KIBIYAR AJALI 14

Advertisement

        

_14_

 

      _NH_Jollof d’in taliya na dafa, kasan cewar na yi ta bana cikin nutsuwa yasa ta d’an fara cabewa kadan. Na zuba cikin kula sannan na yi apple and pineapple juice nasa cikin freezer saboda sai an zauna akan table sannan ake fito dashi asha dan kar a ajiye ya huce. Dakina na koma na dauki wayata ina

dubawa naga 6missed calls na Mas’oud sai 2missed calls na Aisha kawata da muka hadu a British English learning centre. Sai da na fara yin alwala nayi sallah sannan na kira Aisha muka gaisa tare da yin yar hira sannan na kira Mas’oud, yaki dagawa sai da ta katse sannan ya kira ni da kudin sa.

 

“Ni na isa na fara cin kudin Oum Waleeda tun kafin ta zo hannu na, salon tace abu Waleed ba shi da kirki son banza gareshi?” Ya yi maganar ta sigar tsokana.

 

Advertisements

“Ka cancanci ka fara cin kudin ne ai tun a yanzu, dan ka gane cewa lallai Oum Waleed mallakin ka ce da komai na ta.”

 

Ina jiyo sanda ya sauke katuwar numfashi yace.

 

“Gaskiya Allah yana sona gashi ya hadani da abar kauna mai tausayi na tun kafin ta zama a karkashin iko na. Madam ina kika shiga tun dazu daga cewa ina zuwa shikenan naji shiru?”

 

Nayi murmushi ina lumshe idanuwa.

 

“Mami ce ta sani aiki shi yasa kaji ni shiru.”

 

“Yayi kyau Oum Waleedah. Nasan ki akwai biyayya, Allah ya nuna min ke a cikin gida na ganki kina yi min tausa.”

 

Advertisements

Wata irin kunya ta mamaye ji tamkar ina gabansa haka na rintsa ido. Shi kuma ya dinga dariya saboda yasan dole kalamansa zasu sani cikin kunya. Jin na kasa yin magana ne ya sashi tsaida dariyar tashi yana cewa.

 

“Kunya kike ji wai?”

 

“Uhmm toh kai ma meye nayi min wannan maganar bayan kasan dole inji nauyinta.?”

 

“Tabdijan! Wai wannan yar maganar itace ta saki jin nauyi? Kice ma sam ba zaki iya dauka ta ba dan gaskiya ina da nauyi ki dena ganin bani da jiki wallahi. Gwarama ki zage damtse wajan shirya yadda zaki dauki nauyi na idan munyi aure.”

 

Tsabar tsagwaran kunyar da ya kuma sanya ni a ciki ne yasa ni katse wayar da muke yi na kifa kai na cikin pillow ina dariya mai cike da shaukin kaunarsa. Ji nayi kamar naje na ganshi da ido na, dan na hango yadda yake zaro min wadannan bayanan nashi da suke bani kunya. Ya sake kirana na dauka ina murmushi har hakorana suna fitowa a bayyane.

 

“Ya zaki kashe min kira bayan ni na kira madam? Gaskiya ki bari idan ba haka ba zanyo shirin bacci nazo gidan ku na kwana sai naga yadda zaki da wannan kunyar.”

 

“Kai! Lallai ma, kai yanzu sai kazo gidan nan da kayan bacci?”

 

“Tsab ma kuwa, ko na gwada miki dan ki tabbatar?”

 

“Lallai ma kai din nan.”

 

“Bafa ki bani amsa ba Oum Waleed kinsan ai dama ni Waleedah ita ce tawa idan mun haife so.”

 

“Haka dai kake cewa, amman ni ina ji a jiki na cewar Waleed zai fi Waleedah kyau, kar ka dawo daga baya kace na bar maka shi.” Ya sake sakin wata shu’umar dariyar tare da cewa.

 

“Toh mu jira mu gani ko madam? Yanzu dai ki gaya min na taho d’in na taya ki kwana? dan nasan ki da tsoro.”

 

Nayi saurin cewa.

 

“A’a gaskiya ni bani da wani tsoro ka ganni nan, dan babu inda bazan iya zuwa ba cikin dare.”

 

“Bafa irin wannan tsoran nake nufi ba, ina nufin na…”

 

Ban bari ya karasa ba nayi saurin cewa.

 

“Kawu sannu da zuwa.”

 

Cikin wasa nayi maganar dan karma ya karasa nasan maganar ta rashin kunya ce, aikuwa naji kit ya katse babu shiru. Na kwanta kan gado ina ta dariya dan banyi wannan zaton ba na cewa zai ji tsora idan na yi haka koda ma ace da gaske Kawu Isma’eel din ne ya shigo. Ya Waleedah ce ta shigo dakin, nayi saurin mikewa zaune tare da hadiye dariyar da nake yi ina gyara zama na tace min.

