KIBIYAR AJALI 20

Advertisement

 

_I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_

_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_

_Zafafa biyar… Yan biyar masu zazzafar basira🥰 Na gayshe ku.. Gaisuwa mai dimbin fatan alkhairi❤️❤️_

_PG:20_

Advertisements

_BOOK:2_

   Tsantsar kulawa, mai makon na bude bakin..Sai kawai na kawar da kai gefe ina girgiza kai, kamshin duk ya cika min hanci ga baki na da yawun ya tsinke da alama so nake naci amman fadin rai da son nuna cewa be isa ba yasa naki karba. Salman ya kuma matsowa yana miko min. cikin karyar da kai kamar wani marar lafiya da yake bukatar taimako, muryar sa na sarkewa yake magana.

“Ko be yi miki ba my love? Da kai na fa na dafa miki ba wani nasa ba.”

“Nace maka fa naci abinci a gurin Ammi, ni ban san dalilin da yasa kaje kai wannan aikin ba salan mutane suce na shanyeka ka jazamin masifa gurin matarka.”

Ganin yadda nake magana ina hade rai ne yasa shi maida cokalin cikin bowl din, nan fa hankali na ya tashi tare da tunanin kodai ya fasa bani ne dan shi mutum ne da na lura baya son bata min rai koyaya. Kokarin ajiyewa kan bedside yake yi nai saurin rike hannunsa still fuska ta a hade amman dai ba kamar da ina masa magana ba. Ya Kalle ni cikin son jin karin bayani dan shi da zuciya daya ya yi niyar ajiyewa tare da alkawarin ba zai takura mata ba akan sai taci.

Na turo baki ina kifta idanuwa kamar wata marar gaskiya nace dashi.

Advertisements

“Kace kai ka dafa?”

“Kwarai kuwa ci kiji.”

Ya fada yana sake debowa a cokali ya hura shi wai ya huce sannan ya miko min kusa da baki na yana cewa.

“Haaaa.. Ban sa miki yaji da yawa ba, sai dai nasa albasa sosai da yar tafarnuwa saboda tana da matukar amfani a jiki.”

Gyada kai nayi gashi na kagu naji an samin a baki miyau na duk ya gama tsinkewa. Budewa nayi cikin yanga kai kace son ci ne bana yi amman kuma duk salo ne na kar ya rainani. Saboda tsabar rudewa jin wani azababban dadi ban san lokacin da na karbi cokalin da hannuna ba na dinga kwasar romon ina sharba. Harga Allah koni da nake mace ban taba yin Pepper-soup d’in kaji da ya yi min dadi irin wannan ba.

Shi kuwa banda kallo na babu abinda yake yi, da alama ya rasa ma me zai yi ne idan ba kallon ba. Ban ankara da santin da nake yi ba sai da na kusa cinyewa sannan na kalleshi naga yayi zaman dirshan yana ta bina da ido kamar wanda aka ce idan ya rufe zan bace daga gurin.

“Ya haka?” Na tambaye shi dan jin dalilin wannan kallo.

“A karo miki ne madam akwai ragowar.”

Murmushi na yi ganin ya harbo jirgi na yasan cewa santi nayi, amman dan kar na nuna masa sai nace ina ci gaba da ci.

“Daman ka iya girki ne?”

“Gashi kinga zahiri, lallai da alama ya yi dadi gashi har kin cinye baki min tayi ba.”

“Ba santi bane ba, taimaka maka nayi dan karka ce ka kawo min abu naki ci.”

“Hakan ma na gode madam, ai kin taimake ni da kika ci naji dadi sosai my love.”

“Nifa ba santi nayi ba, kuma abinda yasa na tambayeka Ammi ce tace min baka taba dora tukunya ba da nufin yin girki tun tasowarka. Khaleel ne ma yakan yi karan bani amman shima ba wai iyawa ya yi ba. Kuma nasan hadimai na na kasa suka yi maka shine kake cewa kai kayi dan kaga ban fita ba.”

Kallo na kawai yake yi yadda yaga ina ta bayani kamar an kunna tsohuwar radio.. Babu abinda yake tunawa shi kuma sai ranan da ya fara yin tozali da ita , hakan ne yasa da yaga tayi shiru ya yi dariya yana cewa.

“Yar jarida.”

Ya yi maganar cikin wani salo da alama dai yadda nake maganar ya burgeshi ta yadda yake ta faman Murmushi. Nai masa shiru ni dai sai faman lasar lips nake irin na naci dadin nan, ko ganewa ya yi lashewa nake yi? Naga dai ya taso bayan ya karbi bowl din ya ajiye tare da nufowa jikina. Banyi aune ba sai ji nayi ya kwantar dani kan gadon yasa harshensa saman lips dina yana lasa, ni kuwa tsabar mamaki mutuwar zaune nayi Ina fito da kwayar ido cikin din bin mamaki.

