MIN QALB 41

Advertisement

 

*_MQ 41_*

 

*_Masu karanta book din mu Basu biyaba Kuma sunabinmu da mummunan kalami munbarku da Allah idan kunada rabo Allah ya shiryeku_*

 

Wani irin bugu zuciyarta keyi me qarfi da sauri hannuwanta na Yar rawa take kallon anty zarah din da akwatinta datake janye dashi batasan lokacinda wani qarfin hali da juriya suka shigeta ba ta qaqalo wani talwataccen murmushi tana ajiye cup din hannunta ta nufi anty zarah din da itama tafi Amatun dauke wuta tana cewa”

 

Anty zarah sannu da zuwan bazata.

Advertisements

 

Duk yanda anty zarah din taso Nemo qaqalo murmushi ta nema ta rasa sai kawai ta ‘dan washe baki Wanda kowa yagani yasan yaqene Tace”

 

Amatu sannu da gida mun sameku lfy?

 

Akwatinta Amatun ta karba tana qarasa shigo Mata dashi ciki tana cewa”

Alhamdulillah anty.

 

Rasa abinyi tayi sbd ruden datake duk da ba’a iya ganewa sai kawai ta nufi kicin ta hado drinks da snacks a tray ta fito dasu tana ‘dan satar kallon inda ya zauna Yana sauya layinsa zuwa na qasar ahankali ta ajiye tray din gabansu tace”

 

Dady sannu da zuwa.

 

Advertisements

Qwarewa anty zarah tayi da ruwan data zuba bakinta duk suka juyo suka kalleta bandashi daya dauke Kai baima Gama juyowarba tace sannu anty ko ruwan yayi sanyi ne da yawa.

 

Batareda ya kalletaba yace”

 

Ki gyaramin dakin and kiban keys din motarki zan fita urgent.

 

Miqewa tayi tana Dan Jin wani iri ta nufi dakinta ta dauko Masa keys din ta miqa Masa ya fice ta juyo ta kalli anty zarah datai saurin dauke Ido daga kallon datake Binsu dashi tace”

 

Anty zarah Bari nakai Miki kayan dayan dakin tunda anty salamatun ma Bata Nan kafin agyara nasa dakin saiki koma can ki shigo kiyi sallah ki huta idan nagama saina Dora dinner.

 

Batareda tace komaiba ta miqe tabi Amatun har cikin dakin ta ajiye Mata akwatinta tareda ficewa tana cewa”

 

Ina zuwa anty idan akwai Abinda za’a yi Miki ki kirani.

 

Tana fitowa dakin ta sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya tareda dafe qirjinta tana Kiran sunan Allah.

 

Itama anty zarah Amatun ta fita ta sauke numfashi me qarfi tana cewa”

 

Ya Salam.

 

Daukar akwatinsa tayi ta nufi dakinsa ta ita ta ajiye kafin tafara aikin gyaran dakin tanayi tana sauke ajiyar zuciya akai akai.

 

Tana gamawa Ta nufi kicin ta Dora girkin pasta da cabbage source me  kidney aciki.

 

Har lokacin sallar magriba tayi Bata kammala ba sai guraren 7 ta Gama ta jere a dining ta nufi bedroom dinta ta fada wanka sbd ta ‘dan gaji.

 

Sallah tafarayi bayan tafito wanka kafin ta sanya doguwar English gown Mara nauyi kwata kwata black ta sanya hula ta fito cin abinci.

 

Tana fitowa Yana dawowa amatuqar gajiye yake Dan haka Kai tsaye ya nufi  dakinsa Yana cewa takai Masa abinci can Yana Jin yunwa.

 

Nata tafara zubawa taci ta qoshi tsaf abinta kafin ta hada nasa a tray tareda komai ta nufi hanyar bedroom din nasa tanayin knocking yabude Mata sbd tunanin da Kaya a hannunta sai gashi kuwa hannunta dauke yakeda tray

Daure yakeda towel zaishiga wanka kenan yaji buga qofarta shiyasa ya bude matan.

 

Kallo daya tai Masa ta dauke Kai ta nufi table ta ajiye abincin tana cewa”

 

Ko amaida ne saika fito wankan Dan kada ya huce?

 

No Bari naci kafin nashiga wankan Ina buqatan abincin zansha magani.

