MUGUN DUHU 21-22

Advertisement

 

⚫“`MUGUN DUHU“`⚫

_STORY BY MRS ABDULL_✍️

*_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Advertisements

*_____________________________________*

🅿️_2⃣1⃣_2️⃣2⃣

”Haka Wannan mummunan labarin ya iske su Ahmad sun shiga matukar tashin hankali iyaka musamman mijin ta da ƴaƴanta duk da lokacin kamar AHLAN dinne kawai ya data har yasan me ke faruwa”

      Haka akayi wa Asma’u wanka itada danta aka sada su da gidan su na gadkiya.

Advertisements

Bayan sadakan 40 Ahmad suka yi zama da mijinta akan yara,inda ya kawo korafe korafen sa akan inda zai saka su babu shi kuma bashida ra’ayin yin aure a yanzu dan haka Ahmad yace gaba daya zai dauke su babu wani musu aka hada wa sulaiman da amina kayan su sai gidan Ahmad.

    A wannan daren kuma gaba-daya Rasheeda da fauzah suka tashi da naƙuda , suma kai tsaye asibitin aka wuce dasu sosai haihuwar tazo da sauki sai day ta FAUZAH da taso bada matsala amma an shawo kan matsalar inda komai yazo cikin sauki,dukkansu yaya mata suka haifa,bayan an gyara su aka fito aka sanar da mazajensu farin ciki sosia suka yi da gode ma Allah.

  ”bayan wasu awanni ne kuma aka sallame su zuwa gida kowacce yan uwanta sunzo da haka kowa gidan ta aka wuce da ita.

  ”ranan suna aka rada wa yara suna yar wajen fauzah aka saka mata Asma’u ƙanwar su da ta rasu yar wajen Rasheeda kuwa aka saka mata khadijah.

 ”bayan suna al’amurra sun cigaba da guda na rayuwa ta cigaba da gangarawa , ƴaƴan Rasheeda 4 dukan su mata biyu wanda yazo dasu biyu na Ahmad sai ya’yan Asma’u biyu Sulaiman da Amina sai AHLAN kuma ,gidan Musa kuwa ƴace guda daya SAHLA wacce karfi da yaji AHLAN ya sakawa wannan sunan a cewar sa tunda shi AHLAN ita kuma sai ace SAHLA haka nan suna ya bita,rayuwa tana tafiya komai daydya babu wata damuwa dake tattare da wannan iyali sai farin ciki da annashuwa” kowa yana zuwa makarantar sa babu damuwar komai.

    ”matsala daya da AHLAN ya fuskanta shine ya rasa dalilin da Maryam da zainab suka tsani kurwar shi basu son shi ko kadan basu kaunar shi sosai yake basu haushi basuda wani ayki da ya wuce hantarar sa da zagi basa yi gaban kowa ya rasa miyasa ,watarana a gaban ummi(Rasheeda) haka Maryam zata gaggaya masa magana tun baya fahimta har ya fara ganewa idan ummi taga dama ta tsawatar mata idan kuma ta ga dama tana ji zata gana zaginsa ci kanki bazata ce mata ba ,tun bai gane komai ba har yazo ya gane tsantsan tsana ce kawai ke tsakaninsu.

    ”tsakanin su da SAHLA kuwa ba’a magana kullum ya dawo daga makaranta sai yaje ya duba ta ya kai mata sweet SANNAN ya dawo gida sabo ne mai karfi tsakaninsu kowa yasan da haka din tarbiyya sosia SAHLA ke sha wajen umman t babu wasa shiyasa ta taso da hazaka da ilimi.

   ”tunda Maryam ta ƙalla ido taga haka sai haushin AHLAN da take ji ya shafi SAHLA ba dama taga SAHLA sai ta aybata ta ko ta dake ta ko zagi ,inday AHLAN kuwa yana kusa zai taka mata birki da fadin ”yaya Maryam kinga banison irin wannan dan Allah ki daina duk abinda zakiyi min Ni kiyi amma me SAHLA tayi maki yarinya bata ci ba bata sha ba kiyi ta jibgar ta niday gaskiya baniso.

    ”to marar kunya dan rainin hankali idan na sake dukan SAHLA naji ka budi baki kayi wata magana wallahi kai da ita sai na mugun bata maku rai kai da SAHLA duk ina da ikon ladabtar daku ko? Dan haka kada na sake ji.

