GOBE NA 64

Advertisement

 

*GOBE NA…*

By Khadeeja Candy 

6️⃣4️⃣

Iyakar kokarin da nai na danne dariya ta ne domin har ga Allah ya bani dariya matuka, daga ganin amai sai ya sa rai da ciki, ko da yake idan ance ina da cikin ba mamaki tunda mahaifa a bude take kamar yadda Aminu ya fada wai ina ta haihuwa zan tsufar da shi, yau kuma gashi Allah ya kawo ni inda ake kaunar yaya ake son haihuwa.

Advertisements

 Ganin abun nasa ba mai karewa ba ne yasa na nufi gurin da nake aje tsintsiya na dauka na dawo gurin da zimmar gyara gurin sai ya kai hannu ya rike hannuna. 

“That’s my condition idan mace tana da ciki bata aikin komai sai cikin ya tsufa”

Kallon mamaki nai masa. 

“Wani irin ciki dan Allah what if malaria ce?”

Dan murmushi yai murmushin dake nuna alamar be jidadin kalmar ba, ya karbe tsintsiyar ya aje ya matsa kusa da ni ya rike hannayensa yana min kyakkyawan murmushinsa cikin sanyi murya yace. 

“Kin fatar ciki ne mana, da ko ya ko kuma duka biyun Allah ya hada ban ki ba, ina son haihuwa lims ina son yaya, yaya rahama ne sanyin idaniya ne i need my own family too, Hajiya ma tana son na haihu Siyama ni kaina ina son naga yayana na ciki, ko yayana nawa zaki haifa min ina so ni dai fatana su zama masu albarka kuma masu tausayinmu”

Advertisements

Sai kuma ya zaunar da ni ya kara jimke hannuna yana kallona cikin idona da idanuwansa da suka koma kalar tausayi.

“Ba zan iya fada miki yadda na ji a lokacin dana rasa Baby, idan har wannan aman da kikai ya tabbata ciki ne zan fi kowa farinciki Lims, and idan kika duba rayuwar nan bata da wani tsayo wata kila zamu dade wata kila ba zamu dade ba akalla ya kamata ace kamin mu bar duniya mu yi sadakatul jariya, sannan mu haifi yayan da zasu rika mana addu’a bakya fatar ki ga jinina za su yi kyau idan sun biyo ki look at your nose”

Ya fada yana jan hancina yana murmushi, nima hancin nasa naja. 

“Ko kuma idan sun biyoka ba, Allah ya bamu masu albarka”

Kiss ya mannna min a goshi ya tashi yana fadin. 

“Shiga ciki ki gyara jikinki zanje nai sallah na dawo sai na gyara gurin”

Ba musu na tashi na nufi hanyar dakin, bina yai da kallo sai da shiga sannan na ji ya bude kofar falon na fita. Da na shiga bandakin sai na tsaya haban madubi ina kallon kaina.

“Ba dai wani cikin ba ne? Ke dai Mahaifarki a bude take da anyi abu kadan sai ciki, da gangan dai kike yi so kike ki tara min yaya na rasa yadda zan yi nai saurin tsufa, ki hana ni jindadin rayuwa, yaushe kika haye Aiman da har za a ce kin dauki wani cikin? Mtchssss”

Abun dariya wai abunda Aminu yai min a lokacin dana samun cikin Amal ne ya rika dawo min, lallai na yarda bayan wuya sai dadi kuma komai yai farko dole ne yai karshe gashi a yau na aurin wanda jiran haihuwar ma yake ba kyama ba. 

Tufafina gaba daya na cire tufafi na sake wanka nai alwala na fito daure tawul a kirjina sai na same shi gefen gadona a zauna yana ta kallon kofar bandakin kamar mai jiran fitowata.

Gaban madubi naje na tsaya sai ya mike tsaye ya tsaya a bayana yana kallona ta cikin madubi wani irin kallon ne da a zan iya fadar ma’anarsa ba. 

“Da sannu ina ta maye gurbin abubuwan da na rasa”

Na yi murmushi sai ya rumgume ta baya yana sumbantar kafadata dayan hannunsa kuma a kaina yana shafa kananan tsorayen da ke kaina. Juyowa nai ina kallonsa, sai ya sa hannunsa ya lakaci kumatuna. 

“Ya akai?”

Kasa ce masa komai nai sai kallonsa nake ina murmushi a raina ina ayyana irin kyau da Allah ya hore masa ga sura da cikar zati irin na da’namiji. 

“Kin yi sallah?”

Ya tambaya yana had goshina da nashi, hakan yasa nai saurin sakinsa na nufi wardrobe na dauko wasu tufafin na saka ya shimfida min pray mat na saka Hijabi, har na yi sallah na gama banda kallona babu abunda Ahmad yake.

