KIBIYAR AJALI 17-18

Advertisement

 

                   _*17/18_*

 

 

*MASARAUTAR BASANNABAS*

 

Bashi da wata dama ko karsashi da zai kaiwa wani kukansa bare a ashere mishi. Kiri-kiri yana son bayyana abu a zahirance amman sai ya kasa, yaji tamkar ana shake masa wuya. Tsaye yake jikin taga

yana hangen duk wani motsin masu yawo a can harabar gidan, sannu a hankali ya hango mahaifiyarsa tana tafiya jikin ta sanye da mayafi, wanda alama suka nuna daga wani wajen ta dawo. Salman ya dauke fuskar sa daga kallon ta tare da takawa a hankali yaje ya zauna daga kan kujerar da ya taso.

 

Advertisements

“Assalamu alaikum.”

 

Cikin ransa ya amsa be ce komai ba bare ya dago dan ganin wace ce, muryar ta kawai ta shaida masa cewar jakadiya ce.

 

“Allah ya taimaki sarkin sarakuna, an buga an barka mazan fama. Uwar gida kuma gimbiya tace a yi mata iso wajan ka.”

 

Kamar yace a’a saboda shi a yanzu yana da bukatar nazari akan abin da yake shirin yi na auran da zai yi, yana so ya zurfafa tunaninsa ta yadda zai yi ya ware inda zai sanya amaryar idan an daura aure an kawo ta gidan, saboda yasan dole azo a nemi muhallin da zai ajiye ta. Da yake Jakadiya tasan halinsa na shariya, hakan yasa ranta be baci ba har lokacin da ya ga dama yace mata.

 

“Kice bacci nake ji.”

 

Ta kuma russunawa tare da sunkuyar da kai cike da girmamawa tace.

 

Advertisements

“Gyaraaa kintse sarkin sarakuna, zanje na gaya mata kamar yadda kace.”

 

Shi dai be kuma cewa komai ba har ta fita daga dakin, yana zaune ya rasa wane irin tunani zai yi. Jakadiya ta kuma dawowa da alama ma dai ita kanta uwar gidan nashi tana bakin kofa dan yaga Jakadiyar ba ta jima da fita ba yaga ta dawo, yaja tsaki a cikin ransa, zuciyar shi tana zugi saboda wasu mutum biyu da kwakwalwarshi take ta son tuna masa ko su waye a gurin shi amman ya kasa tantance ainahin su.

 

“Allah ya ja da ran sarkin Basannabas, uwar gida tana neman afuwa dai akan son ganin nan naka. Tace kanta bisa wuya, ka tausaya ka bata damar shigowa ciki.”

 

Hannunsa kawai ya daga kuma Jakadiyar ta fahimta dan tashi kawai ta yi taje ta sanar da ita sai gata ta shigo. Tana shiga Jakadiya ta yi sauri ta nufi sashen Gimbiya Jaleela wato kishiyar mahaifiyar sarki Salman. Hango ta tayi tana sakkowa daga bene cikin shiga ta alfarma, tana hango Jakadiya ta kuma tsuke fuska dan dama bata sakar mata fuska duk kuwa da irin yadda munafincin da take kawowa daga lungu da sakon cikin masarautar.

 

“Takawarki lafiya farin cikin marigayi sarki Aliyu, uwar marayun masarautar Basannabas, farin ciki da walwalar bayin Basannabas. Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana uwar daki na mai share min kuka.”

 

Sai da tazo ta zauna ta gyara zama sannan ta kalli Jakadiya cike da iko tace.

 

“Jakadiya meke tafe dake? Ina fatan dai kin zo min da labarin da zai sanyaya min zuciya ta.”

 

“Ina neman afuwarki uwar daki na, sai dai wannan labarin da nazo miki dashi ban san yadda zaki dauke shi ba.”

 

“Ina jin ki Jakadiya.”

 

“Dama yanzu Gimbiya Shaheedah tasa nayi mata iso wajan maimartaba sarki, yanzu haka tana can gurin sa zasu yi ganawa ta musamman tsakanin su.”

 

A fusace Gimbiya Jaleela ta kalli Jakadiya tana hararata tace.

