari din zankoma gidan idan Kuma sun buqaci na zauna harna fita takaban duk Babu illa tunda dai lokacin zaizo.

 

Numfashi ya sauke cikin nutsuwa yace”

 

To Allah ya saukeki lafiya shine fatanmu akan komai.

 

Amin ya furta afili kafin suka shiga cikin zancen karatunsa dayayi nisa yanzu gashi Yana bada himma sosai Dan tuni ya goge cikin masu qoqarin makaranta.

 

Da daddare umme da kanta tazo tayi musu fira har kusan qarfe goma kafin ta tafi anty zarah dai ce Bata sake gani ba sai washe gari anacan ana soyewa da Rabin Rai.

 

 

 

Washe gari qarfe goma sha daya na Rana kawu ya iso zabeera tareda Dr Salman dayaje ya daukosa akan maganar komawar Amatu gida

Dama Suma su Modibbon suna jiransa sbd tun jiyanma da MAHMOUD yayi musu bayanin Abinda kawun ya buqata sukaso zuwa har gida su samesa tun cikin Daren saigashi yace yace zaizo a yau din.

 

Babban palon Andi suka Isa inda andin da Modibbo ke jiran isowar kawun

Gaidasu kawai dr Salman yayi ya ficewarsa ya barsu suka Fara tattaunawa.

 

Cikin nutsuwa Andi ya kalli kawu zaifara Magana saiga MD yashigo batareda yasan kawunma naciki ba.

 

Cikin nutsuwarsa da girmamawa ya gaidasu tareda sanarda Modibbo zaiyi tafiyane yau takamasa Kuma zai kwana biyu kafin yadawo.

 

Kallonsa Andi yayi cikin nazari harya miqe zai fice yace”

 

MAHMOUD dawo ka zauna Magana zamuyi akanka da Dan uwanka marigayi tareda Abinda yabari.

 

Maida kallonsa yayi Kan kawu cikin nuna Masa girma amatsayinsa na mahaifin ‘yar dasuke son abarta cikin zuriar ‘ya ko ‘dan da zata Haifa yace”

 

Mal Saleh tun jiya nakejin saqonka bakin MAHMOUD

Da tun jiyan mukaso ganinka saikuma dai muka Bari yau din tunda yace kace zakazo din akan maganar,

To Mal Saleh munji zancenka amatsayinka na mahaifin AMATULLAH Kuma bamu katsi hanzarinkaba amma maganar barin AMATULLAH kwata kwata zabeera Bata tasoba sbd koba komai dai ga rabo Nan ya ratsa a tsakani Kuma bayan hakan ma tun asali zabeera shiyasa ba’a auren waje sbd irin hakan duk da qaddara ce da Babu me gujewa saidai kuma tunda AMATULLAH tashigo zuria mezaisa ta futa Dan mijinta ya rasu bayan munada Wanda zai Kare mutunci da haqqin iyalin ‘dan uwansa ko ayanzu da babu ran nasa?,

 

Mal Saleh Kai ubane,bazaka so ‘yarka Takoma gabanka ta Dora sabon zama na zawarci duk da Allah ne yaso hakan shiyasa muke fatan kaima kazabi barin ‘yarka a killace cikin inuwar aure sabanin komawarta gabanka,

‘yayanmu idan mazajensu sun rasu suna fita takaba da qanqanin lokaci muke aurar dasu ga Yan uwa mafi kusanci na mazajensu sbd dorewa acikin aure shiyasa ba alfahariba bamada tarin zawarawa acikin zuria sbd zawarcin ba Dadine dashiba,

 

Maganar aure ga me takabar dake cikin takaba haramun ne shiyasa bazamuyi maganar auren AMATULLAH ayanzu ba Amma dai muna roqonka a matsayinka na mahaifin AMATULLAH daka barta anan tayi renon cikinta ta haihu bayan haihuwarta zamu nemawa Dan uwan mijinta mafi kusanci agaresa aurenta wato MAHMOUD Wanda Inshallah aranar sunan Abinda ta Haifa tareda radin suna zamu daura musu aure Inshallah idan harka bamu dama tare Kuma da amincewa.

 

Numfashi me qarfi kawu ya fitar a fili tareda jinjina Kai sbd shima kamar yanda suka fada duk duniya Babu ubanda zaiso yarsa tadawo gabansa ta zauna ta dasa sabon zaman zawarci sai abisa qaddara,

 

Qaddara ce ta saukarwa Amatu Kuma Dole sunkarba hannu bibbiyu saidai tunda tasamu wani tayin auren gskia bazaiqi amincewa ba tunda dama suna tunanin tattarawa ne subar gidan sukoma inda Amatun zatafi sakewa da Abinda zata Haifa to tunda har mutanen nan na qaunarta harda basa iya barin ta fita wani gurin dabam tayi aure Babu Abinda yafi Masa wannan saidai tunda ba halaccin maganar neman aure akanta ayanzu zai tafi da ita still idan lokacin haihuwarta yakusa tunda zata dawo daga baya.

 

Aje numfashi yayi tareda koro musu nasa bayanin bayan amincewarsa akan idan takusa haihuwa Zata koma gida ta haihu gaban uwarta.

 

Ba wani dogon sharhi suka amince akabar maganar akan Babu Wanda za’a sanarwa yanda aka aje zancen sai bayan haihuwarta idan lokacin Daurin auren yayi.

 

Komai bai iya cewa ba sbd zancen baiyi Masa Kama da zai yiyu dinba idan har za’a tambaya ra’ayinsu kafin Daurin auren idan lokaci yayi.

 

Sallama yayi musu tareda ‘yar godiyar da batakai cikinsa ba ya fice Yana duba agogon hannunsa sbd yakusa lattin Isa airport.

##Mamuh#

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 37

Advertisement   MQ 37_*     *_kina da burin koyon sana’a wadda zaki yita daga gida a sauqaqe_*…

MIN QALB 23

Advertisement   *_MQ 23_*   *_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN…

MIN QALB 1 (mamuhgee)

Advertisement  *_MIN QALB_* _Mamuhgee_ 1 Bismillahir-rahamanir Raheem. Qoqarin durqusawa takeyi ta dauki busashen biredin dataga wani yaro yazo…

MIN QALB 18

Advertisement   *_MQ 18_* _Mg_       Koda anty zarah tace yazauna suyi breakfast tare baiso karya…

MIN QALB 10

Advertisement  _*MIN QALB 11*_ _mamuhgee_ Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins…

MIN QALB 41

Advertisement   *_MQ 41_*   *_Masu karanta book din mu Basu biyaba Kuma sunabinmu da mummunan kalami munbarku…