KIBIYAR AJALI 17

Advertisement

 I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p

NANA HAFSATU❤️

BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻

PG:17

Advertisements

BOOK:2

*Da* asubah naji tamkar abu na mun yawo acikin jiki na, Firgigit na mike ina addua, Mezan gani? Hannuwan Salman ne dumu dumu acikin jiki na, Bansan sanda na furta sarata ta kauyen mu ba. 

“Kutumelesin kan babban balain durumin durbun… Meye haka..?”

Ahankali ya bude idanun sa, Dak’yar ya mike yana nonnokewa, Can ya shiga sosa keyar sa yana murmushi,

 “Kin tashi lapia….?”

“A’ah ba lapia ba. Ya ma za’ai ka wani tambaye ni ko na tashi lapia?”

Advertisements

Mik’ewa yai baice komi ba ya shige bandaki, Nasa hannuna akai na saki karar takaici. Ina jiyo sautin dariyar sa. Wani tunani nayi nai sauri na kalli jiki na, Komai yana nan, Sede kayana gaba d’aya sun tukwikwiye, 

“Shikenan ya kallemin jiki na a arha.”

Fitowa yayi, Da alama wanka yayi , Towel dina na wankin kai naga yana goge nasa kan yana murmushi. Muka ha’da idanu na zabga masa harara. Nemen hijabi nake da zan kare jiki na, Can na hango shi akan kujera.

“Dan mikomin hijabi na gashi can….”

Ba musu ya dakko yana sake yin wani Murmushin,Rankwafowa yayi har muna jiyo numfashin juna,

 “zawjat sabah alkhayr…”

Ya fada yana gyaramun gashi na daya zubo ta fuska ta. Na lura yana son gashi a rayuwar sa, Ai kuwa yaga idi dan shaheeda batada shi ni kuma ba zama nazo yi ba. 

 “Baki iya gaisuwa bane…?”

“Ina kwana?”

Na fada ina tabe baki na.. 

“’Ana bikhayrin. ‘anti?”

Yau yan larabcin ne suka tashi kenan.. Na matsa ahankali ina zura hijabi na, Na mike na shiga bandaki, Wankan nima nayo, Nayi alwala. Na cire kayan baccin na wulla acikin washing machine, Zura kai na nayi ta kofa ina kallon sa yana gyara zaman praying mat..

 “Kaga…”

Juyowa yai, Na nuna masa drawer da yatsana

“Dan Allah dan jehomin riga aciki..”

Mik’ewa yai ya bude yana kallon su, Ina ganin sanda ya dakko wata me shara shara,

 “Ba ita ba..”

“To zoki duaka da kan ki.”

“Yi hak’uri kadan ban me kauri.”

Me shara sharan ya dakko ya mikomin, Hannun sa da nawa suka gogi na juna, Na runtse idanu na, Da sauri na karba na koma ciki na zura na dora hijabi akai. Gaban drawer na matsa na dakko zani na dora akai. Sallah yajamu muka sallame atare. Ya daga hannu yana addua muka shafa atare.

Azkhar na koma gefe ina yi, Ina jiyo sautin nasa shima yana yi. Muka kammala a tare. Can karshen gado na koma zan kwanta ya kirawo ni..

 “Zo nan..”

“Bacci nake ji..”

“Zo nan mu gama magana se Kiyi.”

“Gani..”

Na koma nesa dashi na zauna,

“Magana zamuyi dake da sauri… Saboda zan shiga fada, Zan koma bangare na da wuri.”

 “Ai inde maganan jia ne nagama magana, Inason kabani takarda na.”

“Khadijaaaaa! Meyasa kike haka wai?”

Shiru nayi Saboda wani kwarjini daya mun. Ahankali ya matso kusa dani, Ya dora hannun sa kan nawa yana murzawa ahankali,

 “Nasan bakyaso na…. Kuma sigar da nabiyo ta neman auren ki sam ban kyauta ba. Ki yarda dani, Tun sanda na fara dora idanu na akan ki naji ina son ki, Zan iya ce miki banta’ba yiwa kowa irin kallon dana miki ba arayuwa ta, Love at first sight Khadijaa. I love you and your bravery.. So please ki sassauta mun hukuncin saki yayi tsauri, Zan dauki komi banda shi.. Anything for you! Uhibbuk kathirana ya Zawjati atika aleaziza..”

Shiru nayi kawai, Na ma rasa me zance wallahi, Can ta matse masa da son, Na bi son da gudu na kwarfe.  