 

“Me nace miki game da cewa Salman sarki?”

 

“Ki gafarce ni Uwar daki na tuba nake Allah ya huci zuciyar ki, sha’afa nayi wallahi ki yafe min.”

 

“Shikenan amman ki kiyaye gaba. Ina so kuma ki binciko min abinda taje suka tattauna, bana kuma son kuskure kin sani dai.”

 

“Insha Allahu uwar daki na ba za a samu wani kuskure ba, Allah ya ja zamanin ki.”

 

Daga haka ta mike ta fita tana rawar jiki. Bata wuce ko’ina ba sai sashen Gimbiya Najwa wato kishiyar Gimbiya Jaleela, wace ita ce matar marigayi sarki Aliyu Salman ta uku, yar Galadima ce. Ita kuwa tana kishingide a tsakiyar katafaran parlorn ta, hadimanta suna ta faman yi mata fifita, wasu na matsa mata kafafuwa yayin da wata ke gefe tana yanka mata kayan marmari d’aya bayan d’aya tana sha. Gimbiya Najwa na ganin Jakadiya ta yi saurin sallamar hadiman nata, dan tasan tabbas labari ne ta kawo mata game da Sarki Salman ko Gimbiya Shaheedah ko kuma mahaifiyar sarki Salman d’in wato Gimbiya Sa’adatu.

 

Jakadiya daman tasan halayen ko wacce mata dake gidan, saboda duk itace munafukar su, wajan kai gulmar ko wacce a gurin d’aya. Tasan daman Gimbiya Najwa ba zata tambaye ta komai ba har sai idan ita ce ta fara yin magana, wani lokacin Jakadiya takan jinjinawa irin girman kanta da takamarta saboda kawai tana yar Galadima, da ace a yar gidan sarkin kacokam Allah ya yi ta bata san me zata yi ba, duk da cewa a wannan lokacin su Waziri da shi Galadiman sune suke jan ragamar sarautar Sarki Salman, sai abin da suka ce shi za’a yi.

 

“Na gaisheki ta gaban goshin marigayi sarki Aliyu… Jinjina da ban girma gareki shalelen Baba Galadima, uwa ga magajin sarki wato yarima Ilyas(junior). Nazo miki da wani labari.”

 

Kamar ba zata amsa ba tsawon lokaci, sai da ta mulu ta mulmule sannan ta kalli Jakadiya karo na biyu tace.

 

“Idan kin san maganar ba ingantacciya bace karki sanar dani, ki bari idan kin tabbatar da ingancinta, sai kizo ki gaya min.”

 

“Na kuma gaisheki ta gaban goshi, tabbas bani da gamsashiyar magana akan abin da nazo miki dashi. Kamar yadda kika ce, zan koma idan na gama tabbatar da ko menene zan dawo. Na barki lafiya, farin cikin yarima kuma sarkin gobe, shalele Ilyas.”

 

Tufa d’in dake hannunta taci gaba da ci ba tare da ta sake bi ta kan Jakadiya ba, saboda ita Gimbiya Najwa tana da wasu munafukan bayan Jakadiya, dan ita a cewar ta idan wata taga wani abun, wata be zama lalle ta gani ba. Hakan yasa ta rarraba kafa ta baza masu gano mata sirrikan duk wata mata dake cikin gidan. Shi yasa Galadima yafi waziri sanin duk wani abu da ya shafi Gimbiya Shaheeda da kuma sirrin mahaifiyar sarki Salman.

 

  Can kuma bangaran Sarki Salman da uwar gidan sa wato Gimbiya Shaheeda, tana shiga ta zauna gefen shi tana tsotsar alawar da take cikin bakin ta tace dashi.

 

“Wani lokacin kakan yi min abin da sam be dace ba a gaban kaskantattun mutane, wato hadimai. Ya za’ai kamar ni nace ina son yin magana da kai kace a ce min bacci kake yi? Karka manta ban da ni babu wacce zata iya zama da kai bayan kowa yasan cewar ba da kwan haihuwa, ba zaka iya bawa Basannabas magaji ba kamar yadda marigayi ya bar maka gadon mulkin sa wanda kake a kai yanzu.”