 

“Lallai Dije, saboda kawai ance kiyi girki baki ga dama ba shine kika yi ta yadda kika ga dama ko? Suwaye kike nufin zasu ci wancan jagwalgwalon da kika yi? Toh kije Mami tace yanzu ki yiwa Daddy tuwon shinkafa da miyar zogale kafin ya dawo.”

 

Nayi saurin kallon agogo dake makale jikin bango naga karfe takwas da arba’in da hudu na dare, shine ake son nayi tuwo kuma wai na shinkafa saboda tsabar ana son a wulakantani. Toh wai dan Allah me nayi musu? Meye laifi na a cikin gidan nan? A gani na tunda kyautatawar da kawu yake yi min ne basu so me zai sa su hanashi ya dinga yi min tunda sun fini kusanci dashi? Sun takura min Allah Allah suke nayi abinda zasu yi min rashin mutunci kuma Allah yana kare ni sai dai su kirkiro wani abun su lika min. Sai kawai na gyada kai tare da sakkowa daga kan gadon nace mata.

 

“Toh Yaya bari nazo.”

 

“Ya fiye miki kam.”

 

Ta juya ta fita ni kuma na zauna a bakin gado zuciya ta tana zugi. Wai dama haka rashin iyaye yake? Kodai ni kadai ce bana dace da marika nagartattu? Tabbas duk lalacewar iyayen ka, duk talaucin ku, duk tsiyar ku gwara ace kana tare da su akan kana hannun wani da basu ba. Naja majina tare da tashi na saka wayata a charge sannan na fita zuwa kitchen dan dora tuwon kamar yadda aka umarce ni.

 

Ruwan tuwon na fara zubawa sannan naje na debo shinkafar na wanke na zuba sannan na nufi gurin hada abubuwan da zanyi miya. Banda Daddy ne zai ci wallahi sai na yi rashin mutunci naki tuke tuwon sosai, to dan dai kawai shine zan tsaya na yi har ya yi dadi. Ina jiyo muryoyin su daga kitchen, ba bu wanda ya leko ni yaga a wane hali nake ciki saboda ba damuwar su bane ba. Sai wajan tara da hamsin da uku 9:53pm na kammala naje na dora akan dining table a lokacin ne Mami tace min.

 

“Kin gama ne?”

 

“Eh Mami na gama.”

 

“Guda nawa ki ka yi?”

 

“Leda biyu ne Mami.”

 

“Biyu kuma! Me ya sa baki yi da yawa ba?”

 

Nayi shiru dan ba a ce na yi shi da yawa ba, kawu kawai aka ce na yiwa kuma na yi masa dan haka ba damuwa ta bace.

 

“Shikenan dakko min guda daya ki zubu min miya ki kawo min, idan yazo yaci dayan.”

 

Ban wani damu ba, nasan idan tace zata cinye ko su Ya Shukrah suka ce zasu ci ba iya hanawa zan yi ba. Ni fatana kawai Allah yasa kar su kuma sanya ni wani abun, ina son naje na huta nima kamar yadda suke yi a yanzu. Na juya naje na sako mata na kai mata sannan nima naje na dibi taliyar da nayi dazu na wuce daki saboda karma su ganni su dinga aike na ko saka ni aiyuka. A daki na naci na wanke hannu ko plate ɗin ban fito dashi ba saboda bana son ma su ganni wallahi dan babu alkairi tsakanin mu.

 

    Washe gari tunda na idar da sallar asuba na shiga kitchen dan shirya breakfast bana son na makara a fara ganin gazawa ta. Ina tsaye ina kada kwai zan soya dan na kammala soya Irish sai ga Mami ta shigo tana yatsina fuska. Daga bakin kofa ta tsaya tana kare min kallo, na yi saurin durkusawa har kasa kamar yadda nake mata tub farkon zuwa na har yau kuma ban dena ba na gaishe da ita.

 

“Mami ina kwana?”

 

“Tashi tsaye ni ki dena gaishe ni a kasa, so kike mutane suce gallaza miki nake yi?”

 

Na mike naci gaba da aikin ba tare da na kuma gaishe da ita ba.

 

“Kunu zaki damawa Alhaji yace yau ba zai sha tea ba. Kin tambayi su Shukrah sun gaya miki abin da zasu ci ne matsayin breakfast?”

 

“A’a Mami, nasan suna cin Irish shine ya sanya ni yi. Sannan fa shayi can shima nayi, naga sunfi son shi.”

