SARAN BOYE 41

Advertisement

 

No. 41

 

………….Tunda su papa suka koma Abuja Suka kasa zaune suka kasa tsaye shida ƙannensa da aminansa. Sunyi zaman mitin kuwa yafi sau goma.

      A kuma kowanne zama babu abinda suke tisawa da tirzawa sai kalaman baba malam masu cin zuciya da farin ciki.

     A yanzun ma dai suna zaune ne su duka bakwai da suka kasance aminan juna kuma shakiƙai. Papa daketa kai kawo hannunsa goye a baya ya girgiza kansa idanunsa tamkar zasuyi aman wuta saboda jaa. “Bazai yuwuba. Dolene sai mun cimma burinmu akan Hausa man ɗin nan. Dan abinda ya shuɗe tsakanina da shi shekaru kusan ashirin da takwas yana a ransa daram babu abinda ya manta. Idan kuwa har ya tabbata bai manta ɗinba tofa ku sani, ni da ku duk muna cikin……..”

        Da sauri Uncle Mike ya ɗaga ma papa hannu. Muryarsa cike da barazana yace, “Karma kace komai Pastor. Ba’a haifi mahalukin daya isa hanamu cimma burinmu ba bayan wahalar da mukai ta tsahon shekaru. Duk da kuɗin da kuke tunanin hausa man ɗin nan nada shi wannan ba komai bane. Ni inada hanyar da zamuyi amfani wajen cinsa da yaƙi batare da shi kansa yasani ba. Zamu ruguzashi shi da duk zuri’arsa ta hanyar SARAN ƁOYE. Ni dai fatana shine ku bani haɗin kai kawai na nuna muku hanya mafi sauƙin ɓullewa”.

          A take duk suka dubesa zukatansu na samun nutsuwa kaɗan. Ba komai yasa hakanba sai sanin da sukaima Mike wajan iya ƙulla talalar rufta duk wanda suka sakama kahon zuƙa a rayuwarsu. Dan haka babu wani kace na ce duk suka shiga sauke ajiyar zukata.

Advertisements

    Hannunsa ya ɗaura saman tebirin gabansu yana dubansu. Papa ne ya fara aza nashi akan na Mike ɗin. Sai Godwin. Sauranma duk sai suka shiga ɗorawa ɗaya bayan ɗaya alamar tabbatar da mubayi’arsu akan idea ɗin da Mike zai kawo musu wadda suke fatan ta zama hanyar da zasu ɓulle akan baba malam.

 

      Wannan zama shine ya samawa papa ƴar nutsuwa, duk da a kallo ɗaya zaka fahimci yana tare da fushi har zuwa yanzun. Wayarsa ya ɗauka yay kiran Yoohan da a yau ya wuce birnin Lagos. Bai ɗaga ba harta tsinke. Hakan ya sashi tunanin ko baya kusa. Dan haka bai sake kiraba ya ajiye wayar gefe ya cigaba da kora giyarsa.

     Kusan mintuna goma sai ga kiran Yoohan ɗin ya shigo masa. Ɗauka yay fuskarsa cike da fara’a, dan har cikin ransa yana ƙaunar ɗan nasa. A duk irin fushin da yake ciki inhar ya kasance da Yoohan sai yaji ya samu nutsuwa ta musamman.

       Yanda Yoohan ɗin ke gaishesa cike da shagwaɓa ne ya sakashi sakin murmushi. Cikin muryar ɗan mayen daya fara tasiri a kansa yace, “My sweet John yaya dai?!”.

       Cike da ƴar shagwaɓa Yoohan dake zaune a office tare da Richard yace, “Papa na gaji ne, barci nakeji. Kaga tunda nazo Rich bai barni na hutaba sai laftamin aiki yakeyi kamar wani jakki”.

        Ƴar dariya papa yayi yana kurɓar giyarsa. “Oh my Darling kaifa gwarzon namiji ne. karka karaya da sauri haka mana a gaban Richard”.

       “Papa kai masa magana to ya tayani”.