    ”to yaya Maryam way shekara nawa kika bani da kike min wannan abin shekaru biyu kawia shine duka wannan kuna da kuke cewa zaki ladabtar da SAHLA da tayi maki me ? Me taci maki niday na gaya miki wallahi kika sake dukanta sai kinga mai zai faru ,karki saka ina ganin girman ki na daina tohm SAHLA wuce mu tafi ya tura kan SAHLA suka bar wajen.

    ”maryam bana son irin wannan kinga yaron nan tun yana baki girma yazo ya fara rainaki ki rike kanki banason haka kin jini? Cewar ummi !

  ”eh naji Ummi , tohm idan ma bakiji ba zaki gani cewar Rasheeda tana miƙewa ”

   Haka rayuwa take gudu yau dadi gobe akasin haka daga Rasheeda har fauzah babu wacce ta sake haihuwa sai bayan shekara goma sannan FAUZAH ta sake samun ciki,tunda labarin cikin nan ya isa ga Rasheeda ta rasa inda zata tsoma ranta abin yayi matukar girgiza ta yanzu kenan fauzah sai ta haihu ita bata haihu ba ? Yanzu idan ta haifi namiji fa kenan kullum fauzah keda Sa’a ita batada Sa’a ina bazai yiwu ba yanzu menene abin yi?

    ”haka tayi ta rubuta wasikar jaki tana goge wa ,to zakara da Allah ya nufa da cara ance ko ana muzuru ana shaho sai yayi, bayan wata tara kuma FAUZAH ta sunkuto ƙaton danta mai kama da Musa sak kamar an tsaga kara ,kamar sub daya da SAHLA dan itama babu abinda ta bari na mahaifinta 

”tunda Rasheeda taga ɗan fauzah taji inama ace nata ne ina ma wannan da daga tsatson ta ya fito ba daga tsatson fauzah ba, haka day aka yi suna aka cashe  aka raƙashe, 

    ” SAHLA da AHLAN murna ba’a magana musamman SAHLA da kullum take cewa Abban ta ”abba mu gidan nan mu kadai ne miyasa sai yace mata muma zamu cika kamar gidan su Maryam, tayi ta tsallen murna ay Wannan haihuwa kamar ita aka yi wa shi haka tayi ta murna .

   ”to haka day rayuwar ke ta gudu ba kakkautawa su SAHLA ana ta girma inda tana da 15 Yes tayi sauka kuma ta daura da hadda ,gidan baba Ahmad ma daganan ba’a sake haihuwa ba su Maryam anyi aure harda ƴaƴanta biyu ita kuwa zainab daya da cikin na biyu ,sai amina ita ba’a dade da nata auren ba (yar gidan Asma’u) ita da farida yar Ahmad ta farko ,Khadijah tana nan ita sa’ar SAHLA ce sai Sulaiman da AHLAN suma makaranta suke tayi, tsanar AHLAN sai abinda ya karu cikin ran Maryam da zainab ,ya rasa dalili ya rasa wannan abu mahaifiyar su na kaunar sa kamar me komai nata AHLAN komai nata AHLAN har mutane ne faɗin ko dan bata da ɗa namiji ne shiyasa amma su kuma kamar su tsunduma shi wuta musamman SAHLA ya rasa me ta tsare masu haka ,kuma suna can suna wahala a gidan mijin sabida halinsu marar kyau ita Maryam uwar miji ita kuma zainab shi mijin da kanshi to haka day rayuwar ke gudu

    ”su AHLAN an gama makaranta shida sulaiman suna nan ana neman ayki ana haɗa wa da kasuwanci sana’ar iyayen su ,kwatsam AHLAN ya samu ayki dama masscom ya karanta nan ya samu aykin sa a nan babbar tashar radio dake garinsu nan fa aka fara zuwa ayki,yana dawowa kasuwa idan babu ayki yana shagunan iyayen su da suka cika suka tumbatsa da kaya har an bude wasu daban sulaiman bai samu ayki ba har yanzu kayan kawai yake saida wa a kasuwa .

   ”tun suna kananan su AHLAN ya ke son SAHLA Babu wani zancen yan uwan taka da ka ganshi kasan soyayya ce kawia ta aure itama tun bata gane komai harta girma ta fara ganewa ,sosia suke soyayyarsu babu wani damuwa a gaban kowa yake iya nuna mata itama haka saiday irin kunya na mata ta ɓoye, babu damar haɗuwar su da Maryam sai zagi da dunguri tana watsa mata habaici ,tsab mahaifiyar ta tana sane amma ta share a cewar ta babu abinda ya zo wa zama SAHLA kwana nawa zata yi a gida , sun taɓa zuwa FAUZAH (mahaifiyar SAHLA) babu lpya suka sami Hajiya zainab da Jamila da sauran kannen fauzah din suna shigowa gate din suka samu SAHLA na shanye kaya basu san Hajiya zainab na gefe ba ,budar bakin zainab tace ke yar iska ana nan ? Tayi maganar da sigar rashin mutum ci..

