YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 66-67

Advertisement

 

*NUSAIBA*

       *’YAR AMANA*☘️☘️

Littafin Karimatu Abdulhamid

( *MUMMYN MINAL*)

🌹 *SUBBAHANALLAHI WABI HAMDIHI SUBBAHANALLAHIL AZIM* 🌹

*HAMDALA WRITIN’S ASSOCIATION💪*

        _*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL’UMMA📚}}*_

https://www.facebook.com/111403834371046

Advertisements

          *✨✨{{H.W.A}}✨✨*

*Page  65-66*

____ Cikin kuka Anti  Karima tace ” jaririyata natuna lokacinda na haifi jaririyata Fatima fuskarta da komai nata tamkar nawanan jaririyar”

Mum kuwa cewa tayi “to inbanda abunki Karima miye na kukan dole ma suyi kama tinda dukkansu jini daya ne ai”.

Anti Amarya kuwa cewa tayi ” ai dole tayi kuka tinda sace mata jaririyar ta akayi, d’an mutum kuwa ai ba abun wasa bane”

Cikin kuka Anti Karima tace ” A’a ba asace min jaririya ta ba, tabbas natuno da hanuna nabawa wani mutum sai de bansan wanene bane”

Kafin suyi magana daddy ne yazo gurin da murnarsa yana cewa ” masha Allah

Mungod Allah tinda anyi nasara”

Mum kuwa jaririn dake hanunta tamiqa masa tana dariya tace ” Abban yara ga abokinka nan kugaisa”

Advertisements

Bissimillah daddy yayi yakar’bi yaron yamasa addu’a ya miqawa mum sanan Anti Karima tamiqa masa macen tana hawaye, cikin farin ciki daddy yakar’beta yana cewa ” sannu da zuwa uwar gida na”

Cikin tsokana Mum tace ” ai bata isaba nice uwar gida sai de ko tazama amarya.

Anti Amarya tace ” a’a nima banyarda ba nice Amarya sai de tazame mana ‘yar wanke-wanke” dukkasu dariya sukayi amma banda Anti Karima da take hawaye, daddy ne yatambayi dalilin hawayenta, nan Mum tasanar dashi komai.

Daddy kuwa cewa yayi to ” shikenan bari mukoma gida, dolane mutsananta binkice da addu’a akan lamarin.

Daddy ne yatambaya ina ABDULJABBAR.

Dr musa ne yafito nan yake sanarwa daddy akan ABDULJABBAR yana gurin matarsa.

Jingina kai kowa yayi agurin, itako mum cikin masifa tace ” au wato shi bama ta yaran yakeyi ba ko? Shi tamatarsa yake tinda gashi baru sarkin soyayya” haka de mum ta qaraci fadanta bawanda yakula ta.

Shi kuwa ABDULJABBAR yana can dakin da akakai NUSAIBA domin tahuta, yana zaune akan kujera akan gefen gadon da take, yariqe tafin hanunta yana mirzawa. Itako NUSAIBA baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali.

Mum kuwa tini tafara qiran mutane tana fada musu tayi jikoki, nan da nan asibitin yafara cika da mutane domin kuwa Ikiram tazo ita da mijinta daga wasu daga ‘yan uwan daddy da Mum harma dasu ladidin bariki wato ‘yan uwan anti Amarya.

Daddy kuwa gida yatafi  zuwa yamma sai  yasake shirin komawa asibitin inda yasanarwa megadinsa akan anmasa haihuwa,  ai kuwa Baba megadi yace zaibishi asibitin yaga tagwaye, domin kuwa Baba megadi akwai fuskar da yakeso yaqara gani, ba jayayya daddy ya yarda suka rufe gidan suka nufi asibiti.