“Zan samo wacce zata rika dan share share da mopping girki kuma sai na karbo gurin Hajiya”

“Zan iya komai bama bukatar mai aiki, salon wata ta zo ta karbe min kai”

Na fada da iyakar gaskiyata. Ya dan wara ido ya dawo kusa da ni ya zauna.

“Kina tunani akwai wacce zata kwace place dinki? No one i mean no one”

“To idan kuma tai creating nata place din fa”

“Ai ba dadin zama za ta ji ba, kin riga kin karbe Hajiya Siyama ni da duk Family na”

“Ni dai ban yarda ba”

“Dole ma ki yarda wannan ka’idata ce indai macce nada ciki zan barta ta ji da dawainiyar cikin ne kawai sai na dauke mata na gida amman banda kaina”

Ya fada da murmushin.

“To yanzu shikenan sai ka cewa Hajiya ina da ciki Fisabilillahi sati daya da kawo ni?”

“A a ba fada mata zan yi ba, sai sai tace ba mu da hakuri mun yi ciki tun a waje, abun ai da kunya, amman kuma idan kika yi wata 8 kika haihuwa ganewa za yi fa?”

Magana yake da ni yana zaro ido kamar mai magana da wata karamar yarinya har da bude baki. Ni ban sansan lokacin da na fashe da dariyar ba na buge masa bakin sai ya rumgume ni yana kissing dina. 

Kamar wasa, abu ya zama na gaske ko kofina Ahmad baya barin na dauke, idan ya bar ni na yi wani aikin sai idan baya nan, wata tsohuwa aka dauko tana mana aiki wanke wanke da shara sai mopping da karbo mana abincin gurin Hajiya, ban san abunda ya fadawa Hajiyarsa ba kullum sai ta kawo min abincin rana da dare wani lokacin kuma idan bana sha’awar abincin sai ya siyo min. Sai dai tun wacan aman da nai ban sake yin wani ba, kuma a kullum sai Ahmad ya tambaye ni me kike ji me kike so ina ke maki ciwo idan kin ji wani abu ki fada, haka yake kula da ni kamar wacce mai cikin fari, idan ya fita kuma ya ga wani abun kwadayi sai ya siyo min wai be sani ba ko ina so. 

  Be barni naje gida ba sai da nai wata uku da kuwa da irin kewar da nayi da ganin su Inna da Mama, suna Namra kam ko wane weekend sai ya dauko su sun zo mana hutu. Kowa fadi yake na canja wai fuskata ta kara cika fari na ya fito kamar ba ni ba, ni kaina na san na canja domin ina jin nauyin jikina a yanzu sabanin da. A gidan na wuni sai dare yaje da kansa ya dauko ni bayan ya shiga ya gaisa da su Mama yai musu alheri sannan muka kamo hanya. 

“Zaki ci tsire?”

Yana tambaya na hade yawu dan na hango mai tsiren yana gasawa gefen hanya. Sai ya faka motarsa ya fita ya siyo min ya dawo. 

“Sauran ice cream”

“A a ba ki san sanyi yana effecting abunda ke ciki ba? Na lura da ke kullun sai kin sha ruwan sanyi fa sai ma na cire makulin fridge din nan ai”

“Ai kadan nake sha”

Be ce min komai ba ya faka gefen titi ya sake fita ya siyo min ice cream sannan ya dawo motar a lokacin ni kam har na yi nisa da fara cin tsiren. 

Ko da muka isa gida na cinye rabi sai dai ba ni kadai ba har da shi dake tukin miko min bakinsa yake na saka masa. A part dinsa yai bakin motar ya zagayo ya bude min kamar yadda ya saba na fito rike da kedar sai ya rufe motar sannan ya karba ledar hannuna. 

“Jira ni a nan na fito Hajiya na da bako zaki je ki gaishe shi”

A gurin na tsaya har ya shiga ciki ya fito, sannan ya bude motarsa ya dauko tissue ya gyara min bakina kamar wata karamar yarinya ya jefar sannan ya rika hannuna muka nufi part din Hajiya. Sai muna daf da shiga sannan ya saki hannun nawa ya bude min kofar falon na shiga bakin kumshe da sallama Hajiya ce kadai a falon sai mai aikinta sam ban lura da su Kabir ba da wata mai zaman mahaifiyarsa wace suka tafi waje tare da ita da matarsa da wasu mutanen da suke tare da su ba sai da naje zan zauna. Aiko ba shiri na gwalo ido baki saki ina kallonshi shi ko sai dariya yake min. 

“Kabir…..?”

