MOON 43-44

Advertisement

 *_✍🏻43-44_*

“Da Capital letters Moon is your wife Besty,so stay with your parents ko albarkacin hakan”kasa magana Deen yay idanunsa akan bakin mahaifinsa yana jin maganar tamkar a mafarki,tayaya za’ai ace Lolly matarsa ce? Yaushe aka ɗaura auren? Suwaye waliyyan Moon ɗin? Ganin yadda Deen ke kallonsa yasa ya fahimci bai gama gane abinda yake cewa ba,a nutse yake tafiya cikin zallar izza taƙama da haiba

yana tafe yana baza alƙyabbar jikinsa,a gaban Deen ya tsaya yana sakin Murmushi kafin ya sanya hannunsa ya kama hannun Deen ya jasa suka fara tafiya har zuwa wajan wata lafiyayyiyar kujera,zama yay kana ya zaunar da Deen kusa dashi,cikin ƙasa da murya da kuma tattausa harshe yace “Aliyou!!!!” Shiru Deen yay kansa a ƙasa yana da sauke ajjiyar zuciya,kalmar matar kace taƙi gushewa daga cikin kunansa, Eneye ya ƙara cewa “Aliyou!!!” Can ƙasa Deen yace “Abba” girgiza kai Eneye yay yace “Noo!! Besty bana son Abban nan,kace kawai Besty nasan idan kace Abba kana fushi dani ne” Jinjina kai kawai Deen yay  ba tare da yay magana ba, numfashi Besty yaja a hankali kuma ya sanya hannunsa ya jawo Deen zuwa jikinsu ajjiyar zuciya suka sauke a tare,cikin lallami Besty yace “Bana da wani sama da kai,kai nake gani kawai naji daɗi,tunani na kai ne,idan nai farin ciki anyi min maganar ka ne,komai na samu Besty na,to tayaya kake tunanin zan bar rayuwarka ta halaka bayan ina da yadda zanyi na fiddaka daga halin da kake ciki? Ni daman burina bai huce naga ranar da zaka furta da bakinka kace kana son yin aure ba,banda ba’a auran mace tana jaririya to tabbas ko jaririya ka nuna kace kana so babu shakka sai na aura maka ita,bare yarinya kyakkyawa kamar Maimunatou,ba haramun bane Auren macen data girmeka haka kuma ba haramun bane auran ƙaramar yarinya, I’ll do anything for you in dai zakai farin ciki,kana da ikon da zaka ɗauki matarka kaje duk inda kakeso ita ɗin mallakinka ce” wani lallausan murmushi Deen ya saki a lokaci ɗaya dimples ɗinsa da teeths gave ɗinsa suka bai yana,kasa cewa komai yay sai tasbihi da yake ga Ubangiji domin shi ne kaɗai ya ƙaddara faruwar hakan bawai wayonsa ko dabarar sa ba, blue eyes balls ɗinsa ya ɗaga ya kalli mahaifinsa nace cikin ƙasa da murya yace “but how can that happen?” Lumshe idanunsa Besty yay kamar yadda yaga ɗan nasa yay domin kusan habit ɗinsu ɗaya yace “is simple question ai,a ranar da naga kana ƙoƙarin mace min akan soyayyar ƴar ƙwailarka a ranar na sanya aka taramin mutane a acikin Masjid ɗin Masarauta,nasa Chiroma ya zama waliyyinka  ni kuma na zama waliyyin Maimunatou my daughter in-law,a ranar kuma sarkin Adamawa yazu so shi ne da kansa ya bada sadakin Maimunatou,ni kaina kuɗin yaban tsoro 5.7m fa? Amma dake ya tara kuma an tara masa sai ban damu ba,kawai na tayashi addu’ar samun cikar muradin zuciyarsa” rungome Besty Deen yay yana faɗin “Wow Best thank you so much, wlh zuciyarta na gab da bugawa” dry Besty yay yace “akan ƙwailar taka?” Baki ya turo kamar ƙaramin yaro tare da kwaɓe fuska yace “Noo!! Ta girma fa look” ya faɗa yana zaro wayarsa ya shiga nuna wa Besty photonan Moon wanda yay mata a School bata sani ba,shi dai Besty ƙuri yaywa fuskar Moon abune da yawa a ransa,sai kawai ya share domin bai son tunanin yay tasiri a ransa, Nene dai sai Murmushin jin daɗi take sbd farin ciki data hango saman fuskar ɗan nata, miƙewa Deen yay ya ƙarasa wajanta yana zuwa ya rungome ta,kansa ta shafa zare jikinsa yay yace “lemme freshen up” murmushi su kai masa yana ƙoƙarin shiga flat ɗinsa da aka rubuta *OSOHINOYI FLAT* (Yarima flat) yaji an zabga salati ana tafe hannaye idanunsa da suke kamar na mage ya shiga juyawa, Yayinda ce tsaye tana sharce majina tana faɗin “Amma ko sallamme kudai wlh baku iya haihuwa ba,ga yadda ya mayar dani gangalliya bayan nice na bada shawarar ai masa auran sbd zuƙewar da naga ya nayi,a tohh zuƙewa mana yaro jaraba nata cinsa a rai amma babu wanda ya gano sai ni sbd baiwar da Ubangiji yay min,banda baiwa ta Ubangiji tayaya