KIBIYAR AJALI 11-12

Advertisement

 I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p

PG: 11&12

BOOK 2. 

BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻

Advertisements

……Kallon yanayin parlorn suke yi da alama ya tafi da duk wani imani nasu saboda sun kasa sauke idanunsu daga dubawa. Ni kuma sai murmushi nake yi nasan ko babu komai zasu gane cewa maraici ko talauci basu hana d’an adam yin arziki, inda ma aka samu matsalar zuciya ta Sam ta kasa amsar Salman a matsayin miji na. 

”Ina kuma mai gidan naki..?”

Cewar Ya shukrah tana mai ci gaba da karewa gidan kallo.

Na shiga jujjuya amsar da zan basu, Don ni rabon da na sashi a idanu na tun rannan dana same su shida Shaheedah a bedroom d’in sa, Ni kunyar sama na keji wani lokacin saboda kar ya dauka har zuci nake wannan acting din. 

 “Suna meeting ne.. Shi da yan majalisar sarki.”

Tabe baki Ya Hameeda tayi tana mai kallon kayan kwalam da makulashen gaban su. Ni kam na shiga tambayar su Kawu Daddy da Mami..

Advertisements

 “Sunanan qalau.. Amman Dije yaushe kika dawo nan sashen? Kamar da ba nan muka kawo ƙiba ko.?”

“Eh Ya Shukrah! Daga baya na dawo nan d’in..”

“Ina kuma kishiyar ki…..? Ita anan saman take kenan, Ke a kasa?”

Sai da nai murmushi tare da sauke kafata na kalleta sosai yadda zata fahimci bayanin da zan jefa mata sannan nace.

“A’a ai ba zai yu a had’a mu haka ba, kinsan gidan sarauta ba kamar sauran gidajen mutane bane da za’a iya ajiye mata biyu a part d’aya, dole ko wacce da nata bangaran.”

“Yanzu dai kina nufin nan duk naki ne?” Cewar Ya Hameedah tana son jin tabbaci.

“Eh nawa ne.”

Na bata amsa a takaice ba tare da na kuma yin dogon bayani ba, dan na lura har yanzu mamaki suke yi.

“Amman dai kafin mu tafi zaki had’a mu da shi angon mu gaisa, ni ban taba ganin inda ango be san ainahin yan uwan matarsa ba sai yanzu. Ya dai kamata mu ganshi, dan yasan mu muma mu san shi ko Hameedah?”

“Kwarai ma kuwa sissy, wai duk tsahon lokacin nan bai taba zuwa gida ya gaishe da Daddy ba bare kuma Mami, ke kuma tunda kika samu duniya shikenan ba ruwanki da neman mutane.”

Ganin suna shirin gaya min magana a gaban kawayensu da ban san ina maganar zata iya kaiwa ba yasa ni saurin nemo amsar da zan basu cewar.

“Kai ai shi ba ya san hayani, baki ga ko da ina gida be taba zuwa tadi ba? Shifa sam baya san surutu, ni kai na duk surutu na idan ina gabansa hadiyewa nake. Shima Daddy ya sani dan a bakinsa na fara jin cewar sarki Salman baya san magana da hayani.”

Suka kalli juna cikin zaro ido tare da rike baki alamar mamaki, ni kuma na gaya musu iya gaskiya ta d’an kara suyi zaton irin mazan nan ne masu yawan surutu ko shisshigewa yan uwan mata.

“Ke nan muma yanzu ba zamu samu damar ganin shi ba?”

“Gaskiya dai, tunda kunga yanzu yana meeting ban san ma lokacin fitowarsa ba. Babbar matsalar ma ba nice dashi ba Shaheedah ce, idan taga ina zarya gurin shi sai tai zaton wani abu. Amman kuyi hakuri duk sanda kuka dawo zan yi kokarin hada ku dashi sai ku gaisa.”

