MIN QALB 36

Advertisement

 MQ 36_*

 Umme da kanta tabata abinci abaki taci tana qara jinjina zancen Dr Fatima data fada Mata kafin shigowarta akan inda aka tsaya da maganar matsalar,

 

Ita kanta Amatun a sanyaye take sbd rashin sanin makomar abindake cikinta,

Allah yasani tanason babynta Kuma tanason samun Abinda Bata fatan tayi wahalar banza shiyasama tunda sunce saita kwantarda hankali babyn zai samu shima lafiyar da akeso tafara iya qoqarin kwantarda hankalin saidai Kuma Sam tsoro da shakkar halinda babynta ke ciki ya Hana hankalin nata kwanciya.

 

Advertisements

Iyami ce ta miqa mata kofin maganin tsiyayewar zaqi tana cewa”

 

Karba ki Dan Sha ko kadan ne zai taimaka idan haihuwar ta taso gaba data.

 

Kallon kofin tayi tareda karba ahankali ta kurba tana rintse ido sbd rashin dadinsa ta ajiye cup din tana girgiza Kai tace”

 

            Iyami bazan iya Sha da yawa ba wannan ya Isa Yana sakani zafin zuciya da yawa.

 

Fura me sanyi anty zarah ta zuba Mata ta miqa Mata Wanda itace ke cewa tafisonta da sanyi sosai idan ba hakaba Bata iya Sha abin Sha idan baida sanyi Sam.

 

Karba tayi ta shanye atake tana cewa aqaro Mata saidai aka miqa Mata jug din daya Gama daukan sanyi shima.

 

Advertisements

Shan furar takeyi sunata kawo Mata firarraki kala kala Dan dauke Mata hankali kota cire damuwa da tsoron kwata kwata,

Sai dare dukkaninsu suka watse aka barta daga ita sai iyami sai anty salamatu dasuka Zo taredasu maman junior dasu maman basiru Dan dubata kowanne dauke da kularsa ta kayan gargajiya na marmarin me ciki,

Maman junior sakwara da jar Miya ta kawo Mata wadda taji yaji sai maman basiru data kawo Mata danwake dayaji salad da kwai anty salamatu ma taga soyayyar gyada ahanya da Madara gasassa ta siyo Mata duk saitaji idanuwanta sun cicciko da hawaye har batasan lokacinda tasakesu tana sunkuyar da Kai sbd ayau tasake tabbatarda ba jininka ne kawai Dan uwankaba wani Dan uwanma yafi na jini,

Bata damu da son sanin asalintaba ko jininta wainnan bayin Allahn sune Yan uwanta sune jininta sbd suna qaunarta tamkar jininta Dan haka Bata buqatan sanin inda ta fito Dan kula kawu da iyami tareda usinta sune asalinta hakanma ya Isa rayuwa Alhamdulillah.

 

Share Mata hawaye anty salamatu tayi tana cewa”

 

To meyene na kuka Bayan Dr tace ko damuwa ba’a so bare Kuma kuka,

Wannan abin damukeyi duk yiwa Kai ne sbd mu tamkar zuria daya ne idan baki manta ba yawancinmu dake gidan bamuda zuria,bamuda dangi mune Yan uwan junanmu Dan haka meye abin damuwa aciki.

 

Iyami dai batace komaiba sbd ita wani lokacinma ayanda takejinsu aranta har mantawa takeyi da ba itace ta haifesuba sbd har cikin ranta take qaunarsu a haqiqanin gaskia.

 

Take suka cika dakin da hayaniyar gida dasuka Saba ana tuttuna baya da irin fadace fadacen dasuka sabayi Wanda haryanxu ba dainawa sukayiba Nan take ta sake saigata ta washe acikinsu tana walwalarta harda dariya da qyaqyatawa

Taci sakwara kadan hakama Dan waken taci sosai shikam kafin ta Dora da masararta tanaji suna firarsu Basu bar asibitin ba sai goma da wani Abu kafin suka tafi anty salamatu ta rakasu kafin tadawo Amatun tayi bacci cikin nutsuwa Wanda ta kwana biyu batayiba.