Sai da yaji baya jin testing d’in komai sannan ya bar abinda yake a lips din, ya kalleni yana kwantar min da gashin gaban goshi na. Hakika yana matukar son baiwar Allahn nan, yana junta a duk wani sashe dake cikin jikinsa. Murya a raunane yace dani.

“Allah ya maki albarka.”

Dadi ya kamani jin an bani naci na koshi kuma an bini da addu’a lallai wannan mutumin be dauki duniya a bakin komai ba, yadda yake tarairayata Ina jin ko Mas’oud d’in da na kwallafawa rai ba zai min haka ba, musamman yasan Ina mugun son shi. Ji nayi ya dagani tare da sanya hannu ya dagoni na zauna sosai yace.

“Ki huta lafiya zanje sashe na zamu yi maganar daurin auren su Munaya dasu Abdulqadeer.”

Ban samu kwarin guiwar amsa masa ba saboda al’amuran sa sun fara girgiza tunani na. Ya mike a hankali ya nufi gurin kofar da ya biyo yana kallo na kamar baya son mu rabu haka ya hakura tunda ana can ana jiransa kar su fara kwashe masa albarka da sauke mai kwadon tsinuwa dan ba kirki gare su ba…..

<<<<<>>>>>>>

Da daddare saina samu zuciyata da yin wani irin rauni akan yin hidimarsa gareni. Na fara wani tunanin cewa shifa sarki ne, sarkin ma wanda ake ganin girman rawaninsa sama da wasu rawaninnikan a kasar nan. Shi d’in fa jinin milki ne d’an gaske, matashin sarki maiji da kuruciya da sanin darajar lokacinsa. D’an gatan da duk kaddara ta juya masa zukatan dangi zuwa ga kiyayyarsu akan mulkin duniya. Anya kuwa zuciyata da kalmomin bakina suna mini adalci wajan yi masa furuci.?

Ai koban girmamasa a matsayin miji ba ya cancanci girmamawa a matsayin na shugabana mai mulkin jahata. Ya cancanci girmamawa na matsayinsa na babba gareni a shekarun da kuma hankali.

Sarki Salman bashi da wata makusa a halittar jiki data mu’amular rayuwa. Tunda nazo gidansa bai taba munani da wani furuci na baki ba balle a aikace. Ya bani jin dadin rayuwa kamar kowacce mace dake ji da kanta a gidan. Ya bani girma irin na matarsa a idanun jama’ar masarauta dama bani ragamar kula da wani sirrin rayuwarsa. Idanma ta gaskiya za’abi nice na tura rayuwarsa cikin tawa a dole ta hanyar acting da nake yi saboda matarsa. 

Tabbas Allah shine shaida ta, bana jin sonsa a zuciya ta. Amma kuma ban tsanesa ba. Sannan ina kawo masa maganar saki ne dan kawai na samawa kai na lafiya a wani lokacin. Sannan bazance bana son Mas’oud ba har yanzu. Sai dai sonsa ya ragu a raina sosai a yau d’in nan ba kamar sanda muna a tare ba. Bansani ba kodan bana ganinsa yanzu ne shi yasa oho.. Ko kuma saboda irin kulawar da Salman yake bani musamman ta dazu da ya shiga kitchen da kansa dan kawai ya faranta min….? 

Iskar da aka huramin akan idanuwa ya sakani sauke nannauyan numfashi dan ban fargaba ashe na fada duniyar tunani mai zurfi. Da wannan damar Salman yayi amfani wajen kare min kallo tun dazun. Ganin ina kara zurfi ne ya sakashi maidoni cikin hayyacina.

“I love you Deejah”.

Ya fada a hankali gab da fuskata dan ya rankwafo kaina ne. Da sauri nayi baya da jikina ina kyakykyafta idanu zuciyata na wani irin bugawa a karo na farko. A salon da yayi maganar ne yayi matukar tada tsigar jikina. Baya na cigaba dayi yana bina har na kwanta akan gadon shima ya kwanto kaina.

 

Idanu na zaro waje sosai zanyi magana yayi saurin dora yatsansa saman bakina yana kadamin idanunsa da suka sauya launi. Cikin sarkeni da su yace,

“Ban cancanci a soni bane ma’am?Deeja menene laifin ne dan naso abinda ya dace da ni?”