 

Jin kalamanta yasa ransa fara tafarfasa saboda zafin su da yaji, bata da wani abu da take yawan yi masa gori irin rashin haihuwar sa. Amman saboda tsabar shakkarta da yake yi sai bai ce mata komai ba har ta kuma yin magana.

 

“Ni wallahi kasan ba da ban soyayyar da nake yi maka ba, da tuni nasa ka sauwake min naje nayi wani auran na haihuwa. Amman saboda na san babu matar da zata iya auran ka yasa nake daurewa ina lallashi zuciya ta akan ta hakura ta zauna tare da kai.”

 

Ta yi shiru na dan wani lokaci, shi kuma wata irin tsanarta ce take sake zama sabowa a zuciyar shi. Shi be ki ta ce ya sauwake mata ba indai har tana da bukatar yin haka, baya jin komai a game da ita sai zallar shakka da son bin duk wani abu da take so. Kansa a kasa dan ko da ta shigo be dago ya kalleta ba sai ji ya yi tace.

 

“Honey dago ka kalle ni.”

 

Ta na rufa baki kuwa ya daga yana kallanta, ta yatsina fuska tare da mika hannu ta zare bakin glasses d’in idan shi yadda zata ganshi sosai.

 

“Haba Honey, ba na hanaka kallo na da wannan glasses d’in naka ba? Na yi na yi da kai ma ka dena saka baki amman ka kasa bari, idan ka sashi kamar wani tsohon makaho wanda bashi da d’an jagora.”

 

Da yasan wannan maganar ce zata kawo ta da duk yadda zai yi sai ya hana su hadu, sai dai ance rashin sani yafi dare duhu. Kuma idan da sabo yaci ace ya saba da duk wasu abubuwa da ake yi masa a masarautar. Ita kuwa kallon shi kawai take yi tana jin wata zazzafar kaunar shi, hakan ne yasa bata son taji ana cewa ya kara aure shi yasa take kuma rike shi ta hanyar da zuciyarta ta aminta.

 

“Sannan kullum nice nake nema ka kai babu wani abu da yake damunka. Ina tunanin rashin haihuwar nan taka tana da nasaba da rashin sha’awa da baka da ita. Ko kai kayi zaton sarakuna basa mu’amala da matan su?”

 

Salman ya yi shiru dan shi sam ba wani farin ciki yake ji ba idan suna yi. Shi kawai yana yi ne ko Allah zai sanya ya samu rahama, ya kuma fita a hakkin ta na aure. Ganin ba zai yi magana ba yasan yata tashi tana murmushi ta wani jujjuya ya masa kugu ya kawar da kai, ba burgeshi take yi ba, hasalima ji yake tamkar ya fashe da kuka dan haushi da takaicin abin da take yi. Tana fita ya sauke ajiyar zuciya tare da rintsa ido kawai ya hangi Dije tana ta yi masa murmushi a wajan fuskar shi. Sai ya samu kansa da kin bude idon yana jin wani dadi a yadda yake ganin ta. Kiran sallar magariba shine ya tayar dashi daga gurin, ya shiga toilet ya daura alwala daga nan ya shirya ya fito zuwa masallaci dan kagabar da sallah.

 

°°°°°°°° °°°°°°°°° °°°°°°°°°°°

 

Tun da ta idar da sallah ta mayar da goshinta kasa bata sake dagowa ba, addu’a kawai take yi tana zubar da hawaye. Cikin kaskantar da kai take gayawa Allah muradanta duk kuwa da cewa tasan yasan tana cikin halin bukatar taimakonsa. Sannu a hankali ta dago fuskarta sharkaf da hawaye, tasa bayan hannunta tana sharewa. Gimbiya Sa’adatu kenan wato mahaifiyar sarki Salman, mace mai tsantsar hakuri da juriya tare da kawar da kai.

 

D’an ta ne, amman ba ta da wani iko akan shi, daga nesa kawai suke hango junan su amman basa haduwa face to face saboda an riga an janye mata shi daga gareta.

