MIN QALB 38

Advertisement

 

MQ 38_*

 

 

 

Anty salamatu da umme dake qoqarin fitowa mota jikinta duk a sanyaye itama da wannan auren Dan ganin yau anwayi gari wani ya aure iyalin Khalil dinta,

Yarinyar da Khalil dinta yafiso fiyeda komai wadda ya yarda yarabu da kowa da komai akanta yau tazama mallakin wani

Wani abin sai mutuwa Dan kuwa da Babu Abinda zai raba Khalil da Amatu idan ba mutuwarba,

Advertisements

Amma tunda har MAHMOUD ne ya aureta damuwarta qalilance sbd MAHMOUD dinma mutum ne me matuqar mahimmanci da girma a rayuwar Khalil Dan haka take musu fatan farin ciki me darewa a wannan auren.

Fitowa motar taqarasa Yi itada anty salamatu sukai gaba.

 

Qoqarin dawowa tunanin ta takeyi ga bude Ido ta rufe taga tabbas shi din ne take cikin jikinsa da qarfi ta yunqura ta qwaci jikinta tana sake kallon kyakkyawar fuskarsa dayaqi kallonta ya juya Yana cewa Mal Umar ya fiddo Masa luggages dinsa daga mota.

 

Sake tariyo maganar datayi da Salman tayi cikin kanta tana Dan girgiza Kai tana qoqarin yakice zancen cikin kanta sbd bama zai yiyuba ace anyi tunanin hadata aure da MAHMOUD ZABEERA Rabin ran Anty zarah,

Sam bazaima yiyuba wannan hadin Bayan ansan tsakaninta da antynta Sam Sam……

 

Wayarta ta daga hannuwanta na rawa sbd tashin hankali da tsoron Abinda zataji ta lalubo numbern iyami ta Danna Kira tayita ringin no answer

Da sauri ta lalubo ta kawun tayita kira shima bai daga ba kasa hakuri tayi cikin tashin hankali ta nufi su umme dasukai gaba sosai ganin Bata sauri yasa ta Fara gudu tana kiran sunan umme cikin ficewar hayyaci Dan gabaki daya kanta ya kunce gabaki daya so kawai take a qaryata Mata zancen salman zabeera a tabbatar Mata daba mijin anty zarah aka daura Mata aure dashi ba…..

 

Hannunta aka damqo tareda birkitota tadawo baya gaba daya cikin jikinsa akaro na biyu wannan karon cikin tsananin masifa ta juyo zatai magana idanuwanta suka Shiga cikin nasa daya zuba Mata Wanda ke bayyanar da seriousness dinsa ya bude baki bayan ya Dan kalli mutanen dake wucewa suna kallonta yanda tafara keta gudu ga jallabiyarta very attractive sbd irin me shape dinnan ce Kuma gyalen jallabiyar kawai ne tayi rolling dashi sai handbag dake hannunta…

Advertisements

Murya a daqile yace”

 

Nan ba gurin Wasa bane kokuma Zabeera you better behave yourself….

 

Kasa hadiye Abinda ya tsaya Mata a maqoshi tayi ta kallesa cikin masifar da batamasan tanayiba tace”

 

Hakama rayuwata ba abin Wasa bace kokuma Zabeera dazaka shigo batareda sani ko damata ba,

Nafasa tamabayar kowama kaga agabana Kai Zan tambaya tunda mune abin yashafa inason tabbatarda da cewan da waye aka daura aurena ayau din?

 

Sakinta yayi batareda ya kalletaba ya wuce Yana cewa”

 

She’s crazy.