Da sauri na girgiza masa kaina ina kyafta idanu, dan yanda yake magana yana matukar tada min da tsigar jikina. Muryata na rawa na ce,

“Ni bance bana sonka ba. Kawai dai…..” Na kasa karasawa.

“Kawai dai me?” 

Ya tambaya yana dora hancinsa a gefen wuyana da wani shegen Salo na saukar da numfashi.

Jikina ne ya fara rawa. Zan turesa ya rike min hanu yana cigaba da aika min salon dana ke ganin tsantsar mugunta ce.

Bakinsa ya dora saman kunne na ya dan ciza. zabura nayi amma ya sake danneni yana kara raunana muryarsa.

“Ki sanar min saboda me?”.

“Kafi karfi na.” Na bashi amsa cikin subucewar baki.

Da sauri ya dago yana kallona da idanunsa da suka sake komawa kalar tsoro.

“Khadijah banfi karfinki ba, kece ma kikafi karfina ai.” Saurin girgiza kaina nayi kwalla na cika min idanu.

“Mai martaba kaine kafi karfina. Kai fa sarki ne, sarkinma mai tarin abubuwan kwatance a gaban wasu sarakunan. Kai dan gatane mai tarin ilimi da nasaba. Kai jinin mulki ne dan masu mulki jikan masu mulki. Kai mai ilimi ne da tarin dukiy…….” 

“Shiii….” Ya fada da sauri yana kada min idanunsa. Zai yi magana nima na girgiza masa nawa kan hawayen da naketa kokorin rikewa suka zubo min a kumatu.

“Ka barni na fadi abinda yake gaskiya dan Allah. Muna da banbanci sosai, kanada tarin abubuwan da suka ninka wadanda na fada a baya. Ni kuwa talakace, yar talakawa gaba da baya. Yar kauyen kayau. Bawani tarin ilimi ne da ni ba. Ba wata nasabar kwatance ce da ni ba. Bani da wani abunda tarihi zai nuna matsayin dangantaka ta. Tayaya kake tunanin zaman aure zai kasance a tsakanina da kai? Hakan tamkar tauyewa kanka da martabarka kayi a matsayinka na sarki.  Sarkinma da ko a gaban wasu sarakunan sarki ne. Kayi hakuri matarka tafi cancanta da samunka dan itace ke gogayya da kai bisa duk wadannan abubuwan dana lissafa maka takawa. Ni kuwa ka barni na tsaya dai-dai matsayi na kamar zaifi dacewa da ni nim………”

Saukar tausasan labbansa akan nawa ya hanani karasa abinda naso fadan. A karan farko naji bazan iya hanashi yin hakan ba a gareni dan shi d’in mutum ne mai son ganin farin ciki na. Nima sai kawai na lumshe nawa idanun tare da kankamesa saboda tsumar da jikina kemin da gudun da zuciyata keyi tamkar zata faso kirjina ta fito. Haka shima Ina Jin tasa bugun zuciyar.

Tun ina daukar al’amarin nasa karami harya fara zarta gajeren tunanina. Dan kuwa da gaske sai ya tabbatar min tunanina gurbatacce ne. Sai da ya tabbatar nayi laushi bani da ko karfin yin numfashi mai nauyi kafin ya barni. mirginawa yayi ya koma kasa ya maidani saman jikina. Cikin wata kalar murya mai rauni da laushi yace,

“Duk wadannan abubuwan bazasu kasance nawa ba sai da ke gimbiyar Salman. Ki yarda kece mahadin rayuwar Salman bin Aliy. Babu ruwana dake wacece, Babu ruwana da nasabarki, babu ruwana da iliminki, babu ruwana da abinda wani zai fada a kanki. Ke nake so a hankanki. Tarbiyyarki ta isheni komai. Please ki yarda na nuna miki matsayinki a gareni Khadijah. Ki yarda na nunama duniya ke wacece a gareni. Ki yarda na shelantama masu mulki irina su san cewa ba sai mace tana da irin nasabarsu ko nagartarsu bane ta cancanci zama matarsu. Ki yarda nayi koyi da mahaifina Khadijah. Dan shima ya auri mahaifiyata da irin matsayin da kike ganin kanki da shi a lokacin da yake matsayin sarki. Wannan shine sanadin girmama kiyayyarta da tamu a cikin masarautar basannabas. Me yasa bazaki amince tarihi ya sake maimaita kansa ba a garemu dan mu sake zama mabudin karya lagon kaifin duk wani jahilin dake tunanin yar mulki sai dan mulki? Talaka sai dan uwansa talaka.” 

