MIN QALB 40

Advertisement

 ##Mamuh#*_MQ 40_*

 Kasa daukarta bacci yayi Kuma ko juye juye takasa tadaiyi lamo cikin lullubin duvet tana tunanin inda rayuwa ta daukota tun kuriciya da inda zata kaita kokuma inda yakawota yanxu,

 

Auren mijin wata Sam baya cikin mafarkinta ko tunaninta sbd itama tafison ta bugi gaba da mijinta natane bawai na wata tazo ta aura ba Wanda koma dai yayane mijin wata ta aura za’a ce,

Babbar damuwarta yanxu shine rashin sanin makomarta a wannan auren yanxu,

Tarigada tasani tabbas yaudarar kanta take da tunanin rabuwa da Rabin ran Anty zarah sbd a zabeera Kam ba Maganar saki sai bisaga girmammiyar qadda ko mutuwa,

Advertisements

To ita ga mutuwar ma ta raba Amma Basu barta ta tafiyarta ba an daureta da auren Wanda takewa kallon ya haramta gareta sbd Yana mijin Zarah….

 

Motsin bude qofa taji Wanda yasata sake rintse idanuwanta tana sake yin tsit sbd sanin shine yadawo

Bata tunanin iya kallonsa sbd dai ba tantama a daki daya zasu kwana dan haka gwara ta lafe gari ya waye su Dan inda dare yamusu.

 

Kallonta yayi yaga yanda take lullube har Kai sai bai damuba ya nufi closet ya tube yafada toilet yayo wanka Yana fitowa shima kayan baccin ya dauka ya sanya tareda fesa mist ya nufi gadon ya hayewarsa ya kwanta tareda Dan Jan lullubin ya shige a gajiye yake shiyasa Yana kwantawar bacci ya daukesa ba Bata lokaci.

 

Mamakinsa takeyi ta yanda ba wani tunani ya hau gadon ya kwanta bayan yaganta akai kwance,Abinda Bata saniba shi Sam baima San wani Wai ka kwanta qasa ko Kan kujera ko wani dakin Kan kowane dalili ba Abu daya yasani baya sauya gurin kwanciyarsa akan komai,

Ko agida zarah ce ma idan ta fahimci Yana tattareda gajiya wani lokacin take komawa dakinta ta kwana tabarsa ya huta shikuma tunda raayaintane wannan baitaba hanata tafiyar ba saima sakewa dayafi Yi da hakan wani lokacin

Tana cikin tunane tunanen bacci yayi awon gaba da ita.

 

Da asuba saidata Gama sallah ya tadata ta tashi tayo alwala da jallabiyarta tayi sallar tana gamawa ta cire Takoma tayi kwanciyarta Takoma bacci abinta sbd itamadai bazata iya takura kanta sbd shi ba musamman ma data lura idan ta takura kanta din ko ajikinsa.

Advertisements

 

Shima tana jinsa yagama wayoyinsa yazo ya kwanta kusan atare bacci Yakuma daukesu Basu farkaba sai guraren 10 na safen.

Itace tafara bude idanuwanta ta sauke akan fuskarsa dake fuskantar tata tafara kallonsa ahankali tana tuno haduwarsu ta farko data biyu data uku duk agun sata ne take taji kunyar abin nadawo Mata har batamasan tana rufe fuskarta ba tana girgiza Kai saijin tayi cikin muryar bacci yace”

 

Kadama kifara wani banzan tunani akaina I can smell your blushing..