“Kayi hak’uri.. Amma inada wanda… Muka gama alk.”

“Karki karasa dan Allah..! Wallahi wallahi k’aunar ki ta gama yawo acikin bargon jiki na. Khadijaa ban san so ba sai akan ki.. Nagaya miki tsoron taron mutane nake, Ko a gidah ki tambayi Ammi rarely ki ganni muna hira dasu Abdullah. Bana magana da yawa, Banmasan ya ake nake kwarara miki magana ba. Ki bani chance, Zan nuna miki yadda ake..”

“Duk naji..Amma ni kam Kayi hak’uri banda ra’ayin zama a masarautar nan.”

“Inde shine matsalan se na miki gida awani unguwan…”

“No… Bana ra’ayin zama da ka….”

Ban aune ba kawai naji ya dora tattausan leben sa kan nawa, Hannun sa d’aya yasa ya janyo ni na fada kirjin sa dake tashin k’amshi, Wani irin sumba ya shiga yimin wadda gaba d’aya ilahirin jiki na yai sanyi, Duk wata masifa danake shirin surfa masa sena nemeta na rasa, ya zare bakin sa ahankali yana kallona,

“Naji bakya so na…. Na kuma yadda nine me lefi. Amma please ki bari komai ya wuce, Na samu lapia tukun. Karki bari Ammi tagano cewar bakya sona, Zeyi breaking heart dinta… Amma ki rike wannan.. Ni Salman ina miki kauna marar gauraye, Bazan dena kaunar ki ba, Khadijaaa! You are an amazing person, I am glad that I found you. Without you, I don’t know how my world would be. You have totally transformed me. I would love to spend all my life with you. I love you soo much..”

Na juyar da kaina gefe saboda yadda yake shafa mun gashi wani yarrr nake ji. K’ok’ari kawai nake ina mazewa, Mik’ewa yai ahankali yana kallon agogon hannun sa,

 “Zan tafi na shirya.”

“Allah ya tsare.”

“Ameen Zawjati…! I love you..”

Futa yai yana murmushi, Ni kuma na koma gan gado Ina mai shafa labba na, Wannan gigitattan kiss sekace a film. Inata tunanin yadda Zan karbi takarda ta bacci yai awun gaba dani…

Shi kuwa Salman yana fita ya jingina da k’ofar dakin yana murmushi, Ai dai anyi me wuyar ya aureta, So shawo kanta ta zauna tare dashi bazai wahala ba. A haka ya koma sashen sa, Falaki ya shiga tayashi shiryawa zuwa fada… Ruwan tea kawai yasha sai cake guda d’aya..

*SASHEN GIMBIYA JALEELAH…*

Gaba dayan su su ukun suna hakimce a kujeru, Gimbiya Huwaila ta kishingid’e a doguwar kujera mai cin mutum uku, Najwa kuma ta yi wani zama itama na sarauta ta dora kafafunta akan tum-tum. Jaleelah kuma tana hakimce itama akan kujera ana mata kitso, Mai kitson na tsaye a haka take mata..

Hannu tasa tana tattaba kitson,

“Meye hakan? Sam bai kamu ba, Kalli wannan yayi gefe da yawa. Kunce duka nan bangaren ki sake wasu..”

Takarasa tana jan tsaki.. Jikin me kitson sai ‘bari yake yi.. Haka ta shiga kunce shi tana sake wani.

 “Ni kuwa akwai cigaba a turaren da muka yayyafa a sashen Salman na kwanaki dinnan? Sam banji ance ya kwanta ciwo ba.”

Gimbiya Huwaila ta tambaya tana mai cigaba da danna wayar dake hannun ta..

 “Gaskia dai kwanakin nan inata tunanin abun.. Ni fa har jakadiya na bigi ciki ta nuna ba abunda ya faru dashi. Kenan malamin nan ninke mu yai kome?”

Najwa ta bawa Huwaila amsa.

 “Anya kuwa..? Domin aikin na kan dutse akwai ci, Sai dai idan shaheeda ce ta batamana shirin..”

Cewar Jaleelah..

Gimbiya Huwaila taja dogon tsaki kafin tace,

“Ko d’aya makirar ba… Ummiyo (Hadimarta) Tacemin sau uku tana cin karo da Ita Zata shiga sashen sa’adatuh.. Y’ar wahala.”

“Y’ar wahalar gaske.. Ai kinji da aka turawa Salman list din kayan bikin su Munaya bece komai ba, Wambai yace a wajen yace ayi transferring kudin.”