Hawaye nake cigaba da zirararwa ina saurarensa. Ya sake dora bakinsa kan kunnenna yana rada sosai yace, 

“Ki bama Salman bin Aliy bin Salman dama Khadijah. Na miki alkawarin a wata daya kacal sai na canja zuciyarki ta zama mahadin tawa.”

Babu shiri na dago da sauri muka hada idanu. Wani sassanyan murmushi ya sakar min yana kashe min ido daya da dage gira yace, 

“Na yarda da kaina.” 

Sosai yanda yayi maganar ya bani dariya. Nai saurin fisge jikina na sauka daga nasa nai gefe ina murmushin daya subuce min ba tare dana shirya ba.

Shima murmushi yake yi dan har ina jiyo sautinsa. ya murgino ya kwanta a bayana yana sake fadada sautin murmushin nasa.

“Gaba daya y’ar jarida kin maida Salman kamar ba sarki ba. Ni mantawa ma nake da wata sarauta idan ina a gabanki. Da gaskefa a kanki na yarda sarki a cikin gida bawa ne matarsa ke zama sarkin. A waje ne kawai muke fankama da bude hanci.” 

Ai bansan na fara kyalkyala dariya ba da wannan maganar tasa. Sosai na shiga yinta shima kuwa yana tayani. Nace, 

“Karka saka yan masarautar nan su halakani lokacin mutuwata bai yi ba.”

“Ashe kuwa suma duk zasu halaka dan mayaki na gaske zan koma.”

“Tab, ai nasan yanda kake din nan kullum a kwance ba karfi zaka yi ba.” 

Nai maganar ina kokarin tashi zaune. Saurin rikoni yayi na fado kansa. Ya sake tura idanunsa cikin nawa yana wani kankance su.

“Karki damu, zamu shiga filin daga nan da lokaci kankani. Kinga sai ki banbance idan zan iya ko bazan iya din ba.”

Ban fahimci inda ya nufa ba. Amma yanda yayi maganar ne cike da shakiyanci ya sani ji a jikina da wata manufa ya fada. Nai saurin kwace jikina ina fadin,

“Ni Dije meya hadani da yaki ina mace. Ai sai ku maza.” 

Dariya yayi shima yana tashi zaune. Yace,

“To, lokacin ne dai zai nuna mana ai”.

A takaice dai duk yanda naso yabar dakin ki yayi, yabi ya katantaneni dole sai na yarda da alkawarinsa na cewar a wata guda sai ya canja zuciyata ta koma mahadin tasa. Rashin mafita da son ya barni da kunyar data gallabeni tasa a yau nace na amince. Amma idan ya gaza nima zai cika min nawa alkawarin na barina na koma rayuwata dana tashi a ciki.😂👩🏽‍🦯👩🏽‍🦯

A mamakina sai naga babu musu ya amince yana wani shegen murmushi. Da kallo kawai na bisa har yaje kofa sannan ya juyo. Salute dina yayi yana wani yin salo da yatsunsa kamar wanda yake harba bindiga. Ya kashe min ido daya da cewa,

“Daga yanzun wasan ya fara.” 

Baijira nayi magana ba ya fice abinsa yana cigaba da murmushi.

Sai da ya fita da kusan mintuna goma kafin na dawo cikin hankalina da fahimci ramin dana zurma kaina. Me yasa na amince da wannan game din nasa ni Dije?. gaba daya kaina ya birkice na kasa zaune na kasa tsaye. Jinake kamar na bishi sashensa nace na fasa. Haka naita zirga-zirga. Sai nayi kamar zanje sashen nasa sai na kasa na dawo na zauna. Zuwa can saina sake zabura na mike. Da naje kofa kuma sai na sake dawowa kamar mai basir din daya hana sukuni.

***

A sashen sarki Salman kuwa tunda ya baro sashen dije fara’a ta kasa barin fuskarsa. Kadan-kadan sai ya saki murmushi yana wani lullumshe idanu. Shi kadai yasan me yake kitsawa a ransa game da wanan game din nasu shi da Khadijah. A gefe kuma dariya yake mata dan ya sake fahimtar zallar kuruciyarta.

A dai dai wannan lokacin Shaheedah ta shigo, Idanun sa a rufe ta same shi, Yana murmushi shi kadai, Ba ka’dan ba yanayin sa ya dagawa Shaheedah hankali, Tasa hannun ta karkada su a kansa, Amma ina SAS yayi nisa a kogin tunanin Khadija daya tafi..

“My king…. Salman….”

