Advertisement
I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p
PG: 10
BOOK 2.
BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻
*DR ISMA’EL MUHAMMAD RES.*
Advertisements
Alhaji Isma’il ne ke sakkowa daga bene, Shukrah tana biye da shi a bayansa hannunta rike da jaridu fuskarta a hade alamar bukatar da ta gabatar masa tun a daki bata biya ba. Har ya sakko parlorn kasa ya zauna akan two seater ta mika masa jaridun ya karba yasa wasu a gefen sa daya kuma ya fara budawa da alama karantawa zai yi. Shukrah ta kuma marairaicewa kamar zata fashe da kuka tace.
“Kaji Daddy dan Allah.”
Shima ba tare da ya kalleta ba yace.
“Ai na riga na gaya muku idan har ba zaku ji magana ta ba, toh kar wanda ya sake kawo min bukatarsa ya kuma yi zaton zan cika masa ai baku kuka haife ni ba.”
Tasa hannu ta share hawayen fuskarta tana kuma maida kukan da yake shirin fitowa baki daya tace.
“Daddy munje fa aka ce bata cikin masarautar, wallahi Daddy harda kawaye na su Madina muka je amman aka ce bata nan.”
Advertisements
Alhaji Isma’il ya kalli Shukrah da kyau, ya yarda yanzu kam cewar sunje Dije bata nan. Amman dan kar tai zaton ya sakko daga doran fushin da yake yi dasu na rashin zuwa gano Dije, sai da ya mulu sannan ya sake kallon ta yace mata.
“Toh zan sake miki wata, Amman Shukrah wannan itace waya ta karshe da zan sake miki indai ba miji kika fitar ba. Ku kun fiye rigima wallahi, ba ku iya tattali ba, Dije duk ta fi ku alkinta abubuwa mai tsada ko arha. Kunki fitar da mijin aure, yaran abokai na da abakan nawa kansu wasu sun nuna bukatar auranku amman kuka ki, na rasa wannan dalilin tun abin baya damuna yanzu har ya zo ya fara tsaya min a zuciya.”
Ita dai duk fadan da yake yi ko a jikin ta tunda taji ya furta cewa zai sake siya mata sabuwar waya, ta gurin ta ce ta fada cikin toilet a can office d’in ta. Ganin yaci gaba da duba jaridarshi yasa ta mike zata fita yace ta turo masa mahaifiyarsu, ba tare da ta amsa ba ta nufi gurin Mamin su dan isar da sakon shi.
Zaune ta tarar da ita tana daura dankwali ta sanar sa ita kiran da Daddy yake yi mata, cikin turo baki kuma tace.
“Mami wallahi Daddy ya matsa mana akan Dije, yanzu fa ta kai ta kawo duk sanda zamu nemi wani abu ko zamu gaida shi sai yace wai Dije duk ta fimu, ni wallahi abin nan ya ishe ni, ta yi auran ma ba za’a barmu mu huta ba.”
Mami ta harareta ta cikin madubi cike da bacin rai, sannan ta wai go tana yi mata kallon ki shiga taitayin ki.
“Karya Daddyn ya yi ko me? Aikin banza aikin wofi kawai. Shekarun ku nawa a cikin kwaryar kano? Amman ku duba ku gani daga zuwan Dije har ta mallaki sarki, bafa dansa ba, a’a shi sarkin kansa ta aure. Ku kuwa babu abin da kuka yi sai daukar kwalliyar amman kun kasa janyo kwatankwacin sarkin da Dije ta aura. Ni wallahi da ina kamar ku, layi samari suke yi min, kuma ba wai kananun mutane ba, a’a manya masu ji da kansu a cikin Kasar nan. Ku kun zauna banda shegen baccin nan babu abin da kuka sani.”
“Kai Mami kema haka zaki ce?”
“Eh haka zance ko karya na yi? Burin ko wanne iyaye su ga sun kai yaran su mata gidan mazajen su, ko dama ace masu zuwa ne babu da sauki ba zamu takura muku ba. Toh a’a kawai gigin yarinta yana bin ku shine kuka ki tsayawa ku nemawa kanku abokanan rayuwa nagartattu.”
“Nifa Mami ina da wanda nake so. Kawai lokaci nake jira na kawo shi.”
“Dalla rufe min baki, wannan yaron zaki ce min zaki aura? Duk wani take-taken ki ina kallonki Shukrah. Ke ko kunya bakya ji ace tsohon saurayin Dije shi zaki aura? Abin haushin ma ba wai shi yace yana ra’ayin ki ba, ke kika nuna masa kudirinki. Toh wallahi ki shiga ki nemo hankali da tunaninki, wannan shirme duk bana san shi.”
Shukrah ta cakuna fuska saboda taga Mami ba ta yadda da zabin zuciyar ta ba, ita kuma harga Allah tun ran da ta dora idanunta akan fuskarsa taji duk duniya ba bu wanda ya kwanta mata sama da shi. Kuma har yanzu ta kasa janyo ra’ayin sa, ta yi duk iya yinta amman yace shi sam ba zai iya auran koda kawar Dije ba bare kuma yar uwarta. Sai dai duk da haka Shukrah taki yadda sai faman naci take yi masa yana share ta.
Dan Mami ta yi shiru kuma ta jewa da Daddy daddanan labari yasa Shukrah tattara komai ta ajiye gefe, tana murmushi kamar ya kai zuciya tace.
“Gobe zamu je gidan Dije, idan kuma har zuwa wannan lokacin bata nan, gaskiya ba zan sake zuwa ba sai dai idan ita tazo.”
“Wannan kuma ku ya dama bani ba.”