     “Hhhh to babu damuwa zan masa. Kasan miyasa na kiraka?”.

       A nutse Yoohan daya gyara zama yace, “A’a papa, sai ka faɗa”.

       “Humm” papa ya faɗa yana miƙewa. Ya kurɓa giyarsa saboda ɓacin ran baba malam na sake dawo masa sabo a zuciya. muryarsa cike da kaushi yace, “Jiya mukaje kano wajen wancan hausa man ɗin”.

     Sosai gaban Yoohan ya faɗi. Ya ɗan ture files ɗin gabansa yana faɗin, “Kana nufin Sheikh Sooraj jibiya”.

Advertisements

       “Yes! My son”.

  Miƙewa Yoohan yayi da sauri. Ya tura kujerarsa ta zama baya ya bar gaban tebirin Richard na binsa da kallo. A wani irin yanayi yace, “Papa mi kukaje yi wajensa?”.

      Batare da papa ya ɓoyema Yoohan ɗin komaiba ya sanar masa cewar sunje nema masa auren Nu’aymah ne.  shine dan wulaƙanci baba malam yake sanar musu wai shi yarinyarsa bata isa aure ba. Idanma ta isa bai shirya aurar da ita ba……..”

        “Oh my GOD papaa! Miyasa baku sanar dani ba kafin kuje?. Nifa koda nace muku zan aura ƴarsa bawai ina nufin yanzu ba. Da gaske yarinyarfa ƙaramace. Shekararta sha bakwai ne kacal fa…….”

         “My son! kai kake ganinta a ƙaramar, sufa sunama yaransu aure suna shekara goma ko sha biyu. Kawai dai ya shirya wulaƙanta mune saboda…….” sai kuma yay shiru bai ƙarisa ba

       Yoohan da ransa ke a dagule yace, “Saboda mi papa? Ko dai ba neman auren ne ya kaiku ba dama?!. Papa kuna son ku ɓatamin aiki nane kawai kudai. Idan ba hakaba tayaya zaku tafi nema min aure batare da shawarata ba. Inada tabbacin kuma su Uncle Godwin ka kwasa kukaje sukaita masa gadaran da sukema mutane. Shifa wannan ya wuce duk yanda kuke zato, yanada iliminsa yasan mi yake yi. Sannan baya ɗaukar wulaƙanci ga kowa shiyyasa nakeyi komai cikin taku da taka tsantsan a kansa. Idan kuɗi kuke taƙama da shi shima ya tara su. Idan mabiya ne shima yana dasu bama a Najeriya kawai ba. Kaga kuwa tunkararsa sai an shirya”.

           Jikin papa ne yay sanyi. Dan haka murya a sanyaye yace, “Tabbas na sake tafka kuskure na biyu Yoohan. Gaba ɗaya farin cikinka ne ya rufe min idanu na kasa fahimtar zuwa dasu zai iya haifar da matsala. Yanzu dai kayi haƙuri mu nemo mafita zan sake gyarawa da kaina. Kuma zan kiyaye”.

       Duk da ran Yoohan a jagule yake har yanzun sai ya sauke ajiyar zuciya yana gyara tsaiwarsa. “Karka damu zamuyi magana. Yanzu ina kan aiki ne. Amma papa Please ka daina biyema su Uncle Mike suna sakaka zubar da mutuncinka gaskiya”.

       “Karka damu zan kiyaye my son”.

Daga haka sukai sallama.

 

       Yoohan da zuciyarsa ke masa zafi da ƙuna ko sauraren Richard dake jera masa tambayoyi baiyi ba ya tattara kayansa  yace masa zai je gida nanda awa biyu zai dawo ya cigaba da duba marasa lafiyan….

    

 

*_KANO_*

 

         Alhmdllhi, kamar yanda sukai fata an dace. Dan kuwa Nu’aymah ta farfaɗo cikin hankalinta, sai dai ramar da tayi dolene ta baka tausayi, hancin nan ya sake tsaho. Haka ma ta ƙara haske idanun sun fita da ƙyau masha ALLAH. Ramarma sai ta sake fiddo mata da ƙyawun nata.

