KIBIYAR AJALI 16

Advertisement

 

  *Epi: 16*

 

 

  ________Satin Dije biyu a gadon asibiti tayi shar tamkar ba ta yi wani ciwo ba. Hakika mafi yawancin mutane musamman talakawa suna mutuwa ne ta hanyar rashin kulawa ta musamman. Munsan cewa duk wanda ya mutu lokacin shi ne ya yi. Amman mafi yawa wahala da kuma rashin abinda zaka kula da

lafiyar taka yana taka muhimmiyar rayuwa wajan rasa rayuwa kan mu masu tsada. Alhaji Isma’il ya tsaya tsayin daka wajen ganin ta samu sauki kuma alhamdulillahi gashi har an sallame su sun koma gida.

 

Kwance tayi akan doguwar kujera tana waya, kan cikin ta kuma plate ne mai dauke da fruits tana dauka tasa a bakin ta cike da nishad’i. Mas’oud ne yake ta kashe mata jiki da sassanyar soyayyar shi, wacce take sanya ta rasa a wace duniya take tsabar sauki. Shukrah ta shigo tana faman nishi da alamar gajiya tayi, ta bude fridge ta dakko ruwan sanyi tare da budewa tana kwankwada. Sam ba tayi zaton waya Dije kiyi ba saboda ganin idanunta a rufe, tayi tunanin ma bacci ne ya dauke ta da plate d’in a jikinta, sai ji kawai tayi tana cewa.

Advertisements

 

“We are two bodies, but our heart beat as once. Be mine, forever, do not leave me ever Abu Waleed.”

 

Cikin wani irin juyi Shukrah ta waigo tare da zuba idanuwanta akan Dije. Cikin tsantsar mamaki na ganin ashe yarinyar nan idanunta biyu tana jin shigowar ta amman tayi mata banza babu wani alamun taji ta. Da waye take wannan wayar ita kuwa? Allah yasa ba Mas’oud bane data fara ganin sa sandiyyar kwanciyar Dijen a asibiti. domin harga Allah gayen ya yi mata dari bisa dari, zuciyar ta babu abinda take muradi irin su kasance tare, hakan yasa bata fatan ace suna soyayya da Dije dan kar ta zo ta bayyana mutane su ga rashin adalcin ta ko su yi mata fassara da maciya amana. Sai kawai ta samu kanta da zama a parlorn tana sauraran wayar duk da cewar bata jiyo muryar d’aya bangaran.

 

“You’re my dawn, You are my twilight.”

 

Shukrah taji Dijen ta kuma fada, duk da cewar bata san ko waye ba, samun kanta tayi da cewa Dijen.

 

“Wai baki ji ana ta sallama bane Dije? Na dauka ma bacci kike yi ashe kina nan kina yaudara bayan ga Tk can yana jiran ki a parking lot.”

 

Yadda tayi maganar da karfi ne ya sanya Mas’oud jiyo abin da take fada, daman kuma tayi ne dan koma waye Dije ke wayar dashi ya jiyo. Musamman idan Mas’oud din ne da tayi domin shi. Ai kuwa yaji d’in, nan da nan hankalinshi ya yi mugun tashi yana ta tambayar ta.

Advertisements

 

“Ummu Waleedah waye Tk? Meye hadin ki dashi? Wace a kusa da ke?”

 

Dai dai lokacin Dije ta bude ido ta kalli Shukrah da ta kura mata nata idanuwan. Bata ce mata komai ba, haka ma bata dauke ido akan ta ba tace da Mas’oud.

 

“Duk wadannan tambayoyin ni kadai zan amsa su?”

 

“Eh mana, ai nasan duk kina da amsoshin su, kuma zafi ganewa idan kika min bayani da kanki.” Ya yi maganar yana tsuke fuska tamkar suna ganin juna.

 

“Amman fa karka manta da bahaushe yace, idan ka ga kare yana shinshina takalmi, toh dauka zai yi. Ni babu abinda ya hadani da duk wadannan tambayoyin da kayi min.”

 

“Toh wace ce ta yi miki wannan maganar?”

 

“Ya Shukrah ce.”

 

Shiru ya yi na dan wani lokaci yana nazarin abin da tace maza na kare. Murmushi ya yi har ya na dan fito da saurin sa, wanda ya sanya Dije gano cewar ya fahimci abinda take cewa.