zan iya ganowa Danoo aure yake so fisabilillahi? To dai babu ruwana Wlh,duk wanda ya raina uwar wani tasa ya raina,domin uwa ba tafi Uwa ba” tsaye sukai suna kallonta Deen kam haɗe fuska yay bai taɓa jin kunyar iyayensa ba amma yau tasa yaji, juyawa yay ya nufi cikin tamfatsetsan flat ɗinsa, kuka ta saka masu tana ƙara sharce majina tace “kuna dai kallo ko?? Ɗan rungomar da yay maku yake baƙin cikin yay min,to wlh ta Allah ba ta ka ba wannan shegen jikin naka ma me za’ai dashi?kuma shawarar dana bayar kaje ban yafe ba” shi dai ko takan Yayinda bai biba ya shige flat ɗinsa yana taune leɓansa,Nene ce ta kalli Yayinda tace “Ayyaa! Momma ki san halin jikan naki muma baya raga mana bare ke da kike kaka wajansa” cikin kumfar baki Yayinda tace “Yau nake ganin ɓatan nono a ƙirjin budurwa,to ko a suwa? Me akai akayi ko?nace wacce shararce ko? Basai ya gimamani bai girmamaku banda lalacewa ta yaran zamani har Aliyou ne zai mance hallarcin da nayi masa,yay kashi na wanke ya tunbuɗi na wanke,haka zan ɗaga shi sama ina masa rawa ina _caka masinka ɗan Baba,nace caka masa kinka,_ amma yau Danooo ni yakewa baƙin cikin rumgoma dake ya haɗu da sallamammun iyaye suka zoba masa ido,toni ba gantalalliya bace wlh gidan zan bar maku” daga Besty har Nene kasa magana sukai domin sun fahimci yau rikicin tsofanne ya mutsa,dole Nene taja baki tai shiru tana kallon Yayinda ta nufi flat ɗinta tana share majina,Deen na shiga falt ɗinsa shower ya sakarwa kansa,yana jin zuciyarsa tayi masa wasai ciwon daya keji yanzu babu shi,kwanciya yay saman babban royal bed ɗin sa, babu komai jikinsa sai boxer haka yaja pillow ya rungome cikin ƙaramin lokaci bacci yay gaba dashi wanda rabinsa mafarkin Lollynsa ne. Washegari a makaranta ya kasance Monday tun asuba da Moon ta farka bata koma ba,sai ta zama very weak ta zama wata miskila ko magana sai Feenerh tayi da gaske take baya feedback,a haka suka shiga masjid bayan sun fito suka komai Hotel, ruwa ta ƙara sakarwa jikinta kana ta fito a nutse ta fara shirya sai da ta gama sanya uniform waro manyan idanunta waje tayi sbd hijab ɗin da Dad ɗinta yace ta dinga sauya ya zarce tunaninta domin har gwuiwarta ya sakko, dry Feenerh tayi tace “a’a kaga matar malam Mamman,wannan ai da ake bawa Amira domin zaki fi dacewa da ita” harara Moon ta watsa mata idanunta ya cicciko da ƙwalla harga Allah bata son saka hijab ɗin,kaf school ɗin ita kaɗai ce mai babban hijab wasu ma haka suke tafiya babu ko hijab ita kuma sai ta ɓuge da saka wannan kamar wata Malama?yanzu gashi ya riga ya tafi bare tace ya sauya mata wani,ita akan wanne dalilin ba zai ɗauke mata nata ya bata irin na mu’allima,tana cika tana batsewa ta ɗauki school bag ɗinta ta shige class tunda yanzu ba class ɗinsu ɗaya ba,tana zuwa cikin class ɗin data prioud ɗin farko Faizak ne ga mamakin ta kowa ta samesa a class ɗin, agogon hannunta ta duba taga 8 saura 10 minutes at, kanta ta sunkuyar ƙasa ta shiga wasa da yatsun hannunta tama rasa me zata ce  masa,a jikinta taji kallonta yake tana ɗaga idanunta suka haɗa idanu,gira ya ɗaga mata ita kuma ta turo baki gaba kafin cikin siririyar muryarta tace “Morning sir” idanunsa na yawo a kanta yace “mrng late comer, sleeping baby” ba ƙara magana ba ta shige cikin class ɗin wajan kujerar ta ta zauna,kan ta a ƙasa domin dictation yake masu cikin sauri take Rubutun ta cikin good handwriting ɗinta, after 10 suka fita breakfast ita da Feenerh da Amira suka jera a tare suka nufi danning hall, abinda kowa yake so aka kawo masu Moon aka bata arish da tea da kuma dankali da ƙwai,tana jin shirar dasu Amira suke akan abinda su Yasmin su kaiwa wata new student yarinyar hatta faɗa tarkonsu, Murmushin jin daɗi Amira tayi tace “ai Moon ki gode Allah,duk sanda suka so yin abinsu a kanki sai Ubangiji ya kare ki daga sharrin su” Feenerh tace “haka fa,ai shiyasa addu’a tayi a rayuwa kuma Garkuwa ce ga dukkan Musulmi” jinjina kai Amira tayi tace “MANZON ALLAH yace idan muna jin tsoran zaluncin wani mai iko mu ce”.

