SAI A LAHIRA 16

Advertisement

 

*🎀SAI A LAHIRA🎀*

              *NA*

*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

Advertisements

            *🅿️age 16*

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_

Advertisements

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

 *_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

……… Kuka nafisatu takeyi kamar ranta zai fita saboda Abu biyu

Na farko sabon mijin da Azumi ke Shirin kakaba Mata da Raba ta da sadik dinta 

Sai kuma fitinar dake faruwa tsakanin babansu da Azumi 

Tana daga daki tanajin su sunata misayar yawu

“Kaima Nan haka da Kai kasan Rashin mutunci”? To zanga Wanda zai sakar wa wani Wannan rigimar don na rantse maka da Uwata sai nafisatu ta auri bilya in ma bakin ciki kake sai dai ka mutu wallahi…

Shima ya tareta da wani zafin zuciya Wanda Bata San Yana da Shiba

“To Ni Kuma zanga yadda za ayi in dai nine uban nafisatu mujahid ne mijinta a wannan karon Azumi Zan nuna Miki shirun da nake yi Miki  kyaleki kawai nake Amma kin kureni Wallahi in bakiyi sannu ba igiyar AUREN ki ma Zan tsinke su duka wallahi jahilar banza marar tunani sai yau nayi nadamar karbar sadakar auren ki  to ki maida hankali ki kureni…….

“To kasake Ni Mana sai ka auro wadda zata yi maka cefanen ai baka burge ba tunda har ka karbi sadakar aurena ai da sai kace akai gaba baka so Amma yanzu ai nayi maka Rana wallahi tunda na cida Kai na shayar da Kai don kasake Ni sai menene? 

Haka sukayi ta rigima inda Kuma Allah ya kawo baba shitu Wanda yazo ba don ya San abinda ke faruwa ba ya samu gidan a hargitse

“Subhanallah Yaya me ke faruwa haka? “Barni shitu Azumi ta kure hakuri na Kuma Wallahi idan Bata taka sannu ba auren ta ma Zan yafeshi ta koma gidan su don ba Zan yarda da wannan Kama karyar ba.

Ya sanar dashi abinda ke faruwa na Hadin mujahid da nafisatu da yake son yi Azumi tace Bata yarda ba Wai shine take sanar dashi Wai wani daga cikin danginta Yana son auren nafisatu Kuma ta bashi Amma Ni saboda ta Raina Ni tace min ba zata hada iri da Hime ba to ko da nakeyin shiru ina kyale ta Akan abinda ya shafe Ni ne zanyi shiru Amma ba Zan yarda da iko akan ya’ya na ba wallahi bare ta kalleni ta karanto min wannan Rainin to Zan tsaya Ni da ita sai na Gane waye mijin tsakanin Ni da ita….. 

Shitu ya tareshi

“Ba za ayi hakan ba Yaya Kai ayi hakuri abi komai asannu Amma Azumi yaushe ake karo tsakanin KWAI da DUTSE? Me gida yace ga yadda Za ayi kice ba haka ba? Ai tana ganin ta mallake Ni tunda har fadawa kawayen ta takeyi Wai ita ke iko Dani to daga yau  tenuwar ikonki ya Kare akaina nine me iko da gidana da Kuma ya’ya na 

Azumi ta mokade baki tace 

“Shitu bafa Zan fasa hada nafisatu da mijin da nayi niya ba ko da kuwa sama da kasa ne zasu hade

“Iko Kuma da yake magana wallahi ko Hadiza bara’u gidan iko Nan ta ganni Nan ta barni akan iko  bare wani lamis can 

Baba shitu yace na lura Azumi kece Baki son zaman lafiya akan lamarin Nan indai magana ma akan mujahid ake yin rigimar to duk ku hutar da kanku dama nazo ne Yaya don ince maka kazo kuje ku Kai kudin neman AUREN mujahid din don ya samo wata yarinya can hunkuyi maganar nafisatu ku barta Allah yasa haka ne yafi ALHERI 

Azumi tace “kaji gaskiyar magana. Malam lamis ya ce to shikenan shitu Allah baiyi zamu hada wannan zumuncin ba…..

A a Yaya in ba ayi akan mujahid da nafisatu ba to za ayi akan Khalil da badariyya don tuni suka gama hada kansu…… Azumi tayi maza tace “wane Khalil din ? “Wane Kika sani? Babu shitu ya tambayeta

Inda malam lamis yayi murmushi yace Allah ya nuna Mana lokacin dama haka Allah yake da haka baba shitu ya koma kaduna inda Azumi ta sake Dora tukunyar tijarar ta

“Wato anga an bullo ta can na toshe shine aka jonawa Khalil badariyya don anga tayi nauyin kasuwa wato yadda aka shanye shitu shima Khalil shanye min shi za ayi to mu zuba da mutum zai Gane ya tabo abinda yafi karfin shi 

Sadik yazo inda yake sanar da nafisatu Wai yayi mafarki wani Abu ya yadauketa abinda ya kasa Gane ko meye Bata boye mishi abinda ke faruwa ba Amma ta sanar dashi kar ya damu shi take so ba Kuma zata yarda da fin karfin da ake shirin yi Mata ba. Kawai sai ganin Azumi sukayi agabansu ta dubi sadik 

“Kai zo ka shige in Kuma na Kuma ganin ka anan ranka ne zai baci anyi Mata miji jeka can ka nemi wata nafisatun Banda wannan

Haka ta Kare mishi cin mutunci ta Kuma saka nafisatu gaba suka barshi tsaye idonshi na Tara kwalla inda yake Jin inama ya Zama me kudin da ba zai yarda da fin karfi ba? Amma sai ya tuna Allah shine me tsarawa bawa Rayuwa me yuwa haka Allah ya shirya nafisa ba matar shi bace haka ya koma gida jiri da zazzabi suka kada shi 

Inda agefe Daya Kuma bilya barda ya sakewa Azumi bakin aljihunshi har da kyautar kujerar makka inda Azumi ta fashe da kuka

“Nice da ziyarar dakin Allah bilya? Abinda na Dade da fidda Rai? Ashe zanyi arziki Nima na bige da shikar Koko? Wallahi sai ka auri na nafisatu Koda mutanen katsina zasu Kare saboda bakin ciki  kaje ka fara hidimar ka in Sha Allah Nan da wata guda za ayi komai agama 

Yayi murmushi Yana saka hannu aljihu ya fito da kudin ya dire agabanta inda ta Kuma fasa kuka da haka ya barta ya tafi taci gaba da kukanta………

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like