KIBIYAR AJALI 19

Advertisement

 _

I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_

_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_

_PG:19_

_BOOK:2_

Advertisements

*SAS*

Yau dai kam yana son jin muryar Ammi, Tunda ya bada wayar aka kai mata ya sake kiranta yana jin nauyi da kunyarta na tsawon shekarun da suka yi ba tare da sunji muryar juna ba. Sake gyara zama ya yi cike da ladabi tamkar suna kallon juna, hannunsa yana rawa ya dannan sunnan ta tare da karawa a kunnensa. Ammi kam daman tun da Dije ta bata wayar kullum tana hannunta tana jiran kiran nasa, ko toilet zata shiga sai ta tafi da ita dan karya kira bata kusa a samu matsala.

Tana zaune a bedroom dinta tana cin kwadon zogale da Dije ta kawo mata, wayar na kan cinyarta kamar koda yaushe sai taji ringing. Kirjinta ya buga, ta rufe ido tare da yin hailala tayi bisimillahi tare da karawa a kunnanta. Salman naji ta dauka yaji wata irin nutsuwa ta saukar masa, duk kuwa da cewa ba tayi magana ba.

“Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh Yaa Ammi.”

Wasu hawaye masu dumi suka sakko mata kan fuskarta, da kyar saboda farin ciki ta Iya bude baki ta amsawa d’an nata cikin rawar murya.

“Wa’alaikas Salam mai babban suna.”

Advertisements

“Allah sarki Ammi na baki fushi dani ba? Ki yafe min Ammi dan Allah karki fushi da ni ban san abin da ya hau kai na ba naji sam bana tunaninki. Kaddara ce ta hau kai na wacce ban san yadda zan yi ba a baya, amman a yanzu ina fatan na fuskanceta sosai ta yadda zan jurewa cinye ta. Ammi dan Allah karki fushi dani wallahi ina sonki, na kuma damu dake. Da yardar Allah komai ya kusa warwarewa, mu dawo kamar da Ammi, mulki masifa ne Ammi musamman irin wannan da Allah ya dora min.”

Banda kuka babu abin da Ammie keyi wanda ta rasa ko na menene, tabbas taji zuciyarta tayi sanyi ganin hankali da tunanin dan ta sun dawo cikin jikinsa. Sannan kuma zuciyarta ta karaya ganin yadda yake ta bata hakuri kai kace yana sane ne ya guje mata, wanda tasan ya yi hakan ne saboda tsantsar biyayyar da yake da ita. Haka ake son yara nagartattu su dinga kaskantar da kansu a gurin iyayen su koda kuwa a ce iyayen ne basu da gaskiya ko basu kyautata musu.

Tasa hannu ta sharce hawayen da basu dena fitowa daga cikin idanunta ba, tare da jan numfashi tana murmushi tace masa.

“Kafin komai sai mu fara yiwa Allah godiya, Alhamdulillah. Daga nan sai mu yiwa Gwaggo ta Fada jinjina da irin jajircewar da tayi wajan karbo mana taimakon ayoyin ubangiji. Tare da sake din bin godiya gurin Khadija da ta yadda zata taimaka mana gashi har Allah ya amince.”

Lumshe ido ya yi yana ta sauraran Ammi har ta gama magana, ya sake sakin wani murmushin murya can kasa-kasa kamar baya son taji abin da zai furta yace.

“Ammi kinji dadin auran Khadija da nayi?”

Shi kansa Salman da ya yi maganar be zaci Ammi taji ba, sai amsar ta kawai yaji cikin walwala tana cewa.

“Sosai ma kuwa mai babban suna, naji dadi fiye da tunaninka domin Khadija tayi min abinda ba kowa ne ya yi min ba.”

“Ina son ta Ammi….”

Salman ya fada cikin rashin sanin cewa a fili ya yi furucin, Ammi tai dariya cike da jin dadin ganin danta ya samu abinda yake so. Kuma dama Khadija abar so ce tana da kyawawan hali da girmama na gaba da ita. Abu daya ta sani gurin Khadija shine bata san rai ni ko ya yake, dan sometimes takan jiyo yar dabi tsakanin ta da Abdullah, idan kuma a gabanta ne ba ta biye masa sai dai ya karaci shirmen shi ya yi shiru.