 

Biyo bayansa tayi tana sake nanata tambayar Amma ko inda take baida alamun kalla saima agogon hannunsa daya kalla yaga time yayi ya wuce Kai tsaye su umme ma tuni suka shige.,

 

Ganin zata Tara Masa attention na mutune dasuka Fara Binsu da kallo suna Magana qasa qasa gashi wasu sunfara ganesa Kuma da alama akwai ‘yan Media agurin yasan good days dinshi sunzo qarshe dama tunda aka daura Masa aure da wannan crazy yarinyar gashi ranar farko ma zata Bata sunansa a idon mutane…,

 

Juyowa yayi ya fizgota da qarfi tareda kallon fuskarta Yana Kai bakinsa daf da kunnenta cikin bacin Rai Mai tsanani yace”

 

I swear idan baki nutsu kindawo hankalinkiba Zan tabbatarda kinyi nadamar sanin zabeera sbd right this moment Zan rabaki da Muhammad ki koma gida keda ganinsa saina tabbatarda baimasan kece mahaifiyarsa ba..

 

Cikowa idanuwanta sukai da wasu irin kwallar baqin ciki cikin rawar murya tace”

 

Bakada Imani Rabin ran Anty zarah.

 

Sakinta yayi tareda dagowa ya juya ya kalli yanda mutane ke kallonsu suna washe baki sbd sun burgesu sun dauka soyayya sukeyi yayi gaba batareda ya tsaya ya kalleta ba jiki amace zuciya na tafasa tabi bayansa tana ayyana irin tashin hankalin dazai biyo baya sbd har abada Babu maganar aure tsakaninta da mijin Zarah.

 

Acikin jirgi seat dinta ne gefen na umme sbd shi Yana first class

Tana zama ta rufe fuskarta wani irin azababben kuka ya kufce Mata ta rufe baki tahauyi zuciyarta na wani irin quna da qarfi.

Umme tasan ayi hakan shiyasa ma batai yunqurin rarrashinta ba sbd tana buqatan kukan ko taji sanyin Abinda akai matan Dan kuwa da tsananin ciwo da kunya Mara iyaka tareda nauyi a aura maka mijin Wanda ya yarda dakai tareda baka qauna Mara iyaka,

Duk su dukan Kam sai hkr Amma zarah ce tafi kowa cancantar ban hkr sbd kishiya ba Dadi musamman irin wannan ta bazata Kuma da wadda baka taba kawowaba

Gashi Amatu mace ce daba kowane namiji zaisamu ya iya Bari ba sbd ita kanta shaida ce tagani akan Khalil dinta tanadai fatar Allah yabasu rayuwa me albarka acikin wannan zaman nasu.

 

Ganin kukan yaqi qarewa gashi lokaci yaja tafiya tayi nisa yasa umme dafa kanta cikin kulawa da taushin murya tace,

 

Amatu wannan kukan dakikeyi Babu sauki ko mafitar dazai kawo Miki acikin wannan alamarin,

Aure dai anriga andaura Kuma banajin akwai abindazai warware hakan Dan haka amatsayina na tamkar uwa agareki Ina baki shawara da umarnin ki daina wannan kukan da duk wata masifa ki aje gefe neman lafiyar danki mukazo ki maida hankali mu dage muga munsamu Abinda mukazo nema,

Ki aje komai muyi Abinda yakawo mu idan yaso Bayan munyi nasara idan ankoma gida sai ayi maganar auren kinji.

 

Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya me qarfi akai akai sbd qarfin kukan datasha Wanda har lokacin zuciyarta Bata daina Mata zafi da ciwo ba tunanin anty zarah da halin datake ciki da irin kallon datake Mata sun kasa barinta sukuni saidai kamar yanda ummen tace su maida hankali Kan Abinda yakawosu neman lafiyar Muhammad khalil idan sun koma za’a yi Yanda za’a yi a warware auren kokuma tun anan zatasan yanda zatayi ya sawwaqe Mata tun anan suna komawa gida kowa yakama hanyarsa.

 

Share hawayenta tayi ahankali tareda dago idanuwanta dasukai jajir suka kumbura sbd tsananin kuka ta kalli anty salamatu taga bataga Muhammad din a hannunta ba ta bude maki cikeda mamaki zatai magana antyn ta rigata da cewa”

 

Yana gurin MAHMOUD.

 

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda mayarda kanta ta jinginar tana rufe idanuwanta tana tuno zancensa na cewa zai rabata da Muhammad take taji kamar tsoro yanason kamata saidai Kuma ita ba anty zarah bace batajin tsoronsa tafison daganan har qasar sin tabisa akan ‘danta duk inda yakaisa.