   ”ina wuni anty zainab cewar SAHLA, dan uwarki da ban wuni ba zaki ganni shegiya ke ga mai saurayi ko yanzu ina yake kiyi magana na faffasa bakin ki..

    ”to uwar ta da tayi nakudar ta ta haife cewar Hajiya zainab na fitowa da ga wani corridor ,sosia zainab da Maryam suka ji tsoro don sunsha harara da zagin ta amma basu zaton wani ya sani bayan AHLAN da mahaifiyar su , Hajiya zainab ne tace..

   ”ko me taci maku oho wannan tsana haka har mahaifiyar ta ta gane ko kunya baku ji kuna cin arzikin iyayenta kuna cutar ta wallahi zaku gane randa Allah ya tadhi kamaku habaiskanci Ni banson irin wannan lamarin wallahi ku kiyaye kanku, simi simi suka wuce ciki SAHLA kuwa cewa tayi anty zainab wallahi bansan ne nayi masu ball

   Cikin ɓacin rai Hajiya zainab tace ”me kika masu kuwa banda bakar zuciya irin nasu ko ubansu suka ɗebo ma oho Allah ya fisu aniyar su ta bisu Ni banason haka Wallah… Ta wuce tana Bala’i

    ”to rayuwa ta cigaba kwanaki na komawa sati , sati na komawa wata ,wata ta koma shekaru , SAHLA ta gama makarantar sakandare,kafin ma ta gama zancen auren su da AHLAN ya kankama soyayya kam ba’a ma magana ta shekara da shekaru ce ,akan sa tana jin zata iya mutuwa shima haka domin ya tabbatar a duniya babu mai sonsa bayan mahaifinsa sai SAHLA sai kuma yaddikon sa Rasheeda ( ummi) sannan yan uwansa da suke Uba daya su biyo baya da kuma sauran mutane”

    ”maganar auren su ta gama kankama domin an kawo kayan aure an gama komai,auren su saura wata uku SAHLA ta gamu da mummunan ciwon da aka rasa gane kansa ✍️

*Dan Allah ina rokon duk wacce take karanta littafin nan da tayi Saving number ta sannan tayi min magana WhatsApp insha Allah zan gaya mata abinda zai biyo baya dan Allah ina rokon wannan Alfarmar plss sai na jiku….*

_07059305867_

*TALLA TALLA TALLA*

*LITTAFIN JANNAT LITTAFIN DA YAZO DA SABON SALO DA HARGAGI DA RUGUNTSUMI WACCE NI MRS ABDULL NA RUBUTA MAKU SHI WACCE BATA KARANTA BA TAYI MAZA TA GARZAYO DOMIN NEMA TA KARANTA KAN FARASHI NAIRA 200 KACAL DOMIN KUWA JANNAT RETURN YANA NAN ZUWA MAKU DA BAYAN SALLA INSHA ALLAH WANDA ZAU ZO MAKU DA WANI SABON SALON MAI RIKITARWA DA CHAKWAKIYA CIKIN SA WADDA SUKA KARANTA JANNAT SUN SANI KU TANBAYE SU KARON HAJIYA SADIYA DA HUDAY KU TANBAYE SU INA NUWAIRAH,KU TANBAYESU ALWASHIN DA TA BUGA KAFIN A KARKARE LABARIN TABBAS KUNSAN DA CHAKWAKIYA KUN SAURARE NI KU TARE NI CIKIN JANNAT RETURN DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA MAI NEMAN JANNAT COMPLETE ZAI YI MAGANA TA WANNAN LAMBAR IDAN BA BIYA ZAKIYI BA PLS KI HAKURA SAI KIN SHIRYA👉*

_07059305867_

*MRS ABDULL ce ✍️*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MUGUN DUHU 15-16

Advertisement  ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫ 🅿️1️⃣5️⃣_1️⃣6️⃣ ”Daura hannu kawai AHLAN yayi akai yana faɗin sun kashe ta,sun kashe min mata.…

MUGUN DUHU 23-24

Advertisement  ⚫“`MUGUN DUHU“`⚫ _STORY BY MRS ABDULL_✍️ https://chat.whatsapp.com/DvzXXgIpkS09c6HC71vxvf Advertisements *_____________________________________*  *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻*  “`{United we stand and succeed;Our…