“Ammi babu wata damuwar ko?”

Ammi tayi shiru tana son tace masa sauran Khaleel, amman ta kasa. Shi kuma abinda yasa be gaya mata sun hada dashi ba, so yake yai surprising din ta yadda farin ciki zai fi bayyana a gare ta. Can ta numfasa cike da kulawa tare da ajiye ragowar tunaninta a gefe dan karta samishi damuwa shima tace.

“Babu wata damuwa sai farin ciki mai babban suna. Allah ya yi muku jagora a duk lamarin Ku, ya tsare min ku a duk inda kuka sa kafa. A dena mantawa da adkhar, addu’o’in fita daga gida dana shiga harma da na bandaki duk da nasan kana da juriya wajan aiwatarwa, wannan kawai tunatarwa ne nayi maka.”

“Insha Allahu Ammi, na gode Allah ya bar mana ke cikin koshin lafiya.”

Amsawa tai daga nan suka ajiye kowanne yana jin farin ciki marar misaltuwa. Ammi kuwa harda sujud tana yiwa Allah godiya tare da kirari na girmamawa.

*FADA*

Bayan tashin su daga fada, Manyan yan majalisar sarki suka nemi izinin kara ganawa da sarki Salman. Bai musa ba ya basu dama yana mai duba agogon hannun sa, Domin so yake ya je wajen Khadija..

“Ranka ya da’de… Su wambai ke son magana da kai…”

Cewar waziri yana rissina kai..

“Okay waziri… A basu dama. Amma me ke tafi dasu?”

Waziri ya langab’ar da kai yana hada hannuwa,

“Kabar mugun mutum ranka ya dade, Su kadai suka san kutingwilar da suke hadawa.”

Ajiyar zuciya Salman ya sauke yana daga masa hannu aalamun ya bashi dama ya shigo dasu, Waziri ya leka ya shigo dasu, Kowanne yaci magani yana bubbudawa,

“Ran sarki ya dade…. Takawar ka lapia bahon sarki, Baka ajiye ba, Baka ba kowa ajiya ba.” Cewar Galadima yana daria.

“Ita haihuwa ai ta Allah galadima..”

Cewar waziri ransa a bace.

“Waziri kenan.. Tukuf tukuf da kai kamar na Allah, Kai ko kunya baka ji? Yiwa wanda kai jika dashi biyayya?”

“Toh menene inde shugabane? Ai durkusawa wada ba gajiya wa bane..”

“Kaga galadima rabu da wannan.. Muyi abunda ya kawo mu.”

Shi dai Salman kallon su kawai yake, Gashi lamarin waziri sake bashi tsoro yake, Yana tare dashi shekara da shekaru amma yanacin dunduniyar sa? Ashe bakin su d’aya dasu wambai? Idan yana tare dasu yayita yin abu tamkar shidin na kwarai ne?

“Ranka ya dade… Kai ta kwasarrrrrr…”

“Ba’kin ciki….”

Cewar chiroma yana daria kasa kasa. Shida wambai suka hada hannu suka tafa.

“Idan har zancen da ya kawo ku kenan.. To ina ganin tashin ku awajen nan ku fita shi yafi alkhairi.”

Cewar waziri yana nuna musu kofar fita.

Galadima yayi daria yana bubbuga k’afar sa ta dama, 

“Waziri kenan… Karka kuskura ka kaimu karshe, Domin idan ka kaimu karshe.. Yar wazintakar da kake ji da ita zamu tuge ka.. A juri zuwa rafi dai.”

SAS ya dagawa Waziri hannu alamun yayi shiru, Waziri yai shiru kamar wani mutumin kwarai. Su wambai suka shiga magana da fada, Ta inda suke shiga ba tanan suke fita ba, Shi dai Salman idanu ne nasa kawai, Addua yake cikin zuciar sa kan Allah ya bashi ikon ganin bayan su, Allah ya dora shi akan su. 