 

Zaro Ido tayi da sauri cikin wata sabuwar kunya Amma saidatace”

 

Wane tunani zanyi akanka dazaisani Abinda kace kanaji?ni bana tunanin komai….da sauri ta yunqura ta tashi zaune zata sauka ya riqo hannunta Wanda yasata saurin juyowa ta kallesa zuciyarta na Fara bugawa da qarfi shima ahankali ya bude idanuwansa dake rufen bacci baigama dakinsu ba ya sauke akan fuskarta tayi sauri dauke Ido zuciyarta na tsananta bugu har kirjinta na sama da qasa

Ya gangaro da idanuwan nasa Kan kirjinta dake sama da qasa da sauri alamar zuciyarta ce ke harbawa da sauri batareda yayi Magana ba sai ya saketa ta dira da sauri ta shige toilet batareda tasan abinyi ba sai kawai ta bude sabbin brushes din data gani ta dauki daya tafara brush tana kasa kallon fuskarta ko a madubi sbd Jin wani iri kamar kunya kamar fargaba da tsoro.

 

Murtsike kunyarta tayi ta fito tana daure fuska ta tarardashi zaune Kan sofa Yana kunna wayarsa daya kashe da asuba ta nufi fridge ta bude ta aduko lemun carrot da lemon ta zauna a wata kujerar ta bude tafara Sha ahankali batareda ta kalli inda yake ba.

 

Yana cikin toilet aka kawo musu breakfast din dayayi oda da kayan sawa ta karba tareda ajiyewa tana qoqarin duba kayan sbd jeans ne da riguna take gani Abinda takeda burin yiwa Dr khalil zabeera kwalliyarsa har saiya manta da kowace mace duniya Bayan mahaifiyarsa Amma Ashe basuda wannan rabon.

 

Astaghfirllah” tace tana ajiye kayan daidai fitowarsa

Taso Fara cin abincin Amma gabaki daya Babu Abinda ta taba gani aciki bare tasan ya akecinsu shiyasa ta haqura harya Gama Jan ajinsa da ja Mata Rai yazo ya zauna Kai tsaye tace”

 

Nifa yunwa nakeji bansan wanne ne naciba wanne ba’a ci Yi sauri ka nunamin….

 

Baisan lokacinda ya juyo gaba daya Yana kallonta ba wato yamayi sauri…

 

Irin yanda take kallon abincin yasashi sakin wani boyayyan murmushi akaro na farko

Jin shiru tafara hasala tace”

 

Nifa yunwa nakeji nace fa.

 

Baisan lokacinda bakinsa yace”

 

Ok” ba

 

Fara zuba Mata tea yayi ya miqa Mata kafin yafara zuba Mata egg source cikin boiled veggies sbs taji dadin ci Amma Ina tana shanye tea din taci spoon daya na abincin taji zuciyarta na neman tashi ta ajiye tana kallonsa tana girgiza Kai alamar bazata iya ciba.

 

Tea din yasake zuba Mata kafin yasanya spoon yacire komai na cikin tsakiyar burger dinsu ya miqa Mata yana nuna Mata Tasha da tea din.

 

Kaf tea din ita tashanye shi sbd shikadaine Abinda zata iya sawa cikinta shikuma tana kallo yanacin abincin cikin kwanciyar hankali ganin abin zai tayar Mata da zuciya yasa ta miqe ta shige toilet wanka.

 

Bata San yanzu akeyintaba Saida tagama wanka ta daura towel takasa fitowa ta zauna ciki ta shafa Neutrogena oil din data gani aciki tazo jikin qofar ahankali tace ya miqo Mata kayanta…harta juya ta tsaya cak sbd tuno hadda bra zai miqo kenan saiya taba Mata gidan nono da sauri ta fito tana cewa”

 

Barshi barshi nafito Zan dauka da kaina,. tsayawa tayi tana Masa kallon mamaki ganinsa zaune ko alamar ma zai miqo Mata kayan beyiba kamar yanda ta zata kenan da barinta zaiyi a toilet din tayita zaman jira.

 

Takaici yasanyata daukar kayan da qarfi tana daure fuska zuciyarta na zugata akan tabi takan qafarsa ta take Amma ta share ta nufi wardrobe ta bude ta dauko undies dinta tana juyowa taga bayanan kenan yashige toilet a fili taja guntun tsaki tana cewa”

 

Anty zarah kinada qoqari gskia.