 

°°°°°°°    °°°°°°°°     °°°°°°°

 

Kishingid’e gimbiya shaheeda take a doguwar kujera dake tafkeken parlorn ta na alfarma. Wanda komai na cikin parlorn kirar samfarin kayan sarauta ne wanda turawa kewa laqabi da ‘Royal design’. Kai hatta salular da ke saqale ajikin da bango itama ta Royal ce.

 

Bayinta biyu ne a zaune kowanne yana mata tausa a kafa d’aya d’aya. Sai lumshe idanu take ahankali tana mai cigaba da taunar tufar dake hannunta, Wanda take gutsira ahankali cikin k’asaita.

 

Wayar tace dake kusa da ita tayi haske alamar saqo ya shigo, Sai data mula tasha iska tukun sannan ta daga wayar ta duba. Ta jima kafin ta daga musu hannu alamar su dakata, Sannan ta mike ta gyara zaman wani hadadden mayafin jikin ta mai beza. Bayin guda biyu suka bi bayanta kowacce kanta a kasa.

 

Sashen su ta nufa, Dake dare ne, Tarwar masarautar take da hasken lantar ki. Tsuntsaye nata kuka. Shiga tayi cikin wani babban parlor. Duk sun hallara aciki, Kowacce tana hakimce a kujera tana jin kanta. Kallo d’aya zakai musu kasan manyan mata ne masu aji, Wanda ke watayawa a duniyar masu kudi.

 

Gaishe su tayi. Ta samu waje ta hakimce itama. Bayin dake wajen duk suka basu wuri. Babbar matar ta tsakiya dake hakimce ta mike kafafun ta akan center table itace tafara magana,

 

 “Shin ya sanar muku da halin da ake ciki kuwa….?”

 

“Hmm! Ki bari kawai.. Mun fara sanya fa. Yacemin kwana biyu ya kasa gane kansa.”

 

Cewar Haj Huwaila ta bawa Haj Jaleelah amsa tana tana jijjiga kafafu.

 

“Shin Gimbiya Shaheeda kin fara ganin alamun canji kuwa?”

 

Haj Najwa ta tambayi Gimbiya Shaheeda dake kallon su baki d’aya. Gimbiya Shaheeda taja majina tana jujjuya zobunan daham din hannun ta.

 

“Toh.. Gashi nan dai…. Ba wani matsala gaskia. Yanzu ma wanka nakeso nayi ayimin iso wajen sa.”

 

“Karki sakaci da maganin nan Gimbiya. Wallahi Malam ya rantse da abinda zai kashe shi wannan maganin babu na biyun sa..”

 

Haj Jaleela tace da Gimbiya Shaheeda data mike lokaci guda tana Yatsina fuska,

 

“Duk yadda ake ciki…”

 

Sallama ta musu ta dauki hanyar sashen ta. Kallo d’aya tayi wa sashen mai babban daki tayi gaba tana sake daure fuskar ta.

 

Su kuwa ko bayan fitar ta sa zancen ta suka yi a gaba. Sunata shewa suna tafawa. Tamkar ba kishiyoyi ba ada. Aminan juna ne na qut da qut.

 

Gimbiya Jaleela ce ta gyara zama tana faman jujjuya ido tace.

 

“Ni wallahi so nake a fara bawa mata sarauta a kasar nan. Ina ji a jiki na zan iya duk wani abu da ake yi a cikin sarauta. Kuma nayi mafarki nan gaba kadan mata zasu dawo sune suke jan ragamar mulkin masarautar Basannabas.”

 

Ta gama maganar tana dora kafa daya kan daya tare da juyawa ta kalli sauran one by one. Cike da tsantsar dariya irin ta rainin hankalin nan Gimbiya Najwa ta mike tsaye tare da yin taku daya biyu zuwa uku ta tsaya a tsakiyar su tana gyara kafadun rigar jikinta tace.

 

“Kwarai kuwa Hajjaju, ina jin kuma ni aka bawa damar karasa yin wannan daddadan mafarkin naki da kika fara. Domin kuwa ni na hango kai na akan wannan kujerar ta sarauniyar Basannabas. Kuma a cikin d’in bin halacci na har na baki mukamin Baba na, wato waziriya ta. Ke kuma..”

