KIBIYAR AJALI 18

Advertisement

 

_I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_

_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_

_A dear page goes to a dearest one.. Dear billyn Abdul… May you be forever blessed😍❤️kaunar kauna tawaje na.. 🧚🏻‍♂️_

_PG:18_

Advertisements

_BOOK:2_

*GIM. KHADIJAA*

   *Ina* shiga sashe na zauna a parlorn kasa ina kallon tv dake yi ita kadai. Can na canza channel din zuwa iqraa inda suke karatun alqur’ani. Takwas dai dai, Saura awa d’aya naje wajen Salman. Nagaji saboda da yar tazara tsakanin sashen da nake zuwa na Ammi. Kitchen na shiga na samu Na’imah amintacciyar hadimata da Gwaggo ta fada ta samamin. Na sata ta matsemun ruwan dankalin turawa guda d’aya, Na hada da ruwan lemon tsami d’aya shima. Zama nai a kitchen din na shafe fuskata dashi da kuma hannu na. Bazan manta ba Adda Maryama ce tabani sirrin yana gyaran fata sosai. Minti goma sha biyar yai na wanke da ruwa mai dumi, Sannan nayi wankan turare (bath khumrah) Banyi wata kwalliya ba, Na dai canza kaya na zuwa doguwar riga ja mai dogon hannu, Na yafa mayafin akai na, Turaruka masu sanyin kamshi na shashshafa: Shekha/Night oud/Danal banat) Na dan shafa man lebe kadan a baki na. 

Zama nai ina jiran lokaci ya cika, Yana cika na mike na shiga hannu na d’aya rike da jotter da na rubuta komai. Bakina dauke da sallama na shiga. Yana zaune akan dinning table hannu biyu ya dafe kumatunsa, Dagowa yai yana kallo na, Nai saurin saukar da kai na kasa. 

 “Barka da dare….”

“Barkan mu….Zawjati!”

Advertisements

 “Ga ni..”

 “Bismillah… Zo ki zauna.”

Mik’ewa yai ya janyo kujerar kusa dashi yana nuna min, Zama nai ina cije kasan lebe na, Saboda ciwon mara nakeyi nasan nan Kusa mai jar mota zai zo.

“Ina jinki… Naga kinyi abbreviating wasu words din.”

Bude jotter din nayi, Ina nuna masa daga inda nake zaune, Mikewa yai ahankali ya zagayo ta wajena, Ya saqalo wuyan sa saitin fuska ta. Cikin wata irin murya ya nuna wasu kalmomi,

 “Wadan nan fa…?”

Na shiga raba idanuwa, Na kasa magana 

“Uhm….Me suke nufi….? Khadijaaaa”

Ajiyar zuciya na sauke, Turaren jikin sa sai sani cikin wani yanayi yake. Ahankali cikin dauriya nace,

“ NSMHSHDSWDYAKGTB na nufin: Nace su Mama Huwaila sun hadu dasu waziri da yamma a kofar gabas ta bayi.”

“Nan fa….. Uh hummm.?”

Ya furta Uhum din cikin kunne na, Ba shiri na mike ina sosa kai na,

 “Zan tafi..”

“Ina zaki tafi?”

Ya tambaya yana daria wato yana sane kenan yasan abunda ya aikata.

“Zan koma inada abun yi..” 

“Ai nan dinma ba shirme kike ba, Assignment na baki kike presentation.”

“To naji.. Amma ka koma wajen ka ka zauna.. I..I..Idan aka tsaya akai na jiri nake.”

“Tsayawa nai akan ki…? Na dauka na dan rissina ko? Zo mu sake gwadawa.”

“Nooo.. dan Allah ka bari.”

“Toh naji zo ki zauna..”

Zama nayi, Meyakwan ya zauna awajen sa, Sai ya janyo kujerar ya sake matsowa gab dani, Kafafun mu na gogar na juna.

“Ina jinki…”

Bayani na shiga yi masa muryata sai rawa take, Shi kuma ya zuba tagumi yana kallo na kawai, Har wani lumshe idanu yake ya bude su akai na,

 “Na gama…”

“Bravo alaiki Zawjatiii…”

Mik’ewa nai zan tafi ya riko hannu na,

 “K’amshi kike yi…Me tafiyar da tunani na.”

Kwace hannu na na shiga yi ahankali ya mike shima ya janyo ni jikin sa, Na shiga janye jiki na ina tirjewa..

“Dan Allah ka bari…”

“Zawjatuk aleaziza .. rayihatuk jamila.. Kinsan me nace..uhm?”

Yana magana yana neman cire dankwalin kai na, Na zame hannun sa dak’yar ina hade rai,

 “Nace.. Dear wife! You smell nice.”

Shiru nai kawai nide ina sauraron sa, Ya hanani tafiya gashi duk na karar da k’arfi na.

“Khadijaaa… Dan Allah kiyi hak’uri.. Ki dena fushi dani. Kinji? Love.. pls.”

Yau da ace wanda nakeso ne kalaman nan suke fita daga bakin sa da nafu kowacce mace jin dadi. Amma kash, Sam bana jin sa a rai na. 

“Zan tafi.. Bacci nake ji.”

“Shikenan.. Sai da safe.”

Har na kai bakin kofa na juya tunawa da maganar Ammi..

“Kaci abinci kuwa..?”

Da sauri ya girgiza kansa alamar a’ah.

“Meyasa baka cin abinci ne? kamar wani k’aramin yaro.”

Murmushi kawai yayi yana kallo na,

 “Yanzu me kakeson ci?A dama maka oat? Ko porridge? Ko akwai abunda kakeso?”

Gyada kai yayi, Na zauna akan hannun kujera ina binsa da kallo,

“Me kakeso to…?”

“Ke… Ke nakeso Khadija.. You are all I want.”

Kikkifta idanu na shiga yi, Gashi a haka sam ba zaka ce daga bakinsa maganganun nan suke fita ba. Hade rai na d’anyi Ina matsa yatsun hannu na,

“Abinci nake magana.”

“Nima shi nake fada ai… Ko baki gane magana na ba.”

Mik’ewa nai kawai na shiga kitchen, Babu abunda babu, Don haka na hada masa shayi me kauri na kawo masa, Na koma na jima ina aiki kafin na fito da dankalin turawa da kwai sai yar sauce ta kaza. 

“Gashi nan bismillah fara ci. Ammi ta damu sosai, Dan Allah ka dinga cin abinci. Kaji?”

“Ni ban iya zama na ci abinci da kai na bane…”

Na gwalalo idanu tunawa da shi din sarki ne sai kuma na mayar da idanun ina tabe baki,

“Saka suke agaba kaci…? Fadawan naka?”

Murmushi yai kawai yana langabar da kai kamar wani karamin yaro…

“Ki bani da kan ki… Saboda Idan kika tashi ma ba iya ci zanyi ba kasa Zan sauka abuna kawai.”

“Kai da cikin naka..?”

Ya gyad’a Kai yana ko’karin tashi, Nai saurin komawa gaban sa ina masa Kallon sama da kasa,

“Toh Ai kuwa dole ka koya cin abinci, Katoto da kai kamar wani baby..”

“To ai babyn ki ne… “

Nide shiru nayi, Naje wajen sink na wanke hannaye na tas, Sannan na dawo na tsugunna agaban sa,

 “Toh sakko..”

Sakkowa yai kamar wani yaro yana tankwashe kafafu yadda nayi, 

“Bude bakin…. Haaaaa”

Budewa yai ahankali, Na debo dankalin na hada da sauce na cusa masa a bakin, Yana ci yana yanga a haka na gama bashi, Ina hada masa da tea. Lomar karshe ma haka na sa masa abaki ya rike hannun, Yatsuna dana debo dankalin suna cikin bakin sa,

“Sakarmun yatsuna mana…”

Meyakwan ya sakar mun seya shiga lashe su ahankali, Sekace hannu na ne dankalin. Kamar hannun sa haka ya sude su tas yana murmushi. Zanyi magana ya rigani,

“Sunnah ne lashe yatsu idan an gama cinye abinci.”

Ji wani renin hankali wanda ba’atabamun shi ba ko a durbun.

“To ai ba hannun ka bane na wane..”

“Kai da kaya ai mallakar wuya ne. Abincin nan yayi dadi. Gobe ma shi zaki mun.”

Wani kallo nayi masa na debe kwanukan na kai kitchen. Tashi yai shima ya nufi sink yana kuskure bakin sa da mouthwash. Salman ba dai tsafta ba. Komai nashi tsatsaf. 

“To ni zan tafi s…..”

Ban karasa ba, Sakamakon bugun kofar sashen sa da aka shiga yi, Hayaniyar su Mama Huwaila ne, Tamkar zasu fasa kofar, Ina jiyo dogarai na basu hak’uri amma sunki denawa. Wani madanni ya danna naga kofar kasan ta bude, Ta window na hango su da yawa sun shigo ciki suna hayaniya. Nasan dai akan dazu ne, Don haka ko ajiki na, Na samu kujera na zauna ina karkada kafafu,

“Wannan hayaniyar tawa ce… Babu ruwanka, Ni da su Munaya ne, Naga zasu tabo ka da Ammi shine fa nima na nuna musu ba tsoro ne dani ba, Na shake wuyan sabeera take ko sabeena…”

Zare idanu yayi, Na sheke da dariya kawai ina jujjuya agogon hannu na,

“Sun kai ni karshe ne.. Oganniya nake ta Gajiyalle mai yar hakiya… Sanyi nayi wallahi.”

Zai yi magana kenan suka banko kofar, Tuni ya sauya fuskar sa izuwa dolo yana jujjuya idanu,

“Mama barkan ku da dare.”

“Dallah gafaracan… Sullutu kawai, k’aramar Yarinya ta tsare ka agaba tana maka dabaru. Dazu dazun nan ta shake wa yaran nan wuya, Ta musu dukan kawo wuka, Kalli jini a dantsen Munaya, Saboda tsabar mugunta taga saura sati d’aya bikinta.”

Kasa jure jin Sharrin su nayi, Na mike ina tafa hannaye,

“Kai Mama H.. Yo badan kin kusa jika dani ba ai da nace Allah ya sakamun.”

“Kai Kai Kai Kai… Ke Kinsan wa kike gayawa haka kuwa?”

Cewar Munaya.

“Dakata ke kuma can daya … Mama Huwaila ce, Kina wani tashin jijiyoyin wuya ai nasan ba ita ta haife ki ba, ki bari sabeera ‘yarta tayi magana.”

“Ke ni kike gayawa magana..?”

“Ah haba Mama H.. Ni na isa.. Ko sunan ki bakiga na kasa karasa fada ba? Gani nayi duk garin nan waye baisan mai girma chiroma ba, tsatson sarki ismaila rabo, wato jika na farko ga masekiri tajiri.. Allah dai ya Kara miki lapia.”

Ina kallon sanda tayi murmushi tana jin dadi, Kunsan yan sarauta da son girma da kasaita. Ta kasa cewa komai. Gimbiya jaleela taja tsaki tana karasowa kusa dani,

“Akan me… Zaki daga hannun ki ki dora akan fatar yaran nan.. Shin wacece ke? Me kike ji dashi?”

“Haba Mama Jaleelah! Banji dadi ba da kika d’auki wasan mu dasu gaske. Ya za’ai na sa hannu na dake su? Kinji Allah wallahi bandaki kowacce ba. Idan Karya nake dan Allah su rantse da qur’ani gashi nan. Allah ya kara miki lapia, Ai ko dan darajar waziri ba na soma haka ba.”

Shiru Gim. Jaleelah tayi tana kallon su Munaya, Su kuma na tabbatar saboda nace su rantse da qur’ani ne shysa sukai shiru. Kafin Gimbiya Najwa tayi magana na rigata,

“Ranki ya dade barka da dare…Tabbas sai yau na ga ainihin kamar ku da mai girma galadima, Kada na cika ku da surutu, Nadiya yarki naga batada hayaniya ko ita Zata fa’di yadda komai ya kasance. Kuma da zasu fadi gaskia ma.. Su suka takalo komai, Suna cewa ai shaheeda kaza kaza. Gasu idan nayi karya. Amma nasan basu fada muku dai dai bane da da girman ku ba zaku taho nan da daren nan ba, Domin bantaba ganin hakan tafaru ba. Ni zuwa nayi naga jikin sa, Domin kusan kwana nawa ance bayacin abinci, Kuma yana surutai da daddare, Shine nazo yaketa kira na da shaheeda, Tashin da zanyi na tafi kenan kuka shigo.”

Sai kuma suka shiga kallon kallo, A kunyace kowacce ta kwashi jikin ta suka fara fita,

“Munaya… Karki manta a aikomin da kati da dan yawa pls inada gayya.”

Harara ta dankaramin ta fice, Na zube akan kujera ina kwasar dariya.

“Nice moves….Zawjati!”

“Moves ai sai kai… Lalle ka iya acting. “

“Mugayen mutane ne.. Sai kana takatsantsan, Ka samu ka gama komai naka ahankali. Bara na gaya miki komai nasu a takaice.”

Ahankali kuma a nutse ya shiga gayamun irin wahalhalun da yasha a hannun su, Da yadda ya maida kansa soko saboda samawa kansa da mahaifiyar sa lapia. Ajiyar zuciya na sauke bayan ya gama gayamun nace,

“Gaskia na yadda ba Allah a aran su. Domin kaga wahalar danasha kuwa nima? Suka sakarmun da jini na dauka na al’adah ne, Suka sani firgici da daddare na kasa bacci, Ga tsoron masarautar dana dinga yi, Har wani wari Suka sa nake ji ni kadai.. Wasu abubuwan ma na manta, Amma kam nasha wahala.”

“Kiyi hak’uri please.. Insha Allah da komai ya wuce zamu ji dad’in rayuwar mu.”

“Kayi hak’uri… Amman gaskia banda ra’ayin zama acikin masarautar nan…”

Zeyi magana na sake katse shi,

“Banda ra’ayin zama da kai… Da masarautar. Dan Allah ka sawwakemun na tafi. Dan Allah”

“Khadijaaa… Kin dauka na aure ki ne kawai saboda ki kawo karshen matsalolin mu? Wait duk abunnan haka kika dauka ko? Shin me kikeso nayi na ki tabbatar kaunar ki ce tasa na aure ki..? Should I beg on my knees? Wait dole nema.”

Banyi aune ba naga ya zuba gwiwoyin sa ak’asa yana kallo na, Hannun sa yasa ya riko nawa hannayen yana mun wani kallo dana kasa fassara shi,

“Zawjati aleazizat , ‘uhibukkthyraan. wana tazawajtuk lanani ahbabtuk kathira. wala ‘astatie takhayul hayaati bidunik fiha… Yes dear wife, Ina kaunar ki.. Sannan na aure ki saboda ina sonki, Rayuwa ta zata zama wata iri idan babu ke cikin ta… Khadijaaa ki bani dama na nuna miki kaunar da nake miki.”

Gaba d’aya kalaman sa sai suka shiga rudamun ciki ma, Da alamun sun wa kwakwalwata yawa, Ga kwadan salad danaci da alama ya fara aiki shima, Wata gudawa ta matso ni, Ciki na ya shiga kokarin bada iska, Mik’ewa nai zan gudu ya riko hannu na, Lalle gayen nan besan mayuwacin halin da nake ciki bane. 

“Kin yadda…? Kin yadda zaki zauna da ni?”

Kai na shiga juyawa alamun a’ah, Don ko awani hali nake ciki banajin Zan yadda. 

“Tohm shikenan bazan takura ki ba… Amma ki shirya zuwa na gobe, Zan zo mu fara magana ta hankali dake. Zanzo as Salman ba sarki Salman ba. Ina neman yarjewar ki… Kin yadda?”

Yadda ciki na ya murda yasa nai hanzarin daga kai alamun na yadda yazo. Da sauri na yakice hannun sa na fice da sauri, Ina tunanin inde yana sauraran tafiya ta, To na tabbata ya jiyo bada iskar dana dinga yi, Idanuwa na a rufe haka na karasa sashe na, Na shige bandaki da sauri. 

GIM. SHAHEEDAH!

Yawo ta shiga yi da waya a kunnenta tana karkada hannu,

“No hajjaju, Da sauri nakeso, Hajjaju idan ba’a hanzarta ba to zamana a masarautar nan yazo karshe, Domin asiri na dole ya tonu hajjaju. Na yadda dagske auratayya bata taba shiga tsakanin su ba, Amma yanzu fa? Kina tunanin zatai ta zama ne batare da ta bukace shi ba, Shima duk da juya masa tunanin da ake ai dole wani lokacin ya kasa control. Hajjaju I take God beg you.. A shafe gaban ta gaba d’aya, Koda yaje kawai ya nemi hanyar ya rasa, Ashafe gaban uhm uhm Khadija.. Pls. I hate her, I can’t stand her hajjaju. Auren yarinyar nan da zamanta a masarautar nan wallahi har yau nakasa cikakken bacci. Wani irin shegen boka ta samu da alama, Ana aiki aiki bayayi.. Hajjaju hak’uri na ya kare gaskia. Kinsan muddin auratayya ta shiga tsakanin su, Idan aka samu ciki Shikenan hajjaju komai zai bayyana, Bani ba.. Har ku seta shafe ku. Kowa ma in general… .”

Magana take cikin fada da sauri, Gaba d’aya tamkar bata hayyacinta, Tanayi tana daga hannu,

“Nooo Hajjaju… Idan har baze iya shafe gabanta ba, Idan ya isa cikakken boka ya hallakata kawai. Naji zanyi duk abunda yace, Ya rabata da iska yafi komai sauki.” 

Tana gamawa tai culli da wayar tana sakin kara, Hade da jijjiga diddigaggen gashin kanta da tsabar tashin hankali ta manta da gyaran sa.

    *Salman* dake dakin sirrin sa yana kallon ta ya tsaya da biro a bakin sa, Baya sauraron me take cewa amma ya tabbatar maganar sa da Khadija takeyi Saboda yadda yaga labbanta na furtawa, Yayi zooming dai dai bakinta yana karantar haruffan dake futa daga gare su. 

Juyawa yai d’ayar computer dake gaban sa yana kallon Khadija ta ciki, Ta canza kaya zuwa na bacci tana taje kwantaccen gashin kanta na fulanin usul. Lumshe idanu yai ya bude su akanta, Abubuwa da yawa yake ayyanawa akanta.. Gashi tak’i bashi hadin kai, Tabbas daga gareta ne komai zai warware, Amma yaga ta kasa yadda dashi, Ajiyar zuciya ya sauke yana kamo lebensa na kasa yana tsotsa a hankali. 

Abubuwa gaba d’aya sun taru sun masa yawa, Amma yadda Khadija taki yarda dashi ne yafi daga masa hankali, Gaba d’aya daren nan kafin ya kwanta bacci, Tunanin kalaman da zai kwarara mata gobe ya shiga nazari, Ciki harda taimakon Internet. 

______

…Wai cakwakiya, Tawan ta abdul yau dai nima bara nayi ta taki: Man Kai na ya malale 😂💔 Sai dai nace.. Asubah tagari… Salmanul… Dija😍❤️

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

Asha hutun *Sunday* Lapia zafafa fans❤️❤️

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 29

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…

KIBIYAR AJALI 21

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR…

KIBIYAR AJALI 20

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 22

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR AJALI…..!_…