“Na’am….. ”

Kara zaro ido nai jin muryarsa ce da gaske kuma gashi har ya amsa min ga shigarsa tsaftsaf cikin kamala, aiko na nufi cikin wani irin mamaki da bazata sai jin nai an rike ni an dawo da ni baya. 

“Ke”

Sai na juyo na kalli Ahmad baki saki farinciki har cikin raina. 

“Ba ka fada min ya dawo ba”

“Ba gashi kin gani ba”

Ya fada yana kokarin zama har lokacin be saki hannuna ba, aiko dan murya ban san lokacin dana rumgume Ahmad din ba sam na ma manta da zancen wata Hajiya tana gurin, har ga Allah ya jidadin samun lafiyar Kabir hakan ya wanke raina fes. Godiya suka rika yi ma Ahmad da Hajiya kamin su shiga yi mana addu’a kala kala suna saka mana albarka. 

“Ka yi sa’ar mata Halima tana da kirki tana da mutunci kuma ta san kanta”

Kabir ya fadawa Ahmad yana kallona, a nan Ahmad ya wani dauke kai yana murmushin yake kamin ya kalleni murya kasa kasa yace. 

“Tashi kije part din mu ki jira ni”

“Wayyo ina son na ga lafiyarsu”

Yar hararata yai ya hade rai, sun sun na tashi ba dan rai ya so ba nai musu sallama har lokacin Kabir kallona yake yana murmushi na fice.

Part dina nadawo na zauna na karasa cinye tsiren na sha ice cream nai nas raina kuma fes, sannan na dauki waya na kira Hajara da kuma yan gidanmu na labarta musu samun lafiyar Kabir Mama ta ji dadi sosai sai yabawa Ahmad yake tana mana addu’ar karin zaman lafiya da kwanciyar hankali, sai da ya shigo sannan na aje wayar ya zauna kusa da ni yana fadin. 

“Sun wuce daman dogiya suka zo yi”

“Na so naga tafiyarsu, Wallahi kamar mafarki nake gani wai Kabir ya samu lafiya”

“A a ba zan bari ba, naga mutum sai kallonki yake yana fadin na yi dacen mata, kin san zafin da na ji kuwa?”

Na yi dariya. 

“To ai shi bada wata manufa ya fada ba”

“Ya za’ayi na sani namiji ne fa hmmm”

Dariya na cigaba da yi, nikam kishin Ahmad har mamaki yake ba, ashe da shi ne ba zai yarda nai aiki da aurensa ba a kullum idan zan fita Hijab nake sakawa amman haka be hana yace min yaga ana kallona indai muna tare ne ya rika kallon maza kenan ya ga wanda ya kalle ni da wanda be kalleni ba, sai yawan nanata min cewar na dinga kiyayewa shi fa yana da kishi. 

Al-hamdulillah, bayan godiya babu abunda zan yi ma mahallincina, a can baya da nake cikin wuyar ma nai masa godiya balle yanzu da nake cikin ni’imar Allah da Rahamarsa  har na shiga wata na biyar da cikina ban san wani abu ciwo ba, iyakar abunda nake yawan yi kwadayin sai amai shi ma kuma ko da yaushe ba, sai dai na lura wannan cikin ba kamar sauran ba ne, domin wannan yana min girma sosai idan kuma ya tashi min motsi ba guri daya ko biyu nake jin motsin ba. 

  Ranar da na koma asibiti na fadawa likitar wacce ta kasance mace ce yar’uwata, wacce Ahmad ya sama min kuma ya fada min ita kadai zata rika duba ni, duk da irin amincin da ke tsakaninss da Dr Nura kin yarda yai ace shine ke duba ni. 

Sai da ta gama abunda take ta tabbatar da lafiya ta tambaye ni ko ina jin wani abu nace mata a a sai dai motsin kawai ina jinsa ba daya ba.

“Eh daman ai dole zaki ji wannan, Allah dai ya raba lafiya”

Maganarta ta ban mamaki kamar na tambaya sai kuma nai shiru na, wata kila ba daya ba ne shiyasa nake jin haka domin har nauyi yake min, sai a lokacin na tuna Ahmad be bani takadar gwajin da akai ba da hoto ya fadar fada min edd na is 21 on May wata kila ya sani shiyasa yaki fada min. 

 Bayan na fito na kira shi a waya na sanar masa na fito, be dade ba ya kira ni yace na fito muje, fanken da nake ci n aje na dauki haka na rike a hannu na fita zuwa inda yake. 

 A mota nake masa zancen abunda likitan ta fada sai fara dariya yace cewa 

“Jinina mai karfi ne ba daya na saka miki ba biyu ne”

“Da gaske?”

Dariya ya sake yi yana kallona. 

