KIBIYAR AJALI 16

Advertisement

 I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p

PG: 16

BOOK 2. 

BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻

Advertisements

*SAS*

Kishingid’e Sarki Salman yake yana duba ipad dinsa, Dawowar sa daga fada kenan ba jimawa, Yana danna ipad din yana cije lebe, Can ya dubi intercom din gaban sa, Ahankali tamkar mai jin ciwo haka ya matsa kusa da ita, Ya danna wani button ya kara a kunnen sa.

 “Yes…….Kizo yanzu ina neman ki.”

Yana gama magana ya katse batare da ya jira amsa ba.

 *KHADIJA….*

Ina kwance na jiyo karar wayar kan bed-site drawer dina, A dakile na dauka na kara a kunnena, Domin na fara jin bacci wallahi.

Advertisements

 “Sarkin takura..”

Na fada ina hararar wayar tamkar shi nake gani, Cike da b’acin rai na mike, Riga da wandon baccin jiki na na kalla, Hijabi me kauri na dora akan kayan na shige sashen nasa ta baya. Yana parlorn sa ya kwanta akan doguwar kujera yana kallon saman pop. Tamkar zai cinye ni haka ya shiga kallona tundaga sama na har izuwa kasa na.

 ….Dan iska…. Shi yana kallon ka yana wani jan kasan leben sa.

 “Gani…Barka da dare!”

“Barkan mu… Yar jarida. Kina lapia?”

 “Alhamdulillah..!”

Mu kai shiru gaba d’aya, Ni sai kara matse jiki na nake, Yanayin sanyin da ac ke bayarwa yamun yawa, Shi ko ajikin sa , Na lura yanason sanyi. Ganin shiru yayi yawa ga bacci inaji nace,

 “Yallabai… Gani”

 “Ohh… Dawo nan.” 

Na kalli inda yake nunamin da hannu na dan tabe fuska.

 “Nanma ya isa yallabai..”

 “Kar ki bari na maimata..”

Tashi nai na koma kusa dashi, Har ina jiyo kamshin turaren Alharamein din dake jikin sa, Na lumshe idanu na bude su ahankali,

 “Ina…… Ammi?”

Da sauri na juya ina kallon sa, Shin da gaske shine ya furta kalmar Ammi ko kuwa gizo nake. Ya sake maimatawa yana huramin idanu,

 “Tana nan… Dazu ma na fita n…”

“Kikaje ina bada izini na ba…?”

“Wajen Ammi naje na gaidata…”

 “Okayy…. Idan kika sake zuwa… Ki gaysheta, Ina gaysheta sosai. Kinji please.”

 “Insha Allah…!. Amma w..”

“Uhm! Menene..? Kiyi magana.. Ask your questions please.”

“Yaushe aka shiga tsakanin ku da Ammi..?”

Ajiyar zuciya ya sauke yana mai matse yatsun sa,

“Na manta wasu abubuwan.. Amma dai nasan na shaku da Ammi sosai, Duk kuwa da akwai kunyar dan fari da take mun.. Akwai shakuwa sosai a tsakanin mu. Tunda na tafi school har na gama na dora da msc dina babu ranar da bama vid call da Ammi. Bayan na dawo ma an fara shirye shiryen nada ni sarki a sashen ta na tare ina kwana, Kullum sai nayi kuka Saboda banason sarauta, Saboda banida Shekaru da yawa, Sannan banwani taba rike mukami na mulki ba, And again rayuwata a waje nayi ta. Banason shiga mutane sosai inada social phobia.. So bazan iya tuna komai ba, Nasan dai ranar wata jumu’ah na shiga gaysheta tana vid call da Khaleel.,

“Immediate brother na Khal.. Dr ne yana South Korea, Toh lokacin an kai su can cuz shida abdulqadeer acan sukai high school ma suka samu admission na medical school. Shi abdulqadeer pharmacist ne, Shi kuma Khal medical Doctor ne. So tana vid call dashi. Tacemin na karba mu gaysa.. Idan na gama na kira principal din su Abdullah mu gaysa da Abdullah, Saboda yana Kuka wai gida yakeson tahowa, Nide nasan na karbi wayar hannunta na fito waje don muyi magana da Khal.. Daganan bazan iya tuna ko munyi magana dashi ba, Ko na kira Abdullah din.. Wani yanayi na tsinci kai na a d’aki. Na samu jiri da zazzabi. Tunda ganan tamkar an shafemun tunanin Ammi da Abdullah da Khal.. Bansake sanin inda suke ba. Kinga wayar nan? Kusan kullum da sai na kalleta naita k’ok’arin tuno mema zanyi da ita? Sena fasa kawai.. Sai kwanan nan da hankali na ya dawo.. Na gano ashe wayan Ammi ne.. please ga wayar ki bata…”

Tausayin su ya kamani sosai. Allah sarki rayuwa, Lalle Idan kana raye zakaga abunda yafi k’arfin tunanin ka. To menene alfanun shiga tsakanin uwa da ‘yayanta..?

Ahankali na mika hannu na karbi wayar daya mikomin, Fara sol da ita. Shiru naga yayi kansa a sama ya dafe goshin sa da hannun sa na dama.

 “To kasan tsakanin ka dasu wambai kuwa.. Zaman mutinci kuke?”

 “Well.. Tun farko dama nasan basa so na. Suna mun zagwan kasa, Domin kiri kiri suke nuna jin haushin sarautar da aka bani. Saboda kowannen su ya cancanci ya gada.. Nasan maybe Gwaggo tabaki labari ko?”

 “Eh tayagamun komai…”

 “Wambai, Chiroma, Galadima.. Da yan tagwagar su duk nasan basa so na. Kuma harda sa hannun su a komai..”

“Su Mama Huwaila fa?”

 “Suma duk nasan akwai wani abu a kasa.. Look Khadija.. gaba d’aya masarautar nan kowannen su da irin muguntar sa. So Karki yadda da kowa. Harda ni.”

Na tabe baki. A zucia ta nace, To ai ba zama na zo yi ba dama. Ina ruwana da kai. 

 “Waziri fa..”

Shiru yai na tsawon lokaci kafin ya amsa ni.

 “Banajin wazirii yana mun komai..”

 “Meyasa kace haka? Saboda ya nuna yanason ka a fili? ..”

“No waziri gaskia baida matsala…Amma meyasa kika tambaye ni?”

“Kawai naga yadda yake nuna maka kauna akwai lauje cikin nadi..”

 “Meyasa kikace haka….Uhm?”

“Bayan kwana biyu da tafiyar ka… Na ganshi ya shisshiga sashen su Mama Huwaila.. Ni kuma alokacin ina zagaye ne ko zan ga wani abun suspicious.”

Ajiyar zuciya naga ya sauke.. Ahankali ya dora hannun sa kan nawa, Ya juyar da hannun izuwa tafin hannu na, yatsantsa yasa tamkar yana rubutu akan paper. Ya shiga rubutu ahankali.. Tsigar jiki na sai tashi take, Ahankali ya shiga rubuta kowane harafi d’aya bayan d’aya. Yana rubutawa yana kallo na.

 “Good work yar jarida… Tabbas waziri ba masoyi na bane.”

Da sauri na daga idanu na na kalle shi, Cikin tsantsar mamaki nace,

 “Kasani kaima..?”

Da sauri ya lumshe idanun sa ya bud’e alamun Eh.. Na sauke ajiyar zuciya ina taune kasan lebe na nima.

 “Kiba Ammi wayarta.. Na cire wancan sim din nasa wani. Ki briefing dinta akan komai dan Allah.”

 “Okay…”

Mik’ewa nai kawai zan tafi ya riko hannu na, Ban aune ba naji ya janyo ni na fada jikin sa, Ya rike ni sosai yadda bazan iya kwacewa ba, Saitin kunnena ya dora bakin sa.. 

 “Khadijaaaaaaaa.”

Har ga Allah Salman na neman susuta ni, Na had’iye kakkauran abunda ya tsayamun a wuya. 

“Ina zakije…Uhm”

Na shiga raba idanuwa ina matse hijabi na tamau.

 “Please ki yafemun… Nan kusa komai zai daidaita a tsakanin mu.”

Ganin zai susuta ni ban shirya ba na mike da sauri, Na tabe baki hade da matsawa nesa dashi,

 “Kamar yadda kace…. Na temake ka na bi diddigin makiyan ka bayan tafiyar ka. Nima ina rokon kayimun wata alfarma d’aya.”