 

“Jiya ai sunce wainar fulawa zasu ci, dan haka kinga yanzu sai kiyi musu abinda suke so.”

 

“Mami dan Allah su taimaka min su ci wannan d’in, idan na dawo daga gurin aiki sai na yi musu. Wallahi Mami bana son yan gurin aikin mu suyi zaton ko bani da serious akan aikin.”

 

Mami ta saki baki tana kallo tare da fadin.

 

“Inyeeee, lallai seriously?. Wallahi Dije kinga gurin bacci na. Wato kinfa bawa yan wajan aikin ku muhimmanci akan mu ko?”

 

“A a wallahi Mami ba haka nake nufi ba kiyi hakuri.”

 

“No no noooo Dije ai kin isa karki wani damu. Idan kin kammala dama kunun ki kawo min.”

 

“Toh Mami, amman dan Allah ki….”

 

Tayi banza dani ta wuce tamkar ba da ita nake ba. Haka ina ji ina gani na kammala soya kwan daga nan na dora ruwa na dama kunun naje na kai mata dakin ta na kuma komawa kitchen na fara hada kullin wainar.

 

Saboda tsabar rainin hankali sai gasu sun fito lokacin na fara suya, na gaida Ya Shukrah da ta shigo kitchen d’in tana faman gyara earpiece d’in kunna ta. Bata kula ni ba sai kofi da ta dauka taje ta tsiyayi ruwan tea tazo ta dauki wainar fulawa guda daya tare da janyo yaji ta fara ci. Sai da ta cinye wacce ta dakko sannan ta kalle a yatsine kamar ta ga Jummai mai aike a gabanta, ta ce dani.

 

“Kwai nawa ki ka saka a kwabin?”

 

“Guda biyu ne.”

 

“Toh ba bu kwan a gidan ne ki ka saka iya biyu kawai?”

 

“Akwai Ya Shukrah, amman gani nayi wainar da zan yi ba wata mai yawa bace shi yasa ban sa da yawa ba. Kuma a haka tafi dadi akan ace an kara.! kwai da yawa.”

 

“Kinga malama, su wa ki ke yiwa? Mu ko ke?”

 

Haushi ya kamani, toh ko su kadai zan yiwa ai tunda dai zan yi d’in dole nima naci koda kuwa guda d’aya ce. Amman dan kar ta je ta gayawa Mami tazo ta kuma sanya ni wani aikin yasa ni cewa.

 

“Ta ku ce Ya Shukrah.”

 

“Toh sai ki kara mana kwan.”

 

“Toh shikenan bari na kara muku.”

 

Tana tsaya sai da na kara guda biyar kuma duka duka kulin fulawar gwangwani d’aya ne, sai ya yi kauri tamkar ba fulawa ba. Juyawa tayi ta bar kitchen din dama jira take taga ko nayi abin da tace. Na ja tsaki a can kasan magogwaro na naci gaba da su ta, itama Ya Hameedah tazo ta diba ta koma parlorn suna ci. Ko sha’awa bata bani ba haka na shirya na yi tafiya ta gurin aiki. Bayan na shiga na yi program din da zan yi sai kawai fito muka hadu da Mas’oud muka ci gaba da hirar mu ta masoya.

 

      ••••.        •••      •••

 

Haka naci gaba da rayuwa ta a gidan kawu na mai so na, shi kadai ne yake min abu a matsayin uwa da kuma uba da zance na rasa a rayuwa ta. Bayan wasu yan kwanaki naje gurin aiki ina shirin shiga studio na hango M.D da wasu ma’aikatan gidan a tsaye suna magana, sai na juya na karasa inda suke na gaishe su cike da wasa da dariya, har na tashi zan tafi sai mai kula da sashen siyasa na gidan radion ya dakatar dani tare da cewa.

 

“Malam Khadija ko ke zamu wakilta ne?”

 

Nace,

 

“Yallabai ina za a wakilta ni?”

 

“Wajan taron nan da za a yi ranar Asabar. Kawai ke zamu turo tunda dai kina da himma sai kije ki dakko mana rahoton yadda abubuwa suke gudana a wajan.”

 

Murna ta kamani dan ni akan aiki na bana jin wani fargaba ko tashin hankali. Dan haka da murna ta na karbi ta yin da suka yi min tare da yin godiya na tashi na karasa dan yin aiki na. Bayan na gama na fito naje wajan Mas’oud na sanar dashi, yana ta tsokana ta wai kar naje naga abubuwa da yawa na rasa wane rahoto zan dakko saboda rudewa. Nayi dariya cike da shaukin soyayyarsa, dan har ga Allah a koda wane lokaci Allah kara sanya min soyayyar shi yake yi.