“Wannan tashin hankalin nake gudu shiyasa ban fada miki ba”

Bance masa komai ba har muka isa gida, dayan ma ya ka haife shi balle biyu Allah na tuba duk da haihuwa idan Allah ya kawo maka saukinta sai ka samu sa’ida. A lokacin ne na fara laulayi mai wahala irin wanda ban taba yi ba, ga amai da na ci abinci sai amai ga ciwon jiki, komai nake son abu idan aka kawo min shi sai kuma na ji ya fita raina haka dai Ahmad yai ta hakuri da ni sai masifa kala kala, ko be min komai ba na zauna nai ta masa kuka duk yabi ya rude, idan aka samu sa’ida sai fa idan na yi bachi yadda kasan wata yarinyar goye haka na koma sai son jiki da shagwaba kala kala, wanka ma wani lokacin sai na ki nace ba zan iya ba sai dai shi ya min. Kulawa kam ina samunta sosai a gurin Hajiya da kuma danta, domin ko nishi nai da karfi sai Ahmad ya tambayi lafiyata. 

“Lafiya….”

“Zogale nake son ci”

Ya kalli agogon falon wanda ya nuna karfe goma sha daya.

“Ina za a samu zogale yanzun”

“Ni dai ita nake son ci”

Na fada a shagwabe kamar zan fashe da kuka, kuma har ga Allah na kusan kuka dan nauyin cikin ya fara isata ga bachi ina son yi amman ba hali ko na kwanta ba zan yi bachin ba. Tashi yai ya nufi dakinsa sai gashi ya fito sanye da shadda amaimakon kayan bachin dake jikinsa dazun. 

Sai kusan 12 ya shigo hannunsa rike da bowl da murfi a kai, dayan hannunsa kuma rike da bakar leda kusa da ni ya zauna ya aje yana fadin. 

“Gashi an samo”

Tashi nai zaune da mamaki domin har ga Allah ban yi zaton za a samo ba, domin har da neman fitina yasa na ce masa ina son zogale. 

“Ina ka samu”

“Hajiya nai ma magana sai tai magana a gurin Hajiya Binta su wai suma siye da yawa su aje ne har kullin ma ta debo min”

Ya fada yana bude min zogale ce a cikin har da kankararta ta kame sosai. Hannu na kai na dauki kuli daya na fara taunawa sai ya tashi ya dauki zogalen ya zuba mata ruwan zafi sannan ya dawo falo ya cire rigarsa ya koma kitchen din, ina jin lokacin da yake daka kullin a turmi. Sai da ya hada komai sannan ya dauko ya kawo min a falon, kamin ya kwada min yawona kamar za su zuba tsabar kwadayi, ya san halina da son yaji dan haka ya zuba nasa dabam ni kuma ya kara min yajin, ci nai gaba daya na cinye ban raga ba har da sude kwano ba dan kuma na koshi ba daman tun da cikin ya fara girma ba abu kadan ke isata ba sai nai ta ci kamar zubawa ake a wani gurin ba a cikina, hakan kuma be hana na amaye shi. 

  Shi ya kwashe komai ya kashe kayan kallo sannan ya taimaka min na mike tsaye daker muka nufi daki. Sai da nai wanka sannan na dauki wata katuwar ridar yadi na saka domin ita kadai nake sakawa na jidadin kwanciya. Saman gadon na hau na kwanta, sai ya tashi zaune ya fara min addu’a yana tofa min saman cikin sannan ya kwanta bayana ya rumgume ni ya dora hannunsa saman ciki. 

Ga shi ina jin bachi amman idona suka ce fir ba dai bachi ba, can a ji kamar ana saran kashin bayana hakan yasa a tashi zaune ina hawaye a hankali nikam duk wahalar da nake sha a cikin ban taba shan irin wannan ba. Tashi yai shima zaune dan san na kasa bachin ne kamar yadda nake wani lokacin, sai ya matsa baya ya jingina da gadon ni kuma na matsa jikinsa ya rumgume ma kwanta a kirjinsa yana dan matsa min jikin a hankali har bachi yai gaba da ni.

Cikina na cikin wata a bakwai akai shigar kotun karshe akan case din su Abdulhamid, shekara ashiri aka yanke masa hukunci zaman gidan kaso, Abraham kuma da sauran mutanen aka yanke musu hukunci daurin rai da rai domin bayan safarar makama an same su da laifi fashe da makami da cikin har da kisa wani babban dan siyasa. A rana na wuni rai babu dadi sakamakon labarin da na ji ko da ban san shi ba a matsayinsa na musulmi dole na tausaya masa balle kuma akwai yan’uwanta ta jini a tsakani, bayan kuma rayuwar Abdulhamid abar tausayi ce sosai domin be mori komai daga cikinta ba, abun ka da mai neman kuka an fada masa mutuwa sai na zauna nai ta rusa kuka tun Ahmad na ban hakuri har ransa ya bace ya fita ya bar min gidan. 