 

Washe gari da Dr Fatima ta auna BP dinta taga ya sauka sosai sai abin yabata mamaki takalli iyami cikin Jin Dadi tace”

 

Tayi bacci ne sosai jiya?

 

Eh Kam jiya tasamu bacci Dan sallah ma saidai da safen Nan tayita.

 

Masha Allah gskia idan da zata riqa samun hakan to da Inshallah komai zaizo da sauqi yanda mukeso.

 

Jin hakan yasa iyami ta aika salamatu tayiwasu maman junior Magana akan su riwa zuwa Dan Allah suna kawowa Amatun firar dare

Ba musu suka amince sbd Suma zasuso tasamu lafiyar.

 

Aikuwa tuni asibitin Takoma majalisar ‘yan gidansu Dan kuwa idan sunayi dariyar Amatun har qofan daki anaji umme ma data ga hakan saita qarawa zuwan nasu armashi ta aiko musu da lafiyayyan abinci da pepper chicken na kaji kullum aikuwa Suma ganin wannan dadin yasa suka sake dagewa da kullum gida suke kwaso abinsu sai sun iso gida araba abawa kowa nasa Kuma kajin ba ‘yan kadan ba ga drinks gakuma kudin abin hawa da anty zarah ce itakuma ta Basu Wanda zasu riqa amfani dasu Dan da farko kawu ne duk sukazo yake Basu na komawa sai anty ZARAH ta dauke Masa wannan nauyin.

 

 

Kwananta takwas a asibitin ranar na Tara ta tashi da wani mummunan ciwon kai wanda yasanya jini da ruwa 6alle Mata take hankalin dukkanin likitocinta tashi musamman Dr Fatima

Su kansu su umme dasu kawu kowa yashiga tashin hankali musamman ganin yanda take wani wani Abu kamar jijjiga haka aka kwasheta akai labour room da ita aka barsu tsaitsaye suna Kai kawon jira cikin rashin hankali.

 

Kafin qarfe hudu na yamma dukkanin ‘yan uwanta da wasu daga cikin familyn ZABEERA suna asibitin Babu me wata walwala acikinsu sbd har lokacin Babu wani labari daga likitoci sai yawo ake ana fita ana shiga.

 

Dr Fatima ce ta fito Bayan tayi waya da Modibbo ta sanar Dasu komai na halinda ake ciki ta kalli kawu da umme da iyami dake gabanta cikin office dinta dake cikin labour room cikin tsananin damuwa da sanyin jiki tace”

 

Wato Abinda ake ciki shine Amatu bazata iya haihuwa da kanta ba sbd lokacin haihuwar baiyiba gabanta ko kadan bai Fara budewaba gashi baza’a iya jiraba sbd qarfinta zai qare hakama babyn ruwan dayake ciki kowane lokaci zasu iya tsiyayewa Wanda hakan na faruwa hadari ne Mai matuqar girma Kuma barazana ce ga rayuwarsu su duka,

Dan haka bazamu Bata lokaci ba na sanarwa su Modibbo zamuyi Mata aiki saidai Abinda zata Haifa din zamu sakasa a kwalba sbd rashin isarsa haihuwa idan Allah yasa andace…

 

Tsit sukayi kamar wainda sukaji mugun labari,

Koda yake kusan hakan ne Dan umme tuni tafara hawaye sbd tasan rasa babyn zatayi kamar yanda ta rasa Khalil dinta.

 

Numfashi kawu ya sauke cikin jarumata yace”

 

To shikenan likita ba damuwa ayi aikin Allah yasa hakan shine mafi alkhairi yasa Kuma ayi cikin sa’a.

 

Amin tace tana qoqarin amsa wayarta da Kiran MAHMOUD ZABEERA ke shigowa Dan takirasa dazun bai dagaba.

