KIBIYAR AJALI 14-15

Advertisement

 _INA MA’ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA? WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA? TO KU MATSO KUSA… DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._

_LITTAFIN *UNCLE NE…* LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE.._

_”Wait… Dakata hafsat Rano, Kina nufin NIMCYLUV, dai shararriyar murubuciyar nan itace tazo da wani salon rubutun..?..”_

_”Kede bari Billyn Abdul.. Tsaya kiji kanun labarin a tak’aice..*NIMCYLUV* Tace book din a ta’kaice labarin *UNCLE NE* ne yana tafe:_

Advertisements

_Da farko yana mata kallon uwa wacce ta haife shi kuma jigon rayuwarsa, ashe itace silar rushewar rayuwarsa😢yarinyar da yakewa kallon ƙanwa uwa ɗaya Uba ɗaya ita aka wayi gari ta zama MATAR SA🙆🏻‍♀️ ƙaddara ta haɗashi da (Ahlil kitab) kiristan ya bata farin ciki, kulawa, soyayya, harya samu ta musulunta, Dalilinta sbd al’ƙawarin aure da yyi mata,ashe ba sonta yake ba🤔yaje birnin NUFAR domin kai masu tayin Muslunci, sun amince da hakan amma sharaɗin dole ya kwanta da ƴarsu,🤦🏼‍♀️gashi bashi da cikakkiyar lfy mazantakarsa bata aiki😫 ashe mahaukaciya ce ta haife shi.._

“_Kai lalle akwai runguntsumi acikin wannan littafi..  Ba za’ayi babu ni ba, Domin Za’a sha lagwadar romon dadi. shin tayaya ake biya Hansatu?_”

_”Ai ta Abdul..LITTAFIN *UNCLE NE* Naira 300 ne, Idan kuma kana son vip inda za’a ake posting sau biyu a rana kuma za’a baku littafan data rubuta na kuɗi sai ka bada 600 mai ma kon 1k.. number asusu wato bank account details: 0116886423 : account name sulaiman Na’ima S. Bank name: unioun bank: Sai a tura shedar biya ta 08119237616… A nuna mata ƙauna ta hanyar turowa ta account🤲🏻kamar yadda Za’a  faranta maku a littafin UNCLE NE_

_(Best romantic love story of the year//Had’adden labarin kauna na shekarar 2021)_

PG: 14/15

….Ya janyoni sosai tare da kokarin dorani saman cinyarsa, nayi saurin tak’irewa alamar ba zan hau ba. Kuma janyo ni ya yi na fada jikinsa yasa duka hannuwansa ya rungume ni kamar na ce masa guduwa zanyi. Ya yi luf a jikina, kirjina ya dinga bugawa saboda tsoran kar ya yi min wani abun da ban shirya karbarsa ba daga gare shi.

“Ni dai gaskiya ka cika ni zan tsaya na saurareka sosai.”

Advertisements

“Nan zaki zauna saboda gurin zaman ki ne.”

“Wa? ni na isa, wannan gurin na madam gimbiya Shaheedah ne. Ni kam ai yafi karfi na alhaji.”

Ya yi shiru be ce komai ba, haka ya sake tabbatar min da cewa lallai gurin na Shaheedah ne tunda gashi be musa ba. Na tab’e baki tare da yunkurin sake tashi amman ya rike ni ya hanani ko da kwakkwaran motsi. Sai da ya mulu ya mulmule sannan yaja numfashi yace.

“Ina son na baki amanar kai na da rayuwa ta khadija, na yadda da kwarewar aikin ki shi yasa zan nuna miki sirrin rayuwa ta a yau dan ki taya ni kula da ni kai na da duk wani wanda ya shafe ni.”

Yana kaiwa nan gurin yai shiru, ni kuma na kagu naji abin da yake son sanar dani amman ya tsaya sai ja min rai yake yi. Jin shirun ya yi yawa ne yasa ni cewa.

“Uhmmm ina jinka.”

“Ai baki daukar min alkawarin ba, baki amsa min cewar zaki rike min ba ko a’a ba zaki rike ba.”

Wannan karan ni ce nai shiru saboda tunanin abinda ke zuciya ta. Ta ya ya zan yadda na daukar masa alk’awarin da ban san ko na menene ba, ni da ba zama nazo yi gidan shi ba? amman zan iya karba ai tunda amana sai ranta ka ci ta sannan ne ka sab’a. Zan karb’a idan yaso ko nan gaba bamu tare zan yi kokarin rike masa duk wani sirrin sa. Naja numfashi tare da cewa.