 

“Gaskiya ne yar jarida, wato kema kinsan kiyi irin wannan language d’in ko? Wallahi kin bani wahala wajan yin tunanin abinda kike nufi, oya ki lallashe ni kar na yi fushi.”

 

Saboda ta sake batawa Shukrah rai dan ta gane cewa abin da ta fada ba damunta ya yi ba, sai cewa ta yi dashi.

 

“Uhm-uhmm-uhmmm…, ka yi hakuri dear, for you, my heart beat aches, and only you can ease the pain. Kar kai fushi kasan zazzabi yake sani idan kayi.”

 

Kamar Dije tasan amsa zai bata kuma mai dadi ta nuna soyayya, hakan yasa tasa hands-free dan Shukrah taji da kyau ko zata rabu da su. Sai da ya ja numfashi kamar irin wanda ya dawo daga shiga tashin hankalin nan, sannan yace mata.

 

“Har naji dadi, rai na ya sanyaya. Forever walk by my side Oum Waleedah, promise me that you will meet me in my cham…..”

 

Kafin ya karasa ta yi saurin cirewa daga handsfree d’in dan karya fadi abin da zai sanya Shukrah kuma yi mata kazafi, taje tace maganganun batsa suke yi. Cikin jin haushi kuwa ta suri jakarta tayi daki tana masifa kamar wacce a ka yiwa wani abu. Cikin ranta banda bakin ciki babu abin da yake cikin sa, koda ace gaske ne Mas’oud da Dije soyayya suke yi sai ta rugurguza duk da cewar tare ta gansu, kuma ta silar Dijen tasan Mas’oud din. Toh amman ya za ta yi da zuciyar ta wacce a cikin rashin adalci ta sanya soyayyar shi a zuciyar ta. Tayi wurgi da jakar ta tare da fadawa kan gado tana wani irin nishi, ƙirjinta ya shiga bugawa ga zafi da taji yana yi mata (yo bakin ciki ne da hassada).

 

“Abu Waleed yaushe zaka zo ne?”

 

“Uhmmm….zan zo sai ranar da bamu da aiki, kinga yau juma’a, San da kika dawo aiki. Idan kin zo sai muyi shawara ko?”

 

“Toh shikenan Allah ya kai mu.”

 

“Amin my dear wife to be. Bari naje Abba yana kira na.”

 

“Toh shikenan a mika min gaisuwa ta musamman.”

 

“Lalalah! Toh in ji waye zan ce masa.”

 

“Kana nufin kace be sanni ba?”

 

“Mama ta sanki wallahi, kinsan sunan mahaifiyarta gare ki shi yasa take girmamaki.”

 

Wani sanyi ya ziyarci birnin zuciya ta jin wacce zata zama sirika a gare ni tana ganin mutunci na, Lallai idan nayj sa’a, Zan yi dace da uwar miji mai so na. Jin ana ta kiran sa daga nesa ne, Yasa na sauke wayar na katse dan nasan idan ba hakan nayi ba tabbas ba zai tashi yaje kiran da gaggawa ba, saboda baya son rabuwa da ni yana jin dad’in kasancewar mu masoya. Tashi nayi nima na shiga bedroom d’i na, sauki ya samu ba lefi, kuma ya zuwa yanzu nasan yadda zan zauna da kowa na cikin gidan.

 

*MASARAUTAR BASANNABAS*

 

Gurfane yayi a gaban sa tamkar shi ne sarkin, Shi kuma yana hakimce akan kujerar zaman fada ta sarki. Su uku ne kadai aciki. Daga manyan dattawan biyu sai shi sarki Salman, Shi wanda ke kan kujerar zaman sarki ya harde kafa yana dudduba ipad din hannun sa. Sarki salmaan na tsakure a gaban wanda ke zaune akan kujerar. Dayan kuma yana zaune a d’aya daga cikin royal chairs din fadar. Dukkanin su kowanne yasha rawani. Daka gansu kasan sudin jinin sarauta ne kuma masu ji da kambun mulki.

 

 “Ya akai hakan ta faru……?!”

 

Shiru sarki Salmaan yai kawai kansa a kasa, Na kan kujerar sarkin ya sake buga hannun kujerar da yake Kai yana taune lebe,

 

“Salmanu ba magana nake maka ba..?”

 

“Kawu I’ve no idea… Kawai nasan mutane na bukatan abinci shysa nace a kwashe a raba musu.”

 

Ya karasa fada yana mai gyara zaman gilashin dake saqale a idanun sa.

