YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 54-55

Advertisement

 *NUSAIBA*

       *’YAR AMANA*☘️☘️

Rubutawa Karimatu Abdulhamid

( *MUMMYN MINAL*)

*🌹SUBBAHANALAHI WABI HAMDIHI SUBBAHANALAHIL AZIM*🌹

⚖️

*HAMDALA WRITIN’S ASSOCIATION💪*

Advertisements

        _*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL’UMMA📚}}*_

https://www.facebo

ok.com/111403834371046

          *✨✨{{H.W.A}}✨✨*

       *PAGE 54-55*

____ MUM kuwa kallon ABDULJABBAR tayi da daddy sanan tace ” kun kyauta burinku yacika amma inaso kasani ABDULJABBAR ni banyarda da wanan auren naka ba, sanan bazan ta’ba kar’ban wanan munafukar yarinyar ba amatsayin surikata kagane ko? kuma FINAH ba ita kawulaqan taba ni kawulaqanta ABDULJABBAR nagode sbd haka bakai bani tinda har ka iya rabuwa da FINAH, duk irin sadaukarwar da tayi agareka amma yatashi abanza.

Ana cikin haka FINAH tafito da akwatinta tana ja tana kuka Mum ce tanufeta amma FINAH ta d’aga mata hannu cikin kuka tace ” A’a babu buqata nagode da irin kulawarki agareni sanan taja akwatinta tafita ta wulla acikin motarta wanda dama daddyn tane yasiya mata taja motar megadi ya bud’e mata qofa, aguje ta fice a gidan.

Advertisements

ALLAH sarki my FINAH ALLAH yakiyaye hanya😓

Daddy kuwa kallon Anti Amarya yayi yace ” ki d’aure yarinyar nan kubar shashinan”

Anti Amarya kuwa talafawa NUSAIBA tayi taka mata sukabar shashin.

Daddy kuwa kallon Mum yayi yace ” inaso kisani ranar juma’a zan aurar da Ikiram za ayi gangarimar walima sutare a gidan su ABDULJABBAR ma da matarsa aranar zasu koma sabon gidan su.

Cikin Masifa MUM tace ” ni ina ruwana da wani ABDULJABBAR bansan shiba,  IKIRAM kuma ba ubanda ya isa ya aurar da ita ayanzu”

Wani mugun kallo daddy yayi mata sanan yace ” yade rage naki nidai nasanar miki dan haka nafita hakkin ki domin ni bazan bar diyata takoyi baqin hali irin naki ba”

ABDULJABBAR kuwa matsawa yayi kusa da Mum yace ” Mummy dan Allah kiyi haquri ki saurareni kiji abunda zanfada mik…… “A’ a  ni na fada maka bansanka ba kawai kaje abunka banson jin komai daga bakinka!!!!!!!!!!!!. Mum tayi maganar da qarfi.

Daddy kuwa cewa yayi bakomai ABDULJABBAR jeka kawai kabata wani lokaci, sanan daddy yadubi MUM yace ” inaso kisani kowa yatuba dan wuya ba lada, kinde ji da kunenki abunda surukartaki tace, tayi niyar aika tawa sbd haka ma koda tafasa ba lada domin ba don Allah tayi niyar bari ba, sai dan can wani nufi nata na banza sbd haka idan kin kyalewa duniya naki dan kekika cutu, tinda ita gatacan tatafi gun nata iyayen kuma zasu kar’beta hanu bibiyu”

Daddy nakaiwa nan yai focewarsa shima ABDULJABBAR dakinsa ya koma yana zubar da hawaye, Itako Mum mayafinta ta dauka tafice tabar gidan.

   *BAYAN KWANA BIYU*

‘YAR AMANA kuwa abun duniya duk ya isheta domin kuwa kullum a cikin kuka take sbd baqin cikin abunda da ABDULJABBAR yayi mata, gashi kullum sai tanemi JALALUDEEN ta wayar Anti Amarya amma wayarsa taita ringing yaki dauka, dan haka hankalinta yaqara tashi domin tasan JALALUDEEN fishi yakeyi da ita.

Anti Amarya kuwa sosai take kula da NUSAIBA tamkar ‘yarta ko qanwarta dan gyara sosai takeyi mata irin namasu jego sbd aika-aikan da ABDULJABBAR yayi mata.

ABDULJABBAR kuwa kwana biyunan kwata-Kwata baya cikin nutsuwarsa  sbd fishin da MUM takeyi dashi dan duk safiya sai yaje dakinta dan yagaisheta amma haka zata masa korar kare, dan haka ABDULJABBAR duk yafita haiyacinsa danko takan NUSAIBA bai sake biba, amma tana nan maqale azucoyarsa, ga lamarin kess dinsa da su ABBAN FINAH domin kuwa ajiyane Allah yabashi sa’a tarkon da yad’a namusu ya cafkesu domin kuwa ayanzu su Abban FINAH suna can tsare domin zasu shiga kotu, dan haka ABDULJABBAR duk yabi yabirkice domin yana buqatar addu’ar Mum gashi Mum tana fishi dashi, shikam yana tsoron su Alhaji biliyaminu suyi nasara akansa domin yasan tabbas sukayi nasara insuka fito sai sunga bayansa da dukkan ahalinsa, dan haka ABDULJABBAR ya birkice yarasa nutsuwarsa duk acikin kwana biyu yabi yarame ya lalace gashi jibi ne ranar tarewarsu asabon gidansa, to dadinsa daya ma daddy nayi masa addu’a tare da kwantar masa da hankali.

