MIN QALB 37

Advertisement

 

MQ 37_*

 

 

*_kina da burin koyon sana’a wadda zaki yita daga gida a sauqaqe_*

 

*_kin jima kina sha’awar yadda yake hada BIRTHDAY CAKE DA DECORATION amma kin rasa wajen da zaki koya?,ko FARASHIN YA MIKI TSADA?_*

 

Advertisements

*TOFA MATA!*

 

*_Ga dama ta samu_*

 

*_UMMU AYMAAN KITCHEN ta shirya tsaf don koya muku yadda ake hada gangariyar BIRTHDAY CAKE wanda ya gama hada dukkan gamayyar kayan dadi masu sanya harshe su motsa,gefe guda kuma ta koya miki yadda zaki qawata waje da walwali da kuma walainiyar KAYAN ADO DA QAWA na wajen gudanar da SHAGALIN BIKI SUNA TARON BIRTHDAY WEDDING ANNIVERSARY da sauransu_*

 

*_ba’a nan UMMU AYMAAN KITCHEN YA TSAYA BA,tana da ajujuwa na musamman don koyar da mata nau’in girke girke MAIDA TSOHUWA YARINYA,hakanan tana karbar kwangilar abincin taro kowanne iri_*

 

*_ta fannin kayan maqulashe na fulawa ta samar da abubuwa kamar haka_*

Cake perfait

Cup cake

Samosa

Advertisements

Springrolls

Meatpie

Doughtnout

 

*SIYAN DAYA KO SARI*

 

*_za’a koyar dake BAKING AND DECORATION QIRI DA MUZU ta sigar zancan nan da hausawa kance GANI YA KORI JI,gani ga malama_*

*_sa’an nan kuma akwai tanadi na musamman ga masu sha’awar koya ta hanyar yanar gizo wato ONLINE,duka kan farashi mai rangwame_*

 

*_ZA’A IYA SAMUNTA A UNGUWA UKU,LAYIN MAI FATA ZARIA ROAD*

 

KO A TUNTUBETA A WANNAN LAMBAR WAYAR

08032964266

 

*_ZA’A GUDANAR DA KOYARWA NE ON 5&6,GARZAYA MAZA KI REGISTER*๐Ÿƒ๐Ÿพโ€โ™€๏ธ๐Ÿƒ๐Ÿพโ€โ™€๏ธ๐Ÿƒ๐Ÿพโ€โ™€๏ธ๐Ÿƒ๐Ÿพโ€โ™€๏ธ

 

 

 

 

 

Bayan tafiyar Andi gyara zama kawu yayi Yana fiddo wayarsa cikin babbar rigarsa ya Danna Kiran USI Dan sanar dashi komai sbd shi dama iyalinsa sune abokan shawarar sa.

Kamar yanda tsammananta Usman din yayi na’am da ayi auren kafin sutafi zaifi bawa kowa nutsuwa dan haka take suka qara tattaunawa suka Kai qarshe Bayan dawowarsu ayi walima saita tare shikenan.

 

Cikin gidama Yana Shiga Kai tsaye dakin Amatun ya wuce dan tadawowarta gida take kwana duk da komai nata na zabeera har lokacin sbd bawai ansallami Khalil qarami bane Kuma Nan gidansu yafi Mata sauqin zuwa asibitin kullum akan zuwa daga zabeera.

 

Kallonta yayi tana waya da umme ahankali sbd gabaki daya ciwon Khalil ya karyar Mata da jiki da zuciya sai tanajin tsoron rasashi kaman yanda ta rasa babansa shiyasama ta dauki burin samu waraka akan tafiyarnan dazasu Yi a matse take dasu tafi sbd ganin takeyi dasun tafi Khalil dinta zai samu lafiya.

 

Ganin tana waya yasa yafasa mgn ya qyaleta har zuwa gobe yayi dakinsa inda ya tararda iyami ita Kuma tana kunna musu tsintsiyar qamshi bayan tagama gyara dakin Wanda tsafta kyakkyawar dabiarta ce Sam Bata rabo da gyara da qamshi.

 

Zama yayi Kan babbar daddumar tsakar dakin bayan ya cire babbar rigarsa ya sauke numfashi Yana cewa”

 

Iyami zoki zauna Magana zanyi dake akan ‘yarki.