 

Dogon tsaki dayan yaja yana karkada kafa,

 

 “Kar mu sake jin kwatankwacin haka, Shin ya zancen zuwa gidan gwamnati nemo wannan tallafin?”

 

“Munyi magana na tura waziri yace za’a samu.”

 

“Ka dai kara pushing wannan karan banda wasa.”

 

Sarki salman bai amsa ba ya kalli gefe kawai yana taune leben sa,

 

 “Sai ana maka magana ka tsiri wani cin fuska, Wai Kai sarki ko? Sannu sarki… Kar ka kai mu ma’kura wallahi. Kuma ba zeyi wu har mu muna maka magana kana saqale da wannan shegen gilashin naka ba. Na kinubibi..”

 

Cewar na kan kujerar sarki. Mikewa yayi, Ya cilla ipad din akan cinyar sarki Salman.

 

 “Gatanan nayi mailing united nation din suyi haku’ri ba zaka samu zuwa ba. Saboda mun gama magana da madaki watan gobe zaka tafi cyprus taron nan. Kana jina?”

 

Kansa ya daga musu kawai, Suka fuce. Yana jiyo sanda bafadensa na kofa yake musu kirari,

 

 “Takarwar ku lapia.. A sauka lapia Galadiman Basannabas da Wamban Basannabas.. Sarkin kofa na gaisuwa da fatan alkhairi.”

 

Silalewa sarki Salman yai yai zaman dab’aro awajen yana dafe kansa dake masa barazanar fadowa,

 

 “Ya Allah!….”

 

Komawa yai kan kujerar sa ya zauna, Cikin haka jakadiyar sa mai suna Abu (Zainab) ta shigo tana rissina masa,

 

 “Allah ya karawa sarki lapia.. Za’a yiwa wani iso ne? Naga masu jiran nada yawa a zaure na biyu.”

 

Hannu ya d’aga mata kawai.. Da baya da baya ta juya har takai k’ofa ya danyi gyaran murya ta juyo,

 

 “Ina….. Alhassan? (Amintaccen bafaden sa)”

 

“Allah yaja da zamanin Sarkin Basannabas, Shima yana cikin masu jiran.”

 

 “To a masa iso..”

 

 “Allah ya Kara maka lapia da kwanciyar hankali. Yanzu kuwa.”

 

Ficewa tayi da sauri. Cikin mintina k’alilan bafaden ya shigo bayan Sarkin kofa yayi shelar zuwan sa,

 

Yana shigowa ya zube yana kwasar gaisuwa, Maganganu su kai ba masu tsawo ba, Naga bafaden ya fice da Sauri, Shi kuma sarki salmaan ya lumshe idanu kawai, Kafin jakadiya ta sake dawowa tayiwa wasu mutanen iso…

 

         *DR ISMA’EL MUHAMMAD SINGA RES*

 

Zaune Dr/Alh. Ismael yake, Gaban sa kuma wani babban Yaron sa ne (Abdul) dake rike da ma’adanar kudaden sa dake bankuna (banks) kasancewar bashi da ‘da namiji.

 

 “Alhaji ba lefi gaskia cinikin wannan karon yafi kowanne, Sai dai b’angaren taliya ne aka samu akasi, Sun rage ingancinta, Shiyasa mutane suka dena siya Kwana biyu.”

 

“Masha Allah! Haka akeso. Eh itama munyi magana da Alhaji Sabitu zamu tura wakili can kamfanin domin susan yadda ake ciki ko kuwa..?”

 

 “Hakan yayi Alhaji..”

 

Magana sosai suke yi, Mai gadi ya shiga doko sallama parlorn yana zura kansa ta kofa,

 

 “Oga! Ana sallama da kai..”

 

 “Waye?”

 

 “Wani ne wai daga gidan sarki.”

 

 “Toh! Shigo da su.”

 

 “Ai mutum d’aya ne..”

 

 “Eh ba lefi.”

 

  Abdul ya mike da littafan gaban sa yana rissinawa alhajin.

 

 “Alhaji ni zan wuce.. Sai gobe idan Allah ya kai mu!”