 

Bacci ne ya Dan dauketa sbd ciwon Kai me tsanani daya saukar Mata sbd kukan datasha har jikinta sai daya dauki zafi Wanda da wuya idan ba zazzabi bane ya damqeta ga tashin hankali,ga kuka,ga pressure,ga fargaba da tsoro duk sun hadu sun dabaibayeta Dole zazzabi ya damqeta me qarfi kuwa.

 

Koda jirginsu ya sauka saidai anty salamatu ta riqota suka fito sbd jiri jiri take gani.,

 

Basusan Yaya akaiba sai ganin wata white jaguar XK120 tayi parking gabansu yanayin motar kawai yasa umme gane MAHMOUD din ne sbd kusan duk Wanda yayi Masa farin sani yasan irin motocin dayake hawa ko a Nigeria ko aqasashen waje.

 

Zagayawa tayi tabude gaban motar tacewa salamatu” Zo sakata anan salamatu.

 

Qwacewa tafara qoqarin yi Jin ance zata shiga gaban motar umme ta kalleta ba Wasa a fuskanta tace”

 

Salamatu zoki shiga mutafi tunda ita Bata tashi tafiyarba.

 

Jin kamar ran ummen yafara baci yasa ta shiga gaban motar ahankali  tareda rufewa tana jinginar da kanta tana kallo gefe zuciyarta na sake cunkushewa.

 

Shiru dukkaninsu Babu me Magana har suka isa wani kyakkyawan building din dake jerin wasu Athens self-contained flats.

 

Parking yayi acikin qatuwar harabar kafin suka firfito shine yafara wucewa gaba kansa na juyawa sbd  baisan ta Yaya zai zauna da mutane acikin gidansa ba Sam baya iya zama da mutane musamman ana inda yake sakewa yayi rayuwarsa gashi harda umme.

 

Forth floor ne nashi Dan haka suna fitowa lift din forth floor da sunansa baro Baro dake rubuce akan qofar shiga sukaci karo *_MD ZABEERA_*

 

da security password yabude qofar yafara shiga tareda kunna fuse na wutar gidan take komai ya kawo haske anty salamatu ta bude Ido da baki tana kallon aljannar duniya tashigo tana kallon sama idanuwanta kaman zasu fado,

Haduwarsu da familyn ZABEERA yasa idonsu suka Dan bude da ganin rayuwar masu kudi da Kuma ganin daular masu kudi Amma anan Kam taga Abinda duk kyau da tsari tareda dukiyar zabeera Bata gani acan ba.

 

Umme ma data Saba da yawon qasashe Saida Nan din ha burgeta sosai ta yaba saidai flat din 2 bedrooms ne bayan master bedroom dake Dan daga gefe saman qananun stairs Wanda aka zagaye da glass door.

 

Sauran 2 bedrooms din Kuma sune suke kallon juna daga gefen hanyar dining can umme tace su nufa sbd ganin can ne masaukinsu danshi tuni yayi hanyar master bedroom dinsa yashige qofar glass din kafin ya nufi qofar asalin bedroom din.

 

Umme ce tashiga dayan bedroom din Amatu da salamatu suka Shiga daya bayan salamatu ta kwantar da Muhammad toilet tafada da sauri sbd fitsarin datake ji tun acikin jirgi Amma tsoro ya hanata ko motsawa bare tayi Magana.

 

Amatu kuwa bakin gado ya zauna tareda rafka tagumi tana dafe kanta dake tsananin Mata ciwo ga tunanin duniya daya kasa barinta.

 

 

Dayake dare ne Babu Wanda yadamu da wani abinci salloli kawai sukai bayan wanka suka kwanta.

Dadin AC da qamshi me sanyaya zuciya tareda gajiyar dake taredasu yasasu samun bacci me Dadi da nutsuwa.

 

 

Qarfe takwas na safe qarar doorbell yasasu fitowa kowanne a shirye sbd zuwa asibiti.