Sai bayan sallah isha’i ya dawo fuskar nan babu annuri ni ko a lokacin na waye kamar ba ni ba sai faman yawo da katon ciki nake tsakar falo. Ina masa sannu da zuwa ya amsa min ya dauke kai ya shige dakinsa ko kula ni be yi ba, hakan yasa na nufi dakin nasa na same shi yana kokarin cire tufafin jikinsa sai na zauna akan stool din madubin, sai da ya cire rigarsa sannan ya dafa ni. 

“Tashi nan”

Ya zaunar da ni saman gadon ni dai sai kallonsa nake.

“Me aka maka kake bata rai”

“Akan me zaki zauna ki yi ta rusar kuka akan an yankewa wani hukuncin laifin daya aikata”

“Daman ina neman kukan ne”

“To from now on bana son na sake jin sunan Abdulhamid a gidan nan ko abunda ya shafe shi”

Yana fadar hakan ya shige bandaki, haka da yace min sai na ji kamar yace min je ki mutu, aiko a gurin na fara kuka na rashin dalili, daman can sai na yi kukan nake samun natsuwa, ga ciwon jiki ga nauyin ciki ga shi gato duk inda zanje ina nishi kamar na dauko duniya, ga rashin bachi ga shi komai na ci abinci sai na amaye shi tass sannan nake zama lafiya to da wanne zan ji. Har gama wanka ya fito ban daina kukan ba, kusa da ni ya zauna yana dariya. 

“Wannan ciki dai Allah ya taimake ni ki haife min shi lafiya, na lura har ni haushina kike ji” 

Kamar fa ya sani dan zuciyata cike take da haushinsa na rashin dalili tun da ba wani abu yake min ba, ga shi kadai ba har Hajiya da duk masu aikin gidan haushinsu nake ji haka nan dai nake daurewa ina gaisheta kullum, har ta dauke min zuwa sasshenta ganin cikin nawa zama daker tashi daker idan zan zauna tace zauna sannu haka ma idan zan tashi, idan nace ina bukatar abu kuma in ya kai wata duniyar sai ta nemo min shi.

“Mai ciki….. Mai ciki…. ”

Ina kokarin zama yake ce min haka yana min gwalo kamar wani karamin yaro, fillon kujerar na dauka na jefa masa ina dariya sai ya shi ma yasa dariya yana zolayata. 

“Yar Babyta idan fa zaki haihu ni zan miki nakuda”

“A ina a taba ganin namiji yayi nakuda”

“Ni dai sai na yi”

Ya fada yana daga min gira daya sai kace wani tsoron dan iska.

“Ni dai dan Allah Ya Omri ka daina jana ka bar ni na ji da yayanka”

Na fada ina nishi daker daman haka nake idan suka motsa sai su haye min zuciya daker nake numfashi, taso yai ya dawo inda nake zaune ya duka gabana ya bude cikin yana kallon yadda yake motsi sai kuma ya dora kansa sama ya lumshe ido yana murmushi, kamin ya ciro wayarsa ya fara daukata hoto.

Ko da na shiga watan haihuwa ta na zama wata abar tausayi, domin idan zan kwanta sai na nade wani zane sannan na dora cikin akai, dayan fillon kuma na dora kafafuwana sannan nai matashin kai da Ya Omri.

  Ana sauran sati Edd na ya cika na je asibiti sai suka rike ni bayan sun min hoto sun dubani abunda suka fada min wai ba zan iya haihuwa da kaina ba, a lokacin na samu kaina a cikin tashin hankali marar misaltuwa, ba ni kadai ba har da yan gidanmu da kuma Hajiya da Ya Omri, sai a lokacin ne na san cewa abunda ke cikina hudu ne ba biyu ba kamar yadda Ya Omri ya boye min. Sosai ya so fitar da ni waje domin amin aikin acan amman naki domin ganin nake ko mutuwarce kara dai na mutu a kusa da mahaifiyata. Be ki amince min ba sai dai kuma be min yadda nake son din ba domin a cikin kwanakin ya sa aka shirya min komai muka tafi Abuja wata private hospital mai shegen tsada da kyau ga kula kamar za su cinye mutum, yawancin ma turawa ne suke duba matane sai kwararun likitoci. 

  Duk kwana daya a dakin 170k ake biya bayan sauran responsibility na asibiti. 

A ranar Likitan aka min theater kamin a shiga da ni babu wanda ban nemi yafiyarsa ba babu wanda ban yi ma kuka ba, har da amanar yarana na bada hakan yasa hankalin kowa ya tashi, ba ma kamar Ya Omri da har wani rama yai, ni kam har ga Allah na dauka mutuwa zan yi domin duk haihuwa ni nake yi da kaina na tiyata ba, kuma ban tana shan wahala irin na wannan ba. 

Sai dai cikin ikon Allah da iyawarsa da yardarsa sai aka min theater ban san ma anyi ba domin hankalina baya jikina a lokacin, sun dade suna kira sunana kamin na amsa musu domin numfashina yayi nisan zango ga jikin ina jinsa kamar ba nawa ba. Al-hamdulillah likitar da fada tare da sauran nurses da kuma wata likitar ita ma mace Nurses din ma dukansu mata ne. Sun dade a kaina kamin dauko baby dora min a kirji. 

“Duba ki gani me kika haifa”

Cikin lumsasun idanuwana na duba na ce 

“Mace”

Suka sake dora min dayan 

“Namiji”

Suka sake dora min wani. 

“Namiji” 

Na fada idona na cika da kwalla, sai musulmar cikinsu tai hamdalla suka canja min gado suka dora ni akan wani sannan suka rufe min jiki suka turo ni akan gadon aka fito da ni. Mama da Hajiya da Ya Omri ne rike da yaran uku babu komai a fuskarsu sai farinciki. Wani dakin dabam aka kai ni suka jona min gorar jini suka saka min iskar da zata taimaka min gurin numfashi sannan suka min Sannu suka fita. Sai ga Ya Omri na ya shigo rie da Baby fari sol cikin kayan sanye masu kyau da tsada. Gefena na aje baby sannan ya doko ya sumbanci goshina ya rumgume ni hawaye na sauko masa. 

“Thank you so much, Allah ya miki albarka”

“Ya Omri nawa na haifa?”

“Four amman guda ya koma”

Yana rufe baki sai ga Nurse ta shigo da daya Hajiya kuma rike da daya, wani karamin gado dake kusa da ni na asibiti aka jera su, Hajiya ta matso kusa da ni tana min sannu da jiki. 

Naga kulawa na ga gata ba a gurin mijina ba, ba a gurin Hajiya ba duk wani abun da ya take bukata a gurin uwa Hajiya tana min shi, Ya Omri na kam Wallahi yadda yake dawainiya da ni da damuwa har tausayi yake ba ni. Sati na daya suka sallameni muka dawo gida, a nan aka ce min ban ga komai ba indai gata ne da kulawa, daga gurin yan’uwan Ya Omri kamar wandanda basu taba samun haihuwa ba a dangi sai a a kaina haka suka rika kula ni kamar zasu dafa ni su cinye. 

  Madara aka siyo ana hada musu da ita domin nonon baya isarsu bama kamar mazan da ba su iya sha kadan ba. Kayan barkar da Ya Omri yai min sai kace hauka ne ko kuma be san zafin kudi ba, ban cin wadanda nai ta samu gurin yan uwansa da kuma nawa dangin domin kowa ya ji na haifi yan uku sai yayi mamaki kuma ya zo ganinsu. 

Har abokansa ba a bari a baya na gurin bawa yaran kyauta da zuwa ganinsu ga su farare sol gwanin sha’awa ni kaina burgeni suke balle kuma ubansu da ya rasa inda zai dauka ya aje su wanda hakan shi yafi komai yi min dadi, at least na haifa wa wanda yasan darajar yaya kuma ya san kimata domin kullum a cikin tausayina yake da nuna min kauna. 

 Ranar wata Monday akai suna wanda ya kama sati biyu kenan, dayan aka saka masa sunan mahaifin Ahmad wato Muhammad wanda akai wa lakabi da Sudais dayan kuma aka saka masa sunan mahaifin Hajiya Abubakar aka masa lakani da Shuraim, mace kuma aka maida sunan Namra, sai dai ita ana kiranta da Little Namra. 

  An yi shagali iya shagali har abunda ban taba mafarkin za a raba ba anyi, a ranar daga ni har su mum sha bachin gajiya daman tun da suka zo dubiya ba su da aiki sai bachi sai kuma shan nono. 

  Kusan rabin rainon su a hannun Ya Omri na yake indai yana gida to babu ruwana da su sai idan nono za su sha ko madara, idan kuma baya gida ga Baba mai kula min da su ba ni da matsalar daukarsu dan wani lokacin shi da kansa zai musu wanka ko ya wanke musu kashi ko tsarki. 

Sai da su kai shekara biyu da wata biyar sannan Ahmad yasa aka maido da su Namra da Amal da Aiman da Adnan a gidan, sai dai matan dakinsu dabam mazan ma haka, hakan kuma ba karamin faranta min rai yai ba, hakan ne ya kara tabbatar min da cewar lallai Ahmad ya rike yayana kamar nasa, lokaci lokaci  Aminu kan kira shi ya tambayi lafiyarsu wani lokacin kuma sai ya aiko da mota a dauke su ya tafi da su yai musu shopping ya dawo da su, shi kansa rayuwarsa abar tausayi ce a yanzu domin matarsa bata haihuwa ba har yanzu wata kila ma su Namra da yak wulakantawa a baya su ne kadai ya’yansa tun da ita wacce yake aure ta riga ta lalata mahaifarta. Ga dan’uwansa wato Sadi ya zama aban tausayi domin ciwo ya kai shi kasa babu kyau gani, sam ba zaka ganshi kace shine ba, nikam hakan dadi yai min domin kuwa Allah ne ya nuna masa iyakarsa tun a yanzu kamin ayi wani hisabin a lahira….

  Kiri da muzu Ya Omri ya hana ni zuwa barkar haihuwar da Suwaiba ta sake yi na macen da Abdallah baya so, duk kuwa da kasancewar ita din ta zo a lokacin dana haifi yan uku, sai dai mijinta be zo ba kuma be aiko ba be kuma kira ba. Sai na rasa yadda zanyi taya zata haihu na ki zuwa bayan kuma na sani, ai sai ga rashin kyautawa ta, da na san zai hana ni tun farko da ban tambaya ba sai na masa wata karyar na tafi. 

“Idan ban je ba ba zata jidadi ba ko Mama ba zata jidadi ba kuma Wallahi ban kyauta ba, komai fa ta wuce abunda ya faru duk a baya ne”

Banza yai min yana ta wasa da yaransa sai kyalkyalar dariya yake shi da su kamar ma be san ina zaune a dakin ba. Can ya dago ya kalle ni. 

“Magana kike?”

“Barkar Suwaiba”

“Idan ba bacin raina kike son gani ba ki daina min maganar nan, haka kawai ki taka ki tafi gidansa yai ta kallonki”

“Ba zanje lokacin da yake nan ba”

“Na ce ba za a je din ba, ko a munafunce ban amince aje ba”

Ya fada fuskarsa babu alamun wasa, har yanzu yaki yarda Abdallah ya daina so na ya kasa manta abunda ya faru na rasa wane irin kishi ne Ya Omri yake fama da shi ko mai sunan Abdallah baya so, Aminu ma dan ya zame masa dole ne. Duk yadda na so nai convincing dinsa ya amince fir ya ki a dole na hakura sai dai na siye abubuwa na bada nace a kai mata wanda na san hakan ba zai mata dadi ba.

Ranar wata Lahadi ina zaune dakina rike da waya ina chat ya shigo rike da wasu takardu ya zauna kusa da ni yana fadin. 

“Ina tunanin bana da mu za a yi hajji”

Ban san lokacin dana jefar da wayar hannuna ba na tashi na fuskance shi baki sake ido har gurin gira. 

“Da gaske?”

“Yes tun da yara sun yi kwari ai ya kamata ke ma ki kai ziyara, sai mu koma tare, idan Allah kuma ya amince mana kuma sai mu yi ummara idan lokcin yayi”

Rumgume shi nai cikin wata irin murna marar misaltuwa sai ya fara dariya yana fadin. 

“Idan mun dawo zaki karo min yan uku”

“Har yan goma zan karo maka”

Ya fara dariya yana rumgume ni. 

“Kamar gaske, salon kukan ya dawo ta fitina ko”

Murmushi nai sai ya rike fuskata yana kallon cikin idona kamar ba gobe.

“I love you so much”

Ya fada da rada sai ya sumbanci goshinsa na mayar masa. 

“I love you more”

Abunda ban sani ba, ba ni kadai Ahmad ya biyawa ba har da har da Mahaifiyarta da Inna, bayan gyaran gidan da yai musu ga dawainiyar kai abinci duk wata kusan hidimarsu ta dawo kansa, tsanannin dadi da farinciki har na rasa inda zan saka kaina. A tare mu kai hajjin da su wanda su kansu ba su taba saka ran wata rana za su tafi ba balle kuma ni, sai gashi komai ya canja mana kamar ba mu ba, bayan wuya sai dade kuma mai hakuri kan dafa dutse, abunda ban taba zato da tsammani ba shi yake ta zuwa min ba ni da matsala da Hajiya sai dan abun da ba a rasa ba, kusan ma yanzu tafi son jikokin fiye da da domin a yanzu Siyama tai aure tana dakinta ta bar Hajiya sai idan ta kawo ziyara, kamar dai su Hafiza da Husna da Aisha  hankalina a kwance yake a yanzu ga yara a gabana gwanin sha’awa muna rayuwa cikin daula kamar gidan ubansu. 