 

Ta Nuna Gimbiya Huwaila wato yar ciroma tare da cewa.

 

“Ke kuma na yi miki mukamin Baban Hajjaju Najwa, wato Galadima. Na san dai wan…..”

 

Bata karasa ba Gimbiya Najwa tayi saurin da katar da ita ta hanyar cewa.

 

“Ya isa dan Allah, wannan ai shirme ne. Idan zaku dawo cikin serious d’in ku toh ku dawo, amman ta ya zaku zauna kuna ta yi mana wasu zantuka na shirme. Yanzu mu maida hankali wajan ganin yarinyar nan ta yi aikin da muka bata, Salman d’an girman kai ne, ko uban shi be yi wannan jiji da kan ba wallahi.”

 

“Haka ne kam, dan naga kwanan nan itama ya fara yi mata gardama, juya dashi amman sai shigen fadin rai.”

 

Duk suka yi dariya tare da yin tafi da hannayensu. Gimbiya Huwaila ta ce.

 

“Sa’adatu ce ma ni take bani mamaki, matar nan Sam taki yadda da cewa yaran nan baya son ganin ta, amman kullum cikin wahalar da kanta take wajan koke koke da wasu addu’o’in ta na shirme. Ai gara ka yiwa kanka maganin matsalar ka, amman kace zaka jira ai sai ka dade, koma ka mutu baka cimma burin ka ba.”

 

“Ai Baba (Madaki) yace abu d’aya ne yasa shi barin matar nan. Shine baya daukar ta a matsayin mutun mai rai, amman da tuni yasa anyi shekara lahira.”

 

“Gaba d’aya manta ta nake a cikin tsarin rayuwa ta.”

 

Jaleela ta fada cikin yatsina fuska. Haka suka zauna suna ta shirya makircin su kamar yadda suka saba. Ita kuwa Sa’adatu tana sashen ta tana kukan zuci da na idaniya. Kuncin da take shiga wani lokacin har mutuwa take roko tazo ta dauketa saboda wahalar da ranta yake yi. Amman tasa a ranta komai daga Allah yake zuwa, yasan kuma lokacin da zai warware mata wannan masifar da take ciki.

 

Tsab ya yi shirin bacci, yaje ya kwanta akan gado sai gata itama ta shigo cikin shigar kayan bacci masu santsi gasu shara-shara. Gadon itama ta hau tare da rungume shi ya kawar da kai, tunda tasa hannunta ta shafi kirjinsa shikenan ya nemi nutsuwa ya rasa. Kansa ya yi girma yaji kamar an dora masa duniya da abinda ke cikin ta. Wani barin na zuciyar shi kuma yana kusanto masa ita akan ya yi mu’amala da shi.

 

Kafin kace menene ya firgice sun zama abu d’aya, koda suka dawo cikin hayyacin su wani gigitaccen bacci ne ya dauke shi. Ta tsaya tana kare masa kallo mai cike da fassarori kala-kala. Kanta ta dora saman kirjinsa take itama bacci ya dauke ta a jikinsa.

 

   Garin ya yi shar gwanin dadi, sarki Salman ya fito akan farin doki da aka kawata shi da ado mai daukar hankali. A hankali yake tafiya har ya isa wajan wani ruwa inda wata tsohowar mata tana durkushe sai kuka take yi. Ya tsaya tare da sakkowa yaje kusa da ita cikin sassanyar murya yake mata magana.

 

“Baiwar Allah lafiya? Me yasa ki kuka a cikin mulki na?”

 

Ba tare da ta wai go ba ta gyara yagaggen mayafin da ke jikin ta tana share hawaye tace.

 

“Yara na duk sun guje ni, ba su san gani na bare ganin fuskata.”

 

“Suna raye kuma?”

 

Tace,

 

“Ban sani ba ni, sai dai ina ji a jikina tabbas suna raye. Me ye amfanin yaran da zaka haifa da cikin ka amman su guje ka? Me ye amfanin wahalalliyar nakudar da zaka haifi yara amman su gaza sanya ka farin cikin rayuwa? Kaico da irin wannan duniyar mai cike da tsantsar hasara….”