 

Juyowa tayi ta kallesa taga Babu alamun fitarsa daya same ataredashi saita kunna sauran dayar tsintsiyar qamshin ta sokata a jikin qofar shigowa ta qaraso gefensa ta zauna Yana cewa”

 

ALLAH yasa lafiya dai wannan nutsuwa danaga kayiยฟ

 

Nufinki banda nutsuwa iyami?

Wato dai haryanxu duniya batai Miki darasin yiwa miji biyayya ba kokuwa dai sbd kin Raina……..

 

Katsesa tayi da sauri da cewa”

 

Dan Allah Yi hkr ya Isa kada mu komawa halin dare ne ana jinka har maqota,

Munyi jika yanzu wani abin dai Dole mu barshi Dan haka Yi hkr ba nufina kenan ba.

 

Shiru yayi kamar yafasa maganar tsawon mintuna kafin ya sauke ajiyar zuciya yasake kallonta yace”

 

Andi ne da kansa yazo dazun Nan

Sunxo nemawa MAHMOUD auren Amatu abisaga suna neman alfarma sbd basa barin matan yayansu su fita wani gurin dabam suyi aure

Kuma dai ba laifi Nima na yaba da shawarar su sbd kwata kwata bana fatar Amatu tadawo gida ta zauna munsamu tayi aure zata samu ingantacciyar rayuwa saigashi Ashe mijin bame kwanakine agaba ba……

 

Kasa barin ya qarasa zancensa iyami tayi ta katsesa cikin tsananin mamaki da fargabar maganarsa da cewa”

 

Mijin Zarah fa kuke maganar aurawa Amatu idan dai MAHMOUD din Dana sani kuke Magana akai.

 

Wani kallo kawun yayi Mata cikin rashin fahimta yace”

 

Eh shifa mijin Zarah din ake Magana wani abin ne?

 

Ta Yaya kuke tunanin hada zarah da Amatu kishi fisabillah bayan kunsan yanda suke matuqar qaunar juna ga kishi mugun Abu ne Dan Allah ku sauya shawarar Nan idan basaso Amatun tabar zabeera gaba daya Baga Salman Nan ba sai ahadasu Amma Dan Allah Ina Amatu Ina auren mijin Zarah……

 

Kallon mamaki da shashanci yake yimata cikin ‘yar hasala yace”

 

Meya kawo maganar kishi da rashin yuyiwa?

Shine yafi kowa cancantar ya riqe iyalin Dan uwansa dakuma zamowa uban Muhammadu Khalil mu shi muka duba bawai kishi ko wani tunaninku na Mata daban ba,

Yanda suke qaunar junan nasu ai shikenan sunsamu damar zama tare har abada Kuma bawai anyi ne Dan cin zarafin ita zarah din ba anyi ne sbd ganin hakan ne ya kamata,

Shi MAHMOUD tun ranar farko da akayi zancen gabansa akayi Kuma bai musaba Dan haka ni me ‘ya mace bazai yiyu ace ansamu tangarda ta gurina ba Dan gaka ki aje maganar kishi da rashin yakamata a gefe tun kafin Amatun taji ta samu qarfin ji daga gareki,

Sannan Banda abinki shin ba abin farin cikinmu bane da Jin Dadi tareda kwanciyar hankali ace mun aurar da yarinyar Nan ba adaidai irin yanxu datafi buqatan Wanda zata jingina dashi amatsayin Miji Kuma uban danta,

Kina tunanin duk yanda zabeera suke qaunarta da Bata kulawa idan tana gida zaune wata ran sai ta fuskanci juyin rayuwa wani Kai tsaye zai sheganta danta,wani akan ‘dan sai afasa aurenta shin kin manta irin rayuwar data fito ne bayan tsanani da jajircewar Dr khalil aka samu ta watsar da komai shine yanxu zamu vari me tadawo zaman banza Wanda bama fata amma komai zai iya faruwa.,

Ki aje maganar shaquwarsu da yakamatanki mu fuskanci ci gaban yarmu Dan kuwa aure gareta yanzu shine babban rufin asiri.

 

Numfashi ta sauke me nauyi kafin tace”

Dukkanin bayaninka naji amma bana saka ran wannan auren Abune da Amatun zata karba Dan kuwa Ayanda nasan tanajin zarah to zata gwammaci mutuwa ba aure data auri mijin Zarah.

 

Wace irin maganace wannan iyami kike fada?

