SAI A LAHIRA 36

Advertisement

 *🎀SAI A LAHIRA🎀*

              *NA*

*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

Advertisements

            *🅿️age 36*

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

Advertisements

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

 *_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

……..Gaban siyama yayi masifar faduwa inda taji kanta ya Sara idonta ya soma gani dishi dishi ta na tafe ahankali tamkar me tafiya akan kwai har ta karaso wurin motar Amma basu San da zuwanta ba saboda sun shagala da fira sun kafe juna da ido

Har ga Allah ba wani so takewa bashir ba Amma Kuma duk da haka sai da taji Babu Dadi me za a Kira abinda baby tayi Mata? Cin Amana ko snarching? Ganin zata Bata lokacin ta Akan baby da bashir koma meye su suka sani

Ta Kwan kwasa gilas din motar inda gilas din ya sauka sukayi ido hudu da baby da bashir

Akace marar gaskiya ko a ruwa zufa yake Nan ta gano kaduwar da baby tayi inda siyama take duban bashir

“Ranka ya Dade Ashe talaka na ganinku? 

Ya shafi sumar kanshi Yana murmushi

“Haba Ni na Isa siyama ya gida? Gida fa lafiya Lau Ina fatan lafiya ce ta boyeka? Komai fa lafiya

Tayi Jim ko zai sanar da ita wani abu Amma baice Mata komai ba. Ta dubi baby wadda tayi tsamo tsamo

“Dama goggo ke kiranki Amma Bari in fada Mata kina da bako in kin gama Kya taho . Ta dubi bashir

Ranka ya Dade sai ince ka sauka lafiya ko?

“Na gode sosai siyama ya zaro dalolin ya Miko Mata 

“Gashi ki saka Kati….

“Kai haba dai na gode sosai Wallahi ka bar kudinka sai anjima 

Ta juya ta baro su inda taji wani kuka na shirin kwace Mata duk taka mishi birkin da takeyi sai da yafito

Goggo ta dube ta tana sallallami “ya rasulullahi me ya faru ne siyama? Ta share hawayenta tana rattabawa goggo manufar baby ta zuwa gidan su fauziyya don kar taga zancenta da saurayin ta bashir.

Goggo ta dafe kirji

“Wane bashir din ba dai Wanda ya Baki waya ba? Shi fa goggo Wai anty baby ce da wannan aikin dama na karanto wani Abu a idonta yadda take fadin Yana da babbar harka to Amma nayi Zaton ko wani taga zaiyi min haka ita me hanawa ce Amma Babu komai matar mutum kabarin shi

Goggo tayi shiru kafin tace

“Kiyi hakuri kinji ta wajena karki kullaci Yar uwar ki namiji da kike gani ba kowane ke da kirki ba inda da kirki yaushe zai biyewa baby alhalin ke ya fara so? Ki Rabu da ita ko a ido kar ki nuna Mata komai Allah yasa hakan ne ALHERI  ke Kuma ya zaba  Miki miji na gari Wanda ya fishi.

Baby ta shigo gidan jikinta adar dace tana jiran taji wata magana daga siyama ko goggo Amma sai bataji komai ba  shiru ma maganace da dai taga Babu Wanda ya damu da ita sai ta bar zuwa gidan su fauziyya Bashir ya koma zuwa kofar gidan su

Siyama ta fito ta iskesu a mota suna zance ta gaishe da bashir ta wuce abinta haka ne kawai ke hadata da bashir in ta fito su gaisa in Kuma ta Kama ta dawo gaisuwar ce abinda ke hadasu.

Baby ta soma yin sabbin dunkuna tana bada Fadi da hura hancin ta samo babbar harka inda siyama ke binta da ido Wai Kuma sai ta soma daukewa siyama Kai tamkar dai itace tayi Mata snarching sai dai siyama tayi murmushi kawai.

Kwana biyu siyama Bata hau online ba sai yau da hau ta iske wani sako da wata tsararrar lambe me saukin hardacewa

Sakon da Bata San daga Ina yake ba abinda ta kawowa ranta wani ne da Bata San ko waye ba 

Sakon Yana magana Kan yi Mata fatan alkhairin da samun abinda take so DUNIYA da LAHIRA 

Taji dadin sakon matuka gaya har taji tana son ta San waye ya turo Mata shi har taji kamar ta kirashi sai Kuma ta rubuta mishi amsa da godiya da yi mashi fatan alkhairi irin Wanda yayi Mata ta tura mishi ta rufe datar ta aje wayar

Inda taji wayar ta dauki tsuwwa tajawo wayar ta na dubawa inda ta iske tsararriyar lambar Nan ce ke Kira

Ta dauka tare da sallama inda tajiyo muryar shi sai dai Bata Gane me magana ba

Suka gaisa inda take tambayar Bata fa Gane me magana ba.

Ya amsa 

“Ayya malama siyama salim ne 

Ta Kuma SHIGA duhu don Bata taba sanin sunan shi ba har dai ta faba mishi Bata Gane ba inda shi Kuma ya fada Mata sunan da zata Gane wato shoe maker kamar yadda baby ke fada mishi

“Ayya Yaya Salim don Allah kayi hakuri kasan ban San sunan ba ne Kuma tunda ka karbi lambar baka taba Kira ba 

Yayi murmushi “haka ne siyama lamarin ne sai sannu shiyasa na ce Bari in kiraki mu gaisa 

“Aiko na gode yaya Salim ya karfin jikinka? 

“Jiki ya warke siyama Ina godiya da kulawa Allah ya saka da ALJANNAH

Ta amsa da ameen ya Allah suka yi sallama inda siyama take Jin wani Abu na yawo ajikinta ta maimaita sunan Salim yafi akirga

Suffar shi take fasaltowa inda taji lallai Salim wani mutum ne da Ubangiji yayiwa baiwa me yawa tundaga kyau zuwa kwarjini ita Kam tana Jin indai Ubangiji ya Bata irin shi a matsayyin mijin aue zata godewa Allah sai ta roki Allah mafi ALHERI a Rayuwar ta

Kwana biyu bashir ya matsawa baby Kan zai turo magabata atsaida Ranar aure inda ta fadawa baba shitu shi Kuma yace su zo tunda sun gama makaranta idan ya yarda da ci gaban karatun sai ta karasa agidan shi Aiko bashir ya turo magata aka aje magana inda aka tsayar da wata biyu rak inda baby ta shiga jido Kaya na kece Raini Wai gidan babbar harka zataje sai da Kaya irin na babbar harka………..

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like