“Saboda haka lokaci zamu baka…Nan da yan watanni biyu zuwa uku.. Ko dai ka fadi wa’enda kakeso a tsatson sarautar mu.. Ko kuma mu hadaka da duk wa’enda mukaga dama. Sannan abu na biyu, Idan dik zance biyun kayi biris dasu… Toh abdulqadeer shine zai hau karagar mulki, Kai da sarautar basannabas kuma sai dai labari, Domin bakada magaji da zakai tunanin zai gajeka nan gaba, Balantana su…”

“Ba sai ka karasa bama wambai. Mutumin da bai san wayesu ba, Kai ko kasan Khaleel da Abdullah? Ya kuke dasu..?”

Salman yai shiru yana jujjuya kai tamkar wani sauna,

“Bangane su waye ba Baba..”

“Ahap…! Ai na sani. To ko su din da baka tuna su Waye ba, Suma ba zasu gaji mulkin kaba atoh..”

“Yauwa galadima… Sai magana ta gaba. Zancen bikin yaran nan.. Kudin daka bayar basu isaba Salman, Ka karo biyun su, Domin biki za’ai na kece raini, Kaga bikin masarautar kalwa da akai yafi namu, Idan bamuyi wanda yafi nasu ba zamu sha daria ne a idanun masarautun kasanmu, Ina fatan ka fahimta?!”

Salman ya daga kansa alamun Eh. Can ahankali yace,

“Waziri… Kayi musu transfer din kudin account din nan na wajen ka baki d’aya.”

Waziri jiki na rawa ya tsugunna yana rawar baki,

“Ranka ya dade.. Du? Du? Du fa kace? Wannan uban makudan kudin Za’a bayar suyi hidimar miki biki dashi? Haba ranka ya dade.. Tuba nake.. Amma dan Allah ka sake shawara.”

“No… issokay waziri. Baba zasu isa ko?”

“Zasu isa tunda naji yaron ka (waziri) yana kambama yawan su.”

Tashi sukai suka tafi.. Suna sake jadda da masa kudirin su da suka yanke. Parlorn ya rage daga shi sai waziri bayan futar su, Waziri ya rarrafa ya rissina,

“Allah ya kara maka lapia… Bazeyiwu ka janye maganar makudan kudin nan ba..?”

“Bakomai waziri… Ka basu. Allah zai kawo wasu.”

Ajiyar zuciya waziri ya sauke yana kada kansa,

“Samun adalin sarki mai tausayi da hak’uri irin ka sai an tona.. Ran sarki ya dade..Ina fatan mafarkin nan da kakeyi yayi sauki ko..?”

“No waziri… Abu sai dada gaba yake yi. Dak’yar na fito fada ma… Naga wani garin magani daka ban kwanaki na hayak’i dinnan..? Nayi naji mafarkin matar duk na dena..”

Waziri ya dashe baki yana shafa rawanin sa,

“Haka mukeso.. Mugayen mutane ne suke bibiyar ka ta mafarki.. Kuma da yardar Allah karshen su tazo, Zan sake karb’o maka wasu, Zaka dena mafarkan baki d’aya. Yanzu ga wani ma ka sashi a karkashin pillown ka, Ka kwanta kai da mafarkan nan sai dai ka bani labari kawai..”

“Godia nake waziri.. Tabbas ka rike ni tamkar kai ka haife ni.. Ka tsaya tsayin daka akan makiyana, Waziri na gode sosai, Ka zamo min katanga mahallar makiya, Banda bakin godia s….”

Bai karasa ba waziri ya rissina hannu bi biyu,

“Ranka ya dade Ka dena godia dan Allah..Bazan taba cin amanar sarki Aliyu ba, Domin shi ya bani amanar Ka, Hannu da hannu ya riko ni a asibiti yana kan gadon rasuwar sa, Sunan kane abakin sa yana dankamin amana..”

SAS yai murmushi kawai yana jin k’arairakin waziri,

“Ni zan koma ciki… Bana jin da’din jiki na.”

