MOON 47-48

Advertisement

 *MOON*

_✍🏻47-48_

    Mai makon tayi magana duk da tsawar da Deen ya sakar mata,sai kawai ta fashe da kuka iya kar ƙarfinta,baya yay a hankali ya kwanta tare da lumshe idanunsa ya shiga fesar da numfashi,shiru yay mata yana sauraren yadda take kuka bilhaƙƙi! sai da tayi mai isar ta dan kanta tayi shiru ta shiga sauke

ajjiyar zuciya,kusan a tare suke fidda numfashi domin duk sanda zata sauke ajjiyar zuciya sai yaji shima a lokacin ya sauke tasa,shi yay shiru yana son yaji me zata ce masa,ita kuma tayi shiru sbd bata san mene za tace masa ba,jin shirun yay yawa yasa Deen yay clamly muryars very slow yace “What happened to you Lolly??”kuka ta ƙara sakar masa tana ta shiga mutsi da bakinta a ƙoƙarin ta na son faɗin wani abun,but she can’t say anything to her Dad,gaba ɗaya taji ta gaji ta makaranta she need her Dad,runtsa idanunsa yay ya shiga fesar da numfashi da sauri da sauri,da sauri kuma ya zare wayar a cikin kunansa kamar mai neman wani abu haka ya shiga ƙarewa makeken photon Moon dake saman screen ɗin sa ido, cije lips ɗinsa yay kana ya kashe wayar gaba ɗaya ya jefar a saman makeken gadon, bai jira ya kalli lokacin ba ya Miƙe tare da ɗaukan key car ɗinsa ya nufi fita daga flat ɗinsa,wata baiwar sa mai suna Kaltu  tayi saurin shan gabansa kanta a ƙasa tace “Ya shugabana ina dalilin wannan fitar taka??” Ko inda take bai kalla ba ya shige abinsa, Babu kowa a makeken parlour’n dake tsakiyar sides sai ƙarar A.c dake ta kaɗawa ita ɗaya,da sauri yake taka ƙafafuwansa a ƙasa kansa a ƙasa gashin kansa duk ya baje a lokacin idan ka gansa zaka ɗauka wani basamudan ne just like Yayinda’s say, Yana ƙoƙarin fita yaji Muryar Eneye na faɗin “stop here” cak Deen ya tsaya a hankali kuma Besty ya ƙara so inda Deen ke tsaye yana zuwa yace “what are you trying to go?” Shiru Deen yay masa dan shi a yanzu bai jin akwai wanda zai iya hanasa zuwa inda yay niyya,yadda zuciyarsa ke a zalzalashi zuwa gareta ba ƙaramin illa zata masa idan akace za’a hanashi, kafaɗa Besty ya ɗaga yace “anyway idan kaga kamar place ɗin nan toka tabbatar ka zama King of Nufaz” jajayen idanunsa ya ɗaga zuwa ga fuskar Mahaifin na sa,yadda yake kallonsa yasa Besty miƙa masa hannu zai taɓa shi,da sauri yaja baya yana girgiza kansa, cikin ƙara ji yace “don’t ever trying to touch me Abba” waro idanunsa sosai Besty yay sbd sunan Abba da yaji Deen ya ambata,hakan kuma shike nuni da zallar ɓacin ran da yake ciki, ƙara miƙa hannunsa yay zai taɓa shi da sauri Deen ya juya ya nufi flat ɗinsa kamar zai tashi sama,yadda yake fidda numfashi ma kaɗai ya isa mai hankali fahimtar ɓacin ran da Deen ke ciki,kai tsaye side ɗin game ɗinsa ya nufa,yana zuwa ya zare singlet ɗin jikinsa bai tsaya jiran komai ba ya shiga dukan jikin wani ƙaton ƙarfe da iya kar ƙarfin sa. Eki ce tare da Damus zaune suna tattaunawa akan dawowar Deen amma still babu wani impormation daya samu akan yaran da suke da target a kansu, Murmushi Eki tayi tace “wai kayi believe Deen yana aikin da kuka sashi?” Kallonta Damus yay ta ɗaga masa kanta tace “Yeah! Lemme tall you something,Deen ba aikin ku ne gabansa ba,tunda aka gaya masa anyi Missed yarinyar nan,kaga wani action da ya yi akai ne? To Moon she’s with him” Damus da ya kejin abin kamar a mafarki yace “What the you mean by y Eki?” Gyara zama tayi sosai tace bari nai magana cikakken bayani sbd naga kanka babu Uban komai a ciki,daga shisha sai Win, Wannan yarinyar Moon tana wajan Deen,kasan tunda nayi rantsuwa a kansa cewa sai na mallakesa bazan taɓa kaffara ba, muna nan da kai at this week sai kaga Deen yazo,bazan taɓa rabuwa dashi sai na mallakesa,bazan taɓa rabuwa dashi ba sai na rabasa da wannan ƙwailar yarinyar”miƙewa Damus yay tsaye yace “sai yanzu na fahimci abubuwan da nake ta mmki a kansu,Mun saka private investigators,wanda zasu dinga kula da shigensa,to a shekaran jiya yake faɗa min Deen ya dawo gari,na yarda da maganar,kai tsaye na turawa Oga Taju maganar ta email address ɗinsa, nasan bazan taɓa samun magana dashi ko a waya ba ne,amma Oga Taju yace baya son shirme irin wannan,yar dar da yaywa Deen yasan har abada bazai taɓa iya cutar dashi ba,so daga nan ban ƙara magana ba,sbd nasan Oga Taju bazai fahimce ni ba,kaf cikin yaransa babu wanda yafi aminta dashi kamar Deen,tsabar soyayyyar da yake masa fa ya cire gefe guda na sunansa ya bawa Deen,kin san sunansa TAJUDDEEN shi ne ya bawa Deen ƙarshen sunansa, kafin ya yarda cewa Deen yau dararsa yake za’a daɗe,Amma idan har ya san gsky Deen da dukkan family ɗinsa zasu shiga uku tabbas”ya ƙare maganar yana zagaye tsakiyar parlour’n, taɓe baki Eki tayi tace “Wannan matsalarku ce,tawa na riga na shawo akan ta zuwansa kawai nake jira” tana faɗin hakan ta miƙe tsaye tare da nufar ɓangaren en matan gidan,Zau ne ta samesu kowa da abinda yake Salmerh na kusa da Nana wacce take kwance ta lumshe idanunta, Sai kuma Salymat dake zaune tana kallo sai tauna cimgum take,kallon Salymat tayi tace “Saly 2minutes please” tsaki Salymat tayi tace “nifa ba zaki katse min kallo ba,yadda nake masifar son JOHD & AKBAR ɗin nan” kallon cenemar Eki tayi taga yadda Queen Johda da Queen Rakayah,da Queen Salma suke ta fidda makamai suna kaiwa Abu Maleek sara ta ko ina,gefe guda kuma Mahmanga ce da zabgegiyar takobin ta sai sara take kaiwa,gaba ɗaya Masarautar ta birkice,sai ihu Mutane suke an kashe King Akbar,tsaki Eki tayi ta ɗauke kanta tace “Ai ke naga babu tsuntsu babu tarko,lalacewar taki takai kisa Wannan mutanan gaba kina kalla?mai makon kisa romantic film wanda zai kai maki har ka,amma kuma wasting time ɗinki a kan wannan, Allah dai ya kyauta” ta faɗi hakan tana neman wajan zama can kuma tai ƙasa da Murya tace “Wai ya Maganar wajan bokan?anya ba zamu koma ba kowa??” Tsaki Salymat tayi tace “Kina da matsala wlh,da ɗina dake brain ɗinki kamar ta kifi haka take,gaba ɗaya yaushe mukaje? Samnan sati nawa ya bamu yace idan aikin baici ba mu koma?to gaba ɗaya kawo zuwanmu da yanzu ko 4days ba ai ba” lumshe idanunta Eki tayi tace “wlh ba zaki gane ba,a matse nake nafi son ya kawo kansa da wuri wlh” harara Salymat ta fella mata tace “kaji wawiyya,banda hauka gaggawa ai aikin sheɗanne,kawai ki jira soon zaki gansa kamar yadda bokan yace” miƙewa Salmerh tayi tana faɗin “ALLAH ya kyauta” da sauri Eki tace “munafuka ai wlh ko son Deen kike sai dai ki mutu domin na daɗe da fahimtar inda kika dusa”Ita dai Salmerh bata kulasu ta shige part ɗinta, Wayar Nana ce ta fara ihu a hankali ta ɗaga daga can ɓangaren Ovasi yace “Wai Inna ga ta” jin hakan yasa Nana miƙewa da sauri idanunta na kawo ruwa, bakinta na rawa ta shiga faɗin “Innata” da sauri Inna tace “Eh nita walle,Yaya kike?yanzu uban gidanki ya kawo mana kuɗin ai kinki na wannan shekarar,kin san duk shekara sai ya kawo,kedai kiyi