 “Yo me zece Jaleelah? Ai sullutu daban yake. Kadan ma yagani.. Ni yanzu jira nake kawai asa yayi murabus, Abdulqadeer ya hau karagar mulki.. Koya kukace?” Cewar Huwaila.

 “Kibari kawai… Ai ranar da sai na zuba ruwa a kasa na sha.. Allah de ya kaimu, Kuma yakamata mu sake komawa kauyen nan. Domin naga alamun yarinyar nan da ya auro tsageriya ce, Duba fa kiga aikin sa akai akanta amma tamkar ba’ayi, Sai wani daga kai take..” Najwa ta k’arasa fada tana karkada kafadu..

 “Rabu da ita… Yadda tazo haka zata tafi.. Bara na koma sashe na.. Zanga likita saboda kai ya matsamin.”

Hajia Huwaila ta k’arasa fada tana gyara zaman laffayar jikin ta..

 “Okay Yaya… Allah kara lapia.”

Cewar Jaleelah 

“Okay! Sai kin dawo. Allah bada lapia.”

Najwa ta fad’a tana murmushi.

Bayan fucewar Gimbiya Huwaila, Su Najwa suka tasa fefenta a gaba,

“Munafuka… Babu fa inda zata je. Shirin su suke itada abdulqadeer.”

Cewar gimbiya Najwa tafada tana tabe fuska,

“Hmm ki bari kawai Hajjaju.. Ai nasan karya take yi, Yo wannan matar kanta kawai tasani. Danta ya kwaci gado ta fantama ita kadai. Mu zuba mugani.”

Haka suka yita gulmar gimbiya Huwaila, Suna mata zagon k’asa, Bayan ta tafi ba jimawa, Gimbiya Najwa tayiwa Jaleelah sallama itama tatafi.. Tana futa itama Jaleela tafara yi da ita, Ita dai mai kitso sai raba idanu take,

 ‘Yayan iska.. Wai ku masu ‘yaya maza ko? To ku zuba idanu kugani babu wacce ‘danta zai karbi ragamar mulkin basannabas…..”

*GIMBIYAA KHADIJAA*

Sashen Ammi na nufa bayan na tashi daga bacci, Acan naci abincin safe. Lokaci zuwa lokaci mukan taba hira da ita. Abdullah na gefe yana scrolling sunayen universities da zai zaba. Can ya mike ya haye sama.

Wayar dake gefen aljihun rigata samfarin A line na zaro na rissina na mika mata.. 

 “Ammi… Gashi Inji Salman yace yana gaydaki.. Kuma yana kewar ki sosai, Nan da lokaci kalilan zai zo wajen ki ya gayshe ki. Amma kafin sannan Wai ya canza miki sabon sim zakuyi magana ta ciki.”

Idanuwan Ammi suka kawo ruwa, Hannunta na rawa ta karba tana jujjuya wayar, Da alamun ta tuno wayar da kuma abunda yafaru ranar. 

“Yace bayason asan komai ya daidaita yanzu sai nan gaba zai bayyana komai idan ya gama binciken da yake.”

Sam Ammi batai magana ba sakamakon hawayen da take faman zubarwa, daga karshe ya zama kuka Sosa wanda ya saukar mata da mura. Mun jima a haka tana kukan farin ciki kafin tace dani,

 “Nagode Khadija.. Mungode Allah ya saka miki da alkhairi, Tabbas samun ki a sirika alkhairi ne, kin zamar mana wani haske na warwarar matsalolin mu. Allah ya biyaki da gidan aljanna Khadijaa. Nagode Nagode Nagode.“ Ahankali nace 

“Aamin..”

Ban wani jima ba na mike na mata sallama Zan tafi, Har na kai bakin kofa tace mun,

“Amma fa se kina dan takura masa akan abinci… Baya son cin abinci shi yasa ulcer tai masa mugun kamu…”

“Insha Allah Ammi zan dinga yi.”

Na sake mata sallama sannan na fice na koma sashe na ina kambama dattako irin nata. Allah sarki uwa da ‘da..  No wonder bana ganin yanacin abinci ko an kai masa, Ko yaushe yana fama da ciwon ciki.. Girgiza kai nayi na koma cikin sashe na. Kan gado na haye kawai, Sallah ce ke tadani na kuma sake kwanciya.