 

Ta wai go a fuska sai kawai yaga fuskar mahaifiyarsa, ta riko kafafunsa ta riƙe gam tana cewa.

 

“Zan tafi, zan kuma yin nisa da yara na da suka kasa gane matsayina a gurin su. Ka tausaya min ka dawo min da yara na, gwara mu zauna cikin talauci tare da su akan su yi arzikin da za’a raba mu. Karka tafi ka bar ni ya shugaba, ka tuna yadda ake ji idan aka rasa wani bangare na jiki. Ka tausaya min ya……”

 

Sarki Salman dake kwance kan katafaran gadon shi, ga matarsa kwance a jikin sa, kawai sai ji ya yi ya tashi a gigice yana sakin wata firgitaacciyar kara. Jikin shi kuwa sharkaf kamar an tsamo tsumma daga cikin mai….

 

  *KHADIJA*

 

____Wajen Aisha kawata naje, Wadda muka yi British da ita, yanzu ta kai matakin lecturer a jami’a. Mun sha hira sosai kafin na dau hanyar dawowa gida. Ta babbani shawarwari sosai akan rayuwa, Da yadda zan cigaba da gudanar da ita. Kasancewar garin damina ne tuni hadari ya hadu aka shiga kwarara ruwa tamkar da bakin kwarya.

 

Gashi na sallami TK driver tun dazu nace yaje ba komai zan dawo idan na kammala. Adaidaita sahun da nake ciki sai tangadi take a titi tamkar zata kifar damu saboda yadda iskar damina ke kad’a ta. Ganin gamu ga gidan rediyon mu hakan yasa na tsaida shi na falfala da gudu na tsaya a rumfar motoci, Waya na lalubo na kira Mas’oud nasan shi kullum yana nan, Baya da day off Saboda kasancewar sa babban ma’aikaci awajen, Na sheda masa ina waje ruwa ya tsare ni. Cikin barin jiki kuwa sai gashi

 

Da lema a hannun sa ya karo yai saurin rufamin ita akai,

 

 “Sannu Habibaty.. Ya akai haka, Ina kika je?”

 

“Hmm bari dai Habiby.. Wai zuwa nayi na gayda Aisha da naje wankin kai, Kasan kusa da jami’ar sune shine na biya.”

 

“Ayyah sannu, Muje ciki ki huta, Dama wannan damina da ake marka marka..”

 

“Allah yasa mu wuce Lapia..”

 

Nace dashi, Muka shiga ciki, Kowa yagan mu sai ya tsokane mu, musanman ni. Wai na biyoshi wajen aiki na kasa hak’uri. Office dinsa muka shiga. Sai rawar sanyi nake.Rigar sanyi ya dakkomin acikin kayan custume da ake ajiyewa. Muka shiga hirar soyayya hankalin mu kwance,

 

 “Kyanta ace Ruwan nan da ake ni da ke muna matsayin mata da miji. Mezesa mu wani fito aiki.. Ai sai dai ragargazar soyayyah da..”

 

Katshe shi nayi. Domin sai ina taka masa birki, Kunya ce ke lullube ni duk sanda yai wadannan kalaman,

 

 “Wai love sai Yaushe zaka zo ka gayda Kawu daddy ne?”

 

“Zanzo Insha Allahu! Banason zuwa ne batare da komai ya kammala ba. Kinga akwai gini da kawo kudi da sauran su. “

 

 “Gini kuma love?”

 

“Oum waleeda gwara ace son samu komai na rayuwar da zamuyi ya zama na is ready . Banason muyi wahalalliyar rayuwa.”

 

Kullum dai zancen kenan. Na ka’da kai kawai ina mai mamakin kalaman sa. Ni fa wallahi Saboda rin k’aunar da nake masa ko lefe zan iya yafe masa .

 

“Shikenan Mine! Amman da ba sai ka wani wahalar da kanka ba, Ko da irin haya sai mu fara ko..?”