masa biyayya babu ruwana wlh sai yay maki baki ya biki tunda matsayin Uba yake wajanki,to ko Ubanki yay maki haka ne??ai baki samu wannan gatan ba” kasa cewa komai Nana tayi sai hawaye  dake bin saman kuncinta,can Inna tace “Ke babu ruwana fa,ko a can kika samu miji kiyi aurenki kawai,to uban me zaki mana idan kin dawo?aikin ƙafa ta ne tuni anyi min nayi rass dani” Ovasi ne ya miƙa hannunsa zai amshi wayar Inna tayi saurin cewa “Nidai idan kika ɓatawa Uban gidanki rai wlh bada yawo na ba” Ita dai Salmerh bata kulasu ta shige part ɗinta, Wayar Nana ce ta fara ihu a hankali ta ɗaga daga can ɓangaren Ovasi yace “Wai Inna ga ta” jin hakan yasa Nana miƙewa da sauri idanunta na kawo ruwa, bakinta na rawa ta shiga faɗin “Innata” da sauri Inna tace “Eh nita walle,Yaya kike?yanzu uban gidanki ya kawo mana kuɗin ai kinki na wannan shekarar,kin san duk shekara sai ya kawo,kedai kiyi masa biyayya babu ruwana wlh sai yay maki baki ya biki tunda matsayin Uba yake wajanki,to ko Ubanki yay maki haka ne??ai baki samu wannan gatan ba” kasa cewa komai Nana tayi sai hawaye  dake bin saman kuncinta,can Inna tace “Ke babu ruwana fa,ko a can kika samu miji kiyi aurenki kawai,to uban me zaki mana idan kin dawo?aikin ƙafa ta ne tuni anyi min nayi rass dani” Ovasi ne ya miƙa hannunsa zai amshi wayar Inna tayi saurin cewa “Nidai idan kika ɓatawa Uban gidanki rai wlh bada yawo na ba” tana faɗin haka Ovasi ya karɓi wayar tare da kashewa yace “Am going Inna” ita dai bata san me yace ba hakan yasa tace “Au har goyo teke Ita Khadii ɗin?”kallonta kawai yay ba tare da yay magana ba ya fice daga cikin ɗan ƙaramin gidan, Durƙoshe wa Nana tayi a wajan tare da rushewa da kuka,bata jin tsanar abinda yake domin komai tayi a yanzu dai-dai ne,haka kuma babu abinda su Damus zasu sata taƙi yi masu, amma me yasa take jin ƙunci da kuma baƙin cikin a cikin ranta? Tana nan zaune har kiran Ammar ya shigo cikin wayarta kasa ɗauka tayi sbd ciwon da kanta yake mata.A can Masarautar Nufaz kam fada cike take da mutane masu yawan gske,manyan mutane na cikin gari Kogi dake wayanta, Tiraki, Chiroma,Sarkin fada,Sarkin aska,Sarkin yaƙi,Waziri,Sarkin ƙofa,Galadima,Hikimai,Dagatai,Masu unguwanni, sa sauransu,sai kuma Bafadawa gefe guda kuma Ex king of Nufaz ne zaune cikin wata iriyar shiga dasu ta IBIRA,Saman wata rantsatsiyyar Kujera wacce aka ƙawata ta da adon ɗanyar azurfa sai walƙiya take tare da sheƙi, ALIYOU ENEYE AHUOYZA shi ne zaune saman kujerar ransa a haɗe,duk yadda ya haɗe ransa amma hakan bai sanya wani sihirtaccen kyau fita daga saman fuskarsa ba, sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda Orange an sanya masa wata Alƙyabba milk sai ratsin Orange a jikin alƙyabbar,ga wani takalmi Kubta mai gashi-gashi wanda ya kasance half covert shoe a ƙafarsa,Gefe guda kuma Sarkin fada ne yake naɗa masa rawani mai bala’in kyau wanda ya kasance mai dai-dai ci,bayan an kammala aka miƙa masa Sandar girma,can kuma aka ɗauko wata zabgegiyar takobi a cikin gidanta, Lokaci da za’a bashi Takobin sai da kowa na fadar ya miƙe tsaye har da Eneye Ahuoyza,cikin girmamawa aka bashi Takobin kansa a ƙasa yasa hannu ya karɓa yana karɓa ya shigar zagaye kansa da ita,sai kuma ya durƙosa har ƙasa tare da miƙa Takobin gaban goshinsa sai kuma ya dawo da ita wajan bakinta ya sumbata,a hankali ya miƙe tsaye tare da komawa wajan kujerar ya zauna, ɗaya bayan ɗaya 