 

Yau kam aikin sa har dare hakan yasa ba zai samu damar zuwa kai ni gida ba, sai na yiwa driver waya yazo ya dauke ni na koma gida. Mami na zaune a wajan hutawa naje na sanar da ita cewa gobe idan Allah ya kai mu zanje na wakilci gidan radion mu kasan cewa ni aikin radio nake yi, ita kuma Hameedah nurse ce a asibiti. Shukrah kuma business take yi, Kawu ya bude mata botic a can kan titi tana siyar da kaya kala-kala na gida dana waje masu kyau kuma. Kai kawai ta daga ba ta ce min komai ba babu addu’a bare fatan alkairi, duk ta bi ta kwarzabi kanta damuwa ta yi mata yawa saboda kawai ina cin irin arzikin da yaranta suke ci a wajan mijin ta. Na tashi na shige cikin daki na baki na sai addu’a yake na kar Allah yasa su saka ni aikin da zai hanani shirya abubuwan da zan gudanar a wajan taron. Cikin ikon sa kuwa babu wacce da neme ni saboda sunyi baki ya’yan yan uwan Mamin sun zo suna daki sai hira suke yi.

 

*WASHE GARI…*

 

Tsab nayi shiri na cikin wani arnan lace Coffee mai dauke da ratsin milk d’in zare, an yi min din kin doguwar riga wacce ta amsa sunan ta. Nasa mayafi milk da takalmi sai agogo da shima ya kasance ruwan madarar. Na tsaya a gaban madubi ina karewa kai na kallo, wanda nasan idan har Mas’oud ya ganni to tabbas ba zai taba kin bina ba, dan zai ce za a kalle masa ni, yana da matukar kishi dan ko a gurin aiki ya dinga min magana akan yadda mutane suke yabo na da kuma wadanda suke biyowa ta gurinsa suna sake gaya masa yadda Allah ya bani halitta mai kyau.

 

Jakata na dauka na fito ina bin step d’in nan a yangance, yanzu fa babu batun tsoro dan gudun da nake yi a kai ko yan gidan albarka. Na saba da shi yabi jiki na sai kuma nan gaba ban san me zai bani wahala ba bayan shi. Naje dakin Mami na yi mata sallama a lokacin Kawu ya fito shima, muka yi sallama na tafi shima Mami ta raka shi motar sa ya wuce. Da naje gurin aikin banga Mas’oud ba, a gurin Aminu Gumel nake jin wai sun tafi asibiti Abban sa ne bashi da lafiya. Na karbi kayan aiki muka tafi a motar gidan radio d’in. Sanda muka je an taru matuka, na samu naje can kan highe table na kara abinda zan dinga daukar maganar manyan baki sannan na koma gefe inda aka tanadarwa yan jaridu gurin da zasu zauna.

 

Gurin saukar karatun Alqurani mai girman ya kawatu sannan kuma ya yi cikar da alkalami ba zai iya rubutawa ba. Manyan mutane kuwa ba’a magana wadanda suka halarta. Sarkin musulmi, gwamna, Sarkin Basannabas da manya masu mukaman gwamnati da ma yan kasuwa dake jihar.

 

Tunda tashigo wajen yake jin yanayin sa na canzawa, Yana hakimce akan doguwar kujerar girma da aka lullube da farin yadi. Me dauke da tambarin ‘’Sarkin Basannabas” . Lokaci zuwa lokaci ya kan duba designer agogon dake daure a wutsiyar hannun sa, Ba shi da ikon ya nuna gajiyar sa. Shin meyasa ma yazo? Yai taiwa kansa tulin tarin tambayoyin da shi kansa bai da amsa. Bakin sa ya masa nauyi. Sanye yake cikin hadaddun kayan sarakuna. Kallo d’aya zakai masa kasan shidin matashin sarki ne, Mai ji da ado da zatin halitta. Taune kasan leben sa yai ta cikin rawani. Idanun sa na saqale da bakin gilashin sa tamkar na gado. Tun yana makaranta ance kullum cikin saka shi yake. Bai taba bari aga kwayar idanun sa. Sannan baya kallon mutane na tsawon wani lokaci kowaye kuwa kai.

 

 “Ya RABB! I’m exhausted….”

 

Ya furta a labban sa yana jera ajiyar zuciya. Tunda aka fara hidimar saukar ba kallo yake ba. Kansa a kasa yana jujjuya zobunan azurfar hannun sa.