Zubamin idanu yai yana kallo na. Na samu kai na da mika hannu na zare glass din fuskar sa, Subahanallahi! Allah yayi halitta. Kwayar idanun sa kadai ma abar kallo ce. Na shagala wajen binsa da kallo,

 “Shine alfarmar? Ciremun glasses?”

Zanyi magana kenan aka fara doko k’ofar sa. Na manta fa akwai shaheedah, Kodan ni ba wani rayuwar aure muke dashi ba sam mancewa nake. Da sauri na mike, Tashi yai ahankali yaja hannu na. Dakin kusada corridor ya bu’de muka shiga still yana rike da hannu na,

 “Bara mu gama magana da ita ko… Ki jira ni.”

 “Dan Allah bacci nake ji fa… Allah na fara bacci ka tashe ni dazu.”

Bugowa take sosai, Ahankali ya saki hannu na yanamun wani irin kallo.

 “Ki jira ni nace..”

Ficewa yai da sauri, Matsoraci kawai. 

Salman na futa ya budewa shaheeda kofa yana dafe da kansa,

 “Subhan’Allah…! Babe! Bakada Lapia ne? Meya faru.”

“Kai na ne… “

Sai sharaf ya zube akan kujera yana numfarfashi, Shaheeda jiki na bari ta matsa kusa dashi tana kallon sa, A hankali ta zura hannunta acikin d’ankwalin kanta ta zaro wani garin magani. 

 “Salman… Babe..! Kayi baccci?”

Ganin yayi bacci dagske ta dakko maganin jikin ta na bari, Ta zazzaga a hanyar da zai taka ya shiga master bedroom dinsa anan parlorn. Ya bude idanu ahankali yana kallon ta. Tana dawowa ya sauke numfashi yana gyara kwanciyar sa,

 “Ka tashi ..?”

“Na tashi.. Zazzabin ya sauka. Nagode sosai.”

“Godiar me fa? Ko ka ganni inata kallon ka?”

 “Noooo! Da kika tsaya har na tashi a bacci.”

 “Ohh.. anything for my love. Ka tashi kaje Kayi bacci a daki.”

 “Zanyi sallah tukun, Sai na kwanta.”

 “Karka kwanta a parlor, Saboda windows sunyi yawa iska, Karkai mura. Pls ka koma daki ka kwanta.”

“Insha Allah a daki zan kwana.”

“Okay.. Goodnight my love.”

Daga kai yayi, Ta mike ahankali ta sakar masa kiss a Kan sa. Murmushi kawai yayi mata. Amma zuciar shi nata mamakin ta, Wannan wacce irin cuta ce? Dama a cctv yaga sanda aka Kawo mata wasu kullin ledoji kenan duk na tsibbu ne kuma akan sa? Yayi mamakinta Kwarai, Shi yasa yayi alamun rashin Lapia Saboda ta aiwatar da komai agaban sa. Luckily ba dakin da Khadija take ba tasa, Khadija na dakin corridor. Ahankali ya mike ya shiga dakin da Khadija take.

Inata jiran sa har na fara bacci akan sofa, Dakyar na iya bude idanu na jin anbude kofa, Na mike da sauri ina sosa kai na,

 “Tatafi ai ko? Zan tafi nima please.”

 “Ai bamu gama magana ba….”

Tunawa nai da tabbas ban nemi alfarmar da nace zan roke shi ba,

 “Yauwa…”

Komawa nai na zauna, Shi kuma ya janyo kujerar mudubi ya zauna akai..

“Kamar yadda ka nemi alfarma awaje na.. Dama alkawari nima na dauka wa zuciata, Idan har komai ya daidaita.. Zan rokeka ka bani…”

Shiru Salman yai yana kallo na, Sai kikkifta idanu yake..

 “Zan baki me? Fadi komeye shi.”

“Zaka bani takarda ta.. Saboda inason naje nayi wani auren na fa….”

Ban karasa ba ya mike yana kallo na,

“Khadija…. Why…. ? Mena miki uhm? Dan Allah Kiyi hak’uri lokaci kawai na ce ki bani komai zai zama tarihi.. Amma saki fa..? Saki? B. Bazan iya ba gaskia.”

“Saboda me bazeyiwu ba? Idan ba zaka iya ba ni Zan dakko biron da paper na tayaka rubutawa. Look! Bafa auren nagani inaso mukayi ba.”