Cewar Mami tana fesa turaruka a jikinta, Shukrah dai ba ta sake cewa komai ba har ta fita sannan ita kuma tai saurin daukar wayar Mami ta sanya lambar Mas’oud, dai da tai ringing kusan biyar sannan ya daga cike da fargabar Allah yasa ba Shukrah bace, saboda har ya gaji da daukar kiranta, duk da tana yawan kiransa da layuka da yawa. Mas’oud na karawa a kunne tun basu yiwa juna sallama ba, ta fara roƙansa da magiya dan Allah karya kashe kada yaki sauraron ta, haka ya hakura yana jinta zuciyar sa na masa kuna dan ba karamin haushi take bashi ba.
“Wai me yasa baka jin tausayi na ne first love?”
“Ni ban fada ba.” Cewar Mas’oud.
“Ai daman ba fada ka yi ba, amman kuma duk sanda na kira ka sai naji baka farin ciki why?”
Ba tare da ya bata amsar tambayar ta ba, taji yana magana cikin sauri.
“Sorry Shukrah zan shiga studio yanzu, lokacin yin program d’ina ya yi.”
Ya katse tun kafin ma ta furta wata maganar. Tamkar ta hadiyi zuciya haka take ji a ranta, sai dai ta ajiye wayar tare da fadawa kan gadon Mami ta fara hawaye masu zafin gaske. Shin ya za tai da kaunar wannan bawan Allahn? Wa zata gayawa ya shawo mata kansa? “*Allah*”…. Taji wani sashe a zuciyar ta ya tunatar da ita hakan. Sai dai sam ba ta da juriyar yin addu’a, ita tafi gane komai ya zo mata shaf-shaf koda kowa ba nagartaccen bane. Ta dauki tsawon lokaci tana hawaye kafin daga bisani ta lallashi kanta tare da mikewa ta nufi dakin su.
*GIMBIYA KHADIJA.*
Ranar monday da rana ina zaune a parlorn kasa ina yanke farce na da ya dan taru, gefe guda kayan marmari ne a cikin wani kyakkyawan kwando an ajiye min da nufin idan ina bukatar ci. Giftawar wani abu na gani, nai saurin ware idanuwa ina neman abin abin banga komai ba, naci gaba da abin da nake yi still na sake ganin giftawarsa har yana kusan taba min kwayar ido na, na sake dubawa har karkashin kujera da bayanta banga komai ba, na yi auziya tare da ci gaba da gyaran farce na. Can kuma naji wata irin kara mai firgitarwa a cikin kunnuwa na, na yar da nail quarter d’in hannu na tare da toshe kunnen ina rintsa ido.
“A’ouzubillahi minasshaidanir rajim”
Kamar daukewar wuta haka naji shiru babu karar, nai saurin nashi tsaye naje na kunna karatun qur’ani mai girma da nufin ya bani kariya, bana bin kowa da sharri ko bita da kulli bare nai zaton ko ramuwa ake yi. Kalaman Gwaggo ta Fada suka fado min inda tace min, Khadija gidan sarauta sai da shiri, duk wanda kika ga ya zauna a ciki ya dade lafiya lau to be zauna guri guda ba, dole sai da neman kariya kota hanyar Allah ko bokaye ko kuma aljanu.
Komawa nai na zauna ina bin karatun tare da ci gaba da kankare farce na. Sallama naji daga kofar shigowa, na daga kai na kalli hanyar ina mai amsawa. Abin mamaki su Ya Shukrah ne, Sai wasu da alama kawayensu ne tunda ni dai ban san su ba. Kamar nai tsalle naje na rungume su dan murna, amman wata zuciyar ta kwabe ni cewar. ‘Kar ki rawar kai Dije, ki tuna cewa ke yanzu kin girma, ya kamata ki nuna musu cewa jiya ba yau bace.’ Fuskata dauke da murmushi tare da fara’a na kuma Mike tsaye suka karaso. Ya Hameeda (ni xoxo wlh na manta ainihin sunan ta, Kamar dai haka ne, Man kai na ya tsiyaye) da ta kasa jurewa saboda mamaki tace.
“Lallai har yanzu gigin auran sarkin nan yana kanki Dije.”
Maganar ta bata bata min rai ba, dan yanzu na gano cewa su kananun marasa mutunci ne, yanzu ina cikin gagaruman dan haka duk abin da zasu min ba zai dameni ba ko meye shi kuwa. Murmushi kawai na saki ina nuna musu gurin zama da hannu, suka ki zama sai kallo na da suke yi musamman wata yar dwalf dake ta kallon ciki na tamkar wacce ta hango wani abu a ciki, nai saurin komawa na zauna tare da dora kafa daya kan daya ina girgizawa.
“Dije wai kuwa kinji dadin zuwan mu? Bafa yau kadai muke zuwa masarautar nan ne man ki ba ace bakya nan, honeymoon kuka je ne keda shi?”
Na dan yi murmushi ina wasa da cover din wayar hannu na da na dauka, sannan nace mata.
“Ko daya Ya Hameeda, kawai wata yar tafiya na yi amman ai gashi yanzu kun zo mun hadu. Ku zauna mana sai mu gaisa.”
Suka jinjina kai sannan suka karasa kujerar duk suka zauna. Hadimai suka fara aikin nasu na kawo kayan motsa baki, ni kuma ina hakimce kai kace nice sarkin saboda yadda nake karkada kafafu…
_Afuwan lovelies.. A bini bashi😅🤲🏻Insha Allah next page zaiyi tsawo.. Masu comments, Ina godia sosai, Sakon ku yana isowa gare ni.. Kibiyar ajali… Zai cigaba da zuwa muku a hankali cikin nishadantarwa da fad’akarwa… Kaunar kauna❤️❤️_
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma’ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
GIPHY App Key not set. Please check settings