 

Itace tafara Magana sbd tadan fahimci bai cika maganaba yafi saurare Dan haka Bayan ta Masa ya aiki saita Fara koro Masa bayanin halinda ake ciki ta Dora da cewa”

 

Modibbo yace Kaine zaka saka hannu a file din gashi Kuma bakanan and bazamu iya wuce Nanda 20min ba bamu Shiga da itaba ba sbd…….

 

Kai tsaye cikin wata murya me sanyi ya katseta da cewa”

 

I will be there in 10min yanzu nake baro airport.

 

Kafin tayi Magana ya datse wayar ya ajiye gefensa ya sauke sanyayyan numfashi tareda rufe Ido ya bude ya kalli Mal Umar yace”

 

Mal Umar Yi parking.

 

Ba musu yayi parking din saiyaga ya fito daga Bayan motar ya zagayo gurin sit din driver ya bude yace”

 

Fito ka koma baya zanyi tuqin.

 

Fitwo Mal Umar yayi da sauri batareda yace komaiba duk da Yana cikin mamaki Amma dai sanin ba Abinda yafi tsana wani lokacin kamar tambaya yasa baice qalaba ya zagaya ya Shiga dayan gefen ya zauna.

 

Batareda ya kalli gefen mal Umar dinba Bayan ya shiga ya tayarda motar yace”

 

Saka seat belt dinka.

 

Da sauri ya janyo ya saka.

 

Wani lafiyyan speed yabawa motar Wanda yasa Mal Umar saurin hade qafafunsa Yana hadiye yawu tareda damqe qofa Yana zazzare idanuwa dan ba halin Magana bare ya nuna tsoronsa,

Allah ya kaimu inda zamu lafiya yafada cikin ransa Yana satar kallon MD din dake sake bawa motar wani mugun speed din Wanda yamanta rabonsa da irin wannan tuqin qila tun Yana cikin samartakarsa idan Khalil ya matsa Masa Akan suyi tseren mota a Sudan idan yaje gurinsa.

 

 

Fitowa Dr Fatima tayi daga labour room sanyeda kayan CS tana duba agogon wayarta datakeson kashewa kafin Shiga CS din taga minti Tara kenen da wayarsu da MD Amma haryanxu shiru ga kowa jigum jigum shi ake jira yazo yasa hannun ga Modibbo ma ya iso asibitin Amma baisaka hannunba yace ajira MAHMOUD din tunda yace abasa mintuna kadan…

 

Kamar daga sama har zata juya cikin room din saigashi ya doso gurin cikin tafiyarsa me nutsuwa da cika Ido take kowa ya juya Yana kallonsa Yana tahowa in calm Sam baka ganin gaggawa ko sauri ko firgici ataredashi shi mutum ne daya iya controlling yanayinsa duk qwaqwarka baka ganewa saidai idan ka kalla cikin idanuwansa kake iya gane Abinda yake ciki saidai Sam ganin idanuwansa ba Abune me yiyuwaba ga kowa Dan baya Bari.

 

Yana qarasowa ba wata Magana Dr Fatima ta miqa Masa file da biri yayi signing tareda juyawa zuwa blood bank dinsu sbd tun a waya yafada Mata basa buqatan jinin asibiti.

 

 

Anshiga tiyatar da qarfe biyar na yamma shiyasa gabaki daya ward din cike yake da familyn ZABEERA ko biyowa ta gefen ba’a yi sbd ba’a buqatan hayaniya suna buqatan silence sbd suji da damuwar dasuke ciki,

Damuwar iyami da kawu tsakaninsu da Allah tafi karkata ne Akan su samu ‘yarsu tukuna kafin suyi maganar abindake cikin shiyasa sukafi kowa damuwa ga USI da Dr Salman sai Kira sukeyi sun Hana kowa sukuni qarshe ma dai kusan wasu kashe wayoyinsu sukayi wasu Kuma suka sanyasu silent.

 

MAHMOUD na tareda Modibbo a office din Dr khalil zabeera Wanda haryanxu wani bai shigaba tukuna suna jira Modibbo ne Dai ke wayoyinsa shikuwa MD ZABEERA Yana zaune ne yayi crossing legs idanuwansa a lumshe yana karkada qafa.