 

“Allah ya kai mu Abdul.. “

 

Fita abdul yayi, Bafaden sarki kuma ya shiga. Gaisawa su kayi cikin amintawa, Kafin Alhassan ya gyara zama domin shedawa Alhaji abinda ke tafe dashi,

 

 “Ni suna na Alhassan, Babban bafaden sarki ne ni, Domin zuwa na na uku kenan, Bana samun ka sai yau, Na farko naje asibiti ban samu ganin ka ba, Na danyi bincike na gano inda kake a kasuwa, Nan ma ban same ka ba, Da tambaya na gano nan gidan ka..”

 

 “Allah sarki an samu sabani kenan. Afuwan to”

 

 “Haba Alhaji ai mune da ban ha’kuri, Ayi hak’uri, Bafaden sarki ya tafka kuskure, Sabon d’auka ne kansa yana rawa ya aikata haka, Sarki yace a baku hak’uri dan Allah. Tafe nake da asusun bankin sa yace a lissafa dik nawa aka kashe sai a biya. Domin bafaden da ya tafka ta’asar ma tuni an sallame shi ya koma cikin yan lufudi..”

 

 “Haba! Ba wani abu wallahi, Da kam dai banji da’din rashin nuna kulawar da masarauta tayi ba, Amma tun zuwan ka da kayi asibiti an sheda min kuma komai ya wuce wallahi, Lefi kuma bana bafade bane shi kadai harda diyata Khadija.. Kuruciya ce itama da kwadaituwar hazakar aikin ta yasa tayi wannan shirmen. Idan ba haka ba Ina ita ina tambayar sarki kai tsaye.? Uban taro guda? Tayi kuskure itama sosai, Saboda haka a bawa sarki hak’uri Shima dan Allah, Khadija ta tafka babban kuskure, Ina fatan Allah ya huci ran sarki ya yafe mata.”

 

“Babu komai Alhaji.. Allah ya yafe mu gaba d’aya. Toh amma wani hanzari ba gudu ba. Sarki yace yana son ganin ka ido da ido a fadar sa.. Nan da kwana ki biyu kacal. Da yammaci bayan an tashi daga fada.”

 

 “Tohh! Ni? Toh Allah ya kai mu.. Na karbi wannan gayyata da hannu dubu. Allah ya bamu ikon ganin lokacin.”

 

 “Aamin Yaa Rabbi..”

 

Sallama Alhassan yayi masa ya tafi. Dr. Isma’el ya shiga tunanin abinda yasa sarki keson ganin sa? Ko dai bayan ta’asar da Khadija tayi ranar ta kara da wani abun aka boye masa? Tunani ya shiga yi shi kadai yana dirkawa cikin sa ruwa. Zuciar sa dauke da addu’ar Allah dai yasa alkhairi ne yake kiran sa ba sharri ba.

 

Kafin ranar ta zagayo kullum sai Dr. Isma’el ya tambayi Khadija akan gaskiar lamarin da ya faru awajen sauka sau ba adadi. Ranar da zai je masrautar ma sai daya sake tambayar ta tace daga tambaya bata kara ce masa komai ba. Kad’a Kai kawai yayi ya fice yana jinjina wannan al’amari.

 

Kawu Daddy na fita na sake sauke gwauruwar ajiyar har ga Allah na tsani sarkin nan, Wallahi bana son sa, Kai duk abunda ya dangance su na tsane su.

 

 “Shege.. Mumugunci, Uban fadin rai. Wannan sarkin matar sa ta shiga uku da izzar sa. Bare kuma a kai ga yan aikin gidan..”

 

Na sake jan wani dogon tsaki na juya daga kwanciyar da nai. Domin tun da la’anannen bafaden sarki ya rafke kai na ban koma aiki ba, Na dauki sick leave. Sannan duk wasu aiyuka na gida Kawu daddy ya dauke min su, Yace duk Wanda ya sake sa ni wani aiki sai ya mugun sab’a masa. Gaba d’aya yan gidan zaman takun sak’a suke yi da ni.

 

 “Wayata na janyo na rubutawa Habiby na message na masoya, Na tura masa.

 

 “Dear Habiby.. Nothing in this world can ever keep us apart from each other. We’ll always be together no matter where life takes us. I love and miss you so much. Yaushe zaka Zo? Hmm har yanzu ka ki zuwa ka kwashi gaisuwa wajen Kawu Daddy ko?”

 

Minti biyu tsakani ya min reply,

 

 “I choose you. And I’ll choose you over and over, Without any doubt,. I’ll keep choosing you my love, My heartbeat.. My shining light. I love and missed you most. Ina nan tafe love. Zan zo na gayawa Kawu abinda ke tsakanin mu In Shaa Allah!. You are the pillar of my life. I love you.Thank you for being a part of my life.”

