KIBIYAR AJALI 20

Advertisement

 

2__0*

 

 

Sallah ce kawai take ta dani, bayan ita kam babu abinda nake yi banda kukan zuci. Duk tunani na yana kan wanda ake shirin aura min, ban san shi ba, idan ma na san shi to ya boye min tunda ni har yanzu ba wanda ya taba tunkarata fa maganar aure. Mas’oud shine wanda rai da zuciya ta suka amincewa, shi kuma gashi ya yi sanya har an bawa wani ba shi ba. Wayyo Allah na ina cikin kaddarorin rayuwa

mabanbanta, marasa kamaceceniya ta ko wace fuska. Su Mami kuwa babu wanda ya zo yaji kukan da nake yi, sai dai na jiyo dariyar su wacce bana raba d’ayan biyu magana ta suke yi.

 

Har dare ban kuma saka wani abu cikin baki na ba, sam na dena jin yinwa saboda rashin nutsuwar zuciya. Ina idar da sallah isha’i nabi lafiyar gado ina share hawaye. Da kyar na dakko waya ta na kunna tare da jonawa jikin charge, nan naga messages d’in Mas’oud yana ta tambayar lafiya naki dauka, ko bani da lafiya, dan Allah in yi masa reply ko zai ji dadi. Duk na karanta amman naki masa reply d’in sanda bashi da wani amfani, ya riga ya gama da rayuwar mu gabaki d’aya tunda shine ya yi ta jan lokaci, da yazo ya fada ai da duk an san tsakanin mu, amman ya dinga cewa zai zo, zai aiko, gashi nan lokaci ya k’ure mana a sanda mukafi buk’atar kadancewa da juna.

 

Advertisements

Ina ji kirji na yana zafi nasan na yunwa ne amman naki zuwa naci abinci saboda har lokacin bana sha’awar cin komai. Gashi babu mai lallashi na bare a tilasta min ko ruwan shayi nasha, haka na kwanta har gari ya waye banci ba. Koda na tashi da asuba da kyar nayi sallah, jiki na naji yana ta min wani irin ciwo kamar an sassara ni haka na dinga ji. Da yake weekend ne sunday sai na koma kan gado na kwanta, zazzabi ya rufe ni. Allah ya taimake ni da aka fito breakfast kawu daddy yaga bana gurin sai be yi magana ba ya tashi tsam ya nufi dakin da nake. Yana shiga ya tarar da ni cikin blanket, ya dinga kiran suna na amman na kasa Kwakwkwaran motsi, sai yasa hannunsa a goshi na yaji zau kamar garwashi, cikin tashin hankali yake magana.

 

“Innalillahi wa’ina ilaihir rajiun, Khadija baki da lafiya haka? Me yake damunki?”

 

Jin da ya yi bana iya cewa komai yasa shi kiran su Mami da karfi, sai gasu kuwa da gudu suna tambaya daddy lafiya?

 

“Bata da lafiya naji jikinta akwai zafi. Abin da yasa na kira ku ke Hameedah kizo ki bata taimakon farko da ya dace.”

 

“Okay daddy.”

 

Tayi maganar tana taba jikina, tace za’a yi min allura sai ta saka min drip yadda zan ji dad’in jikina. Haka kuwa aka yi ta min allurar ta kuma sanya min drip a daidai wannan lokacin ne Mas’oud ya kira waya ta, Shukrah ta dauka, ganin sunan Mas’oud yasa ta tashi ta fita. Duk da ina cikin wani yanayi hakan da ta yi sai da ya sanya ni cikin faduwar gaba dan ban san abin da zata gaya masa ba. A can parlor kuma Shukrah guri ta samu ta zauna tare da kara wayar a kunne kai kace ita aka kira. Cikin kashe murya da kisisina ta shiga yi masa magana.

 

Advertisements

“Assalamu alaikum.”

 

“Amin wa’alaikis salam, dan Allah bata kusa ne.?”

 

“Eh… A’a.”

 

“Ban fahimta ba.”

 

Mas’oud ya tambaya cikin rashin fahimtar abin da take nufi.”

 

“Wai kana nufin bata sanar da kai abin da yake faruwa ba? Idan kuwa haka ne Dije taci amanarka, har kai zata boyewa.”