 

Ana fitowa sallar magriba nurse na fitowa daga theatre ta cikin labour room fuskarta daukeda da murmushi da farin ciki tun Kan ta qaraso duk suka miqe suna kallon bakinta tasake sakin murmushi tace”

 

Ansamu baby boy…….

 

 

Masha Allah, Masha Allah, Masha Allah alhmdlh, alhmdlh”  Sune kalmomin da suka karade gurin atake kowa na fada Yana washe baki

Umme Kam tana fada idanuwanta na cikowa da hawayen farin ciki hakama iyami da kawu daya kasa zama guri daya yafita waje yadawo.

 

Anty zarah kuwa karo na farko dataji idanuwanta kamar zasu ciko da hawayen kwadayin samun dukkanin Abinda Amatu ke samu musamman irin wannan soyayyar daga kowa ga Kuma babynta tasamu.

 

 

Hamdala Modibbo yayi lokacinda nurses biyu suka fito da jaririn dunqule cikin wani qaton farin bargon jarirai acikin kwalba.,

 

Babu Wanda aka Bari yashiga dakin kwalbar jariran sai Modibbo da MAHMOUD din sbd jaririn baida lafiya sosai Dan gabaki dayama kalar fatarsa ta Dan sauya saidai tubarkalla jaririn Yana haske sosai da dogon hanji kamar dukkanin iyayensa.

 

MAHMOUD Modibbo ya miqawashi Yana tayasu murnar samun qaruwa tareda addua ya fice yabarsa.

 

Shiru yayi akaro na farko yaji hannuwansa na rawa game da daukar Abu sbd kaf rayuwarsa Yana sakaran wannan ne karo na biyu daya taba daukar jariri sbd baida Wanda zai haihu yabasa danshi ya dauka,

Karon farko daya taba daukar jariri shine lokacinda wani babban abokin kasuwancinsa ABDUL LAYE da matarsa ta haihu suna Greece shine yayi Masa huduba ma sbd shaquwarsu sai yau da Allah yabasa ikon daukar ‘dan Dan uwansa Wanda yake shine ubansa yanzu Koda kuwa ace Khalil din na Raye yasan shine zai Masa huduba bare yanzu dayakeda gaba daya responsibilities din na yaron,

 

Fuskarsa yadan bude ahankali ya kalla wani sanyi da nutsuwar zamowa uba na shigarsa

Sai yanxune yakejin Abinda zarah ke fada nason zamowa uwaye suma wata ran,

 

Haka kawai sai yasamu kansa da murmushin dayasa nurse din dake tsaye kusan sumewa tana kallonsa da dukkanin girman idanuwanta kamar zata cinyesa baki sake.

 

Dagosa yayi yakai fuskarsa gurin kunnen jaririn ya karanto Masa Kiran sallah da addua tareda Sanya masa dukkanin albarkarsa dakuma yiwa Khalil addua.

 

Saida ya Dan jima kafin ya miqawa nurse din aka maidashi cikin kwalba ya fice.

 

Office din Dr Fatima data gama sauyawa tagama signing na fitowa tiyata tana zaune tana harhada kayan tafiya gida saigashi yashigo Nan tasake Masa bayanin Alhmdlh Amatu insha Allah komai lafiya data wartsake shikenan ba wata damuwa saidai jaririn Kam baida lafiya sosai saidai yanzu ita matsalar jaririn ba nata bane yanzu Dr fatihu ne zaiji da matsalar jaririn shizai Basu bayanin komai zuwa da safe Dan haka tana tayasu murna da fatan Allah yakawo abin da sauki.

 

Kusan atare itada MD din suka bar asibitin zuwa gida Dan ko dakin da amatun take bai jeba ya wuce gida Modibbo ma tuni ya wuce.