 

Turarensa ta fesa kafin ta shirya cikin kayan ta tsaya tana kallon kanta tanajin wani iri sbd irin pencil jeans dinnan ne yakama Yan dogayen siraran cinyoyinta har gwara rigar is loose me Fadi ce sosai Amma ba wani tsayi gyalen jallabiyarta ta daura akai bayan tagyara Daurin talwataccen gashinta daya dan yamutse gurin bacci.

Zaunawa tayi abinta tana lallatsa wayarta sbd dama can ita Allah beyita da nuku nuku ba Kuma burintane samun wayayyar rayuwar Jin Dadi da sakewa, Bata samu daga Wanda taketa mafarki da buri ba wato Dr khalil dinta yanzun dinma bawai tana maida burinta akan MD bane kawai dai zata sakewarta ne bazata takura kanta ba shiyasama batai wata doguwar damuwar akan kayan ba.

 

Dagowa tayi Jin motsinsa idanuwanta suka sauka Kan budadden jikinsa dake tsiyayar ruwan wanka qugunsa Kuma daureda towel brown da sauri ta dauke kanta tana Dan Sosa kanta daya dau qaiqayin bazata.

 

Ganin da gaske shiryawa zaiyi gata a zaune yasata saurin miqewa Takoma gaban TV ta qurawa Mata idanuwa ko qyaftawa batayi tana jinjina ko inkularsa lallai wannan mutumin dasuke gani a zabeera Basu sanshi ba.

 

 

Tsaf ya shirya cikin qananan kayan wainda suke kalar nata sky blue jeans da farar transparent shirt ko zama beyiba ya kalli Inda take yace ta tashi suje.

 

Da sauri ta miqe zata dauko jallabiyarta yace no need for that

Aiko tabiyosa suka fice.

 

Wata kyakkyawar mota ya karba daga hotel din tareda driver suka fita.

 

Gurin abokanan aikinsa suka Fara zuwa wani hotel dake kusada wani ruwa acan suka kwasa sukai bakin ruwan taredasu da abokin nasa mr folaye da matarsa me sabon qaramin ciki daya ‘dan fito kadan.

 

Sakewa tayi da meenat matar folaye sbd yanda tayita janta ajiki take suka Fara sabo anan ne ma taci abinci sbd na Nan yanada dama sosai akan na hotel dinsu sbd akwai chips da noodles akwai pasta duk tasamu taxi daga Nan suka kwasa zuwa wani farm house inda Nan ma sunyi ciye Amatu tasamu abokiyar ciye Nan tasake suka ringa cin duk Abinda bakinsu zai iya daukar dandanonsa Dan itama meenat zuwansu na farko ne Nan da mijinta yayi da ita.

 

Basu Fara Shirin komawa ba sai dare sosai inda taji tafison masaukinsu meenat yafi Dadi ba kunya ta roqesa su koma can ga mamakinta kuwa baice komaiba Amma saigashi anyi musu folaye yasa anmusu reserving suite sukai kwanciyarsu anan.

 

Washe gari sukaso komawa Amma suka shiririce itada meenat wani gurin shopping da aka kaisu gashi yau dinma qananun kayan ne ajikinsu na yau sunfi daukar kalar fatarsu da yimusu kyau sbd black ne gashi ba laifi dukkaninsu sunada hasken fata matuqa

 

Suna zaune a wani snacks and coffee restaurant dake bakin ruwa saiga Kira yashigo wayarsa Yana dagowa yaga video call zarah na Masa.

 

Sam baisan meyasa zarah yanzu take Masa video call ba Bayan shi tunda sukai aure bai tana cewa sunyi video call.

 

Dauka yayi a natse saigata ta bayyana kyakkyawar fuskarta dataji simple makeup na Masa murmushi

Ahankali ya sauke numfashi Yana amsa gaisuwarta da dorawa da cewa”

 

You look great.

