SAI A LAHIRA 37

Advertisement

*🎀SAI A LAHIRA🎀*

              *NA*

*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

Advertisements

            *🅿️age 37*

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_

Advertisements

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

 *_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

……..Kwanaki suka soma gangarawa inda baby ke ta SHIGA tana fita akan bikin su da Bashir shima din ya sakar Mata bakin aljihunshi tana ta facaka aciki inda take da burin yin bikin kece Raini agarin kaduna fatika ta tsara sun Kai kala goma har da Wanda bata San ya ake yin shi ba

Yayin da ta maida siyama gefe Bata neman shawarar ta Akan komai bare taji Ra ayin ta daga ita sai kawayen ta humaira da zeenat da Kuma fauziyya siyama na gefe guda tana kallon su inda Kuma ba ta nemi tusa kanta ba su humaira ne kawai ke sakota acikin sabgar idan sun sakota to zata shiga ayi da ita inda Kuma sai baby ta samu abinda tace Mata Wanda zai Bata ranta koma ta yabo Mata bakar magana ko ta gwasale ta

Siyama na mamakin wannan karfin halin na baby Wai ita akayiwa laifi Amma ta fita Shan kamshi da gwasala har da hantara. Zeenat Kan cewa baby

“Wallahi Baki da kirki fa baby Wai me yarinyar Nan tayi Miki kike son tozarta ta cikin mutane don Allah? Banga abinda siyama tayi Miki ba kike Mata irin wannan wulakanci ba. Ko ma tayi Miki ba Yar uwar ki bace yarinya tana biye dake tana Miki biyayya Amma kina gwasaleta? Gaskiya ban son haka in kina yiwa siyama muma Ashe ba zamu tsira ba…..

Wannan gaskiyar da zeenat ta fadawa baby ita ta hadasu fada inda zeenat tayi fushi ta yi tafiyar ta don baby ta rufe idonta ta gayawa zeenat magan ganu Wai meye ruwan ta da zata shiga Rayuwar ta? Siyama da humaira ne suka je har gida suka Bata hakuri akan ta dawo ayi hidimar kar tayi fushi kowa yayi na gari akan shi yake gani da haka zeenat ta dawo ta Kuma ce don siyama da humaira ta dawo ba don baby din ba inda goggo ta rufe baby da fada.

“Ban San inda Kika samo bakin hali ba baby”, yarinya tazo hidimar ki kike Mata cin mutunci don ta fada Miki gaskiya? Siyama batayi fushi dake ba sai ke? Inace kwacen saurayi kikayi Mata? Baby ta dubi goggo

“To goggo kice kema kina daga cikin Yan Adawa…..

“Bana daga cikin Yan Adawa baby sai dai nasan mijin siyama da Ubangiji zaiyi Mata misaya ta ALHERI sai yafi naki don yaga abinda akayi Mata ba Kuma zai barta haka ba sai ya share Mata hawaye ki Kuma zuba ido kiyi kallo zakice na fada Miki…..

“Sai dai kuyi hakuri goggo yace ba ita yake so ba Ni yake so sai adora Mana jakar tsaba don dai Rashin son gaskiya haka take fadawa goggo magana son ranta 

Siyama ta dubeta tana Shirin wucewa ta riko hannun ta

“Kar ki Kuma duban idon goggo ki fada Mata duk maganar da tazo bakin ki Zan iya shanye komai akaran kaina Amma Banda goggo wallahi kema in kinyi tunani goggo ta wuce kiyi Mata haka tunda tayi Miki abinda uwar da ta haifeki ba tayi Miki shi ba….

Baby ta wankowa siyama Mari

“Don ubanki naje nayi Kuma Bari in koya Miki hankali don ki kiyayeni.

Akace me hakuri Bai iya fushi ba kokowa ta kaure kafin ma goggo ta shiga tsakani siyama ta dauki baby ta maka akasa  zata bita da naushi ne goggo ta rike ta ta SHIGA tsakani  

Inda baby tace Wai goggon ce ta riketa siyama ta Kada ita .

Haka baby tayi ta tijara  har tana fadin Wai goggo ta tsaneta sai ta soma hada kayanta Wai katsina zata tafi wurin haj Azumi

Goggo tace ” ba Zan barki ki tafi ba sai malam yazo don kar kije ki hada shi da Azumi don tani bana shakka tunda haka Nan ma siddan Azumi zagi na take Amma idan malam yazo inda yafi gidan Azumi ma kije

Aiko baba shitu ya samu labarin abinda ya faru shima fadan ya rufeta da shi inda Kuma yace duk ma inda zataje tayi ta tafiya sai ta dawo.

Bisa Dole ta hakura da tafiyar sai dai ta daukew kowa agidan Kai daga goggo har siyama baba shitu kadai take gaisawa Suma din Babu me shiga sabgarta

Wayar siyama tayi Kara ta dauko ta duba inda taga lambar salim ce ta daga tana mishi sallama 

“Ranki ya Dade malama siyama ya gida ya kwana biyu? Uhmmm Yaya kaima ranka ya Dade ya aiki ya Kuma yanayin Rayuwa? “Komai lafiya dama sako ne na turo Miki nace ko kin duba shi? “A a gaskiya Banga shigowar sako ba Amma Bari in duba in box message ne ko watsapp ne? Eh watsapp ne to Bari na duba 

“To Zan Kira idan kin gama dubawa sukayi sallama.

Ta shiga watsapp ta bude datar wayar inda taci karo da sakon Salim Wanda ya kusa sakata Suma don Dadi . Sakon me magana kamar haka.

Bayan sallama da fatan alkhairi siyama Zan fara da godiya da neman afuwar ki akan wannan sakon me yuwa ki kalle shi kamar Rainin hankali. Maganar gaskiya naso yayarki baby duk da irin cin mutunci da tayi min inda na Gane saboda kawai bani da kudi duk da Bata tsaya ta fahimce yadda Rayuwa take sauyawa ba me yuwa da tayi min uzuri tunda Bata San yadda Zan zamo a gobe ba. Sai dai maganar gaskiya Ranar da nayi ido hudu dake nagane ba son baby nake ba kece nake so sai dai na rasa da wane bakin Zan sanar da ke? Da wane idon Zan dubeki? Me yuwa ma kice saboda yayar ki ta kini na dawo gareki sai dai Allah shine shaidata so guda nake Miki ina fatan ban Bata Miki Rai ba idan kinji kinyi na am Dani zanyi farin ciki idan ko aka samu akasin hakan to inajin nine nafi kowa Rashin sa a a duniya ki gafarce Ni idan sakona ya Bata Miki Rai daga me BURIN kasacewa dake har gidan ALJANNAH wato Salim mubashir  

Siyama tagama karanta sakon Salim inda takejin wani sanyi na ratsa zuciyar ta Ashe Allah zai mallaka Mata Salim amatsayin miji? Tayi murmushi farin ciki na shawagi aranta sai taji tana son sanin shin waye Salim mubashir❓………

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like