Mik’ewa waziri yai, Bayan ya rissina masa , Ya kira dogaran sarki suka kare shi ya mike, Suka rakashi har sashen sa suna masa kirari. Yana shiga ya shige daki, Ya sakarwa kansa ruwa a shower. Yai flushing maganin waziri a masai, Yana fitowa ya canza kaya zuwa wata arniyar shadda ya dora alkyabba akai, Ya taje kanannadadden gashin sa kwantacce sannan ya dora hula akai, Ya shafa turaruka masu sanyin kamshi, Sannan ya zauna akan kujera yana nazari..

Tashi ya yi kai tsaye ya nufi sashen Khadija, lokacin da ya shigo ni kuma dawowata daga gurin Ammi kike nan ina cire alyabbar jikina ya shigo.

“Daga gurin Ammi ko?” 

Ya tambaye ni yana kasa da idanuwasa. Kai kurum na iya dagawa naje na mayar da rigar inda sauran suke, ji kawai nai yace.

“Kina san Ammi na da yawa ko?”

Har cikin zuciya ta naso bashi amsa saboda banga amfanin yin karya ko neman gurin zama ba, ina ci gaba da gyaran wardrobe d’in saboda idan ba hakan nayi ba ban san me zan yi a dakin ba nace.

“Ammi uwace a gare ni, ban taso tare da mahaifiyata ba, shi yasa nake jinta tamkar itace ta haifeni. Bani da wata da zan kalla na nuna ta matsayin uwa sai yanzu da na samu Ammi. Amman uba kam har yanzu Ina dashi, duk da cewar bana manta wanda ya haifeni koda da second daya.”

Salman ya jijiga kai tare da karasowa ciki dan da a kofar ya tsaya be shigo ba. Ganin yana nufowa inda nake ne yasa nai saurin birkito da alkyabban cikin wardrobe d’in, na durkusa da sauri dan na kwashe. Shima sai ya karaso tare da dukawa yana taya ni, daman kuma rike ni ne bana son ya yi dan ya saba duk sanda muka hadu ya wani rungume ni. Murya a sanyaye yana daukar riga daya ya gyara ninkinta yace.

“Ni ne kawai ban miki ba ko?”

Nayi shiru dan bana son furta komai a gurin saboda rashin kyan furucin. Amman ni ba yimin ne beba no, zuciya tace har yanzu ta kasa karbarsa a matsayin abokin rayuwa ta. Na kasa mantawa da Mas’oud da irin soyayyar mu har ma da yadda muka shirya rayuwar mu. Da ace zuciya ta zata amince da Salman da zan zauna dashi na so shi kamar yadda yake gaya min irin wanda yake min. Toh taki yarda da duk wani furucinsa, ta kasa goge tarayyarta da abinda ba muharraminta bane a yanzu, tana son Mas’oud har yanzu kamar tai hauka.

“Toh ko tsufa nai miki ne?” 

Na girgiza kai, taya zance ya yi min tsufa bayan shima din har yanzu matashi ne?

“Okay saboda na aure ki ba tare da na fara tuntub’arki ba?” 

Sake girgiza masa kai nayi tare da cewa.

“Ko kadan daga cikin abubuwan da ka lissafa, kawai dai zuciya ta har yanzu tana gurin wanda ya koyar da ita menene SO.”

Zuciyar Salman ta harba da karfi. Da ace Khadija tasan yadda yaji da ba zata sake gaya masa cewar zuciyarta tana son waninsa ba harma ta kasa mantawa da wancen d’in bare ta karbe shi. Cikin dauriya irin tashi ya mike yaje ya saka mata rigar cikin wardrobe 

dai-dai lokacin da nima na tashi zan saka wacce na ninke muka bugi goshi, nasa hannu da sauri ina shafa gurin nawa, ya yi saurin riko ni cike da kulawa yana mulmula min gurin.

“Sorry my dear.”

Ya fada yana shirin kwantar da kai na saman kirjinsa, amman na hana hakan faruwa saboda ni bana son kusancin mu dashi yana yawa. Baya san bata mata rai saboda nemarwa kansa masauki a zuciyarta, hakan yasa sakar mata jikin ta ya koma yana ci gaba da ninke kayan.

“Naga anata shirin biki ke banji kinzo kin karbi komai daga guri na ba. Shaheedah ta karbi kudi tace zatai kayan fitar biki da kuma gudin mawar da zata bayar, kefa.?”

Cikin tab’e baki ina yatsina fuska, nifa wallahi da zama tare dashi gwara min zama a durbun wajan Gajiyalle tayi ta bani wahala saboda rashin son da nake yi masa. Na mike tsaye Ina cewa.

“Ai ita matarka ce shi yasa ta nemi abu a gurinka.”

“Toh ke d’in meye a gurina?”

Bance komai ba har muka kammala gyara wardrobe din na tsaya na rasa me zanyi ya dauke min hankali daga kanshi.

“Kin abinci kuwa?”

“Eh a gurin Ammi.”

“Alhamdulillah naji dadi, yanzu me kike bukata nayi miki?”

“Ka bani shaidar rabuwar mu da kai shine nake bukata a gurin ka.”

Rintsa ido ya yi ya rasa ya zai yi da ni na dena furta masa wannan kalmar dan baya son jin ta. Ya mike tsaye tare da gyara alkyabbarsa yana murmushi wanda na rasa ko na menene yace.

“Zan baki hakkinki kema kamar yadda na bawa Shaheedah. Amman dan Allah ki dena min maganar saki domin Allah ma baya son kalmar. Ina sonki my yar jarida.”

Daga haka ya shafa fuskata ya juya ya koma sashen shi ya barni Ina karewa bayansa kallo. A raina Ina tunanin anya yana da zuciya kuwa? Taya nace bazan zauna dashi ba amman sai ya zauna dani dan dole, ni wallahi bazan yadda dashi ba Sai ya barni na koma inda nake so dan banga dalilin zama dani ba. Na ciro dankwali na tare da karkade turaran jikinsa da ya barmin a dakin kai kace zai koru saboda haushin Salman din da nake ji. Ganin bani da mafita yasa na haye kan gado ina hawayen bakin ciki.

GIM. SHAHEEDAH!

Gaba d’aya ta susuce da yin abubuwan da boka ya bata na tsibbance tsibbance, Cikin kwanakin har rama tayi. Ta kira hadimarta batula tana ta zagaye cikin dakin a birki ce,

“Ranki ya dade gani…”

“Duba kiga kafa ta dauke a sashen? Kizo ki sanarmun yanzu, Ki tafi da fatanya ki b’oye awani wajen kinji?”

“Toh ranki ya dade…”

Hadimarta na fita ta janyo wata qullin leda da kwado aciki marar rai an daure bakin sa da laya an nannade ta, Ta shiga tuntsura dariya tana babbakata,

“Khadija… Kinyi gangancin shigowa gonata.. Wacece ke da har zaki tunanin jerawa da ni?.”

Hadimarta ta kwankwasa mata kofa, Jiki na rawa ta fita sanye cikin hijabi da nikabi ba zaka taba kawowa ita bace. Sashen Khadija suka nufa, Babu kowa na masu tsaran gate da alamun hadin baki ne. Wurin shuka suka je, Anan hadimarta ta tona rami, Ita kuma shaheeda ta zura kwadon da layar, Suka binne shi acikin ramun suka barbada kasa akai.. Suna gamawa shaheedah ta koma sashen ta cikin sauri, Wani garin magani ta dakko, Ta cire kayan jikin ta tana hayaki dashi. Kaurin marar dadi sai tari take..

“Daga rana irinta yau.. Jin dadin ki cikin masarautar nan ya kare Khadija.. Ke da duk wani mai goyan bayan ki ma tasa tazo karshe. Mu zuba mu gani..”

Haka taita fada tana tari saboda tsabar hayakin maganin yayi yawa.