 

Wani irin Dadi ne yakusa kasheta sbd baitaba yaba kwalliyarta ba sai yau din ta washe baki tana kallon kyakkyawar fuskarsa dake fidda wani sirrin kwarjini da kyau tace”

 

Thank you,ya kake?ya Athens?

 

Dan kallon wuyanta dake bayyane sbd fadin wuyan rigar jikinta yayi ba laifi yanayin shigar ya burgesa baisan yaushe zarah  tafara koyan saka irin kayan Nan ba ya bude baki a hankali yace”

 

Alhmdlh..

 

Amatu dake hotuna da meenat tunda yafara wayar hankalinta ya Dan koma kansa tafara qoqarin sharewa gano da anty zarah yake wayar meenat ta kalleta tana cewa”

 

Da waye MD ke video call and he seems to be relaxed and cool da yanayin wayar?

 

Numfashi Amatu ta sauke tana murmushi tace”

 

Da matarshi yake waya antyna.

 

Kallonta meenat tayi dakyau tana sake duban MD dako inda suke baya kallo sai kawai tura Amatun kansa da qarfi tana cewa”

 

Oh I’m so sorry I lost my y balance.

 

Kyakkyawar faduwa tayo ajikinsa sbd Saida gaba daya qirjinta ya hadu ya manne da nasa dayake shima a bazata yajita jikinsa saiya riqeta sbd karsu Fadi qasa daka Kan kujerar dayake.

 

Anty zarah maganar da zatayi bace Mata tayi sbd ganin Amatun jikin MD ba qaramin raunana ganinta da zuciyarta yayi ba ta maida kallonta Kan kayan jikin Amatun saitaga komai iri dayane Dana MD din banbanci nata na Mata nashi na maza hakama budewar wuyan rigar Amatun yasa taji tana kamo nata tana rufewa sbd Abinda taji Yana danne maqoshinta Kai tsaye ta kashe Kiran da kanta tana barin hawayenta saukowa ta kife Kan gadon datake zaune tareda fashewa da wani irin kuka Mai ciwo.

 

Su kuwa can Amatun ce tafara sakinsa ta sauka daga Kan jikinsa tana qin kallonsa sbd yanda taji hankalinta ya tashi da yanda anty zarah ta gansu wani bangaren na zuciyarta Kuma wani irin nauyi takeji saitaji gurin ya gundureta ma gaba daya ta wuce batareda tacewa kowa komaiba.

 

Washe gari Koda qarfe dayan Rana tayi sundawo harsunyi Shirin zuwa asibiti sbd ranar ne ranar sallamar Muhammad shiyasa duk damuwarta ta kau cikin tsananin farin ciki take su umme ma sunyi waya zasu hade a asibitin gurin daukosa sbd zumudi tarigasa fitowa Yana saukowa suka fada mota suka nufi asibitin.

 

Koda suka Isa sun tarardasu umme

Kallo daya umme tai Mata tasan komai yafara daidaituwa sbd yanayin ‘yar walwalarta daya Fara dawowa.

 

Bayan dogon formalities aka sallamesa aka Basu dansu murna agurin kowannensu ba’a mgn saidai anbasu kakkauran sharadin kada aringa barinsa sanyi na shigarsa sosai sukace sunji.

 

A gida sasai aka ringa kiransu ana murnar samun nasara saidai anhana ashigo jirgi dashi saiyayi qwari sosai yasamu lafiya shiyasa ana sake kwana  biyu umme ta tahowarta shima MAHMOUD din wata tafiya takamashi aka bar Mata anty salamatu.

 

Ahankali suka Saba da zaman qasar da Jin Dadinta tareda Fara sanin gurare Dan suke Kai kansu siyayya da sauran wasu abubuwan musamman dasu meenat Suma sundawo garin saita haihu zasu koma,

Ga Muhammad tuni ya warware yayi girma abinsa yanzu Yana samun nono koyaushe take ya canza yafara girma gashi hadda jiki sosai yayi gwanin sha’awa,

MD na kiranta lokuta da dama Amma iyakacinsu gaisuwa sai ya tambayi Muhammad wani lokacin ma anty salamatu yafi Kira.

Abu daya ne matsalarsu a garin shine rashin turancin arziki tayiwa kawu mgn saigashi kawu yaje har zabeera da kansa yayiwa su Andi tunin alqawarinsu na barinta karatu Allah yasa MAHMOUD din na Nan sai sukai Masa maganar yasanyata makaranta acan da zaman banzar.

 

Tunda anty zarah taji tafiya zaiyi zuwa Greece taji hankalinta nason tashi Amma ta danne sbd ba laifi ya Dade sosai a gida wannan karon saita danne harda saqon gaisuwarta ga Amatu sbd har yanxu tunda akai auren basuyi mgn ba sbd kowa bai Gama daidaituwa da al’amarin ba.

 

Zaune suke a Palo itada Muhammad dake koyan zama anty salamatu Bata Nan taje gidan meenat dake Dan zazzabi sosai ta tayata hidima.

 

Riga da guntun skirt ne ajikinta Wanda bai kamata ba ko kadan sai hular babies dake kanta Bata Gama rufe Mata gashin Kai ba Wasa takewa Muhammad sosai Yana dariya taji bude qofa batareda anyi knocking ba ta juyo da sauri cikin mamaki sai idonta ya gane Mata shi batasan lokacinda ta saki baki ba tana kallonsa da dukkanin zuciyarta.

 

Shima ita din yake kallo yanda Takoma kamar wata yarinya qarama Babu me cewa itace uwar yaron gabanta tafi Kama da yayarsa ta kusa bama ta nesa ba.

 

Muhammad dake bangala dariya ya kalla har baisan lokacinda ya sakar Masa kyakkyawan murmushi ba yana nufosu.

 

daukarsa yayi Yana kallonsa cikin tsananin qaunar yaron yace”

 

Muhammad you’re looking great and handsome.

 

Kallonta yayi ta sauke kanta tana cewa”

 

Sannu da zuwa.

 

Bai amsaba bai Kuma dauke idonsa akantaba saima kissing Muhammad da yayi a fuska Yana cewa”

 

Thank you.

 

Bedroom dinsa ya nufa daukeda Muhammad Yana cewa”

 

Ko Zaki gyaramin dakin bazai rasa quraba.

 

Bayansa tabi da kallo tana mamakin kyawun daya qaro da wani irin haske

Kodan ta Dade Bata gansabane.

 

Akwatinsa ta tura zuwa dakin nasa ta kallo sbd shine shigarta na farko

Dakin komai na cikinsa farine Wanda ta fahimci shi din yanason farin Abu ta dauko mop da bucket da sweeper ta a ajiye tafara gyaran dakin bayan ta sauya Masa zanin gadon ta goge komai Yana palo tafito Bayan tagama komai ta karbi Muhammad ya wuce bedroom.

 

Da daddare Koda anty salamatu tadawo ta tararda zuwansa tunda tashige daki Bata sake fitowaba Saida safe shima tana Gama shirya musu komai ta wuce gidan meenat sbd zasu sake komawa asibiti da ita yau.

 

Dakansa ya dauketa yaje ya Samar Mata admission da komai na makaranta ya damqa Mata daga can gidansu meenat sukaje dubata.

 

Dagacan gurin cin abinci suka biya sukaci kafin suka dawo gida.

 

Kwanansa takwas a qasar kafin yatafi da kewar Muhammad daya shaqu dashi cikin kwanaki qalilan Dan kullum a hannunsa yake Rabin kwana sai dare sosai yake maidasa hannun mamansa.

Itama bayan tafiyarsa yabarsu da kewarsa sbd kwanakin kullum Muhammad na taredashi.

 

Sosai ta nitsa cikin karatunta gadan gadan musamman dayake me wuyane karatun sbd medical ne tana karantar gynecology sai yazamto hankalinta nakan karatu yanzu fiyeda komai,

USI yazo Mata tareda Dr Salman har so biyu Wanda yasata Jin Dadi fiyeda tunani musamman usi daya dauki Muhammad a hannunsa ji yayi kamar zai hadiyesa sbd so da qauna,

 

Kawu da iyami ma kullum cikin waya suke Gama umme Anty zarah ce dai har yanzu ba wani sauyi sbd takirata har so kusan uku Bata taba daukar wayarta ba shiyasa ta Dan dakata tukuna.

Ta bangaren MAHMOUD ZABEERA kuwa Babu wani sauyi a rayuwarsu saina qaunarsu data zama kamar daya akan ‘dansu sbd tunda Muhammad yayi wayon sanin babansa yake zuwar musu akai akai sbd yaron dako yaushe dadynsa yakeson gani Dan tuni yayi wayo sosai Dan kusan shekararsa biyu kenan harda watanni.

Duk Wanda yasanta abaya yanzu bazai iya ganetaba idanba farin sani kayi mataba,

Ta sauya sosai daga Amatun blue fox Takoma AMATULLAH zabeera,

Sam halayyarta da yanayinta sun sauya,

Yanzu ita mace ce me nutsuwa da Kamala,

Mace ce me aji da ilimin Boko ya shigeta yake Kuma bayyane atareda ita sbd ko zaman awa daya kayi da ita zaka fahimci da likita kake zaune musamman gashi suna shekarar qarshe ta kammala karatunta,

Amatse take data samu hutun wannan shekarar taje gida sbd tayi masifar kewar iyayenta Dan tunda tazo bataje gida ba

Har gwara anty salamatu taje gida harta Dade sosai kafin tadawo gashi ko yanzu tana Shirin zuwa ganin gida Kuma tareda Muhammad zataje wannan karon,

Ga USI ma yagama karatunsa yanzu yadan Fara aiki a asibitin zabeera.

 

Yau su Anty salamatu da Muhammad suka wuce tana dawowa daga rakiyarsu airport ta shige daki ta tube tayi wanka tana fitowa ta sanya three-quarter pink da farar riga Mara nauyi ta daure gashinta da band ta saka qaramar hula ta nufi kicin ta hado flakes da sabuwar madarar ruwa me sanyi ta fito Palo tanasha taji ana qoqarin bude qofa Kai tsaye tasan MD ZABEERA ne ya shigo qasar sbd tasaba da duk zuwansa saidai suji bude qofarsa kawai baya knocking kamar sauran baqi.

 

Juyowa tayi gaba dayanta daukeda mug din hannunta ta kallesa da fararen idanuwanta kafin ta qyafta idonta saiga anty zarah ta fito daga bayansa tana shigowa tareda rufe qofar take kofin hannunta yaso kubucewa tayi saurin taresa hannunta na rawa.[

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 50

Advertisement   #*_MQ 50_*     https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg Please subscribe to our YouTube channel 👆👆👆       Advertisements…

MIN QALB 49

Advertisement   #*_MQ 49_*       *_THE FLAVORLAND BY ACEEY_* Ina ma’abotan son ingataccen yaji, Different Flavors…

MIN QALB 10

Advertisement  _*MIN QALB 11*_ _mamuhgee_ Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins…

MIN QALB 48

Advertisement   MQ 48_*   *_THE FLAVORLAND BY ACEEY_* Ina ma’abotan son ingataccen yaji, Different Flavors that complements…

MIN QALB 9

Advertisement  *_MIN QALB 9_* _mamuhgee_ Gabaki ‘daya hankalinsa nakan fuskar amatu da ita Kuma hankalinta nakan usi da…

MIN QALB 3

Advertisement  *_MIN QALB 3_* _mamuhgee_ _Min qalb Na kudine_ Daki ‘daya ya dauka iyami da amatu suka dauka…