 

 

Sosai suke ta hidimar kulada Amatun tun cikin dare data farka tuni nurses suka sake gyarata aka kimtsa komai Koda qarfe goma na safe tayi kowa yazo ya tararda ita a zaune sai abin nasake Sanya kowa farin ciki.

 

 

To kusan dai murna komawa ciki takusa Yi sbd bayanin da Dr fatihu yayi musu dangane da jaririn Wanda yanzu haka da oxygen yake numfashi kadan kadan baya iya shaqar numfashi da kansa,

Sanyi ne da rashin motsawar jijiyoyin yawon jini ajikinsa sukai Masa mugun qarfi gashi ko qarfin kuka yarin baida a taqaice dai Yana buqatar blood transfusion.

 

Babu Wanda yakai MAHMOUD da Amatu tashin hankali sai umme ma da abu yadawo na damuwa shiyasa duk abin yakoma ba murna kamar ba haihuwa akaiba.

 

Ahankali ita ta warware tasamu sauki sosai Dan kullum da kanta take zuwa dakin da yake tadubosa,

Kwana shida dayin CS din ta murmure matuqa sai Dr Fatima tabata sallama Amma sbd jaririn sai jinyarsa ta dawo musu sabuwa saidai kullum tana zuwa gidansu tayo wanka ta huta tadawo.

 

Batareda sanin kowaba MAHMOUD ya bincika wani qwararran asibitin Yara dake Greece take yasa ayi musu Shirin tafiya

Ya sanardasu Modibbo Nan Suma sukai na’am da hakan Dan dama tuni Andi shima yafara bincikawa wasu qasashen.,

 

Da Amatu da anty salamatu sai umme datace zata aka hada tafiyar shi MAHMOUD zasu rigasa zuwama sbd baya iya tafiya da Mata sam.

 

Andi dayazo har gidan kawu da kansa da Daren laraba ya gyara zama Kan tabarmar da aka shimfada Masa bakin masallacin qofar gidan yace”

 

Mal Saleh maganar tafiyar yaran Nan inaga zaifiwa kowa kwanciyar hankali idan aka daura auren kafin sutafi sbd su samu isashen lokacin nemawa KHALIL qarami lafiya daga Nan har lokacinda Allah zai basa batareda mu munshiga wasi wasiba Suma Basu Shiga takuraba

Shiyasa nace amatsayinka na mahaifinta Zan Sanar maka idan ka amince a daura Bayan sun dawo sauran abubuwan sa biyo daga baya.

 

Numfashi kawu ya sauke Yana muskutawa cikin jinjina kai yace”

 

To Nima dai da bakazoba inada niyyar zuwa da safe sbd zuciya data kasa yardarmin tafiyar hakanan sakaikai duk da ba ita kadai bace Amma hakanan nayita wasi wasin su sauran idan sungaji dawowa zasuyi abarota ita kadai sai hakan bai wani kwantaminba gwara a daura Kam Nima yafimin nutsuwa.

 

To shikenan nagode sosai Mal Saleh Kuma Inshallah gobe za’a aiko kudin auren idan Allah yakaimu juma’a sai a daura tunda ranar juma’ar da daddare zasu wuce shikuma MAHMOUD din asabar da safe zai wuce.*_

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 23

Advertisement   *_MQ 23_*   *_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN…

MIN QALB 8

Advertisement  *_MIN QALB 8_* _mamuhgee_ Kallon tsantsan mamaki da firgici yanzu takewa amatu din tana kallon qafafunta zuwa…

MIN QALB 45

Advertisement   MQ 45_*    Sai Bayan sallar asuba jirginsu ya sauka Nigeria ta dayake ta Kira USI…

MIN QALB 26

Advertisement   26_* Zaune suke a Palo itada anty zarah anty zarah na Mata fira Dan sakata nishadi…

MIN QALB 10

Advertisement  _*MIN QALB 11*_ _mamuhgee_ Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins…

MIN QALB 49

Advertisement   #*_MQ 49_*       *_THE FLAVORLAND BY ACEEY_* Ina ma’abotan son ingataccen yaji, Different Flavors…