     Ba ƙaramin farin ciki ahalinta suka tsinci kansu ba. Dan tunda farar safiya aka fara tururuwar zuwa ganinta. Ga ƴan biki dama sun fara cika gidan musamman dangi na nesa. Ganin za’ayi yawa a asibitin Baba malam ya dakatar da zuwan. Ya sanar musu likitocin sun sanar masa a yau ma zasu sallameta insha ALLAH. Daɗine ya ƙara lulluɓe kowa, musamman ma Abdallah da Naser da farfaɗowan Nu’aymah ta sakasu komawa kamar an musu albishir da gidan aljanna.

 

     Duk a yanayin da Nu’aymah ke a ciki su Dr Aysha na sanarma Yoohan. Shi da kansa ma ya basu umarnin sallamar Nu’aymah ɗin, dan insha ALLAHU ya tabbatar ta dawo cikin hayyacinta. Zata kuma lallaɓa jikin har lokacin da za’a fita da ita ai mata aiki a ƙwaƙwalwarta ɗin. Kasancewar yayi niyyar zuwa ɗaurin auren gidan nasu sai ya bari kawai sai ranar juma’ar ya iso kanon da safe, dan a ranar ta kama za’a ƙarama Nu’aymah allura ɗaya daga cikin allurorinta.

 

          Sai wajen sha biyu na rana aka basu sallamar, daga Abdallah har Naseer suna a asibitin. hakama Omar malam ƙarami Yah Ahmad. Sai Abbah Musbahu. Kai tsaye motar Abba Musbahu Yah Ahmad daya kamota ya sakata. Dan ya kula akan tafiyar babu makawa su Abdallah sai sun nuna hali, shiyyasa ya raba gardamar ma tunkan a fara.

      Murmushi kawai Abba Musbahu yayi yana jin daɗin abinda Ahmad ɗin yayi. Sukuwa duk sai suka ja guntayen tsoki kowa ya nufi motar da yazo ciki. A jere suka bar asibitin kamar wasu ƴan kai amarya.

       Gidan bawani cika yay sosai ba. Dan dangine kawai irin na nesa sosai wasu daga cikinsu suka iso. Amma duk da haka daka shigo zaka fahimci bayan jama’ar gidan akwai baƙi a ciki. Da yake duk ba’ai tsamanin sallamar yanzu ba sai babu wanda yaji har suka gama fakin. Abbah Musbahu ya kamo Nu’aymah dake kwance a jikin kujera ya fiddota a hankali yana mata sannu.

      Kanta kawai take ɗaga masa a hankali. Kai tsaye sashen Hajjo ya nufa da ita. Su Abdallah suka take musu baya gaba ɗaya. Sun iske sashen ba mutane sosai. Dan Umm ce ke cin-cin dasu dibulan, nakiya, alkaki da dai sauran kayan gara na fulawa da akeyi. Hakan yasa duk ƙannenta da ƙannen Adda da wasu daga cikin ƙawayensu dama matan gidan da yaran manya na ma’auri duk suna can anata aikin a can sashen.

     Cikin farin ciki Hajjo da Ananah duk suka shiga musu sannu, idanunsu akan Nu’aymah dake langaɓe jikin Abba Musbahu (dama yaya lafiyar kura😂). Har cikin ɗakin Hajjo Abba Musbahu ya kai Nu’aymah. Nan Hajjo da Ananah suka biyosa. Sake yimata dannu sukayi cike da kulawa da tausayi, sunata jera mata addu’oin samun lafiya mai ɗorewa. Itako idanunta akan Ananah dake riƙe da hannunta tanata ɗan murmushi. Dan duk zuwan da sukeyi dubata sai yau ne ta ganta. Suna shiri sosai da Ananah, itaɗin ƴar gaban goshintace saboda sunan hajjo da taci.

     Abbah Musbahu dake kallonsu shima cike dajin daɗi yace, “Ananah tayi wanka sai a bata abinci taci, dan likitocin sunce ta fara cin abinci da gaggawa”.