*بسم الله الرحمن الرحيم، الله‍م رب السموات ورب العرش العظيم،كن لي جارا من (فلان) وآحزابه من خلانقك،ان يفرط على أحد منه‍م أو يطغى،عز جارك،وجل تناوك،ولا إله إلا أنت.*

_(Ya ALLAH! Ubangijin sammai bakwai,da kuma Ubangijin Al’arshi mai girma,ka kasance mai tsari gare ni daga wane ɗan wane,da dukkan rundunarsa daga cikin halittunka kar wani daga cikinsu ya yi gaggawar azaba a gare ni,ko ya ƙetare haddi,kariyar ka ta buyawa,kuma yabonka ya girma,kuma babu abin bauta wa da gaskiya sai kai)_

Shiru sukai gaba ɗayansu ita Moon sai juya tea take ta gagara shan bare taci sauran abun,Amira tace “To! Kowa dukkan wanda ya zamar da addu’a abokiyar faɗan sa a baki tayaya kike ganin zai tuzarta? Ba kuji ance addu’a makarin mumini ba?” Feenerh tace “gsky kam,shiyasa zama da mai ilimi yake da daɗi wlh,ba kowa zai fahimci hakan ba sai wanda Allah! yasa ya gane” karɓar tea ɗin Moon tayi kana ta ajjiye gefe guda tace,kafin taja numfashi ta fesar cikin ƙasa da Murya Moon tace “haka kuma Manzon Allah! yace kayi addu’a yayin gamuwa da abokan gaba kamar haka;”

*بسم الله الرحمن الرحيم، الله‍م انا نجعلك في نحوره‍م،ونعوذ بك من شروره‍م*

Advertisements

_(Ya ALLAH! Mu muna sanya ka a gabansu,kuma muna neman tsarinka daga sharrace-sharracensu)_