 

Sarki Salman Aliyu Salmanu (SAS) kyakkyawa ne na ajin karshe,  Ma’abocin ado (sutura da zuciya) Dauke zuciar sa take da son taimakawa jama’a da kuma alkhairi agare su. A Zahiri ka ganshi zaka dauka ya gama da cewa duniya da lahira saboda yadda yataso cikin gata da ingatacciyar rayuwa, Tun kafin ya gaji sarauta awajen mahaifin sa (Marigayi sarki Aliyu Salmanu Ibrahim) ya kasance mai hankali, Samun kamammen ‘da irin sa sai an tona, Da kamar wuya. Bai dauki rayuwa da zafi ba, Yana bin komai ahankali, Duk da cewa ya tashi cikin gata, Bai taba daukar gatan nasa tabbatacce ba. He’s kind, attentive and most caring..

 

Yana kishingid’e ya jiyo zazzakar muryar ta na masa yawo a cikin kunne,

 

 “Sunana Nana Khadijaa Basheer Inuwa. Ni ce yar jaridar dake wakiltar gidan rediyo da talabijin na DokinKarfe24. A tare da ni akwai matemaki na Ashafa Ghali Dikko.. Shin mai girma sarki ya kaji lokacin da aka ce wannan babbar makaranta zata yi taron saukar karatun Alqurani mai girma a cikin jahar ka mai albarka?..”

 

Kwata kwata sarki Salman bai bi ta kan zancen da take fada ba. Samun kansa kawai yai karo na farko a rayuwar sa da yayi wa bil adama kallon k’urilla har haka. Tun daga tafin kafarta ya fara kallon ta, ya tafi ga tsarin shigarta ta jiki har zuwa kan fuskar ta wacce tasa shi lumshe idanuwa ba tare da ya ankara ba. Ya sake bude ido ta cikin dark shades d’in fuskarsa yana kallon yadda ta d’an rankwafo alamun tana jiran bayanin sa duk da tazarar dake tsakanin su. Bata ankara ba taji an sanya wata zungureriyar sanda tare da buge abin daukar sautin na ta. Kasan cewar idanun shi suna kanta ne yasa yaga yadda tabi wanda ya yi mata wannan wulakanci da kallo tana tsuke fuska.

 

“Karya ki ke yar jarida, sai dai kiyi mana tambaya ba dai da sarki mai daraja ba.”

 

Sarki Salman ya sake kallon ta dan yaga wani irin mataki zata dauka gurin bafaden shi da ya yi mata wannan abun. Sai yaga ta dauki abin daukar maganar tana kallon shi tare da sanya tafin hannunta da yasha jan lalle a yan yatsun suka yi matukar kyau. Sai kuma yaga ta juyo ta kalle shi, ya dauke kai duk kuwa da cewar yasan ba tasan ita yake kallo ba sanadiyar glasses d’in shi.

 

“Amman ya kamata muji ra’ayinsa dan yana da matukar amfani ga al’ummar mu.”

 

“Karya kike yar talakawa.”

 

Bafaden ya sake fada yana bula babbar rigarsa dake nuna cewar shi din bafaden sarkin ne. Wani irin takaici ya rufe Dije, ta sunkuyar da kai kasa. Duk a tunanin sarki Salman kuka zata yi, besan zaka da warwara ta shiga yi da zuciyar ta ba. Sai yaji tamkar ya yi mata magana, amman mulki da izzar dake tattare da sarauta ta hanashi koda yin motsi. Dije ta kuma kallon sarki Salman duk kuwa da banda tulin rawanin sa bata ganin fuskar sa ta sake cewa,

 

“Ranka ya dade gashi an gudanar da karatun saukar Alqurani, ya kaji a ranka game da yaran da suk…..”

 

Bata kai ga karasa tambayar ta ta ba kawai taji saukar sandar nan a gefen kanta, wanda ya yi sanadiyar da yasa ta saki wata gigitacciyar kara mai gigita kwakwalwa, ta kuma sulale ta fadi kasa sumammiya. Dai dai lokacin sarki Salman ya mike aka dora masa malafarshi ya tsaya cak yana kallon yadda yan sanda suke korar mutane dan a samu yadda za a ceci yar jaridar da bafadanshi ya rafke. A hankali ya sakko daga wajan ya nufi motarsa ba tare da ya tsaya ya yi sallama da mai girma gwamna dake gurin ba…..

 

______________________

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA’ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

 

To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.

 

        Ina ma’abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

 

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

 

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana’arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

 

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 28

Advertisement   28….*      _*KIBIYAR AJALI…..!_* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_                  🏹🥰😍    …

KIBIYAR AJALI 1

Advertisement  *KIBIYAR AJALI…..!!!!* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_            🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA…