SAI A LAHIRA 41

Advertisement

 

*🎀SAI A LAHIRA🎀*

              *NA*

*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

Advertisements

            *🅿️age 41*

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_

Advertisements

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

 *_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

……… Siyama ta dafa ta ganin hawaye na bin idonta

“Anty baby wani Abu ya farune kike kuka?

Ta wurgowa siyamar harara

“Na kiraki ne da Zaki saka Ni gaba kina tambaya ta”?, Allah ya Baki hakuri anty baby ban San magabata zatayi zafi haka ba. “Amma don Allah idan nayi Miki wani laifi ne ki yafe Ni ki Kuma sanar Dani don in kiyaye gaba. Ban San me nayi Miki ba kike daukar zafi da Ni ya dace ace matsayin ki na yayata in nayi Miki laifin sai ki sanar Dani don in gyara ba Wai ki dauki gaba Dani ko kyara da hantara ba. Tafiya fa Zakiyi sai mun Dade ba mu ga juna ba  to me zaisa ido yin wuta gira tayi hayaki? 

Don Allah mu yafi juna in Kuma wani Abu nayi Miki ki fada min sai in Baki hakuri Ni dai na waiga na Kuma duba ban hango abinda nayi Miki ba….

“Don Allah malama kin cika min kunne haka saurara min !

Ta fada da tsawa

Siyama tabita da kallo inda su humaira suka shigo kowace taci ado da material na zuwa English home Wanda za ayi a yau Wanda shine dalilin Kiran bashir ya katse Mata wayar bayan ya sanar da ita ba zai samu damar zuwa ba

Zeenat ta dubi siyama

“Ba dai Baki shirya ba kanwata gashi har shida ta kusa bugawa”

“Tuba nake anty zeenat Kaya kurum Zan saka sai Yar kwalliyar da ba Zan Dade ba tafita tana sauri inda fauziyya tacewa baby takira bashir ya turo musu motoci 

Baby da zuciya ke tukuki  take sanar da su yadda sukayi da bashir din…..

“Wai Ashe da gaske yakeyi baby? Wallahi nayi Zaton zolayar ki yakeyi……

“Yo wane irin bahagon taro zamuyi Babu Ango? Cewar humaira

Fauziyya tace gaskiya idan Babu ango abin ba zaiyi armashi ba gara mu hakura kawai inda Kuma zeenat da humaira sukace Yaya Kuma zasuyi da mutanen da suka gaiyyato? Ayi haka Nan ko Babu angon don a sallami mutanen da aka gayyato

Haka kuwa akayi wannan English home Babu armashi Wanda tun Aranar Amarya baby ta soma kokawa akan wannan aure Banda ta tattare dukkan burin ta Akan bashir da daular da ta kwadaitu da SHIGA cikinta da babu ko shakka ta watsa wannan aure don haka jikinta yayi sanyi ta bar wannan ta wuce.

Sai dai agefe Daya Kuma da ace Dan Adam ya San abinda gaibiyya ta kunsa da tun farko baby batayi kokarin murdewa Yar uwarta soyayya ba bare ta tura kanta da karfi da yaji Ashe wannan kukan sharar fage ne gareta

Hajiya Azumi da ta tare gidan khalil ta iso gidan baba shitu inda goggo ke nuna Mata kayan lefen da aka kawo.

“Kai madallah yarinya tayi goshi Allah ya sa ALHERI Kinga da uwarta na Nan ba sai tayi komai ba Amma yanzu sai an nunawa mutane son iyawa ta fada tana yamutsa fuska

Goggo tayi murmushi don tasan dama zaiyi wahala Azumin tazo har ta koma Bata nuna Mata Bakin halinta ba

“In Banda abinki hajiya Azumi meye na son iyawa anan? Ko ance Miki na dauki wani a Abu daga cikin kayan lefen ne?…..

“To Ina Zan sani Abu a duhu? In ma Babu Rami me zai kawo Rami? Nima bude min in dauki na fitar biki  wani ma yayi rawa bare Dan makadi? Na can gefe ma sukayi bare masu dugi? Goggo na kallo Azumi ta darji leshi da atamfa hada takalmi me tsini taka gidan gwamna  acewar ta.

Goggo Bata hanata ba don ta San idan baby taji ba yarda zatayi ba karbe kayanta zatayi sai dai baby sawun giwa ne ya take na rakumi shiyasa hankalin ta ba ga kayan yake ba 

Bisa Dole aka soke fatikan da aka tsara za yi saboda Rashin halaeta ango inda bikin ya koma lami 

Baby dasu fauziyya da humaira ne da zeenat kawai ke sabgar su inda baby Bata sako siyama akomai bare ta nemi shawarar ta koma tace tayi Mata kaza  itama siyamar sai ta kame mutuncin ta tana gefe tana kallon su suna sabgar su masu yi Mata karah ma su kawayen babyn ne su Kam suna saka ta a komai duk da baby ba so take ba haka dai abubuwa sukayi ta faruwa har Allah Ubangiji ya kawo mu Ranar asabar din da za a daura aure. Inda hajiya Azumi ta shigo gidan cikin leshin da ta darza Wanda akayi Mata dinkin fitet da takalmin taka gidan gwamna fuskarta Tasha kwalliya abi dariya abin takaici da Kuma tausayi inda ta kashe ta Kuma tsare  akan komai inda take sanar da baba shitu idan za ta tafi zata tafi da siyama Wai ta Rika yi Mata talla inda baba shitu yace Bai yarda ba itama siyamar aure zai yi Mata Nan gaba kadan idan Allah ya fito Mata da nata GWANIN don haka Azumi ta hakura don tasan baba shitu shima masifaffene Yama fita iyawa don shi in Yana masifar shi har tsalle yake yi kafin ya kawo duka don haka hajiya Azumi ta kyale Bata ja ba.

Da maraice ango ya Kira wayar amarya  baby yace Mata ta shirya akwai perty da abokan shi suka shirya musu don Taya su murnar AUREN su.

Ta sauke wayar ba tare da ta tanka mishi ba don shima so take ta ganar dashi kuskuren shi akan abinda yayi Mata shiyasa ta soma Shan kamshi da daukar Kai

Ta dubi su humaira

“Ku shirya bashir yace akwai party da abokan shi suka shirya karfe takwas na Dare.

Zeenat tace “to wane Kaya zamu saka?

Siyama tace 

“Anty zeenat me zai Hana mu saka lemon green din material din Nan zai haska mu ko? “Kin kawo shawara kanwata shiyasa nake sonki…..

“Ba shi zamu saka ba gold Nan zamu saka”,

Cewar amarya baby

Zeenat tabita da kallo inda siyama tace ai shima zai haska mu Babu damuwa anty zeenat mu saka shi din

Atake suka hau shiri………

.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like