*SAS*

Ya qudiri niyar kyautata mata saboda soyayyar da yake yi mata, zai jure duk wani bakin cikin da zata cusa masa indai zata zauna tare da shi har ta haifa masa yara yan albarka. Bashi da buri da dabara ko hange a yanzu sai na son yadda zai sa Khadija taji dadin rayuwarta, amman wace hanya zai bi har ya cimma manufarsa ta son kasancewa da ita a matsayin mata da miji? Tabbas Khadija qaddararsa ce a cikin qaddarorin rayuwarsa, be tab’a jin wata ya mace tace bata son sa sai akan ta. Shin me yasa take iya kallonsa harta furta masa cewa bata son shi ba ta son zama tare dashi? (Mas’oud ne zabin ta Salman, kasan shi? Kasan yadda suka tsara rayuwar su? You knw nothing Salman shi yasa kake sake shan wahala wajan son sanin meye dalilinta)😉

Tashi ya yi daga kwancen da yake ya nufi bathroom, wanka ya yo yazo ya shirya kansa cikin kananun kaya saboda zuciyarsa taba gaya masa cewar kila dan tana ganinsa cikin rawani da manyan kaya ko sleeping dress shi yasa take ganin tamkar tafi karfin shi. Sosai ya tsuke cikin jan jeans da farar t-shirt, gaban rigar anyi rubutu baki da d’igon ja-ja-jajaja ansa BE MY LOVE. Gyara gashin kansa yayi ya koma balaraben sa sosai, daga nan ya dauki turaruka ya fesa tare da dakko pcap dinsa itama ja ya dora akansa.

A gaban madubi ya tsaya yana karewa kansa kallo, shi kansa a cikin zuciyarsa sai da ya yiwa Allah godiya, daman haka yake, ko ya yaga Allah ya yi masa abu sai ya gode masa a cikin ransa. Ya jiya tare da daukar wayarsa ya nufi sashen Khadijan, wace ke zaune a kan stool tana waya sai dariya take yi cike da nishad’i, alamar babu wata matsala ko damuwa da take damunta. Har ya samu guri ya zauna bata kallesa ba dan ta hangoshi ta cikin madubi, sai da ta mulu sannan tace.

“Shikenan sister Maryama zamu yi waya mu karasa maganar tamu… Okay tom shikenan ki gaida min Gwaggon mu.”

Ajiye wayar nayi akan madubi still ina ta dariya kafin na juyo kamar ban ganshi ba nace.

“Au.. Ashe ka shigo?”

Zare pcap d’in ya yi tare da ajiyewa akan cinyarsa. Gaskiya banda zuciya sakarya ce da kuma kitsawa mutum karya da gaibu, banga abin ki a gurin Salman ba. Amman da yake bana son nashi sai ban wani ji komai ba naci gaba da sabgar gabana, Ina jin lokacin da ya saki ajiyar zuciya ya taso tare da dawowa kusa dani ya tsugunna yana kamo hannuwana ya kura musu ido.

“Madam ya kike?”

Na kawar da kai gefe daga kallon sumarsa dake kyalli da tashin kamshi. Ban kula shi ba sai hannuna da nake ta kokarin ganin na kwace amma yaki sakar min, har sai da ya dago kansa ya kalleni yaga ina faman tsuke fuska sannan ya sakar min hannun kamar yana jin tsoro na.

Tashi ya yi Ya fito ni ban biyo shi ba ashe kasa ya sauka duk hadimaina suka fice ya tsaya a kitchen yana kare masa kallo, can dai ya bude fridge shima ya kare masa kallo ya rasa me ma ya kawo shi kitchen d’in. Google ya shiga shi a dole sai ya yi mata wani abun burgewa wanda zai faranta mata rai.

Pepper soup d’in kaza ya gani cikin sauri ya nemo recipe ya shiga sarrafa kazar nan guda daya da ya dakko. Duk a tunani na ma ya fita har Ina cewa yau kuma turanci ake je da kananun kaya za’a fita masarauta. Tsawon lokaci ya dauka be dawo ba, fitowa ta daman daga toilet kenan na ganshi dauke da tray da bowl a saman sai turiri yake yi, ya ajiye akan madubi tare da kamo hannuna ya zaunar da ni bakin gado. Komawa ya yi ya dakko tray d’in yazo ya durkusa a gabana muka kalli juna ni dashi, Allah sarki gabaki daya ya sauke sarautar da yake da ita ya zama tamkar wani bawa na.

Yana durkushin yasa spoon tare da debowa yana hura min da bakinsa sannan ya doshi baki na dashi cikin tsantsar……

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 10

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 10…

KIBIYAR AJALI 17

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p NANA HAFSATU❤️…