 

“Shi kenan Oum Waleed zan samu alhajin mu da maganar, Kinsan suna ganin Ya Haysam bai aure ba gani zasu yi nayi kankanta.”

 

Cuno baki nayi gaba na masa gatsine,

 

 “Ai. Ai.. Ni dai nai dai nima ba canai nima ayi auren ba. Kawai dai saboda Kawu daddy yasan da kai ne.”

 

 “Haba tawaje na.. Ai ke tawa ce. Nine mallakin gangar jikin ki da soyayyar ki Insha Allah. In Shaa Allahu zaki ji..”

 

Banbashi amsa ba saboda nasan yanzun sai ya kauce hanya. Mikewa nayi na saqale jakata. Ganin ruwan ya tsagaita.

 

 “Zan tafi gida…”

 

 “Okay muje na sauke ki..”

 

Gaba nayi yana biye dani abaya muka shiga mota ya tayar. Tunda ya fara tuki na juya masa baya ina kallon waje. Yanayi na damina gari yayi shar-shar dashi.

 

 “Oum Waleeda fushi ake dani..?”

 

 “Haba ni na isa? Kawai Ina kallon sarautar Allah ne.”

 

“Ina son ki.. Ina miki son so tawan..”

 

Rufe fuska ta nayi da tafin hannaye na da suka sha kunshi na sudan, Sunyi maroon gwanin sha’awa.

 

 “Lallen ki Yayi kyau…”

 

 “Godia nake Habiby..”

 

Har k’ofar gida ya kai ni, Dai dai lokacin da Kawu Daddy ya dawo Shima. Ganin na fito yasa Mas’oud fitowa Shima ya rissina ya gayshe da Kawu daddy daya futo da sauri da alama mantuwa yayi,

 

 “Kawu daddy sannu da zuwa..”

 

 “Yauwa Sannun mu Khadija..! “

 

“Yallabai Barka da rana…”

 

 “Barka kadai… Ya aiki?”

 

 “Alhamdulillah!”

 

Mas’oud ya bashi amsa yana sosa kai, Kawu daddy ya kalle ni ya kalle shi,

 

 “Kamar na san shi ko?”

 

 “Abokin aikinta ne ni yallabai..”

 

Cewar Mas’oud, Na juya na galla masa harara,

 

 “Abokin aiki kuma?”

 

Na tambaye shi ina hade girar sama data Kasa,

 

 “Oganta ne ni.. Naga garin da lema shine na sauke ta..”

 

Mas’oud ya bani amsa yana kallon Kawu daddy. Nayi k’wafa kawai ina galla masa harara,

 

“Ah Allah sarki, ai na gane ka yanzu. Kai ne mai jinyarta a asibiti. Angode sosai. Tukur driver baya nanne?”

 

 “Eh nace ya dawo gida dazun.”

 

Musabaha sukai da Kawu daddy ni kuma na shige cikin gida da sauri, Kawu na biye dani. Ya dauki brief case dina a parlor da alamun shi ya manta, Har ya kai kofa, Ya juyo,

 

 “Khadija..”

 

 “Na’am Kawu daddy..!”

 

 “Idan kin samu Lokaci zuwa gobe haka zamuyi magana Insha Allah.”

 

“Toh.. Kawu…daddy..”

 

Na bashi amsa a rarrabe saboda yadda cikina ya soma hautsinewa, Kodai ban kyauta bane yadda Mas’oud ke kawo ni gida? Wata zuciar tabani amsa da ‘Kwarai baki halacci ba Khadija. Driver sukutum guda da mota fa aka baki..

 

“Kawu kayi hak’uri ..”

 

“Kin cika Shirme! Wayace lefi ki kai? Magana kawai zamuyi ta hankali. Alkhairi ne In Shaa Allahu.”

 

Yana gama magana ya fice da sauri, Ni kuma na haye sama ina hada hanya. To maganar me zamuyi? Oho…..

 

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 1

Advertisement  *KIBIYAR AJALI…..!!!!* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_            🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA…

KIBIYAR AJALI 8

Advertisement   _*BABI NA: 8_*     _*Wattpad:missxoxo00_*                 ***   Advertisements “Hannu malama Mardiyya.”  …