 

Zaunawa yayi yafara cin abincin a natse ga ciwon Kai dake matuqar damunsa sbd stress ta juya zata fice yace”

 

Zansha magani Ina buqatan ruwa.

 

Fitowa tayi Dan dauko Masa sai kawai taga anty zarah zaune a Kan dining turuss ta tsaya wata irin kunya da nauyi yasa takasa daga qafa saidata ga kamar anty zarah adin hankalinta nakan abinci kafin taja qafafunta daqyar ta nufi kicin ta dauko Masa ruwan saikuma taji takasa fitowa ta tsaya karba ruwa ahankali tana tunanin yanda zatazo ta keta anty zarah ta shige dakinsa.

 

Jin shiru Bata dawoba gashi yagama ci ruwan yake buqata yasa ya miqe yafito hannunsa daukeda magani

 

Bai lurada zarah dake zaune tsit ba a dining ya nufi kicin inda yake hango Amatu tsaye tayi nisa a tunani

Tana ganinsa cikin kicin din ayanda tabarosa daki dagashi sai towel ta zaro idanuwa cikin tsananin firgici da tsoro ta janyosa da qarfi sukai gefen fridge ta bayan qofa Ido waje da firgici tace”

 

Bakaga anty zarah ba a apalo zaka biyoni Nan Kuma ahaka ba kaya ajikinka me kake tunanin anty zarah zata dauka..

 

Zuba Mata fararen idanuwansa dasukai laushi yayi Yana kallon  tsoron dake bayyane fili akan fuskarta  da bakinta dake Magana kafin ahankali ya sauke idanuwansa zuwa kallon hannuwanta dake riqe da qugunsa har hannunta dayama nakan daidai mararsa yaji ahankali gajiyarsa da ciwon kansa na warwarewa ya maido da kallonsa Kan fuskarta ta  ankare da inda hannunta yake ta zabura zata janye ya riqeta Yana matseta da bango ga idanuwansa dasuka qarasa hargitsata ta bude baki ahankali murya na rawa tace”

 

Anty zarah na Palo kartayi tunanin wani Abu dabam…….

 

Zancenta yasashi sake matseta jikin bangon tayi saurin rintse iso zuciyarta na harbawa tasake bude baki maganarta na fita a rarrabe tace”

 

Dan Allah anty zarah nake gudun ta…..

 

Bakinsa kawai taji akan nata sbd firgita batasan lokacinda ta qanqamesa da hannuwanta ba tana rintse Ido da qarfi.

 

Qarar faduwar plates yasashi saurarawa daga kissing bakinta dayakeyi cikin nutsuwa ya saketa batareda ya kalli kowaccensuba yabar kicin din Dan yasan zarah tariga taga komai yasamu kansa dajin wani iri kamar nauyintama.

 

Amatu kuwa rawa jikinta ya dauka tahau rawar murya tana zazzare Ido sbd tsananin kunya ko kallon inda zarah din take bata iya yiba ta durqusa tahau kwashe plates din tana cewa”

 

Anty zarah Yi hkr wallahi…..

 

Katseta zarah din tayi cikin wata irin muguwar dauriya da danne kukan dake zuwar Mata tace”

 

Saida safe zanje na kwanta.

 

Juyawa tayi tabar gurin tana rufe bakinta sbd kukan dayake Shirin kufce Mata.

 

Ajiyar zuciya Amatu ta sauke tana miqewa daga durqushen datake tattara kayan ta ajiye tareda barin kicin din itama tana sake tunano Abinda ya wakana tsakaninta da MD ZABEERA.

Tana Shiga daki kwantawa itama tayi tana rufe idanuwanta tana Hana kanta tuno Abinda yafaru Amma kamar bazata hanuba zuciyar.

 

Washe gari tun 6 tafito tafara aikin breakfast sbd tanada karatun dazasuyi da annah wata qawarta a school.

Potatoe ball da toasted bread me kwai tayi musu sai lemon tea Takoma daki tayi wanka ta shirya cikin blue straight skirt da light blue chiffon top Me Fadi tayi rolling ta fito riqeda handbag dinta tana duba agogo batason tayi latti gashi key din motarta Yana hannunsa gashi da alama be tashiba tunda bataji motsinsa ba.