“Na amince zan karba, kuma ni ma nan gaba ina son kayi min wata alfarma.”

Sai da ya dan matsa yatsu na sannan yace.

“Ba damuwa.”

“Ina sauraronka menene kake son bani amanarsa?”

Salman ya daga mu a tare muka tashi tsaye ya kama hannu na muka doshi wajan wasu littattafai. Wani guri kawai naga ya bude sai ga abu kamar keypad ya danna kawai sai gurin littattafan nan ya fara budewa a hankali, sai wata kofa ta bayyana muka karasa wajan ya murda handle din muka shiga yana rike da hannu na. A rai na mamaki nake yi, sak irin boyayyar ma’ajiyar nan irin ta turawa da nake gani a films. Na ware ido lokacin da naga jerin computers, mamaki ya kamani nai saurin kallon Salman din dan jin karin bayani.

Mamaki yake bani idan naga yana abu cikin sanyin jiki tamkar wata mace, ya fara kokarin cire min hijabi na ki yadda, sai ya samu guri ya zauna ba yana bude wani file yace.

“Idan kin shirya na nuna miki.”

“A shirye nake wallahi.”

“Toh ni bana son aikin da hijabi a jikin ki.”

Na zaro ido cike da mamakin jin abin da ya fada, shi kuma ko a jikinsa bama ni yake kallo ba, ga dare nayi haushi kamar ya kashe ni haka na cire hijabi din ina karawa a jikina nace.

“Toh ka gaya min ko mene gashi na cire, ni ban taba ganin aikin da za a ce ba a yi da hijabi ba”

“Harda wanka?”

Yai maganar tamkar ba daga bakinsa ta fito ba. ni kam dai yau naga ikon Allah wajan Salman, ai kuwa ban sake yin magana ba har ya waigo ya kalle ni tare da tasowa yazo gabana ya tsaya. kwace hijab din ya yi tare da cilla shi gefe nai saurin saka hannuwa na ina kare jiki na saboda yar karamar riga ce, gashi ta fito da albarkatun kirjina (Fitilu biyu inji jerry Aneesa didi😂).

Murmushi ya saki tare da kawar da kai yaja hannuna muka nufi wajan computers din, ya kunna wani waje gabaki daya suka kawo haske, zaunar dani ya yi akan kujerar da take tsakiya. Sai ya yi min runfa da jikinsa, ma’ana ya rankwafo ta bayana yana danna keyboard cikin nutsuwa. Ni kam fuska na cakune dan naga sai wani shige min yake yi, ga shi idan kwantaccen sajen sa ya gogi wuya na sai naji jini na yana yawo, amman na dake dan karma ya yi tunanin dad’i nake ji.

Gabaki daya masarautar ta bayyana a ciki, sashe-sashen dake cikin ta suka fito cikin ko wanne screen. Harda sashen Ammi sashen gimbiya Shaheedah da nawa da duk wani guri dake cikin masarautar Bassannabas. Gashi nan kowa yana harkarsa ashe yana ganin komai da yake faruwa a kowanne sashe duk da naga ba a ganin wasu gurin kamar bedroom da toilet, amman ana ganin nawa da na Shaheedah. Ji nai ya hura min iskar bakinsa cikin kunne na, da sauri na rintsa idanuwa, yaci gaba da magana cikin wata irin murya wacce tamkar yana jin bacci.

“Wannan gurin babu wanda yasan ina dashi a cikin masarautar nan sai wadanda suka yi ginin shima kuma a boye akai, sannan sai Falaki da Alhassan sai kuma ni yanzu kuma kin shigo cikin wadanda suka san da gurin nan.”

Yaja numfashi ni kam idanuna suna kan sashen Gimbiya Shaheedah wace ke hakimce a parlour bayin ta sun zagaye ta daga mai yi mata tausar kafa sai mai matsa mata kafad’u sai masu fifita da wace take rike da basket din kayan marmari. Mulki kawai take zubawa saboda an tsotsa har an rasa ina za a sanya izzar mulkin. na kuma maida hankali na sashen da su Galadima suke tsaye jikin wani gini da alama wata maganar suke yi mai mahimmanci a gare su.

“Na yarda dake a dan zaman da nayi kina tare dani, duk da nasan kin tsaneni. Zanyi wata yar tafiya ne ina son kisa min ido akan masarautar nan, ina ji a jiki na kamar masu min zagon kasa sun mamaye ni. Khadija ki min alkawarin zaki rike sirri na ba tare da kin gayawa kowa ba, nai miki alkawarin idan nai tafiyar na dawo zan bayyana miki abin da baki sani ba, zai saki farin ciki ki manta duk wani abu da ya shud’e kinji?”

Yai maganar tare da kai min sumbata a gefen wuyana. Na kasa cewa komai sai wani irin fitsari ma da yake neman takura min saboda kusancin mu yayi yawa, duk ya nanike min kamar wani mage.

Haka Salman ya zauna kusa da ni ya dinga koya min yadda ake controlling cctv din da yadda ake recording da komai, mune har Kusan karfe hudun dare Salman yana ta nuna min abubuwa dangane da sirrinsa. Allah sarki gaskiya yana da mugun kawaici, Cikin rai na ban san lokacin da na dinga zuba masa addu’o’i kala-kala ba. Sai da ya tabbatar na gane yadda suke gashi daman nasan wani abun saboda yanayin aiki na, sannan ya tashi yaje ya dakko min hijabi na yasa min tare da kashe abubuwan. wata kyakkyawar kofa ya bude, abinda ya daure min kai shine ganin mu a cikin tsakiyar bedroom dina wanda nake bacci a cikinsa. na kalli gurin wanda duk a tunanina decoration ne ashe wai kofa ce a gurin, cikin rai na nace ‘Shege bature’ yasan takan tsiya kala-kala.

“Ga hanya nan, Sai da safe, sai ki kula da mutane karsu gane ta. idan zaki shiga ba sai kin bi ta apartment dina ba kai tsaye kawai ki shiga ta nan. Good night yar jarida, sai na dawo ki kula min da komai.”

Yana kaiwa nan ya juya ya tafi, ni kuma na karasa wajan ina tab’a hanyar da tai matukar daure min kai. Komawa nayi tare da hayewa kan gado, sai kuma nayi saurin tashi ina kalle-kalle ina son ganin a ina aka kafe min cctv camera amman ban gani ba, haka na gaji na barshi na dawo tunanin ta yadda zan fara yi masa aikin nan ba tare da kowa ya san da zaman gurin ba bare har na karya alkawari ba.

*SOUTH KOREA*

(GANGNAM HOSPITAL)

Adaidai asibitin motar da aka dakko Salman daga airport ta tsaya. Falaki ya fito ya bude masa murfin motar, Sanye Salman yake cikin kananun kaya samfarin riga da wando yan kanti. Kansa yasa pcap. Yayi kyau sosai, Idanunsa saqale da spectacles dinsa na gado mai dauke da tambarin givenchy, Tafiya yake cikin kasaita, Daga shi sai Falaki. Sunyi ‘badda kama ba zaka taba cewa sarki bane da matemakin sa.

*consultant Ibrahim (Khal) AS*

Dai dai kofar shiga dakin suka tsaya suna duban juna, Falaki ya dafa kafad’ar Salman alamun kara masa karfin gwiwa…

“Ranka ya dade mu shiga kawai dan Allah…!”

Kad’a Kai Salman yayi, Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Falaki ya koma can waiting area ya zauna. Salman kuma ya sa hannu a hankali ya bude kofar, Dai dai lokacin da Khaleel ya daga idanu don ganin waye ke shigowa. Sosai suke kalon kalo tsakaninsu, ko wanne da yanayin yadda yake tunanin dan uwansa. kamar kuma an tsunkuli Khaleel haka ya zabura ya mike daga inda yake zaune.

“Ya…Yay… Yaya Salmaan ne???? Is that you? Is that really you? Ya Salman Kai ne ko kuwa idanu na ne kemin gizo..”

Salman yai murmushi hade da jingina bayan sa da kofa..

 “Ni ne Khal…! Ni ne Salman.. Ashe rai kanga rai? Shekaru nawa rabon dana sakaka a idanu na Khal?”

Wasu zafafan hawaye suka zirarowa Khal a saman kyakkyawar fuskar sa. Ya share hawayen dake gangarowa a fuskar tasa yana mai jujjuya Kai…

“Noo Yaya.. I love miss you soo much!”

Da sauri suka rungume juna.. Sai kuma kuka ya kwacewa ko wannen su sharrr,

 “Ina Ammi take…?.”

 “Tana gida Khal…”

 “Ina Abdullah? Yaya ashe baku manta dani ba.?”

Murmushin da yafi yake ciwo Salman yayi, Ya kamo hannun sa suka zauna yana kalle kallen office din. 

“What a nice office you’ve got…Congratulations Khal..”

Da sauri khaleel ya mike ya sabule white coat din jikin sa.

 “Muje apartment dina Yaya. Kai kadai kazo?”

 “Noo….”

 “Da aminin ka da na sanku tun tuni ko….? Indai kuma ban manta ba… Falaki ne”

 “Well… Yes”

Fitowa sukai su biyu Kowanne fuskar sa dauke da murmushi, Duk kuwa da glasses din fuskar Salman kallo daga zakai musu kasan yan uwan jini ne. Khaleel ya rungume Falaki suka tafa, Kafin su isa parking lot yaja su suka  tafi apartment dinsa. Sai da ya musu ordering abinci suka ci suka koshi, Banda Salman daya caccakuna domin shi ba ma’abocin cin abinci bane sosai.  Tukun sannan Khaleel ya gyara zama ya shiga yiwa Salman tambayoyi. Shi dai Falaki fita yayi ya basu waje saboda su gana sosai..

“Wallahi Ya Salman ban yada ku ba.. Bansan meyasa ba, Danayi yunkurin zuwa gida ko kiran waya sai na kasa.. Nayi attempting several times Yaya na kasa…”

Fashewa yai da wani kukan mai cike da bakin ciki, Salman ya riko hannuwan sa yana bubbuga bayan sa alamar rarrashi,

“Na shiga fiye da yanayin ka Khal, Nasan kuma yadda kaji. Presently ma ni tamkar an juyamin tunani na.. Na jima bana tuno Ammi da ku, tamkar an shafemin sanin ku a kwakwalwata Khal gaba d’aya na shiga cikin matsalar rayuwa..”

“Subhan’Allah…! Kenan ba jimawa komai ya dai daita awajen ka?”

 “Eh to…. Kasan na kira ka last month ko? Zan iya cewa daga lokacin memory d’inku ya fara dawo min, Ammi kuma ba’awani jima ba. So yanzu dai kasan bazai yiwu na nuna na san inda mahaifiya ta take ba, tunda naga hakan ne ke sa su yi mana makarkashiya, Kasan yadda masarautar nan take. Bana son a cutar da ita da ku shi yasa ban nunawa kowa ba.”

Khaleel ya goge hawayen daya zubo mai yana jijjiga kansa,

 “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…. So ya yan majalisar ka? Ka gano masu maka zagwan kasan?”

 “Ai ka bari kawai Khal… ni yanzu na san ina zagaye da makiya gaba d’aya sun yi min zobe. A fuska tamkar masoya amma a zucia ba haka bane..”

“Ya matar ka..”

 “Matan ka zaka ce.. Suna lapia..”

“Ahh na manta fa.. kace min ka yi wani auren Gimbiya Khadijaa itace amarya ko? journalist ce ko?”

 “Eh… Khadijaa ba..! My brave little lioness ba.”

Ajiyar zuciya Khaleel ya sauke yana mai sauke tagumin da yayi..

“Bana tunanin ku, Na kasance cikin wata iriyar rayuwa. Wani lokacin nakan ji tamkar na manta wane ni.. Meya kawo ni nan ma? Daga ina nake? Wallahi Yaya komai goge min yake wani lokacin. Toh sai kwanan nan nafara mafarkin gida sama sama haka, Da Ammi da kuma ku.. Harma naji inason komawa gida, Inason jin sautin muryoyin ku ko da awaya ne.. Sai kawai kuma ka kira ni. Alhamdulillah Insha Allah k’arshen wahalar rayuwar da aka jefamu ne yazo..”

“Ni ma hakan take awaje na Khal.. and sai Khadija ce ke gayamin halin da aka jefa Abdullah ma.. wasu basu da imani Khal.. shin me muka tsare musu Khaleel!?”

 “Qiyayya ce kawai Yaya.. ba’a so aka haife mu ba kagane? So ya za’ai damu! Shi yasa ake tagayyara mana rayuwa yadda aka ga dama…”

“Toh ta Allah bata suba Insha Allah rayuwar mu zata gyaru kamar yadda take a baya. Kasan abdulqadeer ma an bashi sarauta.. Sun sani a gaba dole na bashi.. Yanzu ma sun nemi kudaden auren su munaya a guri na.!”

“So suke ka sauka fa ta dole Yaya.. Zuri’ar Masekiri kuma sani ne basu yi ba amma sarautar su tagama tabarbarewa tun shekaru aru aru baya..”

Ajiyar zuciya Salman ya sauke yana girgiza kansa,

“General Checkup nakeso kuyi min Khal.. Da full blood count dina.. So nake na gano wasu abubuwa a kai na. Wai shin da gaske ne bazan taba haihuwa ba? ko kuma rabo ne babu tsakani na da Shaheedah?”

“Shaheedan? What about her? Shin metayi haka?”

“Birmingham, Cyprus, India , Luxembourg, France, Da Mauritania. Kaga 6 countries ko? Duk Sai da tasa muka jajje Khal… aka ce wai ni… Ni Salman nine bana haihuwa.”

 “Kai….! Kuma ka tsaya Yaya tun a lokacin ba kai komai akai ba?”

“Khal ina tattare da makiya, Na gayama sun zagaye ni, Banida tacewa, Dole na dau zancen tamkar gaskiya, Sanin kanka dana karyata Za’a illata ni tun kafin mu baro kasashen ma.”

 “Subhan’Allah! Allah ya dubemu Yaya. Wannan zancen ya kamata a bayyana gaskiya kowa ya sani.”

 “Abinda ya kawoni kenan Khal.. Saboda nayi General checkup din.. Ya kuma zamto kaima ka dawo wajen Ammi.. Ni kuma daganan zanci gaba da gudanar da rayuwa ta yadda ya dace har sai na kammala bincike na.”

 “Allah ya temake mu Yaya.. Allah ya fisshemu kunya. Ka watsa ruwa ko? Sai mu koma asibitin, Ko kuma mu tafi can Busan ayo maka acan.”

Hakan kuwa akayi. Salman yayo wanka suka sake shiryawa suka nufi busan. Acan doctors suka fara yiwa SAS gwaje gwaje, Har Sai da aka dau tsawon kwanaki 3 ana yi tukun sannan result ya fito. Result yafito lapiar sa kalau babu abunda ke damun sa sai ulcer saboda abinci da bayaci. Amma yana haihuwa kalau yake, Bashi da wata cutar da zata hana shi haihuwa. Kukan farin ciki Salman yayi, Khaleel ya rungume shi.. Falaki yanata murmushi yana yiwa Allah godia shima. 

Satin su Salman d’aya a Korea suka tattara suka dawo kasar Nigeria. Dama ca yai dasu Wambai ya tafi meeting da wani babban dan kasuwa akan project da zasu yi anan masarautar, Lokacin da suka isa airport din kano, wani murmushi yai irin na gefen bakin nan,  Zuciar sa cike da abubuwan da zai aiwatar.. Ta ina zai fara? Akan suwa zai fara binciken sa. Khaleel bai samu damar biyosu ba sai bayan sati biyu, Sakamakon hanashi tafiya da board of directors sukayi.. Kan sai ya gama aiwatar da project din dake hannun sa. Ba kadan ba suke son sa, Saboda Khaleel mutumi ne shi faram faran kuma ya iya aikin sa, Ba wasa. Ko sanda yana gida Ammi da shi suka fi hira saboda baida girman kai da rashin magana irin na Salman da Abdullah…

*SAS*

Tun a airport aka bashi wani daki na musanman ya shiga ya sauya kaya izuwa na sarakuna. Driver ya ja shi suka koma masarauta. A bakin kofar yamma suka sauke falaki ya tafi gida wajen iyalin sa. Har kofar sashen sa akai parking ya sauka ya shige ciki sam baibi takan dogaran dake masa kirari ba. 

Yana shiga ya kishingid’e a doguwar kujera yana tuna khaleel kanin sa da suka sha zumunci. wani b’angare na zuciar sa kuma na jin dadin sakamakon da ya nuna lapiar sa lau.. 

Sanar masa akai zuwan waziri ya bada iso, Waziri ya shigo yana harhada hanya cikin girmamawa,

 “Sannu da dawowa uban kowa, Takawar ka lapia Sarki Salman jikan salmanu, Sawun giwa badda na rakumi shugaban mu, Hadarin sama sai sauraro sarkin mu, Kai ka dai ka iya Kai zaka cigaba da yi baban kowa, Sun buga sun barka ya zasuyi da kai? Dole su goce.. Barka da dawowa sarkin mu.. Yan majalisa da sauran yan zaman fada na murnar dawowar ka…”

Murmushi Salman yai ya mike ya zauna daga kishingid’en da yake..

 “Na amsa waziri… Ina kuma godia.”

 “An baro su lapia…?”

 “Lapia qalau.. Ai ansamu nasara sunce nan kusa zasu fara qaddamar da gine ginen cikin masarautar nan.”

“Toh Masha Allahu! Tafiya tayi kyau. Babu wani kedararren acikin yan majalisa daya kira ka ko? Sanar mun yanzu ba sai anjima ba na aiwatar da hukunci..”

 “Noo babu wanda ya kira.. Ai ka tsayamun waziri.. Godia nake.”

Hira suka taba sama sama, Waziri ya masa sallama ya tafi.. Ahankali Salman ya mike ya kashe hasken wajen gaba d’aya, Dakin sirrin sa ya shiga ahankali. Zama yai akan kujera, gurin tsab tamkar ma yadda ya tafi ya barshi, baya tunanin khadija ta shigo tai mai aikin da ya sanya ta. Yana kallon waziri ta cikin computer, murmushi yai lokacin da ya hango sashen da waziri ya nufa. 

Ajiyar zuciya ya sauke. Ya shiga jujjuya kansa ajikin kujera. Ya jima a haka kafin ya mike ya fita ya koma dakin sa. Wanka yayo yayi sallah, Kallo d’aya yaiwa abincin da aka jere masa akan dinning table ya dauke kansa. Kaya marasa nauyi yasa ya dora alkyabba akai. 

Amintattun dogaran sa guda biyu yasa agaba suka shiga zazzagaya masarautar. A kofar sashen gimbiya shaheeda suka tsaya ya shiga ciki kansa tsaye. Yana shiga hadimanta suka bashi waje. Kansa tsaye ya nufi dakin ta. Ya turnuke da hayaki sai tari take yi. 

Juyowar da zatai kawai tagan shi a kanta, Da sauri ta mike idanunta sunyi jawur saboda azabar tururun hayakin dake tashi…

“Sas..Salman.. Y..Yaushe ka dawo?Tuttu..turara maganin sauro nake yi.”

Jijjiga kansa yai alamun ya yarda, Ya rufe idanun sa ahankali ya bude akanta, Hannunta ya jawo suka fito. Daga ita sai daurin zani. Jikin ta sai kakkarwa yake ta dauka ya gane abunda take zai mata hukunci ne. Dakin kusa da wancen ya shigar da ita. Ya sakata a tsakiyar kofa yana toshe hancin sa da handkerchief..

 “Maganin sauro.. wani iri kike turarawa haka…?” 

 “Bb… Wani ne hadimata ta aikomin .. s.. Saboda sauron da ake kwana biyu.”

“Okay.. Kidena wahalar min da kan ki.. Duk ga masu aiki nan ki dinga sasu kinji?..”

Yana magana ya goge mata gumin dake goshin ta, Dadi taji ya lullube ta, Dama turaren mallaka ne hajian su ta aiko mata.. Da alama aikin sa kamar yankan wuka yake. Domin gashi tun ba’aje ko’ina ba hankalin Salman ya fara karkata izuwa gareta.. 

 “Kinji ko… My Queen..?”

 “Naji my king..”

 “Okay jeki wanka ki zubamin abinci…. Idan na koma danaci sai bacci ko..?”

Dadi ya sake kama shaheeda tayi murmushi tana jijjiga kai.. Da sauri ta shige ban’daki tayo wanka. Ba abinci. Sai Indomie tasa aka dafa jikin ta na rawa tasa aka juye masa a warmer. Har bakin sashen sa ta rakashi, Yana shiga gida ya kira dogarin sa ya bashi yace yace ya cinye. Yoghurt ya dauka me sanyi yasha yana lumshe idanun sa…. Bincike ne da yawa agaban sa da zai yi, yaso suyi tare da Khadija amman a tunanin sa ba zata bashi goyan baya ba saboda tana ganin ba son gaskiya yake mata ba. Kuma Kowanne sai yayi taka tsantsan akan gudanar da binciken kamar yadda ya boye yar camerarsa me recording komai a dakin shaheedah.. Dai dai lokacin daya jinginata a kofa.. Da kofar shiga sashen duk ya saka… 

 “Yaa Allah… Ka bani sa’a a wannan bincike da zan fara aiwatarwa.. Allah ka bamu nasara.. Allah ka dora mu akan makiyan mu..”

Haka Salman yaita maimatawa yana mai daga hannayen sa sama alamar roko izuwa ga mai sama.. Domin shi din mubuwayi ne gagara misali….

Asubah ta gari… Sarki Salman Aliyu Salman (SAS)

..

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 17

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p NANA HAFSATU❤️…