SAI A LAHIRA 18

Advertisement

 *🎀SAI A LAHIRA🎀*

              *NA*

*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

Advertisements

            *🅿️age 18*

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_

Advertisements

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

 *_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

…….. Katuwar notar Alh bilya barda ta faka kofar gidan daidai da fitowar malam lamis inda bilyan yayi azamar fitowa ya zube Yana gaishe shi ya tadoshi Yana bashi hannu suyi musabaha inda bilyan ke nokewa

“Dama Ina son ganinka gashi ko sunanka ban sani ba.

Kunya ta kamashi inda ya fada mishi sunan

“To in Banda abinka alh bilya ka taba ganin inda ake maganar aure da mace? Ko baka damu da ko Yar mace zaka aura ba? Ya dago Yana me bashi hakuri

“Kayi hakuri baba tuni nake son ayi maka magana sai akace anyi maka bayani acikin gida Amma a yafeni hakika Nima nayi laifi

Lamis ya gano makircin Azumi na Hana azo wurin shi don ta San ba bayanta zai bi ba don haka yayi mishi uzuri inda yace Dole yaje kaduna wurin kaninshi shitu ya gaishe shi don shine me daurawa nafisatu aure 

Da haka sukayi sallama  

Harkar biki ta kankama inda bilya yasoma hidima ta BAJINTA  lefe akwatu shida cike da Kaya na kece Raini inda agefe guda Kuma uwar biki Azumi ma ya hado Mata Dan karamin lefe Wai tayi fitar biki ga kudi da yake Aiko Mata da su  inda yace kar ta wahalar da kanta wurin siyawa nafisatu kayan daki shi ya siya Mata komai  wannan albishir shi ya kusa saka  Azumi Suma Bata tsinke da lamarin ba sai da aka kawo Mata abinci daga hotel Wanda zata Raba Ranar wunin bikin 

Abinci kala biyar aka kawowa Azumi daga hotel ga ruwan roba da lemun roba kala kala inda Azumi tayi wunin bikinta cikin bada Fadi da hura hanci har Allah Ubangiji ya kaddaro dauruwar auren nafisatu da Alh bilya barda Wanda aka dauro shi a garin kaduna garin gwamna gidan baba shitu inda daga can din kuwa aka dauko amarya zuwa gidan ango bilya barda dake goruba Road

Wani katon gida me cike da daula da Kuma hargitsi inda aka sada amarya da dakinta Wanda aka zuba daula tamkar dakin wata Yar sarki ko wata matar gwamna hakika gidan barda cike yake da dauloli na Rayuwa irin wadda me imani da ya ganta babu abinda zai tuna sai mutuwa da Kuma LAHIRA Amma me gangen DUNIYA Babu abinda zaiyi sai Mike kafa da hura hanci har yake kallon yafi kowa 

Mata ance Wai ba a rabasu da tsegumi hakan ne ma yasa wasu da yawa suka SHIGA zaga gidan don su bawa idon su abincin 

Gida me cike da kayan more wa Rayuwa furanni masu kamshi da fararen tantabaru masu girma har da dawisu masu Dan Karen kyau da burgewa farare tas sunsha Zane 

Suka SHIGA zagayawa suna sambatu

“Oh Allah me iko Wai nafi ce acikin wannan gida me kama da ALJANNAHR DUNIYA nafisar Nan fa me siyar da Koko.

Wata Mata me suna kuluwa tace

“Aini tsorona Allah tsorona ma aikin Allah kar ace mutumin Nan Dan yankar Kai ne Azumi ta dauki diyarta ta aura mishi don ance fa har kujerar makka ya biya Mata.

“Nima naji haka kin San yanzu in kana da kudi duk irin aibunka ba zaka rasa matar aure ba kowa yasan kwadayi ya Kai Azumi bada Yar ta  ki dai dubi gidan Nan 

Haba jama a kwarya tabi kwarya Yar uwarta idan tace tabi akushi sunanta matatta.

Ina nafisatu Ina wannan gidan ? Suna baka dai muna kunne duk tsuntsun da ya Kira ruwa shi ruwan zai doka 

Can wasu Matan da sukace sai sun zagaye gidan suka suka taho suna ta sauri inda suka kwadow su kuluwa Kira dake tsaye wurin fulawowi Kira inda su kuluwar suka waiwayo 

“Ya akayi ne jummai? 

“Ke kuluwa ku muyi ta kanmu wannan gidan ba lafiya wallahi kuzo mu fice

Kuluwa tace “Wai me akayi ne jummai?

“Can baya da muke zagayawa muka gano duk kaburbura ne me zai kawo kabari cikin gida? Aiko sukace kafa me baci ban Baki ba ? Suka soma ficewa aguje  suna barin gidan inda Matan da Basu zagaya ba aka rakosu da turamen atamfofi har da kudi dubu biyar biyar inda suka baro amarya nafisatu gidan bilya barda ita kanta sai da taji gidan yayi Mata Fadi baka Jin komai sai kukan dawisu da sauka da tashin nau oin tsuntsaye kafin ango ya taho shida abokinshi Garba dauke da manyan ledoji……..

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like