Jikin sa har ya fara rawa, Naja sirirn tsaki, wasu mazan mugayen yan yaudara ne. Dazu fa najiyoshi a parlor sunyi luf Shi da matarsa, amman dan bakin munafurci ni zai fara yiwa rawar jiki yanzu?

Ban aune ba na jiyo ya kamo hannu na, Ya zaunar dani kusa dashi,

 “Wa yagaya miki ba auren na gani inaso mukai ba?”

“Koma shi akai ai ni banga ni naso ba..So please a rabu ta ruwan sanyi.”

Salman yai murmushin gefen baki yana matse kansa. Ganin kamar yanayin sa na juyewa na tambayeshi,

 “Meyafaru..?”

 “Jiri nake ji.. Tsoro nake ji..”

“Tsoran me..?”

Beyi magana ba, Ya ri’ko hannu na yana nunamin wani abu kamar kasa tundaga Karshen carpet zuwa kofar dakin sa na biyu.

“What about it…”

“Shaheedah ce.”

 “Bangane ba.”

“Shaheeda ce ta Zuba, Ta duaka bacci ake.”

Na yamutsa fuska, Ina karewa wajen kallo, can na shiga store na dakko abun kwashe shara na jona na shiga cire su. 

Salman ganin bata gane komai akai ba, Sai ya sake langabar da kai.. Shi a Lalle baida lapia, 

 “Tsoro nake ji… Tamkar ana kiran sunana.”

“To ya kakeso na maka yanzu? Ni wallahi bacci nake ji.”

“Ki kwana anan.”

Na zare idanu ina jujjuya kai..

“Bana iya bacci sai akan gadona..”

“Yauwa.. Muje canma kawai Saboda tsoran nan nake.”

Badan baida Lapia ba dana dankara masa Allah ya isa. Nayi gaba abuna. Ina ganin Sanda ya mike shima ya biyo bayana, Ta kofar sirri muka shiga sashe na. Ina zuwa Na fada band’aki nayo wanka da alwala. Kan gado na haye bayan nai Addua. Sam banmasan inda Salman yake ba ko yana kasa ko Sama.

Shi kuwa Salman ya jima a bakin kofa, Ahankali ya turo kofar ya shiga, ganin ta yayi tayi dai dai akan gado tana bacci. Gashi sam dije bata iya kwanciya ba. Wata wawiyar kwanciya tai rigar baccin ta dage har Kan kirjinta ana ganowa. Salman yai murmushi yana tuno dazu, Ahankali ya karasa ya janye duvet din data rufe k’afarta,

 “Dazu aka hanani gani.. Gasu a arha..”

Ya jima yana kalle dije daga sama har kasa. Ya zare glasses din idanun sa akan bedsite drawer ya ya tottofa addu’oi, kafin ya rungumeta tsam a jikin sa tamkar Za’a kwaceta.. Cikin bacci Khadija taji an kwakwumeta ba shiri tashiga janye shi tana mita,

 “Meye haka… Dan Allah matsa.”

“Tsoro… Tsoro nake ji.”

Ahankali yake magana yana huramin iskar bakin sa a kunne na.

Bacci ne akai na, Don haka naja tsaki kawai na cigaba da bacci na ina kananun mita, Kyakkyawar runguma yai mata yana shafa tundaga gadon bayanta zuwa kwantaccen gashin ta…

 “I like everything about you… My very own wifey. Ina kaunar baby love. Nasan ba lalle ki gane yanzu ba. Amma nanda lokaci kalilan komai zai warware.”

Yana magana yana shinshina bayan kunnenta, strawberry Shower gel din datai wanka dashi yayi masa dadi. Cikin wawiyar kwanciyar datake sai gata ta juyo da fuskar ta, kanta a kirjin sa, hannunta d’aya akan cikin sa. Kafarta akan tasa. Da alama ta duaka bargo ne. Murmushi yai, Ya shiga kare mata kallo, Ya taba nan ya taba can. Daga karshe Ya janyo bargo ya rufe su. Bacci daddada yai awun gaba dashi shima.

_Asubah tagari.. Salmanul_Dijaaa❤️❤️_

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 27

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 22

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR AJALI…..!_…

KIBIYAR AJALI 20

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…