Gobena tai kyau, Gobena ta zo min ta inda ban zata ba, Gobena ta same min mai Annuri da haske. 

*****    *******    *******    *****

AFTER SOME YEARS…

Da gudu Amal ta fito dakinsu Adnan ta ho kaina kamar zata fada kan tsohon cikin da ke jikina sai kuma ta dawo bayana ta boya, Adnan din sai kokarin kamota yake.

“Ya akai?”

“Momy wai ina operating system tazo ta karbe”

“Momy ba tashi bace ta Anty Namra ce kuma tace kar na bari ya dauka”

“To ina ruwanki ki bani karatu nake”

Sai a lokacin na daga kai na kalleshi. 

“Kai ina taka?”

“Ya ki tashi Sudais ne ya saka mata ruwa”

“Amal ba shi idan ya gama sai ya baki ki aje masa”

“A a Momy tace kar na bashi”

“Zan barshi ya doke ki fa”

“Ni dai ba zan bada ba gaskiya”

Ta fada tana make kafada. 

“Je ka dauko ta Aiman kyale ta yar neman fitina”

Da huci ya nufi dakinsu yana fadin duk da shiga hannunsa sai ya doketa, daga inda take tsaye ta rika masa gwalo tana cewa.

“Ai dai na hana, kuma idan ka dake ni idan Daddy ya dawo na fada masa, ai yace ka daina dukanmu”

“Bana son hayaniyar nan sauka saman kaina”

Na daka mata tsawa sannan ta sauka saman kujerar ta nufi gurin Lil Namra, tashi nai na nufi bedroom dina ina tafiya daker…… 

        *TAMMAT BI HAMDILLAH*

Godiya ga Allah mai kowa mai komai wanda ya bani ikon fara rubuta labarin nan 8 months ago har na kawo yau. Darasin da ke cike Allah ya bamu ikon amfani da shi ya yafe mana kuraruranmu. 

Godiya ga makaranta labarin Gobena a duk inda suke, da yawa mun fara rubutun nan da wasu amman ba mu karasa tare ba, sakamakon yanayin labarin, wasu sun fada min basa son labarin da babu soyayya wasu su ce min wahalar Halima ta yi yawa sun daina karantawa so so kaza kaza, a haka dai na daure na cigaba da rubutawa, Na fada tun farko cewar ban sani ba ko labarin zai muku dadi ko akasin haka domin ba zallar soyayya ba ne, rayuwace ta kalubalen da fadi tashin na rai da kaddara, ni na san akwai wadanda suka fi Halima shiga gararin rayuwa a zahiri, kuma bayan wuya sai dadi, sai gashi ina tsaka da rubuta nai ta haduwa da mutane masu kwatanta rayuwarta da ta Halima wata ma idan ta fada min halin rayuwarta wallahi har ta fi Halima shiga matsala, ban da wace akwai tace min sak yadda Aminu yake haka mijinta yake, akwai wacce tace min yadda Sadi ya lalata yar dan’uwansa Namra, haka kanen mijinta ya lalata yarta, wasu kuma matsin lamba ce daga iyayen miji kamar yadda Halima take sha. 

Ina matukar godiya kuma ina jinjina gurin wandanda suka jure karanta wannan littafi har muka kawo yanzu Allah yasa mu amfana da darasin dake ciki. 

Godiya gare ku yan wattpad, da yan Whatsapp, da facebook i love you All Fisabilillah ina godiya sosai Allah ya bar ran so. 

1 ina ya fi burge ki a cikin littafin nan? 

2 Mi ya fi baki tausayi? 

3 ina ya fi baki haushi? 

4 ina ya fi saki dariya?

5Wane darasi kika koya a cikin littafin nan? 

6 Any kuma zaku iya yarda da kaddararku kamar Halimatu? 

 Ance bayan wuya…….☺ 

***   ***   ***

Sai kuma idan mai kowa mai komai ya amince min mun hadu a littafi na gaba. 

Best regards 💚💛💜💙❤

Khadeeja Candy 🌺😍😘

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

GOBE NA 42

Advertisement   *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣2️⃣ Da hannu daya yake tuka motar yayinda dayan hannunsa yake…

GOBE NA 4

Advertisement  *GOBE NA…* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy  4️⃣ “Sa’adatu kenan, kwana biyu ma kin daina dan lekowa,…

GOBE NA 9

Advertisement  *GOBE NA…* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy  9️⃣ “Wannan kaddararen aure yau Allah ya kawo karshensa, ni…