       “Ba laifi auta. Dan wannan ramar da tayi gara taɗan cicciko, koni tsohuwa na fita ƙyan gani ai”. Baki Nu’aymah ta turo gaba tana janye hannunta daga cikin na Ananah datai maganar. Abbah Musbahu dake musu dariya yace, “Karki damu mamana, yanzu zanje na haɗo miki kayan daɗi kema zaki zama ƙatuwa ki fisu. Kuma karki basu ko ɗan cinguli kinji”.

     Murmushi tai tana jinjina masa kai da kallon su hajjo irin bazaku cisa ɗin nanba ko.

 

          Jama’ar gidan da labari ya kai musu ta hanyar yara sunta zuwa yima Nu’aymah sannu. Sai da kowa ya gama shigowa sannan hajjo ta sakata ta shiga wanka da ruwan data haɗa mata mai ɗumi. Yanda take jin jikinta wani irine yasata nutsuwa sosai tai wanka mai ƙyau, dan ta kwashe tsahon lokaci a ciki kafin ta fito. Taji daɗin ganin jakar kayanta, duk da tana kewar Umm ɗinta tanaso ta ganta. Dan kowa ya shigo dubata a agidan banda Umm…….. Shigowar Addah, Amal biye da ita da tire a hannu ya katse mata tunani.

    Duk sannu suka sakeyi mata. Addah ta zauna gefenta tana jawo akwatin da faɗin, “Daughter tashi kisa kaya ga abinci kici kinji, idan naga ramar nan taki hankalina sake tashi yake yi”. Cike da shagwaɓa Nu’aymah tace, “Addah nafi yin ƙyau a haka fa, dan ALLAH Amal banfi ƙyau haka ba?”.

       Amal dake zuba mata abinci tace, “A’a mudai munfi sonki da ɗan jikinki Aymah. Gara ki ciko kafin nanda kwana uku. Yanzu ƴan biki kowa ya ganki sai ya tambaya”.

     “Barta Amal, ɗura zan dinga mata  ai”. Addah ta faɗa tana ajiyema Nu’aymah kayan da zata saka. Dariya Amal tayi da yima Aymah gwalo. Addah kuma ta taimaka mata ta saka kayan. Da taimakonta taci abincin. Ta bata maganganun ta tasha ta kwanta a gadon Hajjo dan ta ɗan huta. Babu jimawa kuwa barci yay ayon gaba da ita.

 

          Sai bayan la’asar Nu’aymah ta tashi. Wanka ta sakeyi da ruwa mai zafi tai salla. Ananah ta kaita falo da kanta ta bata abinci. Ta ɗanci kuwa babu laifi, dan abinda take so ne akai mata. A haka Naser ya shigo ya samesu. Cike da kulawa da tausayi yayta jera ma Nu’aymah sannu. Ita kuwa amsa masa take da ɗan murmushinta. Baifi zaman mintuna goma ba sai ga Abdallah ya shigo shima. Shima dai kulawar ya nuna a gareta sosai da jera mata addu’oin samun lafiya.  Amsa masa tai shima, sai dai babu fara’a sosai kamar Nasir. Haka suka cigaba da zama a sashen suna harar juna har akai kiran sallar magriba. Nu’aymah dai tuni ma ta ɗauke kanta ta maida ga tv kamar ta manta da zamansu a falon.

           Bata saka iyayenta a rai ba sai dare. Baba malam da Umm tare suka shigo suka dubata, zukatansu cike dajin daɗin sauƙi data samu. Tare da tausayin gudan jinin tasu mai tsanani. Sun ɗan jima anan sannan suka fita, ita kuma ta shiga ta kwanta cike da kewarsu. Badan karsu hajjo suka kamar ta raina musu ba da guduwa zatai wajen iyayenta, sai dai tasan koma taje can ɗin ba sakewa zata samu ba dan baƙine acan ɗinma. Musamman dangin Addah da duk biki acan suke sauka dama. Yanzu haka ɗakinta kansa tasan da baƙi a cikinsa.