Inda suna zuwa suka samu NUSAIBA tafarko, inda kowa yamata sannu amma banda Mum, danko kallon inda take Mum bata yiba sai ma fada da takewa ABDULJABBAR wai baya ta yaran sai ta mata,   suma su daddy dakin da NUSAIBA take suka nufa domin suyi mata sannu, suna shiga Megadi yaga Anti Karima, yana takalonta, itama tana kallonsa har idonsa ya sauqa akan NUSAIBA,  sannu ya mata bayan daddy ya mata sannu, itako NUSAIBA kamar amafarki taji kamar tasan muryar dan haka tadago kai tace ” baffana”

Da sauri megadi yakalli NUSAIBA yace ” baiwar Allah ke wacece wlh kina kama da ‘yata ‘yar Amana”

Yunqurin tashi NUSAIBA tayi amma tasa qara sbd azaba da taji, da sauri ABDULJABBAR yamai data ta kwanta yana mata sannu, itako NUSAIBA nuna baffa tayi tana hawaye tace ” baffa nice! Nice ‘YAR AMANARKA ina kashiga ne baffa inayinki kuma gwaggo?”

Shiko baffa kuka yasa yace ” ‘yar amanata yanzu kina nifin kece matar yaron kirki ABDULJABBAR?”

“Eh baffa nice ya akayi kazo nan?”

Kowa nagurin mamaki yarufeshi suna kallon ikon Allah.

Dr musa ne yashigo domin yace suragu hayaniya tayi yawa amma daddy yace bakomai yabar kowa agurin kawai.

ABDULJABBAR kuwa matsawa yayi kusa da baffa yace ” dama Baba kaine baffan NUSAIBA shiya sa nake gani kamar nasanka, amma namanta inda muka ta’ba haduwa”

“Eh ABDULJABBAR nine nima gani nakeyi kamar nasanka amma namanta a ina, ashe siriki nane shi”

Kallon Anti Karima Baffa yayi yace ” baiwar Allah kinsanni?”

Anti Karima kuwa cewa tayi ina tinanin kamarde nasanka”

“Shin kina da jaririya shekaru 20 da suka wuce?”

Tashi Anti Karima tayi tana kuka tace ” tabbas ina da jaririya shekaru 20  da suka wuce aka biyoni domin za’a kasheta shine nashiga  cikin wata rugar fulani cikin dare na bubuga wata bukka sai wani kammilin mutum yafito, na damqa mishi amanar jaririya ta, naci gaba da gudu har nafada wani rami daga nan bankuma sananin meke faruwa dani ba har tsawon shekaru masu yawa har zuwa ranar da ABDULJABBAR yabugeni da mota ashe wai hauka nakeyi bigenin da yayi shine sanadiyar dawowar hankalina Anti Karima taqarasa fada tana hawaye.

Baffa kuwa cewa yayi ” nine mutumin da kika bawa jaririyar ki, kuma jaririyar ki ba kowa bace face NUSAIBA gata nan akwance”.

Nanfa guri ya hautsine inda NUSAIBA tama manta da wani ciwo ajikinta tatashi tsaye tana kuka tana cewa ” baffa dama ina da uwa araye bata mutuba?”

“Eh NUSAIBA kina da mahaifiya araye kuma gatanan itace tabani amanarki”

Ai da gudu ‘YAR AMANA tanufi Anti Karima suka rungume juna domin dukkansu biyun ji sukeyi wani abu najansu, nanfa guri ya hautsine da murna da koke-koke, inda NUSAIBA taga yaranta ahanun Mum aikuwa tasa kuka tace ” akar’bo mata yaranta kar Mum takashesu.

Haba Nan fa Mum tafara kuka tana cewa ” haba diyata Fatima tayaya zan kashe jikokina wlh ina sonsu kuma kema ina sonki ai bansan ashe ke jinina bace.

Haka department asibiti ta hautsine dan haka dole aranar dr musa yabasu sallama, kuma yace norse zata rinqa zuwa duba NUSAIBA har gida.

Haka suka tatara suka nufi gidan Daddy, inda Mum take rungume da yaran bata bawa kowa wai kar su wahala, danko ubansu da uwarsu basu daukesu ba, har yanzu.

Dare nayi daddy yaqira kowa ababban parlour din gidan ciki kuwa harda  Baffa da kuma ‘yan uwan Alhaji halilu wato mahaifin NUSAIBA.

Inda daddy yace  Baffa yabasu labarin yanda akayi  FATIMA tazo hanunsa da kuma yanda akayi sunanta yakoma NUSAIBA………..

Hmm muje zuwa de my pans

Dan Allah inkinkaranta ki tura asauran groups

*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like