_________________________

FINAH kuwa tinda ta koma gida ba ta da aiki kullum sai kuka sbd baqin cikin abunda ABDULJABBAR yayi mata gashi kuma kullum sonsa qaruwar mata yakeyi, Mum dinta kuwa abun har haushi yake bata, dan haka ta shawarci Abban FINAH domin yayiwa FINAH biza tabar qasar tatafi can America, ta qaro ilimi qila tasamu sausauci, koda suka samu FINAH da zancen sai cewa tayi itakam ayanzu bata da qwaqwalwar da zata dau karatu, kawai de tayarda zataje Dubai tad’an huta kadan, domin akwai wasu qawayenta acan.

To Ana washe garin FINAH zata tafine labari yasame su akan SS ABDULJABBAR MAINA yakama Abbanta da abokanansa FINAH tayi kuka kamar me, Kuma taje gurin da aka tseresu din amma ance ba belin domin kuwa dole sai sunje kotu, alokacin nefa FINAH taji tafara tsanar ABDULJABBAR wato duk tsanar da yake mata bazai tsaya akanta kawai ba, harsai yasa iyayenta aciki.

Itako Mum din FINAH yau hargida driver dinta yakawota gurin MUM din ABDULJABBAR, sosai taciwa MUM mutunci akan tajawa danta kunne yafito mata da mijinta haka tagama tijararta tatafi, Itako Mum sosai ranta ya ‘baci dan haka ABDULJABBAR yana shigowa parlour d’in ta tsinkeshi da mari, cikin huci tace ” bani bakai har abada mudin bakaje kafito da daddyn FINAH ba”

“Cikin kuka ABDULJABBAR yace ” haba Mum kamata yayi kiyi binkice kiji sanan ni bani natsaresu ba kudin gwamnati dana talakawa sukaci gwamnati ta tsaresu sbd haka ni baruwa na aikina kawai nakeyi”

Wani marin Mum takuma saukemar tace ” wato ina fada kana fada ko to wlh yazame maka dole kasaki Alhaji Qasimu da abokanansa ko na tsinema”

Arazane ABDULJABBAR yakalli Mum yana kuka yace ” tabbas yanzu zatona yafara gasgata MUM anya kuwa ke kika haifeni?”

“Ita tahaifeka ABDULJABBAR kawai de itadin mahaukaciya ce kuma jahila marar basira balle tunani to wlh kisani muddin kikasa ABDULJABBAR yasaki mutananan to abakin auranki dan har sai na miki saki daddaya har uku, daddy yafada rai ‘bace.

Cikin masifa Mum tace to ” saime dan kasakeni to ni bara kaji ma dama ashirye nake dan inbar gidanka”

Daddy kuwa kallon ABDULJABBAR yayi yace ” inaso kasani koda kuwa zata tsinemaka banyarda kasaki wa’yanan azalumanba, amma inaso kasani inkuma kabiye tata kasakesu itace gawar fari sanan ni, sai kai da matarka da qanwarka, amma inkabari gwamnati tayi musu hukunci dai dai da laifinsu to kaceci dinbin rayuka sama da millions sbd haka sai kazaba, umarni wa zakabi nata ko nawa, sanan ABDULJABBAR koni mahaifinka inka tabbatar da ina cin haqqin da banawa ba to kazo ka kamani.

Sanan tarewarku gobe ne bafashi”.

Ficewarsa daddy yayi agidan baki daya, shiko ABDULJABBAR ranar wuni yayi yana kuka.

Ayau ne aka d’aura auren  IKIRAM tare da wata gangariyar walima da aka shirya,  Mum dan bakin ciki kamar tayi yaya Anti Amarya ita ke tsaye akan komai da yamma ta shirya amare NUSAIBA DA IKIRAM, aka nufi gurin walima inda kowa yazo domin kuwa iyaye maza da mata duk sun halara, da qawaye da kowa da kowa, duk afillin gidan daddy harshi kanshi ABDULJABBAR yayi fes dashi kamar ba mai tatare da damuwa ba, sai satar kallon NUSAIBA YAKEYI.

Itako NUSAIBA inbanda kuka ba abunda takeyi.

MUM kuwa tana can cikin daki tana kuka sbd baqin ciki gashi bata gaiyaci kowa nataba dama ‘YAR uwarta guda daya ce Karima kuma gashi anemeta anrasa daga ita har jaririyarta.

Kuka sosai Mum taitayi na rashin ‘yar uwarta domin kuwa tasan da tananan zata bata shawarar da yadace.