 

________★★★★________

 

          Haka aka cigaba da hidimar biki, baƙi nata sake cika gidan ta kowane sashi. Yayinda jikin Nu’aymah keta ƙara warwarewa. Bata fita ko ina, ko yaushe tana sashen hajjo. Sai dai taci ta ƙoshi tasha magani tayi barci. Wani lokacin Amal da Yusrah kan shiga su tayata hira. Adawiya ce dai tunda aka sallamota bata ganiba. Da dai ta gaji da haƙuri ta tambayi su Yusrah. Sune suke sanar mata ai Adawiya nacan gidan kakarsu da ta haifi Addah, wai bata da lafiya. Tun washe garin da aka kwantar da Nu’aymah a asibiti ita kuma ta koma can.

      Hakan sosai ya bama Nu’aymah mamaki, dan tasan iyayensu sam basa barinsu matsawa ko nan da can. Duk ƙulafucin da Gwaggo kakarta ta keyi akan ta dinga ɗan zuwa mata hutu dole ta haƙura. Dan ba’a barinsu, sai dai taje ta wunar mata ta dawo. Ko kuma idan bikine suje su kwana da Umm. Amma yau sai gashi wai Adawiya ita an barta zama a gidan kakarta.

    

       Ɓangaren su Abdallah kam duk yanda sukaso keɓewa da Nu’aymah hakan yaci tura, iyakarsu zuwa su mata ya jiki kamar kowa shikenan. Ita kanta taƙi yarda ta sake dasu.

      A daren yau da ya zama saura kwanaki biyu ɗaurin auren gidan da daddare su baba malam suka buƙaci ganin Nu’aymah da Abdallah sai Naseer. A sashen marigayi kakansu suka taru, dan canne kaɗai babu kowa a ciki.

         Da hanzari Nu’aymah data fito wanka ta zura dogon hijjab akan zanin wanka ta fita kiran da Amal ta sake zuwa tai mata. Ta iske kowa ya hallara ita kawai ake jira, zuciyarta cike da mamakin taron ta ƙarasa garesu. Kusa da ƙafafun Ananah ta zauna tana gaishe da iyayen nata. Duk suka amsa mata da kulawa suna sake tambayarta ƙarfin jikinta.

      Kanta a ƙasa tace, “Alhmdllh naji sauƙi sosai”. A kusan tare suma sukace Alhmdllhi.

      Abban Adawiya ne ya buɗe taron da addu’a kamar yanda shari’a ta koyar da mu. Bayan sun kammala Ananah ta fara magana akan abinda ya tarasu.

       “To da farko dai zan fara da tuna mana muhimmancin zuminci a addinance da kuma al’adance. mu dukanmu anan babu jahili, kowanne ALLAH yay masa nasibi da sani na ilimi dai-dai gwargwadon iko. Harma takai muna koyar da wasu ta hanyar baiwarsa. Dan haka inason mu nutsu, mu kuma fahimci junanmu. Mudai insha ALLAH ƴaƴa ko jikoki bazasu taɓa shiga tsakanin zumincinmu ni da ƴar uwata da muka rage ba. Sannan kuma ƴaƴan nasan ƴaƴa bazau zama silar ruguza naku zumincin ba. To haka nake fatan kuma su Abdullahi karku bari son zukata ya ruguza naku zumincin. Dan haka sakamakon halin da muka fuskanci kuna neman jefa kanku ne ya sakamu yin wani tunanin da ya kamata a kan matsalarku. muke kuma fatan kawo ƙarshenta a yau a kuma yanzun insha ALLAH. Sai ku nutsu kusa hankalinku jikinku dan ALLAH”.

      Kansu duk suka ɗaga mata alamar gamsuwa da zancenta. Suka amsa kuma da cewar “Insha ALLAH”.

      “Alhmdllh” ta faɗa tana maida dubanta ga Nu’aymah data jingina kanta jikin hannun kujerar da Ananah ke zaune tana kallon tattausan carpet ɗin dake tsakkiyar falon. “Zainabu!”.

      “Na’am Ananah”. Nu’aymah ta amsa mata tana ɗagowa da ƙyau.

      “Zainabu wannan zaman nakine. Dan haka inason ki nutsu waje guda ki tsai da hankalinki. Maganar abinda ya duk ya faru mu ajiyesa mu barsa. UBANGIJI yana kallon kowa yana kuma sane da komai. Duk da bamu gaskataba zukatanmu basu bar rawa da ciwo ba akan batun, amma muna nan akan bincike ainahin gaskiyar al’amarin dan bazamu bari ya wuce a banza ba saboda kiyaye gaba akan na baya. Shiyyasa muka yanke shawarar da mu kanmu muke da tabbacin zata sama mana nutsuwa da ke kanki. Ga Abdullahi nan, ga kuma Nasiru nan. Dukansu ƴan uwanki ne kuma masu sonki da fatan zama dake a matsayin matar aurensu. Kamar yanda a wancen karon bamu tauye haƙƙinki ba, a wannan karon ma bazamu tauye ba. Dan haka munason a yanzu basai anjimaba ki nuna mana wanda kike so tsakanin Abdullahi da Nasiru domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin zuri’ar mu”.

      Wani irin faɗuwa gaban Nu’aymah yayi, ta dubi Nasir ta dubi Abdallah sai kuma ta maida idonta kan iyayen nasu. Muryarta naɗan rawa tace, “Ananah kuma a yanzu?”.

       Hajjo tace, “Ƙwarai da gaske Zainabu, a yanzu zaki nuna mana zaɓinki, dan muna buƙatar salama da zaman lafiya”.

    Zuciyarta na wani irin harbawa ta sake duban su Abdallah. Yanda duk suka zuba mata idanu cike da tashin hankali sai itama suka sake ɗaga nata hankali ƙololuwa. Saurin maida kanta ƙasa tai tanajin anya kuwa zata iya?. A take rauninta ya sake bayyana bisa fuska tamkar yanda suma duk suke a raunane zukatansu na rawa da barazanar son faso ƙirazansu su fito………

        Abbah Musbahu ne ya katseta da cewa, “Mamana ke muke saurare, ki daure ki faɗa mana abinda ke a ranki kinji, kinga dai bazaki auri maza biyu ba, dan haka karkiji komai ki zaɓi ɗaya a cikinsu mu zamu fahimceki suma haka. Zakuma mu saka muku albarka a cikin al’amarin”.

      Kuka Nu’aymah ta fashe da shi, bakinta na sake rawa tace, “Ab…a… Abbah ni dukansu ai ina sonsu”.

        Baba malam da tun ɗazun baice komaiba yace, “Zancen banza kenan. Ai munsan dukan kina sonsu, hakanne yasa mukace ki zaɓa tunda ai baki taɓa ganin ana auran maza biyu ba ko!”.

       Bayan ta ɗan zabura kaɗan ta ƙara mannewa da jikin Ananah. Sai ɗan girgiza kanta take hawaye na zubo mata da sauri-sauri.

    Cikin taushin murya Abban Abdallah yace, “A’a yaya ayi mata a hankali. Mamana ki kwantar da hankalinki kinji, ki faɗa mana a cikinsu dawa zaki iya zaman aure a yanzu? Dan bazamu bari a cuta ma rayuwarkiba insha ALLAH. idan ma dukansu basu miki ba falillahil-hamdu, mu a garemu ba komai bane, sai ki kawo wanda kike so koda ba’a cikin zuri’armu yake ba. Zamu duba nagartarsa idan ya cancanta zamu basa ke”.

     Kanta ta jinjina masa tana share hawayenta. Ta ɗago a hankali ta zubama su Abdallah dake kallonta idanun. Kowannensu a kallo ɗaya zaka fahimci roƙonta sukeyi da idanu ta zaɓesa. Hakanne ya sake saka zuciyarta sake raunana. Cikin rawar hannu data jiki ta nunasu da ɗan yatsa.

      Gaba ɗaya falon inda hannunta ya nuna sukabi da kallo…………..✍

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like