SAI A LAHIRA 24

Advertisement

 

*🎀SAI A LAHIRA🎀*

              *NA*

*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

Advertisements

            *🅿️age 24*

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_

Advertisements

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

 *_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

………”Ina fatan Garba yayi maka bayanin irin aikin da nake so kayi min kwaro”?,

“Eh kwarai ya fada min sai dai ance Waka bakin me ita tafi Dadi zanso inji yadda ka tsara abin duk da inaji ajikina kamar zanyi nadamar hakan Amma kimar Garba tasa na kasa Musa hakan ganin ya nufoni da ALHERI  to Nima Ina fatan tabbatuwar ALHERIN.”

“Gaskiya ne kwaro sai dai gaskiya ina da sharudda idan har zaka iya cika sharudda na to ina me tabbatar maka da zanyi maka ALHERI fiye da zaton ka don ban hada son nafisatu da komai a Rayuwa ta ba.

Sunan nafisatu da ya ambato yasa sadik Jin wani Abu me kama Jan shock inda yake Jin wato matar da zaiyi AUREN kisan wuta da ita irin sunan sahibar shi gateta sai yaji zai girmama ta Alfarmar sunanta duk da ba wani dadewa zasuyi ba.

Bilya barda yaci gaba da bayanin shi

“Ka Gane ko kwaro? Sharadi na me sauki ne Amma me yuwa ka kalleshi marar sauki Amma idan kayi duba da cewa kudin Zan biya ka to ba zaka ji komai ba Kuma don kar kabi ta Kan mamata yasa Zan biya ka da kudi masu yawa.

“Na farko dai auren ba zai wuce sati biyu ba zaka sako min ita. Kuma ban yarda ka kalleta ba in ma tana waje to Kai ka koma daki in kuwa kana waje ta fito to ka fice daga gidan kawai ban yarda ka rike ko da hannunta ba bare tsautsayi ya kaika taba min ita domin ko taba ta shine karshen kuskure a Rayuwa wannan shine sharadi na….

“Kar ka damu alh Zan bi dukkan sharadin ka idana Ranar da aka daura auren kake so na sakar maka ita Ni duk Daya anyiwa tuwo barin Mai. Don tuni na haka Rami na binne soyayya don nayi ta banji Dadi ba ko da ake kiranta da ruwan Zuma Ni ruwan madaci ta bani.

“Da kyau kwaro Zan so ka nuna min kwarewar ka akan aikin Nan in har kayi nasarar gamashi lafiya kana da ladar kudi har dubu dari biyar…..

“Kai lallai kwaro ka cika me sa a Dole in tayaka godiya. Cewar Garba da yakewa bilya kallon zaka Gane kurenka

Da haka sukayi musayar lamba  kwaro da bilya inda yace ya saurari kiranshi don ko wane lokaci za a iya daura auren da haka sukayi sallama Garba ya dauko kwaro ya maido shi wurin aiki.

“Karfa ka manta kwaro Kai sunan ka angon bogi nine angon na zahiri.

Sadik ya dubeshi “Amma Garba kana ganin hakan Babu wata matsala agareku Kai dashi?…

“Babu wata matsala ai ta Yan duniya kawai Zan mishi baka kula dashi din wani sauna bane? Nima sai na auri nafisatu na more don Ni in har ta shigo hannu na ma to tagama komawa gareshi don baisan nafi shi sonta ba Kai dai Zama cikin shiri kwaro har kayi nasarar karbe kudin ka Nima Zan Kara maka da dubu dari uku Kai Kam ka tsinci Dame akala da haka suka Rabu

*****  *****  *****

Malam lamis ya dawo inda Azumi ke fada mishi nafisatu tayi Bari Wai Kuma har wani ya ce zai fito neman Aure

Yayi kamar baiji ta ba kafin ya bude Baki ya kwala Mata Kira ta fito ta rusuna ya dubeta.

“Sannu nafisatu Ashe raggon Kaya kikayi? To Allah ya Baki lafiya

Amma meye naki na garajen neman mijin Aure nafisatu?

Ta dube shi da Rashin fahimta

“Azumi tace min wai kin samo mijin aure shine nace saurin me Zakiyi? “To Ni dai baba ban San dashi ba abinda dai nasani bilya ya zo Wai in koma nace ba Zan koma ba tunda saki uku yayi ta iya yuwuwa wani ne da Ni ban sani ba.

Yayi murmushi “Ai na gano Allon nafisatu sun gama mugun qullin su shi da Azumi ne zai turo wani ya Aure ki auren kisan wuta ai in me fadar magana wawane to Bai kamata  me jinta ya zamo Wawa ba don haka tashi kije zanga ta inda za ayi hakan.

Azumi ta soma zazzaga masifarta akan har auren kisan wutan sai anyi wallahi tunda ma sun gano manufar ai shi kenan.

Ilai kuwa sai ga bilya ya zo Yana sanar da Azumi an samo Wanda zaiyi aikin inda tace to ya tura shi wancen da zaiyi aikin kaduna wurin shitu suce lamis din ya turo su. Haka kuwa akayi kwaro da Garba suka nufi kaduna wurin baba shitu inda bilya yayi musu rakiya sai dai bai yarda ya fito daga mota ba don kar balli ya tashi.

Aiko baba shitu ya karbesu da karmci suka fada mishi masu son auren nafisatu ne Kuma Wai lamis din ne ya turo su inda yayi mamaki don shi Bai San auren nafisatu ya mutu ba don haka ya ce su Dan dakace shi 

Ya shiga cikin gida yasa badariyya ta Kira mishi wayar hajiya Azumi inda take ce mishi ai auren nafisatu ya mutune kafin tayi idda Kuma cikin da ta taho dashi ya zube shiyasa zatayi wani auren don ta samu me sonta 

Yaso yaji ta bakin yayan shi Amma Azumi ta toshe duk wata kafa da zaiyi magana da lamis haka baba shitu ya dauro auren suka taho

Bilya ke Kara jaddada wa kwaro yau din Nan za akawo amarya ya tabbatar da ya ki yaye dukkan sharudda ya amsa mishi da ko yanzu yace ya sakar mishi ita to zai saketa da haka suka aje bilya inda Garba ya wuce Kai kwaro shima Yana Kara jaddada mishi manufar tashi 

Da haka ya aje shi ya tafi inda yake son ganin Wai wace kalar macece da har take hada Kan abokai tana gwarawa? …….

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like