Har akama gama walima aka tashi Mum batafito ba alokacin ne kuma za akai amare gidan su, dan haka Anti Amarya Takawo Ikiram gun Mum domin tai mata fada amma Mum taqi kulasu itako Anti Amarya fita tayi tabar dakin, Anti Amarya nafita Ikiram tafada jikin Mum tana kuka nan MUM tarungumeta suka ci gaba da kukan tare can Ikiram tace ” dan Allah Mum kiyafemin laifukan da namiki kinga gidan wasu zani”

“Bakomai Ikiram nayafemiki Allah yayi miki Albarka kuma kiyiwa mijinki da ‘yan uwansa biyayya shikenan fadan dazanmiki Ikiram”  Ikiram kuwa cikin kuka tace ” dan Allah MUM kiyafewa yaya ABDULJABBAR naji ance ranar Monday zasu shiga kotu kiyafemasa MUM ko zaiyi nasara akansu”

“A’a Ikiram ba ruwanki amaganar nan… Anti Amarya ce tashigo takama hanun Ikiram, suka fita ad’akin inda Ikiram tana tayiwa MUM magiya akan tayefewa d’an uwanta, haka anti Amarya tasa Ikiram amota wata qanwar daddy da sukazo biki tashiga akatafi kai Ikiram gidan masoyinta.

Mus’af, itama ‘YAR AMANA aka wuce da ita gidan ABDULJABBAR.

‘YAR AMANA kuwa ana ajiyeta kowa ya watse yabarta kasancewar dama bata da qawa sai Ikiram gashi itama IKIRAM tana nata gidan, kuka sosai NUSAIBA takeyi, baqin cikinta ma bata da waya, da taqira JALALUDEEN awanan daren haka NUSAIBA tagama kukanta har bacci ‘barawo yayi gaba da ita.

Shiko ABDULJABBAR yana shigowa gidan kai tsaye d’akin ta Yanufo bude qofar yayi yaleqo yaganta tana bacci qundune gu daya tamkar da acikin uwarsa, tausayinta yaji dan haka yashiga dakin yatsaya akan ta yatofeta da addu’a sanan yakai hanunsa dan ya gyara mata kwanciya caraf ta kamo hanunsa cikin baccin aikuwa ya fado jikinta rungumeshi tayi tace ” dan Allah JALALUDEEN karka rabu dani domin kai nakeso bazan iya jure rashinkaba”

Wani takaicine ya tsaya a zuciyar ABDULJABBAR ji yayi kamar yarufeta da duka amma ya duba fuskarta yaga baccinta takeyi muraran.

Yunqurin tashi yayi amma NUSAIBA tasake rungumeshi kam, dole ya haqura duk sanda yai qurin tashi saita rungumeshi,  tana sunbatun son JALALUDEEN qarshe de haqura yayi suka kwana haka wanda takaici ya hanashi yin bacci sai da dare ya tsala sosai sanan ya zame jikinsa yaje yayi wanka tare da alwala yai ta sallah da karatun alQur’ani har asuba tayi sanan yatafi massalaci.

********        **********       *********

IKIRAM kuwa agidan ta a daren kwana farin ciki sukayi rungume da juna ita da Mus’af domin yayi mata alqawarin bazai ta’bata ba harsai taqarasa karatunta dan haka suka kwana suna yiwa junansu kalaman soyayya, washe gari hajiyar su Mus’af ta aiki Sakina takai musu breakfast mai rai da lafiya.

Shiko ABDULJABBAR yana dawowa daga massalaci yayi wanka ya shirya tsaf cikin qananan kaya, yayi kyau abunsa sai sheqi yakeyi ‘bangare daya kuma azuciyarsa damuwa ce fal.

NUSAIBA ce ke zaune tana karin kummalo kallonta yayi yace ”  kintashi lafiya amaryata, wani matsiyacin kallo tamasa ruwan lip ton din da takesha wanda Anti Amarya ta aiko musu da sauran abubuwa sai qamshi ke tashi ruwan lip ton din yakai hanunsa kan nata ai kuwa ta ajiye kofin, daukar kofin yayi yashanye sauran sanan yace ” ni zantafi kotu kiyimin addu’a domin ina da buqatar addu’arki dan wata shara’a zamuyi.

Wani mugun kallo NUSAIBA tamasa sanan tace ” ina ruwana kar Allah yasa kayi nasara mmmmmttttsssssss. Taja wani uban tsaki…………………..

Hmmm muje de zuwa

*Albishirunku masoya MUMMYN MINAL ko kunsan inanan tafe muku da wani qayataccen littafi mai suna( MIJINKI MIJINA NE )HHHHHH, HHHMMMM, Kede ‘Yar uwa d’an uwa kune mi naku kusha karatu domin kuwa nashirya tsab domin baku ni shadi acikin novel din MIJINKI MIJI NANE, wanda ya tatara gwarama da soyayya, da kuma mulki, da zalinci muje zuwa my pants ALLAH yabamu sa’a*

Dan Allah inkin karanta kiyimin shere

*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAKA*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like