 

“Innalillahi wa’ina ilaihir rajiun. Idan har na fahimce ki dai dai, kina son gaya min cewa akwai abinda ya kamata na sani a gurin ta amman taki gaya min ko?”

 

Sai da ta yi farrrr da kwayar idanunta sannan ta gyara zama tace.

 

“Kwarai ma kuwa, ba abin wasa bane dan yana da kyau ka sani tunda naga kamar kun zama aminai.”

 

“Toh dan Allah ki had’a ni da ita muyi magana please sister Shukrah.”

 

Tayi mamakin yadda ya gane cewa itace, sai dai ranta ya d’an so su da taji ya damu da jin Dije, amman ba bu yadda ta iya dole da d’an daure da kishi tace.

 

“Yanzu kam ba zata iya daga waya ba, sai dai idan anjima kila idan taga dama.”

 

“Shikenan Shukrah na gode sai anjima.”

 

Be kuma jiran cewar ta ba kawai ya katse zuciyar shi ta shiga cikin tunanin abin da yake faruwa. Shi sai yasan babu abin da ya had’a shi da Khadija na rashin jituwa. Amman wane irin abu ne Shukrah tace ana boye masa? Dole yana son jin koma menene, kuma daga bakin Dije dan ita zata warware masa kullewar da kansa ya yi. A ranar shi kansa da kyar ya gudanar da wasu al’amura sa, still kuma ya ci gaba da kiran ta amman a kashe, hakan ya sake tayar masa da hankali har ya fara shirin zuwa gidan na su.

 

Tsab Mas’oud ya shirya cikin manyan kaya shadda ruwan kasa wacce aka yi masa gajeren d’inki, sunyi masa kyau ya dora hula wacce ta dace da kayan jikin nasa ya dauki turare ya dora tare da jan mukullin motar sa ya fito. Addu’a kawai yake yi Allah yasa yaje yaji alkairi daga bakin Khadija, yana jin zuciyar shi tana karfafa masa gwiwa wajan samun nasara akan duk abin da zai zo bakin ta, bai taba kawowa rabuwa zasu yi ba dan yana da yakinin aure a tsakanin su. Ya yi horn mai gadi ya leko, ganin shi yasa ya bude ba tare da wani shakku ba. Wajan motar da ake kai ta gurin aiki ya aje tashi, tare da dakko wayarsa ya kuma kiran ta, cikin sa’a kuwa tana zaune kan sallaya taga sunan shi ta dauka ba tare da tace komai ba.

 

“Ki daure ki fito ina compound d’in ku.”

 

Duk da irin dauriyar da take janyowa hakan be haka muryar ta yin rawa ba, taja majina waje silar kukan da tayi ne ya sakar mata da tsinkakkiyar majina marar kauri tace.

 

“Me zan fito nayi maka bayan ka riga ka tarwatsa mana duk wata dama da muke da ita?”

 

“Bana gane abin da kike nufi shi yasa nazo kafa da kafa dan na ganki. Dan Allah ki daure kizo muyi magana ta fahimta.”

 

Kamar karna je haka nake ji, amman kuma zuciya ta tana son ganin shi a zahiri dan na kalli yadda zai dauki maganar. Katsewa nayi dama da hijab a jikina na tashi da kyar na fito, babu kowa a parlorn sai na fita kai na tsaye ba tare da na sanar da Mami ba. Tsaye na ganshi gurin motar shi yana latsa waya, yadda naga ya kuma yin kyau ne ya sake ruda ni, kamar nayi shekara ban ganshi ba haka naji. Na daure na karasa har wajan sannan na tsaya ban kula shi ba saboda haushin sa da nake ji.

 

“Da alamu nayi babban laifi da har na cancanci irin wannan horan ko Oum Waleed? Kin san yadda rashin daga wayar ki yasa hankali na ta shi? Wallahi tun jiya na kasa cin abin cin arziki saboda tunanin abinda ya hanaki daukar wayata. Shin me nayi miki sweetheart?”

 

Naja wani gauran numfashi mai radadi a zuciya, hawaye suka zubo min nasa hannu da sauri na share dan bana son dogon zancen da zai min, nace dashi.

 

“Yaushe ne zaka zo gidan nan kace kai ne wanda zaka aure ni?” Ya kalle ni tare da cewa,

 

“Na yi miki alkawari nan da karshen wata uncle’s dina zasu zo gidan nan nemar min aurenki harda saka rana.”

 

Wata kwallar bakin ciki ta sake sakkowa kan kumatu na, naja kukan da yake tahowa na hadiya ina kallon kasa nace.

 

“Nayi zaton zaka ce gobe da sassafe, ashe har yanzu jinkirin a gurin ka yake. Ban san me zan ce maka ba, sai dai kawai nasan kai ne ka janyo muka rasa junan mu Mas’oud.”

 

“Ban fahimta ba Oum Waleedah, ta ya muka rasa juna bayan duk gamu a raye muna numfashi.?” Na yi saurin cewa.

 

“Numfashi marar amfani ba, ta iya yiwuwa kai a gurin ka kana yin mai amfani, sabanin ni da zan shiga gidan mutumin da ban san ko waye ba, ta ya za kai kace ni ina numfashi? Ka wahalar dani Mas’oud, ka koyar dani darasi mai matukar wahalar da zuciya. Bana tunanin zan san meye jin dadi da yanci a cikin rayuwa ta, zanje na rayu da wani ba kai ba Mas’oud, kana ji kana gani za’a kai ni inda bana so. Dan Allah Mas’oud ka rufa min asiri kar na rasaka please ka ceci rayuwa ta saboda da kai ta fara soyayya….”

 

Cak numfashin sa ya tsaya na dan wani lokaci, baki bude yake kallo na cikin zare ido da alama yaji maganar ne cikin tsakiyar kansa. Ya matso dap dani har ina iya jiyo bugun da zuciyar shi take yi da karfi sannan kuma cikin sauri. Kamar zai rike ni haka ya soma yi yana magana a daddaburce hankali a tashe.

 

“Dan Allah idan mafarki nake yi wanda yake kusa dani ta yi gaggawar tayar dani. Wallahi tunda nake ban taba yin mummunan mafarki ba irin wannan.” Cikin kuka murya a dashe nace dashi.

 

“Ba mafarki kake yi ba da gaske ne wannan maganar da nake maka. Sai dai nima ina fatan kawu daddy ya dawo yace min da wasa yake yi a yau din nan.”

 

“Innalillahi wa’ina ilaihir rajiun na shiga uku ni Mas’oud wannan wace irin mummunar kaddara ce? Oum Waleed dan Allah karki bari a rabu mu, wallahi ina sonki. Gobe zan turo uncle’s d’ina ayi maganar koda basu taho da kudin ba, su san da zaman mu ni dake kar su rabu mu dan girman Allah.”

 

Yadda yake magana a gigice shine ya sake tayar min da hankali na tabbatar da idan bamu yi da gaske ba komai zai iya faruwa. Kamar na juya na tafi saboda naga shima ya fara zubar da hawaye, sai dai na juyo ba tare da na bari mun had’a ido ba nace masa.

 

“A wannan gabar bani da ta cewa Mas’oud, sai dai ina fatan zaka yi duk yadda zakai wajan karkato da zuciyar kawu daddy har ya amince da auran mu. A shirye nake tsab da idan ya kuma tuntuba ta da maganar ka zan amsa dan kar na cuci kai na, amman fa ni bazan iya zuwa yanzu nace dashi ba zan auri wanda ya bani ba, saboda yadda baka cancanci wulakanci a guri na ba, haka ma kawu daddy be cancanci tozarci daga gare ni ba. Dama tuntuni damar tana hannunka, yanzu ma tana hannunka sai ka nema mana mafita.”

 

Ina gama magana na ruga gida da gudu ina wani sabon kukan wanda yafi na farko zafi da radadi. Ban san yadda ya kare ba a compound, sai dai wajan karfe goma naji kawu daddy ya shigo yana yiwa Mami magana.

 

“Ikon Allah, yaran zamani sai addu’a kawai.”

 

“Alhaji me kuma aka yi maka? Ko samari ne ka hadu da su akan titi marasa kunya.” Yana kokarin zana ne yake cewa.

 

“A a babu ko d’aya daga ciki. Yaron nan ne Mas’oud abokin aikin Khadija. Ina jin ko labarin auran ta yaji yanzu shine ya kawo kanshi wai shi da ita sun dade suna soyayya tare da burin yin aure, wai yana ta shirin turo manyan sa sai yaki ance an bayar da ita. Shine nace da me ya hana shi bayyanawa tuntuni sai yanzu?”

 

Jin maganar aure na ne yasa Mami sauya fuska, can kuma sai ta ce tana zuba mishi juice a glass cup.

 

“Kaima Alhaji har yanzu ka ki gaya mana waye wanda zaka aura mata. Ni ban taba ganin inda aka yi wannan abin ba, ko dan bani na haifi Dijen ba shi yasa ake ta boye min shi?”

 

“Ko daya wallahi Hajiya, abin da yasa ban fada ba shi angon ne ya roki arzikin dan Allah karna fada sai ranar auran. Kinji dalilin da yasa ko ita Khadijan ban gaya mata waye ba.”

 

“Ai shikenan, idan ta fashe ma gani ai.”

 

“Zaku gani kam insha Allahu. Yaron ma na bashi hakuri nace ya yi hakuri aure nan da rana ita yau za’a daura shi da ikon Allah.”

 

“Uhmm Alhaji kenan, kana bani mamaki tun zuwan yarinyar nan gidan nan, komai na ta baka nuna min shi kai tsaye sai ka yi kwana kwana. Amman ba komai lokaci ne tunda gashi ta kusa tafiya nata gidan.”

 

“Ki dena yi min fassara akan komai Hajiya. Yarinyar nan marainiya ce kin kuma san yadda Allah ya bayar da amanar rikon maraya. Dan Allah ki tayani faranta mata har zuwa ranar da ya rage mata a cikin gidan nan.”

 

Tamkar ya yi da gunki ta yi masa banza hakan ya kara tabbatar masa da cewa idan ya gaya mata wanda Dije zata aura akwai rashin hankali. Sai ya kuma jan bakinsa ya yi shiru be sake cewa komai ba har lokacin kwanciya ya yi ya tafi daki. Ni kuwa tunda naji yace ya bawa Mas’oud hakuri na koma gefe naci gaba da kuka na wanda babu mai lallashi.

 

*MASARAUTAR BASANNABAS*

(Sarki Salman Aliyu Salman SAS)

 

Kafin kace wani abu tuni sarki Salman ya kuma susucewa akan son auran Dije, sarautar ta kuma fita daga cikin zuciyar shi ta yadda ko sunan sarki baya son yaji an ambata masa. Duk da ya rage sauran sati daya a daura auran sa, ga kuma ta fiyar da aka ce zai yi zuwa Cyprus, kuma babu wanda za a fasa indai yana da rai da kuma lafiya a jikin shi. Komai dama da ya dace ango ya yiwa amarya, Sarki Salman ya bawa Alhaji Isma’il kudadenda za’a siya. Shi kuma ya kai wa wata mata kwangilar hadowa ba tare da ya sanar da ita ko na meye ba, daman ita aikin ta kenan, duk abinda mutum yake bukata a had’a masa na aure ko na gida tana yi a biya ta.

 

Yana zaune a cikin fada yama rasa abin yi saboda Sam baya cikin hayyacin shi, ya jiyo muryar Ciroma yana gyaran murya yana cewa.

 

“Allah ya taimake, rana ita yau shine ranar da zaka je taron nan, an shirya maka komai sai fatan zuwa da dawowarka kawai, Allah ya kara maka lafiya.”

 

.._Afuwan! Kunji shiru ko? Wallahi kwana biyu inata fama da chronic ulcer. Har takai na kwanta a asibiti na yan wasu kwanaki shysa kukaji shiru, Shekaran jia akai discharging. Ina fatan na same ku lpy? Nagode k’warai da addu’oin ku. KIBIYAR ajali zai cigaba da samuwa Insha Allah da zarar naji karfin jiki na sosai.. Na gaishe ku, Gaisuwa mai kima.._

 

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 11

Advertisement                  *11*         *Ranar* wata sanyayyar asabar da damina, Muka tashi da babban tashin…

KIBIYAR AJALI 31-32

Advertisement  _*KIBIYAR AJALI…..!!!!*_ _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_            🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA…

KIBIYAR AJALI 28

Advertisement   28….*      _*KIBIYAR AJALI…..!_* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_                  🏹🥰😍    …