Banda juyi babu abinda nake yi akan gadon, Gaba d’aya tunanin dazu da asubah na shiga yi, Na sauke ajiyar zuciya, Can na rufe idanu na na kara lulawa duniyar tunani a haka bacci yai awun gaba dani.. Nide Ranar haka nayi bacci rabi da rabi, Da safe na shiga sashen Salman nan sarkin dogarai yake cemun sarki baya nan yayi tafiyar gaggawa tun jia da yamma, Banma sani ba. 

*WASHE—GARI*

A hankali na bude idanuna, kawai naga mutum a tsaye ya kura min ido ko kiftawa bayayi.

Nai saurin tashi zaune Ina kara bude ido, Sanye yake cikin jallabiya ruwan zuma, tayi masa masifar kyau. Bai ce min komai ba sai guri da ya samu ya zaune a gefen gado yana kuma bina da kallo ta cikin glasses din fuskarsa.

“Good morning… Bar..barka da dawowa.” 

Yaki amsawa sai cewa yai dani.

“Any news?”

Kamar ban fahimci abinda yake nufi ba, na sosa cikin idona Ina cewa.

“Na me fa?”

Ya juya yana kallon kan bedside drawer din dake kusa dashi, yasa hannu ya dauki jotter da biron da ya gani akai. Cikin sauri na yunkara zan kwace yasa daya hannun nasa tare da kamoni yana min kallon kurullah, na gane hakan ne ganin yadda ya janyo fuskata kusa da tashi.

“Ni ka bani abu na.”

“Baki aikin da na baki bako?”

Yayi maganar yana kokarin bude jotter din, still kuma yaki sakar min jiki na. Haushi ya sake kamani da sauri na fincike dan naga alamar idan bana yi da gaske zai Iya cin galaba a kaina, bayan kuma babu soyayyarsa ko kwayar zarra a cikin zuciya ta. Ina yi masa abubuwa ne kawai saboda alkawarin Gwaggo ta Fada dana karba na bada gudin mawa wajan ceto rayuwar su ba dan nafi kowa ba sai dai sunan da nake takawa a gareshi shine zai ba da damar isar da wani tallafin gare shi.

A hankali ya dinga bin bayanan da na dinga dauka kadan kadan na fara bincike akai, hakan ne ya shagalar dashi be sake bi ta kaina ba. Na zabga masa harara cikin zafin zuciya na tashi na nufi bathroom ina jin takaicin ganin yadda baya damuwa da tawa matsalar sai tashi. Ina shiga nasa key dan kar ma ina wanka ya biyo ni, nai kwanciya ta a cikin bathtub saboda na dad’e nasan idan ya gaji da jira na dole ya tashi ya tafi. Shi kuwa Salman yana zaune yana duba jotter din amman ya kasa gane abin da take nufi, sai ta fara tubutu tiyan-tiryan sai yaga ta goce ta rubuta wasu arbitration yadda ita kadai zata gane abin ta. Jin shiru bata fito ba gashi lokaci yana ta tafiya kuma zai je fada yasa shi tashi bayan ya bar mata dan note.

Sai da na tabbatar ya fita sannan nai wanka nayo alwala na fito, ina goge jikina da towel na hango pepper din akan gado na dauka tare da karantawa.

“Anjima ina nemanki 9:00pm.”

Tab’e baki nayi tare da yaga takardar na dauke jotter din naje na boye sannan na fara shirya kai na. Ina gamawa na sakko kasa na nufi kitchen inda ma’aikata na suke ta faman aiki cikin tsari da nutsuwa, duk suka gaishe ni na amsa musu cike da fara’a sannan duk suka fita, daman yawanci haka suke yi duk lokacin da na shigo kitchen din sai su koma waje saboda na fi son na samawa kai na abinda zanci saboda tsaro ba dan tsoro ba. Dan waken flour nayi sai green tea dana dafa ina gamawa na zuba nayo parlour hankali na kwance. Sai da na gama ci sannan na tashi na sake komawa bedroom na kuma yin nazarin da nake yi, daga karshe kuma na fito dan zuwa sashen Ammi.

Ina baro gate dina na hadu da su Wambai suna tafiya bayin su na take musu baya, nai kamar ban gansu ba saboda tun lokacin da naga sun shiga gurin su Gimbiya Najwah tare da basu wasu layoyi na tsane su, shakku ya shiga tsakani na dasu. Ina gaf da wucewa naji suna miko min gaisuwa wacce nasan ta munafinci ce, basa gashe dani sai sunga idanun jama’a da yawa saboda sun tsane ni.

“Ranki ya dade za a dan zaga masarauta ne?”

Sai na samu kai na da jin izza lokaci guda, hakan kuma ya bani damar buga musu tambayar da ta kusa dabar-barta su.

“Eh zan dan zagaya. Ku kunje gano iyali, ya aka baro su?”

“Wa? Mu wai ranki ya dad’e? A a wallahi can wajan sarkin dawakai mukaje mun tarar dokuna biyu sun mutu.”

“Ayya Allah ya tsare gaba, mai martaba ya sani kuwa?” 

Na tambaya cikin son Jin karin bayani dan Ina da yakinin ba zasu sanar mai ba idan ban sako musu zancen ba.

“Ah’ah’ah ai yanzu abin ya auku muka je, idan ya fito fada zamu sanar dashi.”

“Allah ya taimaka ya kara lafiya Baba Wambai da Baba Chiroma ko?” Nai alamar tambaya Dan na sake tabbatar da su waye.

“A’a Wambai ne da Galadima ba Chiroma bane.”

Cewar Wambai yana ta faman murmushin yake, mukai sallama suka wuce nima na tafi wajan Ammie. Su kuma suna yin nisa Galadima ya saki tsaki tare da gyara rawaninsa yace da Wambai.

“Banji dadi ba da ka tabbatar mata da cewa ni ne, naso ka barta a sunan ni Chiroma ne. Shegiyar yarinya ka bibiya bokayenta ba a kasar nan suke ba, dubi yadda muke b’arin kudi akan ta amman kamar muna yi akan iska haka aikin yake wucewa ba tare da komai ya same ta ba. Duk duniya a yanzu babu wacce na tsana sama da yarinyar can wallahi.”

“Rabu da ita ai idan tasan wata to bata San wata ba, zamu yi maganinta tun kafin wadanda zai auro su shigo. Karka ga yadda Humaira take masifar son Salmanu, amman shi be ma san tana yi ba taki ta bayyana masa saboda gudin wulakancinsa.”

“Kuma haka ne fa Wambai, wallahi idan muka samu yaran nan suka shiga daga ciki, ba wannan yarinyar ba kadai ba, hatta Shaheedah sai ta dawo karkashin mu.”

“Uhmmm-uhmmm Galadima, gwara dai mu dinga rage kiyayyar mu akan Shaheedah, kasan dai mahaifinta shi da kansa yake yiwa kansa duk wani tsibace-tsibbace a masarautarsa ta Bullo. Idan muka shiga gonarsu tabbas zamu Iya rasa mukaman mu ba mutunci ne dashi ba kasani. Gwara dai mu tsaya Iya Salmanun da ita wannan talakan takalak din matar da ya kwaso.”

Galadima ya jinjina kai da haka har suka karasa runfar da sauran yan majalisar suke suna jiran fitowar sarki Salman dan su karasa cikin fada.

Ni kuwa ina zuwa sashen Ammi na tarar da wasu matasan yan mata, ban gane su sam dan babu wacce na taba gani a cikin su. Na yi sallama duk suka juyo suna kallo na amman babu wacce ta amsa min sallama ta sai Ammi wacce ke zaune tayi kasa da kanta da alama ba mutanan kirki bane ba. Har na karasa kusa da Ammi babu wace tai min magana bare gaisuwa, hakan ya kuma girmama hasashena akan sanin su waye. Muka gaisa da Ammi cikin mutunci sai dai da ka ganta kasan ba ta cikin walwala.

“Baki kika yi ne Ammi?”

Kafin ta bani amsa naji muryar daya daga cikin yan matan tana cewa.

“Mu ya kamata mu tambaye ta bakuwa ce ke ko kuwa, dan bamu sanki ba a cikin masarautar Bassannabas.”

Murmushi na yi cikin rai na ina cewa kila jinin masarautar ne, dan naga Isa da kasaitar ta yi yawa. Amman dai ban ce komai ba saboda a gaban Ammi ne da na gaya musu abinda zai hana su yin walwala a yau.

“Munaya kuyi shiru dan Allah, wannan ko babu komai Yaya ce a gurin ku tunda matar shi ce.” Da sauri suka hada baki wajan furta.

“Wa…!?”

Nai saurin basu amsa dan naga Ammie tana jin nauyin furta sunan shi nace dasu cikin gadara.

“SAS, idan kuma baku gane ba ina nufin Sarki Salman Aliyu Salman. Nasan yanzu kun fahimce ni tsab. Kuma zaku gane ni kodan gaba.”