Mutane suka dinga zuwa  gabansa suna zubewa tare da kai masa gaisuwar ban girma, lumshe idanunsa yay sbd nauyin da yaji yana masa,ashe haka sarauta take? Haka take sawa Mutum yaji wata izza da girman kai na musamman,sai yaji bakinsa ya ƙara yi nasa nauyi fiye da ko yaushe, ɗan gyaran murya yay kaɗan tare Mutsa sandar hannunsa, Sarkin fada ne yace “Ma sha Allah kamar yadda kowa ya sani yanzu King Aliyou Eneye Ahuoyza shine sarki,kuma nan da wata uku cif za’ai bikin rantsar da shi kamar yadda akewa ko wanne sarki,muna gdy ga dukkan wanda yazo wannan taron sai kuma ALLAH ya nuna mana ranar da Za’ai bikin rantsar dashi tare bashi sandar girma na gold” daga nan zaman fada ya watse, Deen na ganin mutane sun ragu a fadar ya miƙe da sauri kamar zai tashi sama,da sauri shima Eneye ya miƙe yabi bayan Deen, kai tsaye flat ɗinsa ya shige ya shiga fatali da alƙyabbar jikinsa ya shaddar kawai ya bari,bai tsaya ɗaukan komai ba sai A.t.m ɗinsa da abubuwa masu amfani a garesa, kayansa yasa a trolly sannan ya fito Wata Jakadiya sai kirari take masa,a haka ya nufi babban parlour,a tsaye ya samu Nene da Eneye murmushi Besty yay yace “kana tunanin zan habaka hanaka zuwa wajan matar ka ne?tun ka amshi buƙatata zaka iya zuwa duk inda kakeso but make sure ka dawo before 3mouths” jinjina kai Deen yay sai kuma ya nufi wajan iyayen nasa a hankali ya rungomesa yana basu peak,suma peak sukai masa Nene tace “Allah ya ƙarawa Sarki lfy” Fuska ya kwaɓe ya kalli Besty a marai-raice yace “Abba ka ganta ko??” Dry yay yace “rabu da ita ƴar adawa ce Allah ya tsare ya kiyaye, Allah yasa matar kada tayi fushi dakai”shi dai bai ce komai ba ya kama hanya zuwa harabar Masarautar,nan ya samu fadawa tsaye suna jiransa,samun kansa yay da tafiya a hankali amma ba can ba Sannan kuma bai hana fadawan binsa ba,kansa a ƙasa har zuwa wajan motarsa kai tsaye back seat ya shiga sai kuma driver yaja motar suka nufi Airport.Moon ce tare da Amira suna tafe a hankali domin zuwa wajan football ɗin su kasancewar yau Sunday shine ranar da suke game, Amira ce tace “Moon ke a tunaninki mene yasa ya kashe maki wayar??” Shiru Moon sbd kukan daya tawo mata,tsaki Amira tayi tace “uhm Allah ya kyauta,komai yay zafi maganinsa ALLAH!” Hawaye ne ya sakko daga cikin idanunta cikin ƙasa da Murya kamar zatai kuka tace “He far away for me Amira,wa nake dashi a duniya sama dashi? sai dai naga a zuwa ganin wasu Amma babu ni,he promised to me zai dawo but he broken his promised Amira,kina ganin Yaya Farouk duk sai yazo ban wani ƙalla halaƙa dashi ba amma baya gajiya da zuwa gare ni,why Dad zai manta dani?” Ta kai ƙarshen maganar tana sakin kuka,tsayawa sukai a wajan dake gaba ɗayan su sanye suke da kayan ball na Amira farare na Moon pink,wando da riga ne sai ƙaramin hijab,ƙafarsu sanye da combus da duguwar Safa mai kauri,gaba ɗaya wandon da ƙyar ya huce cinya,ganin sun tsaya yasa Faizak sakin murmushi a hankali ya ɗauke camerar wayarsa daga kan Moon kai tsaye yaywa Mai martaba sending na vedio’n Moon da yay mata, Juyawa Amira tayi sbd ƙarar camera da taji Maimakon taga Faizak sai idanunsa ya sauka akan Deen wanda yake jikin mota ya harɗe hannayensa a saman ƙirjinsa,gashin kansa ya sauka har gefen fuskarsa yay bala’in kyau sbd saloon ɗin da akai masa,ya ƙara fari da ƙiba ga ƙirjinsa daya ƙara faɗi sosai ya zama wani Jibgege, bakin a Amira har rawa yake wajan faɗin “Moon look your Dad is here look at him” da sauri Moon ta juya nan idanunsa ya sauka akansa akaci Sa’a suka haɗa ido,bata san lokacin data saki dry ba sai kuma hawaye ya shiga sakko mata,da sauri ta yarda ball ɗin hannunta ta nufi inda Deen yake tsaye,shikam idanunsa a lumshe suke yana mmkin yadda a kullum ƙara girma take, ga wani shegen hijab data saka,har wani ball take salon a buɗa masa mata, Moon wani ihu tayi ta shiga faɗin “Dad!!Dad!!” Tana zuwa wajansa ta faɗa jikinsa tana sakin kuka.

_Tabbas idan banga comment ba Wlh Wlh ALLAH! Sai nayi sati banyi new update ba_

Advertisements

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MOON 65-66

Advertisement   *MOON* _✍🏾65-66_ DON ALLAH SUBSCRIBE MY YOUTUBE CHANNEL  Advertisements https://youtube.com/channel/UClywbagpRx5qlVyOy0ZPPDA Ware idanunsa Mutumin dake tsaye gefen…