SAI A LAHIRA 22

Advertisement

 

*🎀SAI A LAHIRA🎀*

              *NA*

*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

Advertisements

            *🅿️age 22*

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_

Advertisements

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

 *_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

………Wani irin so da Bai taba zaton yanayi Mata ba yaji Yana dukan Zuciyar shi. Me ya kaishi furta kalmar da ya furta ta saki?

Me ya kaishi yin abinda yayi? Gaba daya ya nemi ficewa hayyacin shi inda ko ruwa ya gagare shi hadiyewa bare abinci Wanda in ba nata ba yake Jin kowane abinci garo garo ne. Garba ya iso gidan don ya kalle nafisatu ko zai samu zuciyar shi ta barshi ya huta da yawan mafarkan nafisatun inda ya iske bilya cikin wani hali inda ya ce m

“Mutumina me ya sameka ka yi irin wannan fadawar haka?

Bai boye mishi komai ba ya fada mishi tsautsayin da ya sauko mishi har yayiwa nafisatu saki uku inda yake Jin bashi da sauran Zama lafiya matukar dai Babu nafisatu acikin Rayuwar shi.

Garba yayi murmushi don Yana ganin anzo inda zai fake shima a inuwar nafisatu

“Me kake ganin zanyi don dawo da nafisatu Rayuwa ta Garba?

“Me fa zakayi Banda tayi AUREN kisan wuta ka dawo da abinka.

Ya motsa azabure Yana kallon garban

“Kwarai kuwa Garba wallahi hakan za ayi Bari ka gani in tashi in fita in cigito Wanda zai yi min hakan ko biyan shi ne sai inyi don na gama Gane Rayuwa ta ba zata taba cika ba matukar Babu nafisatu acikin ta tamkar ma Ruhin mu ahade yake …..

Garba ya tareshi Yana riko hannun shi

“Zauna Mana mutumina gani kusa da Kai zaka fita neman Wanda zaiyi maka wannan Yar Alfarmar? Ni Zan auri nafisatun in Kuma sako maka ita ba ma tare da ka biyani ko sisi ba ai tare ta wuce komai,

“Bilya ya soma kada kanshi 

“Ban Yar da dakai ba Garba .

Na fa sanka ciki da Bai har yanzu fa bakayi aure ba kace tunda ga Matan bariki ba zakayi aure ba sai Kuma in hada ka da nafisatu? Ka ko San yadda nake kishinta araina?

“To Bari kaji duk Wanda Zan samo don ya Aure ta sai na kafa mishi sharudda na ko kallon ta ban yarda yayi ba bare ya rike hannun ta bare Kai da nasan zaka iya rike amanar komai Amma Banda amanar mace don haka cire kanka gaskiya ban yarda da Kai ba.

Garba yayi murmushi

“Mutumina har da sharri Kuma? To naji na Kuma yarda ka Bari akwai yaro na Nan Yana min gyaran mota Wanda na kula Babu sabgar Mata agabanshi Wai saboda kawai yaso wata yarinya an Hana shi shine yayiwa Mata kudin goro har Yana cewa ya haka Rami ya binne soyayya kaga idan shi na samo maka tunda har yayiwa Mata bakin fenti inaga ba zai bi ta kan matar ka ba ko Yaya kace?

“Eh to ka kawo minshi don Zan fi yarda da shi akan ka Kuma ko shi sai na shinfida mishi dokoki na idan har zai iya kiyayewa…

“Kar ka damu zai kiyaye don na fada maka yayi Mata jumla soyayyar ma ya binne ta kushewa Bari inje in taho maka dashi.

Da haka sukayi sallama inda shi Kuma ya SHIGA wanka don yaje gidan hajiya Azumi su gyaro ta kudi ne dai zai sakarwa Azumi inda zata gyara mishi wasan shi.

Nafisatu ta iso gidan su inda ta iske an gyara gidan tamkar ba Shiba an rushe an sake sabon gini me ban Sha awa inda zuciyar ta ke fada Mata aikin bilya ne don ya siye imanin Azumin 

Ta SHIGA inda ta iske Azumi ta na saka ruwan leda cikin sabon firich din 

Azumi ta dubeta a sheke 

“Kinyi sanadin da ya sakoki ko? Bata Bata amsa ba ta shige daki saboda cikinta da ya isheta da ciwo inda baby da siyama suke ta wasa atsakar gidan Wanda aka shafe da suminti

Azumi ta tura uzairu Wai ya Kira mata bilya Amma ya dawo yace Mata gidan arufe yake

Malam lamis ya dawo ya iske nafisatu agida ya tambayi ba asi ta Kora mishi bayani 

“To kiyi hakuri nafisatu dama duk abinda Babu Allah acikin sa karshen sa kusa yake Allah yayi Miki zabi mafi ALHERI.

Washe gari nafisatu ta tashi da ciwon ciki me tsanani kafin ma su tafi Asibiti cikin ya zube  inda Kuma bilya ya sallamo gidan  hajiya Azumi ta shimfida mishi tabarma aka gaisa inda take ce mishi sai taga nafisatu ta dawo gida fatan dai lafiya?

Ya sanar da ita yadda sukayi akan dai maganar zubar da cikin har zuwa zancen sakin

Azumi tace

“Ban so kayi saurin sakin ba me ya Hana kazo ka sanar Dani bilya? Saki nawa ne kayi Mata?

“Saki biyu ne hajiya”

“Kayi hakuri don Allah daga yanzu idan ta Kuma yi maka laifi  irin wannan kazo ka sanar Dani ba haihuwa biyu ba ko kurmi da singa ta haife Bata wuce duka wurina ba don haka Bari ta fito ku wuce don yau din ma raggon Kaya tayi 

Ta shiga kwalawa nafisatu Kira ta fito tana yin arba da bilya tayi maza ta hade fuskarta inda shi Kuma ya zuba Mata ido Yana Jin wani Abu ta fizgar shi tamkar mayen karfe 

Azumi ta ce “sai ki dauko mayafinki ki bishi Allah yasa ya Kara cewa kiyi ki kiyi kiga yadda ake wasan gibi da langabu wallahi har gida Zan iskeki in Baki Kashi

Nafisatu ta dubi Azumi

“Ina Zan bishi hajiya? “Ina Kika sani Yar Rainin wayo? Azumi ta Bata amsa tana zaro Mata idanu

 

“Gaskiya hajiya Babu inda zanje Bai fada Miki ya sake Ni ba? To gashi Nan ki tambaye shi Kuma ko da ba saki uku yayi min ba ba Zan koma gidan shi ba sai an baje komai a faifai an fidda me laifi an fiddo me gaskiya.

Azumi ta dubeta

“Ke kar ki kawo min wani guntun iskanci kinji ko? Ba saki uku ba a yanzu saki bakwai ma ana kome bare ke me saki uku indai ba neman magana ba tashi wallahi ko Kuma yanzu in rufe ki da duka tunda kin soma Zama Yar iska…….

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like