“A’a a’a kedai kawai kice boye mana shi kike yi, lallai Dije abin naki dada shahara yake yi amman ba komai.”

Ya Hameedah ta fada tana janyo bowl d’in pepper soup d’in cow leg, daga nan suma sauran suka fara dibar abinda zasu ci. Wayar telephone dake can gefe ita tai ringing, ba kowa bane face Salman dan shi kadai ne yake kira a cikin ta idan yana nema na urgent. Cikin rawar jiki hadima ta dake kusa da gurin ta dakko ta kacokam ta kawo min, na karba sai dai ban daga ba saboda jan aji, ta katse ya sake kira, still ban daga ba sai da ya sake kira karo na uku sannan nai picking na kara jikin kunne na.

“Please..I need your help.”

Cike da takama kamar ina gabansa nace mai.

“Yaushe fa.?” 

Yace.

“Yanzu please.”

“Ina da baki ne, sisters dina sun zo. K…”

“Na ce yanzu.”

Ya fada cike da nuna iko, karo na farko kenan da ya nuna min ikon sa a kai na. Ya kuma katse nai murmushi dan kar su yi tunanin wani abu na hada da cewa.

“As you wish.”

“Ya fito daga meeting d’in kenan?” 

Ya Shukrah ta tambaye ni cikin zakuwa, ashe duk kunnuwan su yana kai na oho ni Dije.

“A’a bashi bane ba.” 

Na samu kai na da shirga musu karya, nan san me yasa ba haka kurum bana son su hadu dashi yanzu, kodan nasan har yanzu ni kai na ban san matsayina a gurin sa ba.

“Ku gama ci bari naje na dawo.”

Na fada tare da tashi na shiga daki. Sake gyara fuskata nayi na kuma dauki mayafi na yafa sannan na fito na bi ta d’an wani corridor yadda ba zasu gane nayi wani gurin ba, cas na fada sashen Salman ina ta mamakin wannan kiran nasa da ya yi min.

Kamar yadda nayi tsammani hakan ne ya kasance, wato sashen nasa shiru sai fadawa dake aikin gadin ko wane sashe na part d’in. Duk inda na gitta sai sun gaishe ni har na karasa bedroom d’in sa, wani irin kauri naji wanda yasa ni kwarewa babu shiri, nasa hannu na toshe hanci na ina kalle-kalle dan son hango inda yake.

Bathroom naji an bude, nai saurin kallon gurin naga shine ya fito, sai dai ya rufe duka fuskarsa da towel d’in wanka alamar shima mafita yake nema.

“Yar jarida…”

Nija ya fada a hankali, ban san lokacin da na harare shi ba.

“Sunan da nake dashi a gurinka kenan? Tukunna ma wannan kaurin kuma fa daga ina?”

“Kina ina please.?”

“Gani nan.”

“Toh d’an matso.”

Kamar wata sokuwa haka na matsa kusa dashi, yasa hannu ya lalibo ni bayan ya gama yawo da hannunsa a jikina.

“Kinji warin nan ko? Toh nima haka naji shi har ya sani amai. Dan Allah ki taimaka kisan yadda zaki sa na dena jinsa.”

Haushi ya kamani, me yake nufi to da zai ce na kawar masa da wannan fitinannan kaurin bayani ni kai na ban san ta ina yake biyowa ba. Ko yana tunanin nice na saka masa har ya yanke shawarar kirana dan na gyara?

“Nima fa ban san daga ina yake fitowa ba, dama na sani ne da sauki.”

“Please yar jarida bazan iya zama a cikin dakin ba.”

“Ikon Allah, wai laifi na ne?”

“I dunno, ni dai ki taimaka min bana son warin.”

“Shikenan to sakar ni naga me zan iya yi.”

Babu musu ya sake ni nasa mayafi na nima na toshe hanci ina ta karanto adduoi . Na dinga dube dube amman banga komai ba, na kalleshi yana tsaye yaki bude fuskar kamar wani karamin yaro. Cikin sauke numfashi na mike tsaye ina cewa.

“Toh waye ya shigo cikin dakin? Ni dai na duba banga komai ba wallahi da yake sa wannan kaurin.”

“Kowa be shigo ba, oh su..matan baba sun zo duba ni dazu.”

“Mata? Wane irin mata kuma?!”

Yayi shiru tsawon lokaci sannan ya ce.

“Mama Huwaila.”

Na tabe baki a hankali naje na dakko turaran kamshi na jona burner na zuba, nan da nan kamshi ya gauraye dakin, na karasa kusa dashi tare da jan hannunsa na kai shi kan kujerar da yake hutawa ya zauna sannan na warware masa towel d’in na ajiye a gefensa.

“Kana jin warin har yanzu?” Ya daga min kai alamar eh.

“But kadan-kadan ne.” Ya fada yana satar kallo na.

“Okay karka damu zai dena gabaki d’aya insha Allahu. Bari na koma sister’s dina ne suka zo.”

Kamar zai hana ni sai kuma ya jin gina bayan sa jikin kujerar tare da lumshe idanunsa be ce min uffan ba. Ni kuwa na juya na tafi dan kar su yi zaton wani abun bare suje su gayawa Mami cewar nai musu rashin mutunci. Koda na koma bangan su a parlorn ba, ina shirin tambaya na jiyo muryarsu a sama suna ta shewa, mamaki ya kamani. Sai na bisu har ina hardewa, na hange su a wani bedroom suka kalle ni cikin rashin damuwa Ya Hameedah tace.

“Zazzagawa muke muga yanayin gidan.”

“Ah lallai Dije duniya sabuwa irin wannan daula haka? Kinga bathroom d’in nan? Wallahi tuna min ya yi farkon zuwan ki gidan mu kika kasa shiga bathtub, amman yau gashi ke ce mai wannan dankareran jakuzzi d’in.”

Ya Shukrah ta fada cikin shakiyan ci, duk sai na kasa magana ganin yadda suke ta dariya harda kawayen su. Nai murmushi tare da karasawa na bude wata wardrobe na ciro wasu laces da material ina cewa.

“Kunga wasu kaya ina ta so randa zanje gida na tafi muku da shi sai gashi kunzo. Idan zaku tafi sai a sa a mota.”

Ganin irin dankara-dankaran laces d’in yasa suka kasa rejecting, hannu biyu-biyu suka karba, sai dai Ya Hameedah sai da tace.

“Wai yau Dije ce da yi mana kyautar bajin ta. Aure mai dadi mu ma dai Allah ya kai mu lokacin namu muji yadda ake ji.”

Duk suka yi dariya tare da tafawa, ni kam na kagu su tafi musamman da naga suma kawayen sun fara yi min abinda suka ga su Shukrah nai min. Allah ya taimake ni suka sakko tare da shirin tafiya, bayan ko wacce ta dauki abin da take so a gidan, ban yi magana ba ni dai buri na kawai su kara gaba, naji dadin ganinsu dan a kalla nasan mutane zasu san nima ina da dangi. Har wajan gate din sashe na nai musu rakiya suka tafi suna ta magana da ban san ko ta menene ba, kai tsaye na shiga toilet nai alwala.

*<<<<<>>>>>>>>*

Sallama dauke cikin siririyar murya ta na shiga bedroom d’in nasa, Salman tsaye wajan mirror ya gama shirinsa na fita fada zai gana da wasu ƴan majalisar jiha. Ban ko kalle shi ba na wuce zuwa inda ake ajiye masa tray din coffee ko tea ko dai wani abin da yake so.

Ya juyo yana kallo na wanda na gane hakan ne a jiki na, sai dai bai ce min komai ba nima kuma ban juya ba sai kokarin had’a masa coffee d’in da nake yi. Cikin rai na haushi ne cacim saboda rashin kulawarsa gare ni tana bata min rai duk da ba wai ina bukatar ta bane. Har na kammala hadawa na rufe ban juyo ba duk da cewar babu abin da nake yi a wajan, naji ya tako a hankali ya tsaya a baya na yana bin kai na da kallo.

Dan kwalin naji ya cire nai saurin mikewa tsaye babu shiri, ido waje kuna na kalle shi dan tsananin mamakin shi. Da kyar na daura d’an kwalin kasan cewar na lace ne kuma yana da nauyi, amman shine saboda ya lalata min ya kama ya cire min ba tare da sani na ba. Yadda yaga ina kallonsa ne ya tabbatar masa da cewa rai na ya baci, amman ko a jikinsa dan bai nuna ba a fuskarsa, cikin yatsina fuska nace.

“Ya haka? Kasan da yadda na daura shi?”

Bai ce komai ba sai kallo na da yake yi, cikin jin haushin dark shades d’in idanunsa masu kallon mutane ba tare da sun sani ba, nima nasa hannu na ciro shi ina tsuke baki.

“Ni ma na rama.”

Na fada cikin gaskiya ta. Maimakon ya kalle ni a’a sai kawai ya lumshe idon sa da haka ya miko hannusa tare da kamo kafaduna ya rike, ban yi aune ba kuwa naji ya sanya ni cikin faffadan kirjinsa, tare da dora habarsa a kai na. Ware ido nayi ina jiran jin abinda zai wakana, sai kuma naji tattausar muryarshi a cikin kunne na yana cewa.

“Baki iya gaisuwa ba?”

“Oh ai ban san da mutum a ciki ba, dan nayi sallama amman ba’a amsa min ba.”

Ya sake sanya bakinsa cikin kunne na ta yadda na dinga jiyo numfashinsa wanda ke sa tsigar jikina tashi. Nai saurin kawar da kai na, ai kuwa muka hada fuska dashi a lokacin ne kuma ya bude idonsa muka hadu da na juna kowannen mu da abin da yake sakawa a cikin ransa. Bashi da niyar yin magana hakan ya bani kwarin guiwar fincike jikina zan matsa Salman ya yi saurin janyo ni, naki waigawa saboda abin nan nashi ya ishe ni, sai dai yai ta yin shiru kamar wani kurma, yana ji kana magana amman yaki kulawa. Rai na a bace na fara magana dan ni dai gaskiya ba zan ci gaba da jure wannan wulakancin nasa ba.

“Wai kai dan Allah a haka kake yin mulkin naka cikin shiru da rashin yin magana? Ta ya kake sauraran talakawan dake karkashinka bare har ka tallafa musu a inda suka kawo kukan su? Wannan shirun naka yana yin yawa gaskiya, gashi nan har ta kawo baka kula mahaifiyar ka. Ammi  tana t…..”

Ammi da na furta shine ya sanya shi saurin fisgoni ba tare da na karasa maganar tawa ba. Ya yi min wani irin kallo wanda na kasa gane ko na menene. Shin na tsana ne ko gargadi ko kuma mamaki? Ban sani ba ni dai, zafin rike min gashi da ya yi yasa ni cewa.

“Ni ka sakar min kai na, dan sauran kiris ka dena gani na a cikin sashen nan naka, bana son yin taraiya da wanda yasan mahaifiyarsa na da rai amman be damu da rayuwarta ba, bai san ina take ba bare yasan ya ta kwana ta tashi tsahon lokaci kuma a gida d’aya. Shi yasa lokaci nake jira wanda zaka sallama min naje nai rayuwata yacce naga dama, ba da kai ba da ban san dali…..”

Ban karasa ba naji muryarsa cikin tsawa tare da sake matse min gashin yana kuma dago fuskata.

“Ya isa! Ya isa haka please.”

“Toh naji sakar min kai na nima.”

“Ki min shiru na ce.”

“Ashh… Wayyo Allah kai na zai cire min gashi.”

“kin rai na ni ne?” 

Ina faman matse ido saboda zafin rikon da ya yi min nace. 

“Ban gane ba.”

“Kince kin dena zuwa nan ko?”

“Eh na fada fa, amman cewa nai idan baka gyara mu’amalarka da Ammie ba.”

Ya yi saurin sakar min gashi tare da dafe kanshi ya sunkuya zuwa kasa yana furta

“Kai na… Kai na zai…zai ci…..”

Hankali na yai mugun tashi ganin yadda lokaci guda ya birki ce min, ban san sanda na durkusa a wajan shi ba ina bashi hakuri a gigice dan nasan koma menene ni ce sanadi, na fahimci indai zan ambaci sunan Ammie toh dole yana shiga cikin wani yanayi da shi kansa be san yana shigarsa ba. Kofar da naji an kwankwasa ne ya kuma tayar min da hankali, kafin nai wani motsi an bude an shigo ciki.

Jakadiya ce kanta a kasa kamar tsohuwar munafuka, nai saurin kallon ta ido waje. Ganin yadda take kallon Salman yasa ni nace.

“Daman kina da damar shigowa nan Jakadiya?” 

Cikin sauri tace.

“A’a wallahi ranki ya dade, ina parlor ina jiran na yiwa Gimbiya Jaleela iso ne sai naji kamar kin kira ni.”

“OH kinsan ina ciki kenan?”

“Wallahi tallahi ban sani ba ranki ya dade, dogari ne ya sanar dani.”

“Okay please bashi da lafiya ba zai iya ganin kowa ba a halin yanzu.”

“An gama ranki ya dade Allah ya ja kwananki.”

Ta fada tana mai bita da baya da baya cike da son ganin gulma. A rai na nace zan yi maganin ki babbar kawai.

*SAS*

Tsaye yake a jikin window din dakin sa, Sanye cikin bathrobe, Da alama wankan bacci yayo. Agogon dake saqale a jikin wallpaper ya kalla, Sha biyu saura kwata, Yanzu ne lokacin da Khadijaa ke fitowa daga wanka itama, Dama sashen sa yana kallon nata. Kuma curtains din dakin da take kwana a saman irin shara-shara dinnan ne, Yana hango ta idan tana shiryawa. Kansa ya dafe da hannu d’aya. Saboda tsananin yadda yake sara masa, Gashi bayaso ko da second d’aya ya kauracewa kallon ta. Tun sanda tazo yana tare da shaheeda dinnan bata sake komawa ba. 

 “Gani kike ko bana sonki ko?……Lokaci zai bayyana komai.”

A hankali ya fada yana mai zama akan kujerar dake kallon setin windon ta. Cikin haka kuwa sai ga Khadija tafito, Itama da rigar wanka, Ta wanke yalwataccen dogon gashinta baki sidik, A hankali ta shjga saka comb tana taje shi,  Salman ya jinginar da kansa a jikin kujera yana lumshe idanu.. Lokaci kawai yake jira ya bayyana mata zuciar sa. 

Tashi yai da sauri yana zura kansa ta window tamkar zai fada ganin tana kokarin sab’ule hannun ta d’aya na rigar wankan jikin ta. Abun karo ganin abu ya sanya a idanun sa yana kara zooming dinta. Tamkar ta gane ana kallon ta. Ta maida hannun rigar ta mike tsaye ta fice..

Cizon yatsan sa yayi ya koma je gaban closet dinsa ya ciro kayan bacci ya saka, Turaruka masu sanyin kamshi ya fesa a jikin sa, A hankali ya sauka kasan sashen sa. Wani da’ki ya shiga acan karshen kurya wanda ba zaka taba cewa daki bane, Dubada wajen anyi shine kamar ma’ajiyar littattafai.. Hannun sa ya dora akan wani waje ma’ajiyar littattafan ta bude Shi kuma ya shiga ciki.. Ba zaka taba cewa ba wajen aikin computers bane. Gaba d’aya conputoci (computers) ne kala kala awajen. Kowacce tana nuna reshe da reshe na masarautar baki d’aya… Idan ka cire sashen Ammi. 

Zama yai akan kujera ya shiga duba wata computer dake gaban sa bayan yasa medicated spectacles a idanun sa. Tamkar ba Salmaan ba haka ya dawo, Nazari yake sosai da takardar gaban sa. Ya dakko waya a gefe ya kira falaki..

 “Ka gama shirya min komai….? Yess! Yes! Jibi da sassafe zan tafi. Ka tabbatar jirgin nan an gama cajeshi ba matsala… Kasan mutanen ka ba’abin yarjewa bane…..”

Kit ya katse wayar ya ajiye a gefe… Photo album din gaban sa ya dakko ya shiga dubawa yana nazarin sa sosai…Ahankali tamkar mai ciwon baki yace,

 “Khaleel….. Da Abdullah..”

Dai dai lokacin da ya d’aga kansa kenan ya dubi wata computer me nuna hotunan mutanen dake wucewa ta kofar ‘kyaure… Abdullah ya gani. Wanda ko dena gani yai ya dawo aka nuna mai shi zai gane shi. Tamkar zai cikin computer haka ya zura kansa yana kallon sa, Shi kuma Abdullah waya yake dannawa da alama chatting yake. Haka Salman yaita kallon sa har ya tafi….

Wayar sa ya dauka sai kuma ya ajiye yana rike goshin sa. Meya tuna oho sai kuma ya rufe wajen ya gyara koina ya haye saman sa hankalin sa a kwance.

Dakin sa ya shiga, Ya fara yo alwala.. Ya yiyyi sallar nafila kafin ya koma kan gado ya kwanta. Ruwan roba ya ciro a mini fridge din dake gefen gadon sa, Ya shiga sha a hankali yana runtse idanu hade da girgiza kai…

“Ammi…. Ammi….! Tabbas a yanzu na gama gano wacece Ammi .. Ammie nahhh! Ammi kiyi hak’uri, Ammi ki yafe min… Yanzu kam Khadija ta tuno min wacece ke agare ni, A baya na kan tuna ki, amman…Mintina kalilan kuma tamkar an goge ki acikin zucia ta.. Amma Insha Allahu! Nan da lokaci kalilan komai zai warware kansa. Akwai abubuwan da nake son na gama bincike akan su Ammi….. Dana gama zan zo gare ki cikin aminci… Khal and Abdullah.. I love and miss you too.”

Hawayen da suka gangaro masa ya goge… Ahankali ya janyo farar wayar kusa dashi, Ya kunna. Hotan Ammi ya bayyana akan screen din wayar, Gallery ya shiga yana mai dudduba hotunan ciki, Shi ne da su Khal kafin a wargaza musu rayuwa. Girgiza kai yayi ya kashe wayar ya maidata ma’ajiyar ta ya boye, Ya dakko wata yar takarda yayi rubuce rubucen sa aciki ya ajiye, Wanda koda nan gaba ya manta komai daya karanta zai iya tuna wasu abubuwan. 

Tamkar ya tashi ya tafi wajen Ammi haka yake ji, Amma bayason ya bayyana komai sai ya gama shirin sa a nutse, Ya gano komai tukun sannan.. A hankali ya maida kallon sa window din Khadija.. Ya sauke gauruwar ajiyar zuciya.. Shi da matar sa amma ba shida damar bayyana mata komai sai nan gaba kadan. Da tunane tunanen tafiyar da zai yi jibi bacci daddada yai awun gaba dashi…..!

      *DURBUN………*

Zaune Gajiyalle take ta kara manyanta amma kamanninta nada suna nan, Tayi yarkace yarkace Da daurin zani tana tankade tsakin kuka.. Ladiyo matar Mudikalle tafito hannun ta rike da wani yaro hancin sa dagaje dagaje da majina,

 “Gajiyalle… Wai kina nufin baki ma daura sanwar rana ba?”

“Haba Ladiyo… Yar aikin kice ni da zaki tsayamin kerere aka kamar wata bishiya? Kizo ki dafa mana ke.”

 “A hayye nanaye! Ni ladiyo nai abinci? Tabdi jan, Yasin bazan ba, Banda naci da kulafici dole sekin zauna tare damu? Ki je ki kama daki mana ki zaman kanki.”

Gajiyalle zatai magana kenan, Mudikalle ya shigo hannun sa rike da leda baka sai busa hayakin taba yake.

“Kai.. Wai wane dan kut.. kai wane dan haka kaza ta ubanne acikin ku ya fara taro match? Sai hayaniya kuke haba.”

 “Dan guzumar ubanka ni Gajiyalle kake gayawa haka? Mudi ka shiga taitayin ka fa.”

Ashar ya lailayo ya dura yana banka mata harara,

 “Ke kuma ungo naman tsiren bakin kasuwa ne, Kici keda Halipha.”

Ladiyo zata k’arba Gajiyalle ta wafce tana dire tsallan albarka,

 “Na hada ka da ita da shi na nanawa ubanka dan uban ka tsiren bakin kasuwar zaka bata ta cinye da shege? Wohoho lalle Mudi ka manta alkhairi.”

Ladiyo ta sheke da dariya tana tafa hannaye,

 “Baa shege d’aya sai biyu, Banda abinki Gajiyalle waye baisan me kika aikata a karkarar nan ba? In shegen na haife ina uban sa daya sa akai cikin shi na aura?”Ladiyo ta karasa tana mai jan dogon tsaki, Hade da wafce ledar tsiren hannun Gajiyalle, Ta sunkuci halipha suka shiga ciki

Mudikalle yaja dogon tsaki yana mai hararar Gajiyalle, Jan wajen kwata ya matsa ya fyace hancin sa, Ya goge da hannun rigar sa yana kwakular cikin hancin haka ya fuce yana waka. Gajiyalle tai zaman dirshen a kasan kyauren dakin ta, Magana take tana mai daga rariyar tankaden kukan da take sama,

 “Wai ni Ladiyo ke gayawa magana? Ada sanda nake da kajina, Da dabbobi na da zabi na ba uban dake yadamun magana, Wai yau Ladiyo yar Uwannaniya me yakuwa ce ke gasamin magana? Guzumar uban can kayya kai… Auren nan ba inda zashi tunda na rariya ne, Idan asiri ne a tafe na kwan muje zuwa Ladiyo daga ke har Uwannanniya sai naga bayan ku. Sai dai kuwa jarin yakuwar taki ya kare. Bankadaddu!”

Cikin haka Ladiyo tafito tayi shegen dauri fuskar nan tasha dige digen jambaki daka ganta kaga tsohuwar yar tasha.. 

 “A hayye nama dadi.. Tsiren bakin kasuwa yasin duniya ne. Kai mijina Allah dai ya kara arziki na jiya da daddare yayi dadi amman na yau kam ba’a magana…”

Tagama ta wulla takardar waje ta kurkure bakinta tana sakin wata shegiyar gyatsa,

 “A gama tuwon kuma mu kora dashiiiii..”

Daki ta shige tana mai cigaba da wak’ar ta. 

Tsabar bakin ciki Gajiyalle batasan ta zubar da rabin kukar a kasa ba. Sai da Ladiyo ta shige sannan ta lura..

Kadan kenan daga rayuwar Gajiyalle a kauyen Durbun…..

..Kaunar k’auna masoyan zafafa 5❤️❤️

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 22

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR AJALI…..!_…

KIBIYAR AJALI 21

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR…

KIBIYAR AJALI 10

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 10…

KIBIYAR AJALI 32

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…