 

Karantawa nai na lumshe idanu ina tuno yadda muke ragargazar soyayya a wajen aiki. Kowa kiran mu yake da Romeo and Juliet.. Da wannan tunanin na mike murmushi fadade a fuska ta na shige bandaki don yin wanka.

 

 

        *MASARAUTAR BASANNABAS*

 

Tunda aka tashi daga fada yake jin tamkar yaje amma ya kasa. Ya jima yana kallon sashen da zai sadaka da wajen mai babban daki (mahaifiyar sa) tamkar ya sauke yaje, Amma da yayi taku d’aya biyu zai aiwatar da hakan sai yaji tamkar an fusgo shi ta karfi an hana shi. Wani bangare na zuciar sa na aiyana masa abubuwa marasa dadi. Kallon wayar sa yayi ta gefen ido. Akwai abinda yakeson aiwatar wa amma ya rasa menene? Lokaci zuwa lokaci ya kan tuno sunayen Khaleel da Abdul a zuciar sa. Amma shin su waye su ma? Rike goshin sa yayi da tafin hannun sa na dama, Dakyar yai ajiyar zuciya kawai ya shiga gyara zaman alkyabbar jikin sa, Sakin labulen yayi.

 

Ya sauka daga stairs din sashen sa, Masu bashi kariya na biye da shi da fadawan sa suna take masa baya. Sai kirari ake masa. Ya shiga cikin fada idanun sa saqale da bakin shades dinsa. Wani parlorn sirri dake cikin fadar ya shiga ya zauna. Hannun sa na dama yasa ya dafe k’irjin sa yana taune kasan lips dinsa ta cikin rawani..

 

 “Yaa Rabbi….!”

 

Wani madanni ya danna, Sai ga bafaden sa Alhassan da Dr. Isma’el Sai raba idanuwa yake. Domin dik kudin ka da kamalar ka inde kazo gaban sarki Salman sai ka rissina. Ma’abocin ado da zatin sarauta. Me kwarjini da farin jini abun so ga kowa. Kwasar gaisuwa Dr. Isma’el yayi awajen Sarki Salmaan. Aka basu waje su biyu, dama parlorn soundproof ne ba’a iya jiyo komai dake wakana. Sannan babu cctv aciki.

 

Gaban Dr. Isma’el sai dukan tara tara yake. Ya sosa k’eyar sa yana numfarfashi da sauri.

 

Gyaran murya Sarki Salman yayi. Dr. Isma’el ya dago kansa sai kuma ya mayar saboda cikar idanun da sarkin ya masa. Gashi dai matashi yaro dashi amma sai kwarjini.

 

 “Allah ya karawa Sarki lapia…”

 

Izzar sarauta da kuma halitta irin ta sarki Salman na rashin son magana yasa ya jima kafin yace,

 

 “Ya….Mai jiki?”

 

 “Da sauki ranka ya dade. Taji sau’ki tamkar bata yi ciwo ba.”

 

“Alha….Alhasan ya gaya min komai. Kun yafe abunda aka kashe na asibitin ko..?”

 

 “Allah ya kara maka lapia. Yasa kafi haka! Allah yaja da zamanin ka. An kammala komai ranka ya dade. Ai lefi na ita yar wajena ce. Ina ita ina yiwa uban kowa tambaya a bainar jama’a? Amata afuwa karamar yarinya ce, Kuma sabon shiga ce a aikin nata.”

 

 “Ma….”

 

Shiru Sarki Salmaan yayi yana ayyana yadda zai fito da maganar,

 

 “Ma.. matar aure ce ne?”

 

“Ranka ya dade ba matar aure bace. Ba ta dai tsada tsayayye ba amma tanada manema sosai. (Tanada su ko?) Dr. ismail ya karasa fada yana mai tambayar kansa, Domin shi bai ma taba ganin tana zance ba. Bare yaganta da wani saurayi.

 

Jujjuya me ze fada Sarki Salmaan ya shiga yi. Shin ga zancen a bakin sa amma yanajin nauyin fada, Wai shi mighty Salmaan shi zai furta yana neman amincewar mace yau? Siririn Tsaki ya saki wanda har sai da Dr. Isma’il ya dan dago ya dube shi.