Duk sai suka bi juna da ido suna bude baki, na saki murmushi ganin yadda suke mamaki dan bamu taba haduwa dasu ba, basu sanni ba nima ban San su ba sai iyayen su kawai. Na dakko jarkar ruwan da na gani kusa da Ammi na bude tare da zuba mata cikin cup na mika mata ina cewa.

“Ammi sha ruwa ki kwanta, naga kamar har da bacci a idanunki.”

Naji dadi da bata musa min ba, ta karba Tasha na janyo mata pillow tasa kai tana lumshe idanuwa. Nai saurin mai da kallo na gurin su ina kare musu kallo, daga masu riga da wando sun dora wata munafukar after dress, sai masu dogayen riguna da suka bayyana surorin jikin su, na ce.

“Amman dai baki ne ku ko?”

“Ke dalla can bama san bariki kinji, mu zaki rainawa hankali dan kina matar juya da bai Iya ajiye magajinsa ba kamar yadda aka ajiye shi. Kin ganmu nan ko? Kakaf din mu jinin sarauta ne, jinin da yake yawo a mahudanar mijin naki, shine muma yake yawo a jikin mu, Kinga har gobe zamu Iya samun sarautar nan da yake kai.”

Na saki murmushi Ammi dai ba ta sake cewa komai ba dan taga nima dai-dai nake dasu, kuma Ina Iya yina wajan ganin ban furta abin da zai sa ta yi mamaki na ba sai dai su nayi su dinga jin kamar zasu tsire ni. Ganin naki magana yasa Baheeya yin magana, gata yar karama amman rashin kunya a bakinta kamar me, tace min.

“Kin yi shiru ko babu amsa?” Ina shafa fuska nace.

“Bani da time din magana daku yanzu, amman zaku Iya zuwa ku bincika wacece ni ta yadda ba zan dinga baku wahala ba wajan jiran amsoshin tambayoyin ku.” 

Carab Nadiya ta cabe zance.

“Kema kin zata yana haibuwa ne kika aure shi? Aunty Shaheedah fa har yanzu ta kasa haihuwa saboda ance shi bashi da lafiyar da zai haihu.”

Wannan karan mamaki ne ya cika ni, na kalleta ganin ta yar firit da ita amman wai har ta Iya yanko wadannan manyan zantukan. Na rike baki tare da kallonta nace.

“Ke yarinyar nan har kin fara zancen wanda yake haihuwa da wanda bayayi? A bakin wa kika ji cewar baya haihuwar?”

Ta murguda baki tana fari da idanuwa irin na rashin kunyar nan, su kuma sai faman jinjina mata suke yi. Sabeera ta mike tana dariya tana tafa hannaye tace.

“Toh karya tayi ne? Da yana haihuwa kila da yanzu Aunty Shaheedah tana da yaranta. Amman da yake juya ne kinji shi shiru, dama suma ba ta hanyar Allah aka samar da s…..”

Ban san lokacin da na tashi naje na shako wuyan ta ba, duk suka taso suma zasu shigar mata nai saurin juyowa Ina musu wani irin kallo mai cike da fita hayyaci, duk sai suka tsaya suna huci kamar wasu zaku na nace.

“Duk iskancin da zaku yi karku sake ku iskanta min miji, idan kuma ba haka ba zaku yi yin nadama marasa tarbiya kawai. Kuma ku tashi ku fita tunda ba sashen iyayen ku bane.”

Na sakar mata wuya na tsaya kuma Ina jiran su fita dan idan suka tsaya komai zai iya faruwa tsakanina dasu. Don basu sanni bane, Oganniya nake ta Gajiyalle mai yar hakiya.. Dijangala yar baffanta. Aikuwa suka fice suna ta zage-zage, naja tsaki tare da komawa na zauna raina a mugun bace. Ammi ta dinga lallashi na tana cewa na dena biye musu idan ba haka ba abubuwa zasu kara baci tsakanin mu da iyayen su. Da kyar na samu na iya hakura saboda taji dadi, amman a zuciya ta na kuduri aniyar sai na gyara musu zama a cikin masarautar nan, Bayan mun dan yi hira ne na tashi na koma sashe na…..

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

Asha hutun *Sunday* Lapia zafafa fans❤️❤️

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 21

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR…

KIBIYAR AJALI 16

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 16…

KIBIYAR AJALI 20

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 33

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…