 

Wlh maganar gskia kenan nake fada maka

Amatu bazata yarda da auren mijin antyntaba nake fada maka

Tun wuri kafin Azo aji kunya kayi Magana da ita kaji Dan Nafi kowa sanin ba amincewa zatayiba

Ai ana barin wani halak din ko Dan kunya,

Amatu tafison koba soyayya tsakaninta da salmanu ta auresa idan anyi Mata tilas dadai ta auri MAHMOUD.

 

Shiru kawu yayi zancen iyami na sanyasa nazari,

Idan Amatu ta bijire ta dage tabbas zasuji kunya Kuma dai Allah yasani yafi buqatar tayi aure ayanxu data zauna zaman zawarci Kuma,

Gskia bazai Bari hakan yafaru ba zai tabbatarda ta amshi wannan auren hannu bibbiyu Amma kafin Nan bazai sanar da ita komaiba sai andaura auren Inshallah ta yanda kotaqi kotaso bazata iya kubucewa aurenba.

 

Kallon iyami yayi Yana tattaro dukkanin hankalinsa yace”

 

Kada ki sanar da ita komai dangane da hakan yanxu sai Bayan auren

Kin fahimta ko?

 

Da mamaki tace”

 

Meyasa??

 

Sbd kada asamu damuwa.

 

Shiru tayi ta danyi nazari kafin ta jinjina Kai tana cewa”

 

To shikenan Amma dai dakun sanar da ita tukuna zaifi..

 

Zan aurar da ita amatsayina na ubanta Bayan auren Zan Sanar da ita alokacin danaga ya dace Dan haka na rufe zancen daga Nan.

 

 

 

Washe gari kamar yanda Andi yace da yamma sun aiko da kudin aure tareda sadakinsu da katin daurin auren Wanda aka bugo da safen sun karba tareda adduar zaman lfy me dorewa ga auren.

 

Take maganar Daurin aure ta Bazu koina sbd fitar katikan Daurin auren ga Kuma sanarwa agidanjen radio da talabijin musamman daya kasance auren mutum me suna kamar MD ZABEERA guda,

 

Take abokanan hurdarsa manyan mutane suka Fara Kira suna tayasa murna tareda saka zuwa Daurin auren cikin mahimman aiyukansu na washe gari.,

 

Umman zarah ce tafara Jin wannan mugun labarin Wanda ya sanyata cikin tashin hankali da rashin nutsuwa saidata Kira zarah din wadda daga bakin umman tata itama tafara Jin wannan mummunan labarin daya sanya qafafunta qasa daukarta ganinta ya dauke ta sulale agurin ta Fadi zaune tana qoqarin Kiran sunayen Allah Amma suna bace Mata sbd tashin hankali daqyar ta iya cafko sunan Allah daya ta furta tana lalubar wayarta tareda shiga social media take kuwa ta ringa cin karo da hotunan  katikan Daurin AUREN dakuma masu cewa zasu sako hoton macen datai sa’ar shiga rayuwar MD ZABEERA akaro na biyu bayan matarsa ta farko wadda haryanxu duniya batasantaba.

 

*MAHMOUD DAHEER ZABEERA* da *AMATULLAH K SALEH* sune sunayen datake ta maimaitawa akan hoton Daurin auren idanuwanta nason kawo ruwa Amma tashin hankali da tsoro yaqi Bari.

 

Sama ta nufa dakin MAHMOUD din Wanda tun rana daya dawo ya shige bai fito ba Ashe sbd yasan fitinar daya dauko ne,

 

Babu bugawa yau Kai tsaye ta bude kofar palonsa ta shigo ta nufi bedroom dinsa ta tura ta shige zuciyarta na wani irin harbawa da sauri sbd gaf kwanyarta take da zautuwa,

Bayani kawai takeso daga MAHMOUD din kokuma Amatun sbd wata zuciyarta takasa yadda da wannan Abinda saitana kallon abin tamkar a mafarki Sam takasa gasgatawa.

 

Kwance yake Kan gadonsa ya qure AC idanuwansa a rufe daga gani ba bacci yakeyiba saidai Kuma batada tabbacin idonsa biyu,

Farin wando da farar rigace Mara hannu ajikinsa sai fararen qafafunwa dayau bai sakawa safa ba sunyi fari tas dasu tafin qafar kamar Baya taka qasa fuskarsa sai annurin kwarjini yake fitarwa take taji hankalinta yasake tashi da kishinsa duk da tasan bama Abune me yiyuwaba mijinta yaso Amatu sbd halayensu sunyi gabas da yamma sam Babu Abinda zaisa ma ya iya kula Amatun amatsayin Mata.

 

Qarasowa kansa tayi ta tsaya zatayi Magana sai kawai kuka ya kufce Mata Mai Dan qarfi batasan lokacinda ta durqushe agurinba tana rufe fuskarta kukan na qara tsanantuwa.

 

Bude idanuwansa yayi dasukai jajir sbd pressure dayashiga shima akan wannan auren Wanda yayi Magana dasu Modibbon sun nuna babu fashi kawai yaje yayi Shiri,

Bai iya hayaniyaba bare gardama da manyansa shiyasa kawai ya taho sbd bazai iya tsayawa hayaniyar gardama ba dasu Modibbo musamman da Andi yafara daukar zafi kamar zai Dora laifin akan Modibbo shiyasa kawai ya taho yabarsu suyi yanda suka dama din,

Yaso yayiwa zarah bayani Amma sbd Koda yashigo yaganta cikin walwala saiya share da nufin idan yadawo tafiya zaifada Mata idan Kuma taji shikenan saisuyi mgnar.

 

Tashi zaune yayi ahankali tareda miqewa tsaye Yana zuba Mata idanuwansa dasukai jajir ahankali yaringa nazarinta sautin kukanta na fita ahankali Yana shigarsa sai kawai yaji zuciyarsa da jikinsa sunyi sanyi tausayinta na sake kashe jikinsa ahankali ya durqusa ya kamota ya dagota tareda sanyata cikin jikinsa ya rungumeta sosai Yana Dan bubbuga bayanta batareda ya iya cewa komaiba.

 

Kusan mintuna da dama suka shanye a tsayen Yana sake Bata kyakkyawar runguma harsaida kukanta ya rage Takoma ajiyar zuciya tana sake shegewa cikin jikin nasa.

 

Zaunawa yayi bakin gado tareda zaunar da ita Kan cinyarsa ya kwantar da kanta Kan kafadarsa Yana hade hannuwansu cikin na juna suka damqe ya dago ya kalli cikin idanuwanta da itama shi take kallo ya sakar Mata wani kyakkyawan murmushin daya saka jikinta mutuwa ya bude baki ahankali yace”

 

Zarah kada ki taba tunanin bana son ki sbd irin rayuwar zaman damuke,

All my life Babu abin Dana sani Bayan kadaici,

Bansaba rayuwa da kowaba,

Bansan ta Yaya Zan sake cikin mutaneba nayi rayuwar walwala ba acikinsu,

Mutanen waje sune wainda na Dan Saba dasu sbd sune mutanen dasuka Saba Jana ajikinsu batun yanzuba shiyasa su nake iya sakewa acikinsu,

 

Khalil was the only family dana dauka inadashi sai Modibbo Wanda shima tsakanina dashi umarni ne kawai da bada oda,

Khalil shine kawai Dan uwana Dana sani Wanda yake tsananin qaunata da damuwa Dani tun Muna Yara harya rasu yabarni ni kadai nasake komawa tamkar banida kowa again,

 

Shigiwarki rayuwana da farko na dauka kamar takurawane Amma daga nabawa alaqar dama da mahimmanci saidai daga gareki ke bakya min kallon miji abokin rayuwar dazamu sake kamar kowane normal couples kina min kallon abin tsoro,

Abin shakka dakuma son muyi rayuwa kamar yanda kowannenmu ke buqata wato ta rashin shiga takurawa kowa Wanda yasani Barin muyi irin rayuwar da Kika zaba Mana wato kowa yayi nasa since you don’t want to give it a chance.,

 

Zarah kadaki dauki wannan auren cin Amana ko cin zarafi daga garemu mu duka sbd you know me Sam Banda sha’awar wani Tara Mata,

Dagani har ita yarinyar ma Babu Wanda akai Magana dashi wannan umarninsu Modibbo ne and na amince da umarninsu sbd Inada raayin cigaba da kula da yarinyar da Muhammad so please kadaki ga laifin kowa akan maganar Nan ki mu duka muyi accepting sabon canjin dazamu samu banason doguwar damuwar dazata kawo hayaniya anan,

Idan kin kwantarda hankalinki is nothing compared to ace wani labarin ne na daban kiyi sbd kanki kiyi sbd ni Kuma kiyi sbd ita me zuwan sbd kowa ya zauna lafiya,

Kinsaba zama da ita ai so Kinga ba sabon Abu bane.

 

Wani qaton Abune yazo ya tsaya a maqoshi kamar zai toshe numfashinta idanuwanta dasuka Fara kumbura sukai jajir ta qurawa fuskarsa Ido tanajin da ace da Hali data cire sonsa aranta ta huta da Abinda takeji kamar zata shide,

Sai dai kamar yanda yace kowa ya dauki dangana sbd azauna lfy bazata tayarda hayaniyaba saidai tana buqatar kasancewa ita kadai yanzu sbd tunanin Abinda yakamaceta Dan kuwa idan har Amatu ce za’a aurawa MD din tanajin kamar bazata iya daukaba gwara a aura Masa kowama Banda Amatu bazata iya kishi da Amatu ba zuciyarta bugawa zatayi.

 

Sakinsa tayi ahankali tareda zare hannunta tana kallon cikin idonsa dashima ita din yake kallo kamar bashine yayi dogayen maganganuba yanzu din,

Sakinta yayi shima ta miqe tana share hawayenta dasuka kasa tsayuwa ta bude baki zatayi Magana saikuma ta kasa tayi saurin juya Masa baya ta tattaro jarumta ahankali ta iya bude baki ya furta”

 

Inshallah bazaka samu damuwaba akan hakan ta gefena saidai ka tayani da adduar cigaba da jurewa hakan.

 

Da sauri ta fice ta sauko da gudu ta nufi dakinta tana Shiga ta zauna tsakiyar dakin tareda fashewa da wani irin kukan tsananin baqin ciki tana rufe bakinta sbd kada ya sauko yajita.

 

 

Amatu kuwa kawu da kansa yasameta har daki cikin Daren ya zauna Kan daddumar dakin Yana kallonta da kyau cikin sauti Me nuna matuqar mahimmancin zancensa a natse yakira sunanta ta dago ta kallesa dakyau tana amsawa gabanta na tsananin faduwa..

 

Amatu bani na haifekiba Amma wallahi inajinki tamkar ‘yar Dana Haifa ta jinina,

Kisani duk Abinda Zan iya zartarwa akan ‘dan dazan Haifa Zan iya zartarwa akanku ku biyun sbd irin qauna danake muku keda Usman,

Ni ubane da bazanso ace ‘yata tadawo gabanaba tana zaman jiran wani yazo gareta,

Kinyi aure cikin zuriar dasuke tsananin qaunarki da ganin mutuncinki tareda matuqar qaunar ‘danki Wanda har suka kasa hakurin jure tafiyarki ki barsu,

Amatu amatsayin na na uba gareki kamar yanda na dauki kaina na zarce hukunci akanki batareda na nema shawarar kiba sbd tunanin ke din Zaki karbi duk wani hukuncina da Isa dazan nuna akanki.

Mahaifan Khalil sunzo nemawa ‘dansu aurenki sun roka alfarma nakuma amince musu gashi min yanke shawarar tunda tafiya zakuyi gwara adaura auren sbd samun nutsuwar kowa duk da bataredashi zakuyi tafiyarba goben…..

 

Kalmarsa ta qarshe tasanyata sauke wata qaqqarfan ajiyar zuciyar da saura kadan zuciyar Tata ta buga Jin yace batare zasuyi tafiyarba kenan ba MAHMOUD bane kamar yanda ta zata da farkon zancen na kawu Wanda saura qiri ta zunduma ihun dabata shiryaba Dan tuni zuciyarta tafara harbawa ashe bashi yake nufiba

SALMAN””zuciyarta ta ayyana Mata take tayi saurin rintse ido saidai kalmomin da kawu yayi amfani dasu da farko na ikonsa akanta yasa ta sauke ajiyar zuciya Kai tsaye Dan gajarta zancen tace”

 

Shikenan kawu duk Abinda ka yanke akaina wallahi na amince maka Kuma Dan Allah kadaina cewa bakai ka haifemu ba sbd mu bamuda Wanda yahaifemu agurinmu idan bakaiba,

Ni yarkace zaka iya yanke kowane hukunci akaina batareda ka tambayeniba,

Tunda Dr khalil ya rasu walh Banda raayi gameda zaben miji sbd ra’ayina ya rasu tareda Mijina Dan haka Banda zabi sai Wanda kayi.