 

 “Idan babu damuwa… Zaka bani auren ta, ina da bukatar masu irin aikin ta a kusa dani. Amma idan har babu neman auren wani akanta, Domin neman aure akan aure haramun ne.”

 

Wani dindirus Dr. ismael yaji zancen, me kenan sarki yake nufi akan na bashi auran ta? Taya zai tambayi auran Dije bayan yasan wadanda suka fita a cikin duniyar nan. ‘Hadin Allah’ yaji zuciyar shi ta bashi amsa ganin dole yana bukatar hakan. Sai kuma wani farin ciki ya mamaye ransa, Yarasa me zeyi ma, Tamkar yayi tsalle ya rungume sarkin dan murna, Samun kansa yai cikin tsananin farin ciki, Wai Dijen sa ce yau Sarkin Basannabas yake neman auren ta. Allah kadiran Allah man yasha, tabbas wannan shine gata na biyu da zai yiwa Dije, wato ya aura mata mutum mai daraja da mutunci. Cike da tsantsar gamsuwa da amincewa yace.

 

 “Allah ya karawa sarki Lapia da kwanciyar hankali.. Khadija ‘ya ce awaje na. Mahaifiyar ta Kanwa ce agare ni. Marainiya ce uwa da uba duk sun rasu, Rikon ta ya dawo hannu na. Tabbas a yadda na sani Khadija babu neman auren kowa akanta, A matsayi na na mahaifin ta, Ranka ya dade, Na baka auren ta, Na baka damar auren Dije. Ina fatan hakan ya zamo alkairi a gare ku baki daya…”

 

Sarki Salman ya samu kansa cikin madaukakin farin ciki na jin an bashi auren Khadija, Yarinyar da yasan a yanzu duk duniya babu wandanda ta tsana kamar masarautar shi..

 

 “How sweet..? Beautiful soul….”

 

 “Masha Allah! Ranka ya dade magana kake?”

 

Sosa bayan rawanin kansa sarki Salmaan yayi, Yai saurin girgiza kai yana hade fuska tamkar ba shi yayi magana ba. Ya sake jan numfashi yana jin tamkar ana ingiza shi akan lamarin, wanda beyi tunanin shi ba ko kusa, wato kara aure bayan matarsa da suke tare, Ya numfasa tare da cewa Alhaji Isma’il.

 

“Ina son auren ya zama sirri, bana son maganar ta yadu a duniya. Abin da nake so kawai shine. Ka tanadi waliyanta, ni kuma ni zan zama waliyin kai na.”

 

“Duk abin da kace dai dai ne ranka ya dade, kuma Khadija yarinya ce mai tsantsar biyayya. Nasan ba zata watsa min kasa a ido ba, bare idan taji labarin kai ne zaka aure ta, nasan zata yi farin ciki tabbas.”

 

Sarki Salman ya yi shiru, duk da cewa yana cike da tsantsar farin cikin amincewar da aka yi masa, amman ba zai nuna ba saboda izzar sarauta.

 

“Idan babu damuwa, ina son ayi komai a cikin wata d’aya kacal.”

 

Cewar sarki Salman cikin nuna iko. Alhaji Isma’il ya sake dukawa tare da kai gaisuwa yace.

 

“Ko a yau kake son a yi, za a yi shi ranka ya dade da ikon Allah. Allah ya kaimu lokacin yasa a yi damu baki d’aya.”

 

Gyada kai kawai ya yi bai sake cewa komai ba. Alhaji Isma’il na fita daga wajan sarki Salman, kawai sarkin yaji wani irin muguwar faduwar gaba, cikin sauri ya dafe kirji yana rintsa ido tare da kiran sunan Allah. Dafe kai ya yi yana jin idanunsa suna neman rufewa, kamar wanda ake shirin zarewa rai. Tunani ya shiga yi na anya za a barshi ya yi wannan auran kuwa? Tabbas abubuwa da yawa suna shirin jagule masa, ta yadda yake ganin kamar ba zai iya warware su ba. Sai dai wani barin na zuciyar shi yana sake kwadai ta masa son yin auran sirrin ba tare da an sani ba har sai bayan an daura aure koda kuwa duniya zata ji……..

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 1

Advertisement  *KIBIYAR AJALI…..!!!!* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_            🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA…

KIBIYAR AJALI 13

Advertisement                   _13//KASBTSTW_     *BRITISH ENG LEARNING CENTRE*   Idanuwa na shiga zarewa a lokacin da…