SAI A LAHIRA 35

Advertisement

  • 🎀SAI A LAHIRA🎀

              

*NA*

*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

            *🅿️age 35*

Advertisements

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

Advertisements

 *_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

……… Soyayya me armashi taci gaba da gudana tsakanin siyama da bashir inda duk kwana biyu bashir na tafe daga Abuja zuwa kaduna 

A yau da yazo ma hada tsarabar katuwar wayar Samsung Galaxy S7 me Dan Karen tsada inda ya kawo Mata Wai su rage kewar juna 

Ta dubeshi “Da baka wahalar da kanka ba bashir don ni waya Bata cikin abinda ke burgeni tunda na gano itace hanyar farko dake gurbata Rayuwar Yan Mata ta Kuma karkatar da matasa ta hanyar social media Wallahi sai naji na tsani waya

“Karki damu siyama duk abinda Kika ga mutum yayi a waya shi yaso ki karba ki kuma kiyaye duk abinda Zakiyi sai kiga Ashe saka Kaine ke Kai murum gurbin da yake. Da haka ta karbi wayar tana godiya sukayi fura kafin suyi sallama.

Ta SHIGA gida inda take nunawa goggo wayar da bashir ya Bata goggo ta karba tana dubawa

“Kai wannan waya da kyau take siyama Allah ya sa ki kashe da kanki.

Baby dake daki ta fito tana kallon wayar Amma fa zuciyar ta a kuntace 

Siyama ta Miko Mata wayar 

“Anty baby Kinga wayar da bashir ya bani

Ta karba tana dubawa wayar da take burin mallaka sai gashi siyama ta rigata samu ta mikawa siyama tana fadin 

“Tayi kyau”.

Samun wayar siyama ya ragewa bashir yawan zirga zirga ko da yaushe suna like a waya har dai ya budewa siyama watsapp yake Kuma turo Mata Kati da data yayinda baby take da wata tsohuwar tecno itama daure take da kyauro  inda take neman hanyar da zata samowa kanta mafita.

Ta dubi siyama “wayar ki da akwai kudi in Kira humaira? Tace Mata eh akwai ta Miko Mata wayar inda baby ta duba account din wayar inda ta iske kudi kusan dubu Sha biyu 

Sai Kuma ta shiga duba contact din wayar Daya bayan daya har tazo Kan lambar Bashir da sauri ta kwafe lambar a wayarta ta mikowa siyama wayar tace Wai Bata samu layin ba.

Tun daga wannan Rana baby take wayar tsakar dare wato free call indan siyama tayi bacci sai dai rajiyota sama sama

Sai ya zamo an kwashi kwanaki masu yawa bashir bai zo ba Bai Kuma kirata ba haka ma bai turo Mata sako ta watsapp Jin shirun yayi yawa yasa ta Kira shi inda take tambayar fatan lafiya ta boye shi ya Kuma sanar da ita lafiya Lau yayi tafiya ne inda tayi mishi fatan dawowa lafiya suka aje wayar

Baby taci gaba da yin wayarta a tsakiyar dare inda siyama Bata kawowa ranta komai ba inda kuma bashir shiru bai zo ba Bai kirata ba inda har ta rabu dashi sai dai ta Yi mishi magana ta watsapp Amma Kuma bai maido da amsa ba Kuma ta ga alamar yabude sakonta sai kawai ta watsar da batun bashir in wani Abu tayi mishi ai sai ya fada Mata.

Kawai sai gani tayi baby ta sauya waya irin tata sai dai Bata fadawa kowa ba bare ta Fadi inda ta same ta. Sai Bata tambaye ta ba don ita da ta samu tata ai ta nuna Mata sai ta share ta 

Suka shiga kasuwa siyowa goggo kayan hadin zobo kantin Dan matashi sai kawai suka hade da Salim inda suka gaisa da siyama tana jajanta mishi goshin sa da ta ga an manna mishi bandeji

Ya shafi goshin ya na fada Mata ai ya kusa warkewa tayi mishi fatan samun lafiya

Inda ya dubi baby dake wurgo musu harara

“Baby don Allah ki bani lambar ki….

“Yanzu ko Zan baka lambata”

Ta bude Jakarta ta fito da takardar naira dubu ta soma rubutu akan kudin in da ta rubuta mishi zagi na Rashin mutunci ta Miko mishi

“Ga lambata Nan idan ka dauki lambar sai ka kashe dubun don nasan rabon da ka rike dubu daya tun kakarka na budurwa  yo nawane ake wankin takalmin ne da har zaka samu naira dubu?

Ta fada cikin gadara da takama inda matasan dake wurin suka dauki ihu suna fadin kaga babbar yarinya in Banda bada Kai ina shi ina me zafi irinta? Ai ko kanta ya Kuma Kumbura ta soma tafiya tana rausaya inda siyama take bashi hakuri 

Yayi murmushi

“Kar ki damu siyama wallahi Babu komai tuni na bar komai bana damuwa kema taimaka min da lambar wayarki

Ta rubuta mishi ta bashi inda ya Kuma Bata kyautar dubu biyu duk da kin karbar da takeyi sai da ya Bata ta karba tana godiya da haka suka yi sallama.

Baby tacewa goggo zata je gidan su fauziyya wata kawarta dake bayan gidan su 

Sai ya zamo kullum baby na gidan su fauziyya

Har dai goggo tace Mata Wai me kike yi ne gidan fauziyya? Yo me ko zanyo goggo Banda zumunci? 

Ayau goggo ta Kira siyama take tambayar ta me baby ke zuwa yi gidan su fauziyya? Tace wallahi ban sani ba goggo na dai ji rannan tana bada kwatancen gidan su fauziyya nafi zaton mahada ce takeyi da samarinta don tana ganin idan tace Nan ne gidan su ta fado kin santa da karya 

Goggo tace to tashi kije gidan su fauziyya ki gano min abinda takeyi don hankali na Bai kwanta da zuwan gidan su fauziyya ba.

Siyama ta saka hijabinta ta nufi gidan su fauziyya inda tun anesa ta hango motar bashir inda baby ke gaban mota suna zance ita da bashir din………

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like