SAI A LAHIRA 34

Advertisement

*🎀SAI A LAHIRA🎀*

              *NA*

*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

Advertisements

            *🅿️age 34*

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

Advertisements

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

 *_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

……….Siyama da taga Yana tunkaro su sai tayi maza ta raba motar shi ta wuce yabita da kallo

Inda baby ta soma nuna ajinta irin Wanda take nunawa idan anzo wurinta sai dai tanajin irin wannan babbar harkar da take fata da buri ba zata tsaya Jan wani aji ba ya tsinke ya barta da Allah ya Aiko

“Kuyi hakuri fa na tsaidaku a hanya

“Ba damuwa baby ta fada

“Don Allah ko wannan da ta wuce sister kice?

Baby tayi sak don tasan ba ita yake muradi ba siyama yake so sai taji wani takaici na naushin zuciyar ta.

“Eh kanwata ce ta fada cikin hade fuska

“To yayar mu afuwan dai Allah yasa Zaki bani kanwar ki don kadan ya rage in buga motar nan wurin kallon ta ban taba ganin macen da ta fizgeni irinta ba.

Wani bakin ciki ya soma sukuwa azuciyar baby Amma ta shanye don ta gama Tara buri akan irinsu sai gashi siyama ce me wannan dacen

“Me zai Hana in baka ita matukar zaka saki hannu? Yayi murmushi ” to antynmu shigo mota sai mu karasa gida ko? Ta SHIGA motar inda sanyi AC ya daketa ta sauke ajiyar zuciya inda taji hawaye na Shirin kece Mata me yasa Rayuwar da ta tarawa buri zata zo Amma ga siyama da Babu irin wannan tsarin agareta? 

Suka taho Yana Kara fada Mata yadda ya azabtu da son siyama tun daga kallon farko inda taji duk sanyin AC din da take fatan dauwama acikin na motar shi ya fara fita ranta saboda irin wannan sabanin da aka samu na cikar burinta har ta kagara su iso gida ya sauke ta.

Taci gaba da amsa mishi Amma fa zuciyar ta fal bakin ciki da takaici

Har suka iso gida inda tuni siyama ta rigasu Zuwa 

Tana fitowa daga motar ya zaro dalar amurka sabuwa dal har  dala dari biyar ya Miko Mata ta karba tana yake da sunan murmushi tana godiya tace ya Bari ta shiga ta fito mishi da siyamar

Ta shigo gidan inda siyama ta dubeta.

“Sai dai kiyi hakuri don ba Zan fasa fada Miki gaskiya ba Anty baby babu dacewa mace me mutunci tarika tsayawa da maza a bakin titi ba sai kace wata karuwa.

Me sonka da gaskiya gidan ku ya kamata ya iske ka….

“Ba wurina yazo ba malama bakon kine in da hali Kya iya zuwa don naga akwai harka Atare dashi har ya soma yi min kyautar dala dari biyar

“Ni Babu ruwana da wata babbar harka dake tare da shi Zan fada mishi gaskiyar abinda ke Raina don ma ban iya wulakanci ba wallahi da babu wani namiji da zai tare Ni ahanya in saurare shi

Ta fita waje inda katuwar motar me numfashi ke fake inda ya fito Yana haske ta da murmushi suka gaisa yake fada Mata ya ganta ne Yana so har ya kusa buga motar shi garin kallon ta.

Ta dubeshi 

“Ayya na gode sosai da so da kauna sai dai gaskiya anyi min miji sai dai in baka hakuri Allah ya hadaka da wadda tafini

Bata jira cewar komai ba tajuyo gida inda sukayi kicibus da baby a soro wadda ta hasaso labe tayi Mata

“Ba dai har ya tafiba? Cewar babyn

“To me zai jira tunda ban boye mishi ba na fada mishi gaskiya? 

“Kar dai kice min Bai Yi Miki ba siyama?

