SAI A LAHIRA 38

Advertisement

 

*🎀SAI A LAHIRA🎀*

              *NA*

*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

Advertisements

            *🅿️age 38*

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_

Advertisements

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

 *_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

……..Siyama ta runtse idonta tana hango suffar salim fari ne tas har yellow yellow yakeyi  dogone me suffar karfi sumar kanshi a kwance yayin da jikinshi yake lullube da gargasa 

Manyan ido da dogon hanci garin kyawawa ma Salim me kyau ne kuma duk inda ya shiga Dole akalle shi akuma yarda me kyaune sai dai in an saka hassada da Jin zafi  Nan ne fa za a kushe shi ko da Dan Adam yake Tara Bai cika goma ba inda aka rage Salim shine mahaifiyar shi domin ko macece me son kanta da Kuma tsanar talaka.

Abinda ya daurewa siyama Kai akan Salim shine wanene shi? Bata zaton shi din shoe maker ne irin wadan da suke hauro wa birane don neman kudi tunda ita Kam har gobe bataga me wayewar Salim a mafi yawan shoe maker ba kwanaki wani turanci da yayi lokacin da baby ta watso mishi ruwan wanke wanke sai da tayi mamaki don ta tabbata ba ita kadai ya sani ba. Fatar jikin shi Bata gogu da Shan wahala ba irin ta masu yawo cikin Rana Kuma duk lokacin da zata ganshi tsab yake Babu alamun wahala a tare dashi har dai daga karshe ta yarda koma waye Salim tana son shi tana Kuma tare dashi…….

Wayar ta ta katse Mata tunanin da take inda taga shine ke Kira sai Kuma taji kunyar shi tamkar agabanshi take

Wayar na dab da tsinkewa ta daga tana sallama ya amsa shima cikin Jin nauyin ta don Bai San ya ya zata kalli sakon shi ba.

“Ina fatan sakona Bai Bata Miki Rai ba siyama, “ko daya wallahi Yaya Salim  wacece Ni da sako kawai zai Bata min Rai ?

“To Allah yasa Ina daga cikin masu sa ar zuwa duniya siyama don da gaske nake wallahi rasa soyayyar ki dai dai yake da rasa farin cikin Rayuwa…

“Kar ka damu Yaya Salim Kai me bawa wani in Kuma yi biyayya  Ina fatan hakan ya zamo ALHERI tsakanin Ni da kai…..

Kalmar godiyar da yake ta jerawa Ubangiji har ya Bata mamaki

“Siyama da wane bakin Zan godewa Allah”? 

“Da wannan dai bakin da kake magana dashi sai dai da zakayiwa ANNABI salati da sai yafi godiyar…

“S A W  ya amsa itama ta tayashi amsawa inda ya katseta

“To siyama Kinga dai Sana ar tamu Allah yasa Zakiyi hakuri da duk abinda ya samu….

“Kar ka damu Yaya salim a kamanni ne kawai nake Kama da anty baby amma halayyar mu ba iri daya bace Kai nake so ba dukiyar ka ba  Ina fatan ma Ubangiji ya bani abinda Zan baka saboda darajar so haka Nima komai ya fito daga hannunka Ina sonshi…….

“Na gode sosai siyama Ubangiji ya bani abinda Zan fita hakkin ki da kunyar ki, yanzu yaushe Zan zo muyi fira mu Kuma Kara kallon fukar juna? Tayi murmushi “duk sadda kazo Ina maraba da kai. To Bari Zan duba Ranar da ta dace sai inzo da hakan sukayi sallama 

Goggo da kanta ta Gane siyama na cikin farin ciki Bata kyale ba sai da ta tanka.

“Kai ta wajena me Kika samu ne kike ta annushuwa da arerewa da farin haka?

“Ke dai Bari goggon mu Ina saurayin Nan da na taba fada Miki anty baby ta watsawa ruwan wanke wanke da saka yara sukayi ta jifar shi har suka fasa mishi goshi? “Naji dai inji goggo. To shine yake fada min yaso baby abaya ta wulakanta shi tun daga Ranar da ya ganni yaji Ni yake so ba baby ba Ni Kuma Allah yasani Ina tausayin shi…..

Goggo ta rike Baki tace “ikon Allah daga tausayin Kuma sai me ta wajena?

Siyama ta sunne kanta kasa. Goggo tace

“Kice dai kwacen samari kuke ke da baby ta kwace naki kema kin kwace nata Kinga kun Raba…..

“Wallahi goggo da ace tana son shi da ba Zan karbe shi ba to Amma Akan idona take mishi wulakanci shiyasa nakejin tausayin shi.

Goggo tace haka Allah yake Al amarin shi Ubangiji yasa albarka acikin auren ku ya baku Zama lafiya siyama ta amsa da Amin

Ranar juma a Salim yazo cikin shigar jallabiya baka da farar hula tashi ka Faye naci  kallo daya zakayi mishi kasan lallai shi din me kyaune Kuma shigar ta karbe shi siyama ta fito suna Jin kunyar juna ita da shi 

“To Yaya za ayi kenan siyama muna ta Jin kunyar juna?

Haka dai sukayi firar me armashi inda ya kawo Mata kyautar turare designer Wanda ta San kudin shi inda ta Kuma SHIGA cikin duhu akan Salim

Lallai me zuciya ne abokin tafiya ba me dukiya ba ga alama fa zai kula da iyali

Tuni soyayya tayi nisa tsakanin salim da siyama sai dai baby Bata San da kwanan soyayyar ba saboda sabgogin bikin ta sun Sha kanta inda ya rage saura sati biyu a daura aure inda ta fitar da anko kala uku leshi da atamfa sai material  inda Kuma Bashir ya sakar Mata bakin aljihunshi take ta wandaka da warisa tana bada Fadi da Shirin yin bikin kece Raini agarin kaduna

Humaira da fauziyya da zeenat suka shigo gidan don zuwa siyen ankon bikin inda siyama ke kichen tana taya goggo girki bayan sun gaisa zeenat ta dubi siyama 

“Kanwata ban dake ne za aje kasuwar Naga kina ta girki? Siyama tayi murmushi don tasan zeenat na kaunar ta da kulawa da lamarin ta tace

“Anty zeenat kudi na Basu Kai na siyen kala uku ba siyasa ba Zan biku ba Amma idan sun cika Zan siyo duka.

“A a taho muje ki fara siyen Wanda ya samu in ma cikon babu yawa Zan cika Miki kanwar Amarya guda ace batayi anko ba ai sai azagemu. Humaira ta dubi baby 

“Wai tsaya baby kar dai siyama Bata samu acikin Wanda bashir ya siyawa Yan Matan amarya ba? 

Baby ta ya mutsa fuska

“Bata samu ba gaskiya don kawayen da yawa

Siyama ta dubi humaira da zeenat kar ku damu anty humaira muje sai in siyo Wanda ya samu

Humaira da zeenat suka jinjina wa Rashin mutuncin baby da har ta iya bawa kawayen ta anko ta Hana kanwar ta

Da haka suka fice zuwa kasuwa inda kuma cikin sa a suka Tara’s da Salim Yana wankewa me shagon takalmin shi inda humaira ke cewa baby

Kawata ga mutumin ki fa. Baby taja tsaki”Dan anace zakice humaira ai Allah yasa wancan mutum yaci naci ya kora da ruwan Rashin zuciya kwana biyu dai haukan shi Bai motsaba an kyale Ni na sarara…

Wani Abu ya naushi zuciyar siyama Jin irin tozarci da yarfen da baby kewa Salim inda taji har wani yaji yaji idonta keyi tamkar ta gaura Mata Mari Amma sai ta maze ta Rabu da ita inda aka soma fito musu da ankon inda siyama hankalin ta ya tafi ga Salim dake can yana wankin takalmin me shagon Yana kuma Jin abinda baby take fada akan shi inda shima hankalin shi na wurin siyama inda ya gama wankin ya nufo shagon don kawowa me shagon takalmin shi……

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like