Breakfast ne umme tayi odar daga wani restaurant data bincika online Dan haka Babu Bata lokaci sukaci Wanda suka iyaci Amatu da salamatu suda Basu taba fita waje ba.

 

Bayan sungama anty salamatu batareda kowa ya sataba ta tashi tahau gyaran koina tana gamawa me gidan na fitowa sanye cikin qananan Kaya hannunsa daukeda key din mota da wayarsa sai zuba qamshinsa yakeyi ba kowa a palon sai anty salamatun Dan haka suna gaisawa yace ta sanarwa Amatu Yana mota tafito da Muhammad.

 

Yana ficewa tayi daki ta tararda ita zaune tana hawaye bayan Gama wayarta dasu kawu da iyami da wayar umme da layinta na qasar sungama qara Mata zafi da maganganunsu akan auren.

Kallonta tayi ta fada Mata saqon MAHMOUD din ko kallon anty salamatun bataiba ta miqe ta dauki Muhammad ta fice zuciyarta a cunkushe.

 

Suna barin gidan umme takira yayarta Prof zainab zabeera tace a aiko driver yazo ya dauketa bazata zauna a gidanba sbd irin wannan auren na Amatu da MAHMOUD suna buqatan abarsu su kadai Dan asamu su fahimci juna su bawa auren dama sbd so take kafin sukoma komai ya daidaita tsakaninsu duk da ita sati biyu zatayi Takoma tabarsu anan din.

 

Anty salamatu dataga ummen zata tafi duk sai taji wani iri za’a barta ita kadai tsakiyar amaren duk da umme ta jaddada mata akan ta bada himma matuqa gurin taimakawa komai yatafi daidai tsakaninsu.

Bayan tafiyar ummen wanka tayi itama ta kwanta bacci bayan ta rufe dakinta.

 

A asibiti duk wasu formalities sun cike anyi komai an kwantarda Muhammad din yabiya komai da komai anan zasubarshi saidai su riqa zuwa dubasa shine qaidar asibitin, basubaro asibitin ba sai maraice inda yunwar cikinta ta isheta  gashi asibitin da nisa sosai.

Ahanyarsu ta dawowa Babu me mgn saishi dayake amsa waya akai akai tanaji hadda anty zarah yayi waya.

 

Wanine ya damesa yanason ganinsa akan project dinsa na Nan Athens daya tsaya sbd wata babbar matsala Dole ya juya Kan motarsa ya nufi private joint dake cikin babban hotel din Athens din Yana daukar baqin mirror goggles dinsa ya sanya daidai lokacinda suka shigo gurin Wanda matakan tsaronsa da securities dinsa sukai yawa sbd girmansa da haduwarsa ga mutane sai abubuwan gabansu sukeyi.

 

Shine yafara fitowa Bayan yayi parking kafin yagama fitowa security ya bude Mata motar itama bataso fitaba sbd bataga dalilin zuwa da itaba Amma tsoron gurin da yanayin yanda gurin yake yasata fitowa ta tsaya gefensa yagama waya kafin suka nufi cikin gurin Yana sake amsa wata wayar.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 16

Advertisement   MQ 16_*   Zaune take gaban madubin dakin daya zama Mata tana kallon fuskarta datayi haske…

MIN QALB 41

Advertisement   *_MQ 41_*   *_Masu karanta book din mu Basu biyaba Kuma sunabinmu da mummunan kalami munbarku…

MIN QALB 42

Advertisement   MQ 42_*     Da lakabe anty zarah takai kanta cikin daki sbd dishi dishi da…

MIN QALB 9

Advertisement  *_MIN QALB 9_* _mamuhgee_ Gabaki ‘daya hankalinsa nakan fuskar amatu da ita Kuma hankalinta nakan usi da…

MIN QALB 46-47

Advertisement   MQ 46/47_*     _INA MASU SHA’AWA DA QAUNAR KARANTA LITTAFIN DAZAI SANYASU CIKIN NISHADI DA…

MIN QALB 45

Advertisement   MQ 45_*    Sai Bayan sallar asuba jirginsu ya sauka Nigeria ta dayake ta Kira USI…