“Ke hakan na nufin babu wata halitta data isa ta cutar dakai a yayinda kayi Wannan addu’ar,koda ta cutar dakai bawai wayonsu ya sanya hakan ta faru ba,haƙiƙa Ubangiji yay mana gata da yayomu a musulmai kuma masu riƙo da addininsu, Uwa ba kuma yadda da ƙaddara,koda su Yasmin sunyi min wani abu ni nasan cewa hakan wata sabuwar ƙaddara ce data bijiromin,kuma ance ƙaddara lokaci gareta wani lokacin sai dai ka bata labarin abinda ya shuɗe,dan kuma ka shiga cikin wata masifar hakan ba yana nufin wai ƙarshen rayuwarka ne yazo ba, a’a nan ma wani lessons Ubangiji yake nuna maka mai hankali ance shike gane ɗin gishin ƙwaɗo,to thank God! Ni Maimunatou idan har addu’a na zama gari ya to tabbas ta zama gari ya gareni domin babu abinda su Sumy suka isa suyi min” gaba ɗaya suka kalleta can kuma Amira tace “Amma wacce damuwar ke hanaki cik abincin?ina lura dake sam baki son cik abinci” murmushi kawai Moon tayi idanunta cike da hawaye tace “wata damuwa tana zama dole kayi ta,domin baka san lokacin da take faɗa maka ba,ji nake kamar zan yi rashi ina jin kamar Dad na bazai dawo gareni ba”. Da mmki Feenerh tace “kmaryay?” Ka faɗa ta ɗaga masu ba tare kuma da tace masu wani abu ba,ganin time na tafiya yasa suka miƙe gaba ɗaya su kowa ya shige class ɗinsa,a last prioud ɗin su Ass-headgril ta kalli Moon tace “Teacher Faizak yana kira a office nasa” juyawa fararan idanunta Moon tayi kamar ba zata ce wani abu ba sai kuma tace “kuma at this time?” Girgiza kai tayi tace “no yace after class” ɗauke kai Moon tayi tare da gyara farin glass ɗinta,suna gama class ta nufi office ɗinsa ta rataya school bag ɗinta,a zaune ta samesa yana operating system ɗinsa shiru tayi masa shi kam duk abinda take yana kallonta ta cikin system ɗinsa,kamar daga sama taji muryarsa yana faɗin “you look like familiar Maimunatou!!” shiru tai masa tana kallon fuskarsa amma a zahiri tunaninta yana ga Dad ɗinta,can taji yace “Yeah! Kina kama da Mai martaba sosai,ban san me yasa ba,ko ni ɗaya nake ganin kamar ohhhu! Amma duk wanda yasan Mai martaba kuma ya ganki dole zai ga kamar” da ƙyar ta buɗe bakinta tace “Ohhh! ALLAH! sarki” miƙewa yay tare da nufar inda take a gabanta yaja ya tsaya, lumshe idanunsa yay yace “su waye samarin jiya??” Idanunta wanda yake ƙara jan hankalinsa ta juya masa kafin tace “samari kuma?”kai ya ɗaga mata yace “Uhm” shiru tai masa ganin hakan yasa yace “da farko kin tsaya da wani har ya riƙe ki,na biyu kuma wani ya ɗauke ya fita dake daga cikin makaranta” sarai ta gane mai yake nufi sai kawai tace “Ohhh! He’s my father” taɓe bakinsa yay still looking in to her eyes yace “Tab, babu kama abin” da rashin fahimta ta kallesa tace “Kamarya?” Ka faɗa ya ɗaga mata yace “nothing” kafin yace “what about your family?” Kai tsaye tace “shi ne ko mai nawa ai, family, friends siblings anything” da sauri yace mata “Out” kamar jira take yana faɗin hakan ta fice,shi kuma saman sofa ya faɗa yana jin zuciyarsa nayi masa zafi,yabar baƙin ciki a can gida,tunda ya kalli Moon yaji soyayyyar ta kamashi amma ya fahimci abubuwa da yawa a tare da ita,me zai mata? Dole ne ya nemi mafita dole ya jawota jikinsa, Moon a coner su ta haɗu da Sumy da Yasmin sun sanya wata yarinya a tsakiya sai shafata suke, Sumy na ganin Moon ta saki yarinyar ta nufi inda Moon take tsaye, harɗe hannayenta tayi tana jiran zuwa Sumy,da farin ciki a fuskar Sumy ta ware mata hannayenta alamar ta isa gareta,wata uwar harara Moon ta watsawa Sumy dry Sumy tayi tace “Yasmin zoki riƙe min ita” da sauri Yasmin ta nufin wajan Moon kafin ta ƙarasa Moon ta saka wata gigitacciyyar ƙara da gudu ta nufi inda Yasmin take tana zuwa ta jata ta haɗa kanta da bango,wata gigitacciyyar ƙara Yasmin tayi sbd zafin daya ratsa ta,nan take kuma kanta ya fashe ganin hakan yasa Sumy tayi waje da gudu domin neman ɗauki,Moon na ihu Yasmin na ihu haka Moon ta danne Yasmin sai duka take.

Kuyi share ɗinsa please fisabilillahi

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MOON 25-26

Advertisement   *⚡ MOON⚡* _✍🏻 Wattpad Nimcyluv_ _25-26_ Advertisements *DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV* https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ Kafin Eki ta sauke…