 

Zaman jira ta dasa tanayi tana kallon agogo har kusan awa daya sai kawai ta hkr ta miqe ta fice zata hau taxi.

 

Anty zarah ce tafara fitowa Bayan ta Dade da tafiyarta ma  anty zarah din na zama a palon sai gashi yafito a shirye shima da kayan zaman gida ta tashi ta nufesa tana qoqarin Hana shedan Sanya Mata tunanin ko tare yakwana da Amatu ta Dan rungumesa tana qaqalo murmushi tace”

 

Good morning.

 

Dafa kanta yayi Yana amsawa kafin suka nufi dining Yana cewa ta dubo Amatu.

 

Tayita knocking shiru saita bude kawai ta shiga taga Bata Nan taje har qofar toilet din dakin takira sunanta shiru saita tura qofar bayin nanma Bata Nan ganin sanyin toilet din yasa ta fahimci tayi wanka may b ta fita to

Tazo ta fada Masa sai alokacin yayi tunanin may b tawuce makaranta.

Breakfast dinsu sukayi anty zarah ta tattare gurin Bayan sun Gama tadawo gefesa ta zauna tana kallon news taredashi yanayi Yana amsa wayoyi ahankali.

 

Da Rana ganin sun buqaci abinci yasa anty zarah dafa Masa noodles da kwai  itakuma tasake cin sauran breakfast din dasuka rage sbd yafi Mata dadi.

Wanka takuma yowa ta sanyo riga da skirt na atampa tafito tana waya da ummanta dake sake jaddada Mata tayi hkr da dauke Ido akan duk Abinda zai Bata ranta Dan Abinda bakada maganinsa gwara ka rungumi hkr da dauke Ido Dan ita umman batamaso zarah din tabiyosaba da nufin Wai zata Zo duba Muhammad ne sbd tunda aka taho dashi Bata taba ganinsa ba saigashi suna zuwa sukuma suna tafiya.

 

Zama tayi daidai fitowarsa a shirye kamar fita zaiyi ta miqe tsaye tana Yana kyawu da cikar haibar mijinta Wanda kullum sonsa ke qara Shiga Yana Kama kowane lungu da saqo na zuciyarta..

Gabansa tazo ta tsaya tana kallonsa shima ita din yake kalla ganin irin kallon qurullar datake Masa yasan ba komaine ke dawainiya da itaba sai sonsa sai yaji tausayinta da qaunarta na sake shigarsa ya janyota ahankali ya rungume cikin jikinsa Yana shafa Bayanta ahankali Jin yanda take sauke ajiyar zuciya ta dago kanta ta kalli fuskarsa cikin sanyin murya tace”

 

I love you so very much MAHMOUD ZABEERA..

 

Dora bakinsa akan nata yayi ahankali Dan nuna godia ga Abinda tafada din.

 

Qarar rufe qofa da qarfi dasukaji yasashi dagowa yana kallon qofar shigowar sukai Ido biyu da Amatu dake Masa wani irin kallon tsana zuciyarta na harbawa da qarfi saikuma ta maida kallonta Kan anty zarah da itama takejin wani iri akaro na farko dataji kaman taji kunyar Amatun ta qaqalo murmushi tana basarwa ta qaraso ciki tana saka wayarta cikin handbag tace”

 

Anty zarah sannu da zaman gida nafita Baki tashiba shiyasa na fice bansanarba gashi ma wallahi lattin danai gudu saidanayi.

 

Ayya bakomai Nima ai nayi tunanin kinjira banfito da wuri ba.

 

Hanyar bedroom dinta ta nufa batareda ko inda yake ta kalla ba batama nuna alamar tasan da mutum ba tana cewa”

 

Bari nashiga ko sallah banyiba wlh.

 

Kamar bazai kalletaba saikuma ya Dan  juya yabi bayanta da kallo kafin ya juyo ya kalli zarah yace suje.

Daki taje ta dauko mayafi da wayarta ko jaka Bata daukaba suka fice.

 

Tunda tagama sallah tayi wanka ta fito taci abinci take zaune Palo tayi waya dasu iyami,tayi da kawu,tayi da umme,tayi da Dr salman zabeera tayi da USI Wanda sukafi awa suna Magana duk Dan tasamu sauqin Abinda takeji aranta Amma takasa samun salama sai kawai ta kunna TV tafara kallo tana dariyar qarfin hali kamar wata wawuya.

 

Kallon agogo tayi taga qarfe goma harda minti arba’in ta miqe taje kicin ta hado tea tadawo ta zauna tana durawa cikinta idanuwanta akan kallo.

Goma da Sha daya da minti Tara taji bude qofarsu ta Dan kalli agogo taga lokaci taci gaba da kallonta tana Shan tea suka shigo ta Dan dago ta kalli anty zarah ta saki murmushi tace”

 

Lah anty Ashe fita kukayi banma Ankara ba wlh na dauka kina ciki kina bacci.

 

Kallonta yayi da mamaki saidai ko inda yake batada niyyar kalla ta tashi tana cewa”

 

Anty kawo kayan na riqe Miki.

Ta karbi kayan hannun anty zarah din yakai Mata har dakinta ta fito tana cewa”

 

Bari naje na kwanta gobema inada zuwa makaranta da safe.

 

Shigewa tayi ta rufo qofa ta Isa bakin gado ta zauna tareda sauke ajiyar da numfashi me qarfi idanuwanta na cikowa da hawaye batasan lokacinda ta kifeba Tana sakin kukan kewar Dr khalil dinta.

 

Washe gari ko abincin breakfast qin Yi tayi ta wucewarta makaranta taga keys dinta na mota ya ajiye Mata a palon taqi dauka ta tafiyarta.

Bata dawoba sai yamma tayi shigewarta bayan tashiga har dakin anty zarah sungaisa.

Washe gari ma haka takuma ficewarta ba Wanda yaganta sai abin yazama kamar tana wasan buya dasune Dan tasawa kanta zama very busy kullum Babu me ganinta take fita har gwara idan tadawo sukan gaisa da antyn tata ogan gidan kuwa Sam taqi Bari suga juna tuni kewar su Anty salamatu da Muhammad suka sanyota gaba gashi meenat batanan bare taje gidanta,

Wata Rana idan tafita shopping kawai take zuwa idan ba makarantar sbd kawai ta Hana kanta zama gidan.

Kusan kwana takwas kenan tana wannan wasan buyan dasu duk da itama ta matuqar gajiya da wannan yawon hutu take buqata Amma bazata iya zama gidan ba matuqar ba tafiya sukaiba sbd har yau fama take da ciwon zuciyar Abinda idanuwanta sukai Mata gani shiyasa ta zabi raba kanta da zaman gida.

 

Yau sai magriba tadawo gidan amatuqar gajiye take Bata tararda kowa agidan ba da alama sun fita basa Nan Dan har dakin anty zarah tashiga Bata nan sai kawai tayi wankanta tayi sallah ta sanya wata qaramar riga Mara hannu red da bumshort baqi wanda ko cinyarta bai saukaba sosai tafito ko dankwali Babu akanta taje ta sanyawa qofar shigowa key tana sakin numfashi Dan rabonta data sakata acikin gidan tun ranar dasuka Zo tasaba Bata cika son Kaya masu nauyiba yanzu kullum kayanta gajeru ne dasuna sukadai Amma tunda sukazo take a takure.

 

Kicin ta nufa ta hada celeals din Muhammad Tasha acan kicin din Tasha ruwa tadawo Palo zata zauna sai ganin mutum tayi zaune Yana waya a natse cikin tsananin firgici da tsoro ta bude baki Yana lurada Abinda zatayi ya janyota ta Fado kansa ya sanya hannu daya ya rufe Mata bakin Yana kallon cikin tsakiyar idanuwanta dake kallonsa ahankali yace”

 

Shihhh wayana me mahimmanci ne don’t make a sound..

 

Tsit tayi tana kallon bakinsa dake Magana da Wanda yake wayar cikin burgewa da rashin garaje.

Maida kallonta tayi Kan qofar shigowa taga tananan rufenta to kenan Yana dakinsa Koda tayi tunanin basa gidan.,

Qofar dakinsa ta kalla batasan lokacinda tace”

 

Ina anty zarah??

 

Wani kallo ya juyo yayi Mata na tsawon mintuna kafin ya datse wayar dayakeyi ganin yafara rasa gane Abinda suke tattaunawa ya ajiye wayar Yana kallon fuskarta da ba annuri ya sake matseta cikin jikinsa yace”

 

Mezaki Bata da kike tambayarta?

 

Qin kallon fuskarsa tayi tafara qoqarin qwacewa tana cewa”

 

Sakeni kada ta fito ta……

 

Menene koyaushe kike cewa kada ta fahimta?

 

Kallonsa tayi a gundure tana sake qoqarin qwace jikinta tace”

 

Matarka ce Dan haka bazataji dadin ganinka da wata ba..

 

Bakinta ya kalla cikin taushin muryar son qureta yace”

 

Hakan kikeji shiyasa kike ganin kaman itama hakan takeji.

Da sauri ta kallesa tace”

 

Menene?

Ni banma San me kake cewaba.

 

Matsota yayi ta qarasa mannewa jikinsa ya kalli fuskarta zuwa bakinta dazaiyi kissing saikuma ya fasa ya miqe da ita a jikinsa ya nufi hanyar dakinsa sbd dukkaninsu idan ya fahimci matsalarsu ta baifi kowacce data Ganshi da ‘yar uwarta ba Amma na Amatun yanason tabbatarwa ne idan yashiga zuciyarta kamar yanda yake tunani sbd zafin kishi me tsananin daya hango a idanuwanta.

 

A tsakiyar gadonsa ya kwantar da ita tareda sakar Mata dukkanin nauyinsa ta rintse Ido sbd idanuwansa dake son karya kuzarinta tadan juyarda fuskarta ta bude baki daqyar sbd mutuwar jiki tace”

 

Anty zarah zata…..

 

Rufe Mata baki yayi Ahankali da nasa Yana Dora hannunsa Kan wuyanta zuwa kirjinta dake harbawa da sauri har batasan lokacinda ta qanqamesa ba tana bude idanuwanta akan nasa idanun dake kallonta cikin wani irin yanayin daya qarasa kashe jikinta

Ya saka hannu yafara zare qaramar rigar jikinta ahankali tayi saurin rufe Ido sbd rigarce kawai ajikinta batada ko bra…

 

Qarar doorbell ne yasata bude idanuwanta ahankali ta Dora akan nasa idanun dasuka sauya kala ta janye jikinta ahankali tareda mirginawa gefe tana Jan duvet ta rufe qurjinta ya saki wani qaramin numfashi tareda tashi zaune yafara daidaita kansa ya miqe ya fita dakin.

 

Kobaa fada ba yasan zarah ce tadawo daga gidan qawarta dataje Dan haka Kai tsaye ya bude qofar fuskarta daukeda murmushi ta shigo zatai Masa Magana yanayinsa yasa gabanta mummunan faduwa ta kalli fuskarsa da sauri zatayi idanuwanta na cikowa da hawaye ganin hakan yasashi Dan dafe goshi Yana cewa”

 

Wat a hell””zama da Mata fiyeda daya.

 

Kallonta yayi Kai tsaye sbd bai iya kame kame ba yace”

 

Zan kwanta and kada ki nema AMATULLAH zata Kwana adakina after 2 days Zaki kwana so please don’t make it too difficult for me kije ki kwanta I know you’re tired.

 

Kadan ya rage anty zarah ta Dora hannu akai ta zunduma ihu

Tafi kowa sanin MAHMOUD din Dan Kai tsaye ne bai iya kwana kwana ba Amma Bata dauka rashin kwana kwanarsa yakai hakaba da zai iya haikatata wata ran.

##mamuh#

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 11

Advertisement  _*MIN QALB 11*_ _mamuhgee_ Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins…

MIN QALB 18

Advertisement   *_MQ 18_* _Mg_       Koda anty zarah tace yazauna suyi breakfast tare baiso karya…

MIN QALB 4

Advertisement  *_MIN QALB 4_* _Mamuhgee_ #ZAFAFA BIYAR#PAY@+234 903 234 5899 OR 09033181070  Tana fitowa dakin ta washe baki…

MIN QALB 42

Advertisement   MQ 42_*     Da lakabe anty zarah takai kanta cikin daki sbd dishi dishi da…

MIN QALB 15

Advertisement   MIN QALB 15_* _mamuhgee_     Jin idanuwa ajikinsa yasashi ‘dan dagowa ya kalli inda suke…

MIN QALB 23

Advertisement   *_MQ 23_*   *_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN…