KIBIYAR AJALI 19

Advertisement

 

1___9*

 

_Zakuga canjin sunan masarauta daga BARNABAS… zuwa BASANNABAS. Ko ince tun d’and’ano ma na canza. Na manta ban sanar ba.. My baddd! So dai komai yana bukatar sanarwa. Bayan nayi

bincike nagano BARNABAS. Wani suna ne ko ince abu ne daya danganci ma’abota littafi. Sunan yazo acikin bible ma sunce: The Gospel of Barnabas is a book depicting the life of Jesus😅so BARNABAS din Joseph dinsu ne acikin bible.. To avoid consequences 😂💔salin alin se muka koma da BASANNABAS. Duk kuwa da kirkirarren labari ne gara a canza din🤤 case closed ko? .. To acigaba da gashi🤗😉_

 

*MASARAUTAR BASANNABAS*

 

 

Advertisements

     *Yadda* taga yana ta waige waige kamar yana neman wani abu a kusurwoyin dakin yasa itama ta tsorata tare da rike shi. Nan take taji ya yi wancakali da ita yana kuka mai firgitarwa, hannayensa dafe a kai yana ihu. Tabbas akwai abin da yake damun sarki Salman wanda ta kasa fahimta, da tana tunanin ko maganin da tasa masa a cikin pillow ne, wanda su Gimbiya Najwa suka bata suka umarce ta da ta sanya masa, ko shine yasa shi yin wannan abun cikin talatainin dare? Babu mai ba ta wannan amsa, har sai taji abin da ya sanya shi yin wannan abun.

 

Gimbiya Shaheeda ta riko gaban sleeping dress d’in ta da botiran suke a bude, ta sake matsowa kusa da shi a tsorace dan gaba daya ya canza sai faman cije baki yake yi da hakoransa. Leka idanunsa tayi taga yana zubar da hawaye, abin da ta dade bata gani ba a tare da shi. Sai ta marairaice tana share masa kwallar saman kirjinsa, murya a sanyaye ta fara masa magana.

 

“Na tsorata da ganin ka cikin wannan yanayin, nasan mafarki kayi, kuma da alama bashi da dadi duba da yadda kake zubar da hawaye. Shin me ka gani a cikin mafarkin naka?”

 

Ya yi shiru ba tare da ya kalleta ba, ga wani irin azababban sanyi da yaji yana huda duk wata kofar gashi dake jikin shi. Zare hannunsa ya yi daga rikon da ta yi masa, ya janyo jarkar ruwa tare da budewa ya kafa kai yana sha. Tun da ya fara sha bai sauke ba sai da ya kusa shanyewa taji ya ja wani dogon numfashi tare da saukewa yana lumshe ido.

 

“Ko mafarkin Ammie ka yi?”

 

Sai tambayar ta ta tayi matukar daure masa kai, ya dago tare da kallon ta da jajayen idanunsa. Take yaji wani faduwar gaba, sai ya sunkuyar da fuska yana girgiza mata kai.

 

Advertisements

“Idan mafarkin ta kake yi ya kamata ka dena, domin Ammie sam bata kaunarka. Ka manta sanda za’a nada ka matsayin sarkin Basannabas ita tazo ta dinga gayawa mutane cewar kai juya ne baka haihuwa kar a baka? Ka manta?”

 

Salman ya yi shiru kafin daga bisani ya daga kai alamar haka aka yi. Shaheeda ta yi murmushi sannan ta sake matsawa jikin shi ta shige tana faman shafa shi, cikin tsantsar makirci tace masa.

 

“To ka dena damuwa da duk wanda be damu da san ganin abinda Allah ne ya mallaka maka shi. Ni zan kasan ce da kai a duk yanayin da kake ciki, zafi rana da damuna ba zan taba rabuwa da kai ba.”

 

Cikin matukar farin ciki Salman ya jinjina kai, sai kuma ya matsa ya kwanta akan pillow still tana jikin shi sai lailaya shi take kamar ta samu jariri sabuwar haihuwa. Daga haka ya manta da wannan mafarkin da ya yi da mahaifiyar shi, bacci ya kuma daukar shi. Gimbiya Shaheeda ta mike zaune lokacin da ta tabbatar da cewa ya yi bacci da gaske. Sakkowa ta yi daga kan gadon ta ciro wani farin zare daga cikin gashin kanta tana kare masa gani kafin ta yi murmushi wanda ita kadai ce tasan matsayin shi.

 

Boyewa tayi sannan ta shiga toilet ta tsarkake jikinta ta fito ta shirya ta kwanta tana jin farin ciki. Basu farka ba sai wajan karfe shida, ya bude ido da kyar sai yaga Shaheeda a kusa da shi, ya fara duba jikin shi. Gabaki d’aya bai san sunyi wani abu ba sai yanzu da yaga yanayin shi, ya duba agogo yaga lokacin sallah har ya wuce. Da sauri ya tashi ya tashe ta sai tace masa ai tayi wanka tun dare. Yaji haushi kuwa sai dai ko a fuska kasa nunawa ya yi, kawai ya wuce bathroom shima ranshi a bace.

 

*KHADIJA (Dije)…..*

 

Tun da na idar da sallah nake jiran kiran kawu daddy da yace zai ganni da anjima amma naji shiru, sai na fito daga daki naje parlor na koma kitchen amman shiru yana daki be fito ba. Hakura na yi na koma daki na zauna ina duba wani littafi. Kamar jira ake na zauna sai ga kiran shi ya shigo waya ta, na daga yace na sakko na same shi a parlorn kasa. Jiki na rawa na dauki hijab nasa na fito dan na kagu naji abin da zai sanar da ni, wanda sam na kasa kawo ko meye a cikin zuciyata. Yana zaune rike da waya yana dannawa nayi masa sallama ya dago ya kalle ni, kafin na zauna ya ce yace na rufe kofar naje na rufe sannan na dawo na samu gefen kujera nesa dashi na zauna. Ya yi gyara murya tare da aje wayar a gefen sa ya dan matso daga gefen kujerar yace.

 

“Alhamdulillahi Khadija a kullum na kalli yadda rayuwar ki ta dawo na kanji dadi da farin ciki. Gashi cikin ikon Allah ya sake daga daraja da mutuncinki ta hanyar da bamu tunani ba, yanzu bani da wani buri irin naga na mika ki zuwa dakin mijin ki, wannan shine buri na na biyu akan ki Khadija. Ina fatan zaki ci gaba da kulawa da kanki kamar yadda kike yi a koda yaushe. Na ga yanzu Allah ya baki miji wanda nake saka ran insha Allahu shine fitila na gaba da zai ci gaba da haskakawa a cikin duniyar ki. Ni dai ya yi min, tarbiyarsa, dabi’unsa da kuma kalamarsa duk ba bu wanda ban duba ba. Kema nasan zai yi miki, naga yaro ne matashi mai jini a jika, Allah ya daukaka shi a cikin tarin ni’imomin da yake da su.”

 

Kai na a kasa farin ciki ya mamaye ni, ashe kawu daddy kallon takun mu kawai yake yi nida Mas’oud bamu sani ba? Lallai babba-babba ne inji bahaushe da yace yaro ko ya hau rimi ba zai iya hango komai ba. Wayyo Allah dadi sai na hango gashi har an daura mana aure an kai ni gidan Mas’oud birnin zuciya ta muna ta shan soyayyar mu.

 

“Nan da dan wani lokaci za’a daura auran ku insha Allahu. Duk da cewa bani ne wanda zai bada auran ki ba, amman na dauki alkawarin zuwa can dangin mahaifinki da kai na nayi musu bayani yadda zasu fahimta. Allah ya yi miki albarka Khadija tashi kije daki ki kwanta nasan gobe akwai aiki.”

 

Ciki da jin kunya na tashi na ruga da gudu, farin ciki da nishad’i na suka dadu ba. Kan gado na fada ina tsalle tamkar wata yar shekara uku, na kagu Mas’oud ya kirani dan na kyankyasa masa wannan zazzafan labarin wanda nasan idan yaji ko bacci ba zai iya yi ba saboda murna. Wani ikon Allah sai be kira ba sai sako da ya turo min na text message cewar suna tare da Abban su ba zai samu damar kira ba mu hadu gobe a gurin aiki. Banji komai ba saboda ina cike da murna na je kitchen na zuba abinci naci sannan na dawo na kwanta cike da zakuwar ganin gobe.

 

*WASHE GARI*

 

Yau kam na fi koda yaushe saurin shiryawa dan zuwa gurin aiki saboda zumudi, na shirya tsab na dauki jakata Tukur driver ya dauke ni sai gurin aiki. Babu kowa sai wadanda suka yi aikin kwana, na shiga muka gaisa sannan na wuce office na zauna dan jiran lokacin da zan yi program dina. Bamu hadu da Mas’oud ba sai wajan karfe goma sha d’aya dalilin rashin zuwan sa da wuri. Sai da na jira har karfe d’aya lokacin da ya gama nashi sannan mukai sallah nace ina son yin magana dashi. Yana ta zolaya ta ganin yadda na cika da nishad’i ba kamar kullum ba, ya samar mana gurin zaman muka zauna.

 

“Ko ranar da aka daura mana igiyoyin aure sai haka madam, irin wannan murna da farin ciki haka, meye sirrin a ban nasha nima.”

 

Na yi dariya tare da rufe ido da hannayena, na bude ina wasa da zoben yatsa na nace.

 

“Albishirin ka?”

 

“Goro Oum Waleedah.”

 

“Fari ko baki?”

 

“Ahhh! Sai ma an jani tukunna? Toh na zabi uhmmmm… Uhmmmm… Zabar min dai da kanki.”

 

Ya yi maganar cike da shagwaba, ban san lokacin da na saki dariya ba ina cewa.

 

“Gaskiya kai zaka zaba, ai ni zan gaya ma albishir d’in.”

 

“Toh shi kenan na zabi fari tartar.”

 

“Yauwa jarumi na kasan me?”

 

“Sai kin gaya min da bakin ki sweetheart.”

 

“Kawu daddy ya gano cewa muna soyayya, jiya da kanshi ya kira ni yace ya yaba da hankalin ka ya amince za’a yi auran mu nan ba da jimawa ba.”

 

Mas’oud ya bude baki tare da zaro ido cike da tsantsar mamaki, ya kasa ma magana saboda yadda abin ya zo masa daga sama.

 

“Wai kina nufin kice min min daddy da kanshi ya gano cewa soyayya muke yi?”

 

Na gyada kai ba tare da na yi masa magana ba sai dariya nake yi. Kasan cewar a cikin office din su muke, kuma babu kowa a ciki sai kawai ya taso tare da yin juyi yana rawa ina dariya. Kusa dani na ji ya matso tamkar zai hade jikina da nashi nayi saurin rintsa ido saboda na riga na saddakar da faruwar hakan, sai naji yace.

 

“Ina ma ace ina da wannan damar, dana nuna miki irin tsantsar farin cikin da na shiga ta hanyar baki lafiyayyan runguma. But ya zama bashi, Allah ya kai mu lokacin da zamu zama abu d’aya zan biya ki harda na yau.”

 

Sai ya d’an matsa daga kusa da ni ya zauna akan kujerar da ya taso, sannan ne na samu damar bude idanu na.

 

“Kin fiye jin tsoro Oum Waleed, ya kamata kuma na rage miki yawan shi.”

 

“Ai ni wani lokacin wallahi tsoranka nake ji, dubi yanzu fa kana kokarin taba ni.”

 

“Ban taba ba ai Oum waleedah, but soon zan yi miki abin da yafi tabawa ma.”

 

Na share shi dan idan na biye masa tsab zai sanya ni cikin wani yanayin da ban shirya zuwan sa ba. Muka ci gaba da hira saboda zakewa harda yadda bikin zai kasance muke ta tattaunawa hankali kwance. Tun daga wannan lokacin muka sake d’in kewa ni da Mas’oud saboda ganin zamu mallaki juna. Daga ni har shi bamu taba kawowa cewar kawu daddy ba junan mu ya mallakawa ba, saboda bai fito fili ya bayyana mana cewa ga yadda yake nufi ba. Haka muka ci gaba da rayuwa lokaci yana ta tahowa, Mas’oud yana ta hada kudin da zai turo gidan mu dan nema masa aure na kamar yadda ake yi.

 

*FADAR BASANNABAS*

       

Tunda yai mafarkin nan yake jin jikin sa yana rawa, Tunani ne dankare a kirjin sa. Amma ya kasa samun nutsuwar yadda zai warware shi. Dafe kansa yai ya rintse idanun sa. Yana zaune a fada amma bai bada damar aiwa kowa iso ba. Jakadiya sai zarya take tana sanar masa isowar mutane. Dakyar ya bari tabawa waziri dama ya shigo,

 

 “Allah yaja zamanin sarki adali. Allah ya Kara Maka lapia da nisan kwana mai amfani ranka ya dade!”

 

Hannu sarki Salmaan ya daga masa yana dafe da habar sa,

 

 “Allah ya tausasa ran sarki! Allah yakara maka dattako baban kowa. Shin akwai abunda ke damun Sarkin mu ne? Sanar min ko menene shi shugaba na.”

 

Sarki Salmaan ya d’anyi murmushin jin dadi. A duk duniya waziri na cikin sahun mutanen farko da yake so. Saboda a kullum sai ya tambayi abinda ke damun sa yana kuma k’ok’arin ganin ya yaye masa matsalolin sa,

 

 “Waziri… Nayi mafarki irin na kwanaki. Menene gaskiyar al’amari?”

 

 “Allah ya karawa sarki lapia. Tabbas shakka babu zamu iya fassara hakan da cewar sharri ne na mafarki. Amma kuma idan aka auna abun a mizanin hankali za’a gano akwai kullalliya ko makircin bil adama..”

 

 “Menene mafita to…?”

 

 “Kamar dai yadda na nemo maka hayakin nan da ka yiyyi kwanaki? Yanzun ma zan koma wajen Malam din na karbo maka wani..”

 

Kada kai SAS yayi kafin su cigaba da magana data shafi fada. Mikewa sarki yayi. Dogaran sa suka rufe shi ya wuce sashen sa jin yadda yake wani irin jiri mai gigita kwakwalwa, ga ciwon kai da yake kuma barazanar faduwa. Waziri ne ya cigaba da zaman fadar, inda ya zauna dasu Galadima, ciroma, wambai da sauran su. Ya sanar da su rashin lafiyar sarki Salman tare da umartar wani babban hadimin sa da cewar yana son ya kuma karbo masa wannan hayakin a wajan malam kamar yadda ya taba karbowa kwanaki.

 

Galadima ya kalli ciroma suka saki wani murmushi ta cikin rawanin su, da alama wata damar ce zasu samu wajan kuma yiwa sarki Salman wani makircin. Nan dai suka nuna jimami da alhinin rashin lafiyar, amman a zukatan su ba haka abin yake ba, wata muguwar manufa ce a rasu. Ciroma da kanshi yaje ya karbo wasu kayan tsibbun wanda yake dauke da tsana mai karfi tsakanin sarki Salman da mahaifiyarsa, ganin ya fara mafarki da ita sun tabbatar zasu iya shiryawa, wanda shirin zai iya wargaza musu duk wani shiri da suka yiwa masarautar. Shi kuma tunda ya shiga daki ya kwanta yake wani irin bacci mai nauyi da ko wane irin ihu ba zai iya farkar da shi ba.

 

 ____Cikin wasu furanni masu launin shudi da rawaya yake hangenta, sanye da kaya na alfarma sai faman murmushi take yi. Shi kuma yana daga gefe zaune da jarida yana dubawa sai idanunsa suka sauka akan ta, ya dinga kallon ta yana son kuma ya gano wa take yiwa wannan fara’ar mai tsadar gaske. Ya mike cike da kasaita yana isa gurin da take sai yaga shi take yiwa dariyar, ya kuma kallon ta tare da kamo hannunta sai kawai ta shige jikinsa tana kankamewa, murya a raunane yaji tana cewa.

 

“Nagode ya kai annurin da yake haskaka min zuciya ta, tun dazu nake nan ina jiran zuwanka.”

 

Shafar bayanta kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Shan kamshin nan nasa yana sake sanya ta cikin begen sa, ta dago fuskarta tana kallon tashi tace.

 

“I love you my hubby.”

 

Sai ga Shaheedah tazo gurin, gabansa ya yi mugun bugawa, amman sai yaji Dijen ta rike shi tana cewa.

 

“Kadena jin shakkarta saboda ita ba komai bace face azzaluma, ba ta son ka shi yasa take cin zalinka. Allah ya fita babu abin da ta isa ta yi maka ina tare da kai my hubby.”

 

Ya samu kansa da tsayawa a gurin na ta duk da tsoran da yake tattare da shi na Shaheedah. Daga gefe ta tsaya itama tama miko masa hannu wai yaje, sai ya kalli Dije ya kuma kallon Shaheedah yana tunani yadda zai yi. Zuwan wani saurayi gurin yana kuka shine yasa Shaheedah barin gurin, Dije kuma ta kama shi suka tafi daki. Sai ya kuma jin nutsuwa yana yiwa Allah godiya da ya bashi Khadija matsayin mata abar alfahari. Sam be yi zaton a bacci yake ganin hakan ba sai sa ya farka ya ganshi a tsakiyar gadon sa yana juye-juye a kai. Tabbas yaji a jikinsa Khadija itace zabin zuciyar shi, dole ne ya ci gaba da farautar neman auran ta koda kuwa yin auran zai janyo abubuwa da dama a cikin masarautar. Sai da ya yi wanka ya shirya sannan ya nemo amintaccen bafadensa wato Al-hassan, suka kebe yace masa yana son a ci gaba da shirye-shiryen auran sa kamar yadda suka fara. Ya amsa sannan ya sake komawa wajan Alhaji Isma’il wanda ya tabbatar da cewar zai je dangin mahaifin Khadija ya sanar dasu, idan yaso yana dawowa sai ya sanar da a shirya daurin auran.

 

Haka kuwa aka yi Alhaji Isma’il be sanar da su Mami zai je ba, sai shiryawa ya yi da shatara ta arzikinsa ya je ya sanar dasu komai, suma dai be gaya musu wanda zata aura ba, ya ce musu dai ya amince da tarbiyar yaron dan gidan mutunci ne iyayensa masu daraja ne. Suka amince tare da bashi ragamar aurar da Khadija, a cewar su ai shine uwa da uba na ta dan haka babu wani abu da zasu ce sai fatan Alkairi a cikin auran. Bayan ya dawo ne yake sanar da Mami cewa yaje can sun gama komai sannan ya kira yan uwansa suma ya gaya musu sunce idan lokacin yazo yasu bar komai su zo ayi dasu. Bata damu ba dan bata yi zatan wani mai daraja za’a aurawa Khadijan ba.

 

Tunda aka fara wannan abun Dije da Mas’oud basu yi zaton ba junan su zasu aura ba, basu zaci hangen da kawu daddy ya yi ba akan su yake ba, sai da abin yazo gab har ana sauran sati daya biki sannan ne yace da Dije zai kuma yin magana da ita idan ya gama komai. Kasan cewar da yamma ne ta gaya mata kuma Jumma’a ce yana ganawa da mutane yan kasuwa, shi yasa ta bari zuwa gobe idan Allah ya kaimu.

 

°°°°°°°°°°°    °°°°°°°°°°°°°°    °°°°°°°°°°°°

 

*WASHE-GARI*

 

Tunda Kawu daddy yace zamu yi magana daren ranar ban runtsa ba har wayewar gari. Kasan cewar asabar ce, Ina malale akan gado gaba na sai dukan uku-uku yake. Shin akan me zamu tattauna? Nasan tabbas lefi nayi. Kuma duk yadda akai akan bana bari TK ya dakko ni wani lokacin idan na fita. Ko kuma su Mami ne suka qulla min qullalliya a gurinsa? Ko kuma zancen iyayen Mas’oud zai min kila yace nace ya turo. Ganin sha biyu ta kusa ban ci abincin safe ba hakan yasa na diro daga gado ina mika, Band’aki na shige nayo wanka na canza kaya cikin doguwar rigar A line marar shape. Na taje kai na dakyar saboda inayi yana zamewa saboda santsi da cikar sa, Na d’aure da ribbon. Dauri me sauki nayi na shafa man baki na sauka kasa. A dinning area na tarar da Mami dasu Ya Shukrah suna cin abinci suna hira.

 

 “Mami ina kwana..? An tashi lapia.”

 

 “Lapia lou..” Ta bani amsa a tak’aice tana mai cigaba da kurbar tea dinta.

 

“Ya Shukra ina kwana? Ya Hameeda ina kwana.”

 

Kowannen su ya amsa babu yabo babu fallasa. Ganin haka na mike na daddebi abinda zan ci a plate na koma k’arshen parlorn nakeci acan. Sai bayan na kammala ina zaune ina karanta wani book na wajen aiki sai ga Kawu daddy yafito. Sanye cikin jallabiya.

 

 “Kawu daddy…Barka da safiya Kawu daddy! An tashi lapia?”

 

 “Alhamdulillah Khadija.. Muje ko?”

 

 “Toh Kawu..”

 

Su Mami suka bimu da kallo, Yana gaba ina biye da shi ya shiga parlorn sa ya zauna akan babbar kujera ni kuma na tsakure a gefe,

 

“Hau kujera ki zauna mana.”

 

“Nan ya isa Kawu….”

 

Gyaran murya yai. Ya rage volume din CNN dake faman yi,

 

“Kafin dai mu fara magana ina son tabbatarwa kai na Kamar yadda kika sani, wannan maganar da muka yi dake a baya na aure ita ce ta kuma tasowa. Amman Shin ki na da saurayi ne dake zuwa neman ki gidan nan? Kai bama wannan ba. Akwai wanda ya taba yi miki zancen aure? Dan ni dai nasan da akwai zan sani ko kuwa..? Dan naje munyi magana da dangin mahaifinki, sun kuma bar min komai a hannuna cewar na yi komai da komai a game da auranki.”

 

Wani daskararren abu naji ya tokare min a wuya. Shin menene yake shirin faruwa dani.? Ko wani sharrin aka kullamin?

 

“Magana nake miki Khadija kin yi shiru…”

 

“Kawu daddy.. Ba.. babu!” Na samu kai na da bashi amsa haka! Kawu daddy ya sake yin shiru na dan wani lokacin kafin yace,

 

“Tun wannan dai wanda nazo nace miki na yaba da hankali da tunaninsa, gashi kai tsaye ni ya nema kinga kenan da gaske yake yi ko?”

 

Sake samun Kai na nayi da kada kai. To me zance? Shi kansa Mas’oud din yana namiji ya boye alakar mu bare ni Mace?

 

“Toh shikenan! Alhamdulillah tunda babu wata magana tsakanin ku da wani. Kinsan babu kyau neman aure akan aure. Wannan yaro me hankali da dattako ne, ya fito daga gidan mutunci. Yana neman auren ki.. Kuma azahirin gaskia ma nace na bashi. Saboda ko da kina da wanda kike so din a matsayina na mahaifi agare ki. Babu wanda ya zo ya same ni. Manya basu shigo ciki ba, Dama already blood sample/genotype dinki sunyi kyau. Kowa zaki iya aura, Kuma Khadija…”

 

Ai bai karasa magana ba na fashe da kuka, Me yasa su Ya shukra da Hameeda su ba za’ai musu auren ba sai ni? Okay! saboda ni ba yar gidan bace ba ko kuwa? Ko dan banda gata ne? Tsana ce wannan kome? Wayyo Allah na ni Khadija..Ashe daman ba Mas’oud aka zaba min ba? Kuka Sosai nake yi ina rike kai na. Duk duniya babu d’a namijin da nake so, gangar jiki na keson mallaka irin Mas’oud ba. Ina son Mas’oud saboda shine first love dina. Ina son Mas’oud saboda shi ya koya min so har nasan menene so? Ina son Mas’oud saboda shi ya rai ni zucia ta ya koya mata abinda take so. Ina son Mas’oud saboda yana so na so mai wuyar fassarawa.

 

 “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

 

Shi naketa nanatawa a fili ina bubbuga kai na ajikin kujera, Kawu daddy ya sauke zuciya ina jiyo sautin ta,

 

“Kiyi hak’uri Khadija. Na rantse da Allah ban amince da aura miki shi ba don na cuce ki. Wallahil azim ba zan kai ki inda zaki wahala ba don na lalata miki rayuwa ba Khadija. Wallahi Khadija wannan auren ni inaji ajiki na alkhairi ne a gareki damu gabaki d’aya. Saboda Ina ji ajiki na nan gaba zaki ya ba min wannan rana..”

 

Kuka nake sosai shabe shabe ina fyace majina da kasan dankwali na.

 

“Kawu Mas’oud fa.. Mas’oud Kawu! Ina son Mas’oud.”

 

 “Wanene haka kuma Khadija.?”

 

“Kawu shine wanda ya ke sona. Tun service dina muke tare Kawu daddy. Munyi alk’awarin aure dashi wallahi Kawu daddy..”

 

“Khadija me yasa be zo ya same ni da zancen ba? Akalla kafin ya fara neman ki sai ya nemi yarjewa ta kamar yadda wannan ya yi. Amman Me yasa bai turo Manya sunzo ba idan har da gaske yake yi Eh?”

 

Shiru nayi ina ajiyar zuciya.

 

 “Yace ne.. Ko wansa bai yi aure ba kuma shine karami. Sannan bai gama ginin sa ba..”

 

 “Sai Yaushe kenan zai fadawa manyan ki Uhm!? Ko kuwa zama za kiyi tayi kina jiran sa kina faman tsufa agida? Shi kuma yana bata miki lokaci? Daga karshe ma yazo yace miki an hada shi aure da yar uwar sa! Uhm? Shikenan tunda baki dauke ni amatsayin uba ba Khadija. Na ky’ale ki sa..”

 

Riko kafafun sa nayi ina Kuka, Ni din banza zan ki amincewa da maganar Kawu daddy? Mutumin da ya mayemin gurbin uwa da uba? Halacci d’aya zanyi shine na amince. Ba Wai don ina son wanda za’a daura min aure dashi ba. Kawai dai saboda Kawu daddy ne. A duniya banida mafiyin sa idan ka tsame sauran yayyun Umma ta.

 

“Bar Kuka Khadija.. Na kyaleki wallahi. Zan ku..”

 

 “Na amince Kawu daddy.. Na amince wayyo Allah karkai fushi dani.”

 

“Allah ubangiji ya miki albarka. Ya biya miki bukatun ki na alkhairi, Allah yasa wannan auren ya zamo wanzuwar farin cikin ki, Yasa ki zama wata aba a rayuwa, Allah yasa ayi a sa’a. Nan da sati d’aya wato mai kamawa za’ayi in Shaa Allah!..”

 

Kasa magana nayi, Ni wallahi ji nake tamkar bacci nake yi. Gaba d’aya bana gane me kawun yake fada. Na sandai nace na amince amma gaba d’aya wani dishi dishi ma nake gani. Zucia ya da idanu na Mas’oud kawai suke nuna min, Sanye cikin kananun kaya yana rataye da ID card dinsa na wajen aiki. Cikin haka Mami ta banko kofa ta shigo,

 

 “Meye haka ne? Koke-koken me aketayi ne uhm? Tun daga karamin parlor nake juyowa, Me akai ne?”

 

Tana magana tana sakace hakorin ta da toothpick.

 

 “Babu komai ya akai..?”

 

Kawu daddy ya tambayeta yana duban ta da kyau .

 

 “Koke koken da muketa jiyowa ne shysa na shigo ganin Lapia? Kar ma’kota su fara lek’owa suna tambaya.”

 

“Lapia Alhamdulillah Hajia. Ba kukan wani abun bane na farin ciki ne.”

 

 “Toh faa! Tooo”

 

Mami tace hakan tana mai zama a gefen sa.

 

 “Tashi kije Khadija. Allah ya miki albarka Khadija!”

 

 “Aamin Kawu daddy..”

 

Mikewa nai dakyar ina tafiya. Ina jiyo mami nata tambayar sa menene?

 

 “Wai meke faruwa ne alhaji. Alkhairin menene?”

 

 “Hajia.. aure ne! Wani bawan Allah ne ke neman auren ta ya biyo ta kai na.”

 

“Aure..”

 

Mami tafada tana dafe da kirjin ta, Ni kuwa sauri nayi Na fita na jawo musu kofar. Ina fita na haye sama ina mai bude sabon shafin wani kukan. Mami ta muskuta kusa da Kawu daddy,

 

“Alhaji bangane me kunnuwa na suke jiye min ba, aure? Aure fa kace? Waye zai auri wa?”

 

“Hajjaju da hausa fa nake miki magana. Nace neman auren ta akazo waje na.”

 

“Au ashe da saninta ma shine take kukan munafurci kuma?”

 

“A’a Hajia wanda takeso daban. Wanda kuma yai tambaya daban.”

 

“Toh fa! Alhaji Kai wa ka bata kenan..?”

 

“Wanda ya fara magana mana.”

 

“Shi din wanene shi! Wai ka na nufin bada masaniyar ta ka bayar da auren nata ba? “

 

 “Eh ban isa bane? Ni ba mahaifin ta bane.?”

 

Yatsina fuska Hajia Abeeda tayi tana sosa idon ta,

 

“Toh shi wannan Waye manemin kenan? Dan wanene?”

 

 “Wallahi wani bawan Allah ne kawai nutsatstse ya kwanta min arai kuma.”

 

 “Ya’yan abokan ka Wai..?”

 

 “Ko d’aya wallahi.. wani ne daban. Marainiya ce gwara na aurar da ita hankali na yafi kwanciya.”

 

“Dankari Makari.. Ai shikenan! Toh su Shukra Alhaji ka nemo musu mana acikin yaran abokanan ka. Ko Yayan commissioners dinnan da kukayi makarnta.”

 

“Ai nagaya miki inde sai dan wane da wane zaki bari su aura ni babu ruwana na tsame hannu na, Muyi ta zama ana k’irga mana shekaru tare.”

 

“Wai dan anbiyo takan ka ance anason Dije? Tab Alhaji ai wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, Dai dai ruwa dai dai tsaki. Su ana ganin kai ne mahaifin su babu kasakantaccen da zai biyo takan ka yace yana neman auren su.. “

 

Dr. Ismael yayi daria yana kurbar ruwan hannun sa, Yasan halin matar sa sarai, Shi yasa bazai taba gaya mata gidan da dije Zata shiga ba sai an daura aure ko kuma an kawo kayan aure abu ya kusan tabbata. Yasan kuma Zata titsiye Dijen da tambaya shiysa bai sanarwa Dijen bama, Duk ya tattara ya rufe su a fai-fai. Mami ta jima tana neman bugar cikin Dr. ismael don jin waye? amma tsabar zurfin ciki irin nasa duk nacinta haka ta hakura bataji Waye manemin na dije ba. Data dame shi ma sai ya rufe fuskar sa da jarida wai kansa ciwo yake. Tashi Tai ta fice ta kyale shi.

 

“Mami ya akai kuma..?”

 

“Kukan me take Mami.?”

 

Shukra da Hameeda suka tasata a gaba da tambaya ganinta fito daga wajen Dr. Ismael

 

“Hmm! Makira algunguma aure Zata yi fa..”

 

“Aure! Wa Zata aura Mami..?”

Hameeda ta tambaya tana raba idanuwa.

 

“Ba dai Mas’oud ba?”Shukrah ma ta tambayi Mami tana dafe kirji.

 

“Waye Mas’oud kuma? Du basu bane. Wani ne daban yazo neman auren ta. Shine take wannan kukan batasan wanene ba..”

 

“Kuma Daddy ya yadda?”

 

“Kwarai kuwa.. Yace ma afara shiri sabon sati me kamawa zaayi bikin.”

 

Hameeda ta tabe baki,

 

“Allah ya raka taki gona..”

 

Shukra ma jin ba Mas’oud bane sai ta samu kanta cikin jin dadi,

 

“Masha Allah! Allah ya kai mu.”

 

Harara Mami ta dankara mata. Tanemi waje ta zauna,

 

“Gwara kuma ku fito da mazajen aure…”

 

“Soon In Shaa Allah!” Cewar Shukra tana murmushi.

 

Hameeda khma ta shiga raba idanuwa. Haka dai suka tasa zancen auren agaba sunata ta kwashewa dije albarka. Musanman Mami dake bakin cikin auren dw zatai. Amma Idan ta tuno kila ba auren jin dadi bane sai ta shiga  murmushi kuma tana k’ada k’afa.

 

Ni kuwa inacan d’aki ina kuka. Ba kalar wanda ban ba. Kai har karamin hauka sai da nayi. Naita buga kai na ajikin bango duk ya daddauje. Naita bori. Ina tunanin ko hada kayana zanyi na gudu ne yadda ake a film. Wata zuciar tace bakisan halacci ba.

 

Dole nayi hak’uri zuciya mai halacci bata manta alkhairi komai girman sharri . Kawu daddy ya zamar min uba ya zamarmin uwa. Shine gatana. Yana gatantani fiye da tunani. Me yasa zan bijirewa abinda yake so ya kuma nuna isa akan sa? Wacece Ni? Dole na hakura. Illa dai koma wanene ya yankemin buri na na auren Mas’oud saiga rayuwa. Wallahi sai ya bambancewa aya zakinta na shiga hurumin soyayya da yayi. Ina ruwan sa? Lallai ni na hadu da sharrin late comer mai datse farin cikin zukatan masoya biyu . Bansan ka ba, Dan jaraba da kalata kace ni kakeson aura? Wannan wacce irin bahaguwar kaddara ce? Wata zuciar tace taki kaddarar kenan Khadija. Zaki shiga wata ukubar rayuwar kenan ta uku. Na bigi wajen kirjin nawa inda zuciar take tamkar dai zaucacciya. Ni kadai nace ah k’arya kike wallahi sai dai shi ya shiga uqubar rayuwa. Ba shine ya ce yaji ya gani yana so ba? Ai kuwa zai San ya tafka babban kuskure.

 

Mas’oud sai kira na yake na kasa dauka. To me zance masa? Koma menene shi ya janyo mana wallahi. Ni dai ranar gaba d’aya haka na yita rabi kuka rabi zancen zuci, rabi magana ni kadai. Wani lokacin kuma na bubbuga kai na a jikin gado. Wayata kuwa daga karshe kashe ta ma nayi gaba d’aya. Oh ni dije. Wai ni za’aiwa auren dole da wanda bansani ba? Kuma cikin wata d’aya jal aka gama komi. Nashiga uku sau dubu uku. Haka nayita sallolin nafila ina wa Allah kuka a sujjada kan ya tarwatsa wannan auren da za’a yi min koda kuwa anzo daurawa ne……

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 8

Advertisement   _*BABI NA: 8_*     _*Wattpad:missxoxo00_*                 ***   Advertisements “Hannu malama Mardiyya.”  …