 

Da zallar mamaki iyami da kawun ke kallonta saidai tunda ta gajarta zancen ta amince Babu amfanin dogon bayani Bari abar zancen ahaka har zuwa bayan Daurin aure agani.

 

A daran kukan rashin Dr Khalil yadawo Mata sabo tayi kuka kamar mutuwarsa na sabuwa,

Ayau itace zata auri Salman mutumin data dauka aboki Kuma Dan uwa ta Yaya zatai rayuwar aure da wanin Dr dinta,

Wayarta ta janyo ta Kira anty zarah ki zataji sanyi Amma Bata daukaba kusan Kira bakwai no answer

Miqewa tayi tayo alwala tazo tahau nafila tana jaddada adduar ta ga ubangiji akan yabata juriya da hkr na rashin Dr tareda sanyawa wannan auren dazatayi dawwamร mmiyar albarka.

 

 

Koda gari ya waye anata Shirin Daurin aure itakuma da anty salamatu sunata Shirin tafiya sbd jirgin qarfe biyu zasubi Daurin auren Kuma daya da rabi ne after jumaat.

 

Ba wani dogon noqe noqe iyami ta hakura hakanan ta babbata wasu Yan magungunan masu kyau da qarfi tareda yimata gyaran jikin gaggawa Wanda Sam duk basa gaban Amatun hardai qarfe daya tayi aka wuce gurin Daurin auren daya Tara dubban JAMA’A aka shaida akan sadaki naira dubu hamsin kacal.

 

Koda Yan Daurin auren suka dawo su Amatun sungama Shirin komai na tafiyarsu sbd qarfe biyu zasu tashi shiyasa Koda kowa yadawo Dan kada asamu Yan kanzaki akayi airport dasu cikin shirinta na doguwar rigar jallabiyar Kuwait datai mugun yimata kyau Muhammad khalil na hannun anty salamatu suka fito cikin mota a airport din wayarta tayi ringin saiga sunan Dr salman zabeera ajikin wayar take taji jikinta yayi sanyi waifa yanzu mijinta ne ta sauke ajiyar zuciya tareda daukar wayar zatai magana ya rigata da cewa”

 

Congrats Mrs MAHMOUD DAHEER ZABEERA.

 

Ciro wayar tayi daga kunnenta ta kalli sunan Wanda suke wayar takuma mayarwa kunnenta tana cewa”

 

Salman ne??

 

Eh Mana nine kokina jiran Kiran mijinkine MD ZABEERA yanzu yabar zabeera Yana hanyar airport yafasa zuwa daga baya tare zasu tafi…..

 

Salman me Keke cewa yimin bayanin dazan fahimta waye aka daura aurena dashi kaine kokuwa sbd banason boye boye fadamin…..

 

Mezaisa adaura Miki aure Dani Kuma?

Da MAHMOUD ZABEERA dai aka daura muku aure……..

 

Juwace ta dibeta tayi baya gabaki daya jikinta asaki taji antarota jikin babbar rigarsa Fara qal dabai cireba ta Daurin aure.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 6

Advertisement  *_MIN QALB 6_* Wani ‘dan murmushin mamaki haj Maryam tasaki tana miqewa tsaye bayan ta ajiye qaramin…

MIN QALB 1 (mamuhgee)

Advertisement  *_MIN QALB_* _Mamuhgee_ 1 Bismillahir-rahamanir Raheem. Qoqarin durqusawa takeyi ta dauki busashen biredin dataga wani yaro yazo…

MIN QALB 21

Advertisement   MQ 21_*  *_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA…

MIN QALB 7

Advertisement  *_MIN QALB 7_* _mamuhgee_ Kai tsaye change room dinsu ta nufa ta sauya kayanta zuwa na aiki…

MIN QALB 40

Advertisement  ##Mamuh#*_MQ 40_*  Kasa daukarta bacci yayi Kuma ko juye juye takasa tadaiyi lamo cikin lullubin duvet tana…

MIN QALB 50

Advertisement   #*_MQ 50_*     https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg Please subscribe to our YouTube channel ๐Ÿ‘†๐Ÿ‘†๐Ÿ‘†       Advertisements…