“Anty baby kenan nifa ban dauki wannan duniyar da zafi ba bare zafinta ya kone Ni

Babu ruwana da daular dake tare dashi Bai Kuma yi min ba na Kuma fada mishi gaskiya

Baby Bata Kuma tankawa ba ta shige daki tana tufka da warwara

Can aka Aiko ana Kiran baby azaton ta bakon siyama ne sai ta fito da sauri inda tayi arba da Salim

Wani bakin ciki ya turnuke ta ta wurga mishi harara tamkar idonta zai fado

Ya Yi murmushi Yana kallon ta inda ta juya zuwa bayan gidan su inda yara ke taruwa suna wasa ta tattaro yara suka taho inda tace yaran suyi ta jifar shi da duwatsu

Aiko yara suka soma aikawa Salim ruwan duwatsu akace tsautsayi in ya wuni baya kwana wani yaro ya wurgo dutsin sai akan kyakkyawar fatar goshin Salim Aiko jini yayo sallama

Baby na tsaye tana kallon yadda yaran ke jifar shi har zuwa inda akayi mishi rotsen Amma Bata Hana yaran ba 

Siyama taji ihun da yaran keyi ta fito inda ta iske Salim sunkuye goshi ya fashe jini na diga inda taji wani Abu ya soma bin jikinta sai taji ciwon tamkar ajikinta yake

Ta fito da sauri ta iso gareshi inda ta Kora yaran da suke fadin mahaukaci ne ta kwabe Dan kwalinta ta Mika mishi akan ya daure goshin sa ya dago Yana kallon ta fuskar shi ta baci da jini

Ya karbi Dan kwalin sai kuma yaga zai Bata Mata abinta da jini

Sai ya maido Mata 

“Nagode siyama kar na Bata Miki Dan kwalin  Bari naje Asibiti ayi min dressing nagode sosai so ne sila.

Tana kallo ya soma tafiya har ya bacewa ganinta inda taji hawaye nabin idonta

“Me yasa so baya da adalci? Me yasa ne ba zai hakura da soyayyar baby?

Ta shiga gida Bata cewa baby komai ba ai shiru ma magana ce ga me hankali

Inda baby Kuma wancan saurayin da siyama tayiwa wulakanci yayi Mata tsaye arai.

Washe gari sai ga Kira Wai ana Kiran siyama da sauri baby ta fito inda tayi arba da saurayin da ta gama tattare buri akanshi

Suka gaisa inda yake fada Mata abinda siyama tace mishi shi Kuma ya kasa hakuri da sonta Wai Bai ma runtsa ba siyama ta Hana shi sukuni inda zuciya baby ta cika taf da bakin ciki Banda kar ta bayar da Mata ai da tace ya Rabu da siyamar yazo wurinta to Amma idonta da kunya don haka sai tace ya Bari zata lallaba siyama 

Ya Kuma yi Mata kyauta da wata dala dari biyar ta shiga ciki take fadawa siyama bakonta na waje Yana jiranta idan tana da halin fita.

“Banda halin Nan anty baby saboda na fada mishi banayi sai ya saurara min.

Goggo tace “ban sanki da haka ba ta wajena jeki kiyi mishi hikimar nan Taki kin San ko baka son mutum to kar ka fito fili ka nuna mishi yi mishi siyasa ku rabu lafiya da haka siyama ta fito ta sameshi suka gaisa inda yake fada Mata ya kasa samun nutsuwa ta  daure ta karbi tayin soyayyar shi . Ya soma yi Mata kalamai har dai taji tana tausayin shi akan son da yace yanayi Mata sai taga Bari tayi amfani da shawarar goggo kar ta nuna mishi Amma fa gaskiya ba Ra ayin shi take ba don akwai Wanda zuciyar ta ke hange don haka sai tace Allah ya zaba abinda yake ALHERI inda bashir yaji Dadi har ya sanar da ita sunan shi da garin da yake zaune wato Abuja sai aka shiga soyayya abinda baiyiwa baby Dadi ba…..

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like