Riko hannun ta yai, Duk daukar sa ya dauka Khadija ce, Zai rungumo k’ugunta kenan yaji kamshin turaren jikin ta ba irin na Khadija bace, Khadija na saka wasu turaruka masu ratsa zuciyar sa, Kuma a jikin ta kawai yake jin kamshin, Ita kuwa shaheedah har wani kauri kauri na magani yaji tana yi, Don haka ya waske yana dafe kansa…

“Jiri nake shaheedah… Ki tallafe ni.”

“Sannu My king…” 

Riko shi tayi ta temaka masa ya kishingida a doguwar kujera, Sai gumi take kallo d’aya zaka mata kasan batada gaskia. Amma tsabar kishi ya rufe mata idanu sam ta kasa daidaita kanta,

“Ya nagan ka cikin kananun kaya…? Kasa turaruka da yawa. Kana Zaune anan kana murmushi Kai kadai.. Salman bangane ba.”

Duk da yana cikin halin acting, Sai daya kasa danne dariyar sa, Ya danyi murmushi yana jan numfashin ciwo kamar gaske..

“Heeeedah…! Menene baki gane ba? Wani yanayi na shiga, Kwana biyu keda waccen… Kun dauke mun kafa, Sai na samu kai na da tuna baya.. Sanda ina school,Muna moot a court. Shine kawai.”

Shaheeda tayi murmushi tana gyara zaman dankwalin kanta.

“Kwana biyu tun ranar dana karb’u kudin nan awajen ka nake fama da zazzabi.. I’m very sorry for not checking on you. Kaji?”

“Nine me laifi da banajin lapiar ki.. Kiyi hak’uri.”

“Ka tashi ka koma daki ka kwanta to..”

“Tohm bari ya dena ciwon zan tashi.”

“Ina ita waccen din…?”

“Wa kenan…?”

Ya tambayeta yana sane. Ya Kara da cewa

“Akwai wata bayan ke ne..?”

Girgiza kai tayi cike da jin dadi, Ta mike tana gyara rigarta.

“Tunda baka da lapia yanzu… Zan dawo da safe, Nayi kewar ka. Kagane ai.”

Juyar da kansa yai gefe, Saboda yadda turaren datai na hayaki yake hawa kansa. Sumba takai masa gefen kumatun sa, Dak’yar ya tsaya tayi yana murmushi. Ficewa tai a hankali tana karkada jiki. Shi kam shaheeda na bashi Mamaki, Sam babu tarairayar miji, Tun farkon auren su bata damuwa da yaci abinci ko bai ciba, Damuwarta kawai tasani. 

 GIM. KHADEEJAH! 

Duk na gama sauraron abubuwan da suke cewa Shi da ita, Wani nai dariya wani na bata rai.. Wai waccen…! Na maimata a hankali ina gatsine. Na hararo kofar kawai na juya na sauka kasa. Dakin sirrin sa na shiga, Bayan na danna password. Na zauna akan kujera ina kallon kowacce computer, Ta sashen shaheeda da tawa. Ganin duk ba wani abun kirki sai wulgawar dogarai, Ahankali nasa hannu na na danna recording din baya wato wanda ya wuce bana yanzu datake dauka ba. 

Shaheeda na hango tana tsaye a dakin ta.. Ba kaya sai zani data daura, Nai saurin juyar da kai na, Can sai ga ta kuma ta dakko kaskon turare, Ta banka wani garin magani a ciki, Tuni hayaki ya gauraye, Ni da nake gani ta na’urar computer sai da na dena ganin komai tsabar hayaki. Inaya ita dake cikin wannan hayakin? Shin bazai illatata ba? 

“Subhan’Allah….!”

Najiyo tamkar murya a baya na. Kan balai nasan ni kadai ce awajen wani tsoro ya shige ni, Ban yi aune ba sai ji na nayi a jikin mutum na kwakwume shi. Ahankali ya shiga shafa bayana yana kwantar mun da hankali..

“Ssssssh! Isssokay.. Menene? Uhm.. Na baki tsoro ne? My badddd.. Kiyi mun afuwa gimbiya tahh, You are my Queen.. And my little heartbeat, I will never play with your heart. As I only want to see you glow with happiness.. Khadijaaa, If I could I would give you the universe and a constant state of pure bliss. Love you to the moon and back baby love…”

Ahankali na zare jiki na daga nasa, Na shiga nuna masa cikin computern, Dai dai lokacin da Shaheeda ta zaro kwado daga leda da makulli ajikin sa an d’inke da zare, Tamkar laya ce a bakin sa.

“Innalillahi wa’inna ilaihirrajiun….”

Na shiga furtawa Ina jujjuya kai na, Salman ya janyo kujera ya zauna yana kallon screen din tamkar idanun sa zasu fado, Juyawa nai zan fita ya janyo ni jikin sa ya zaunar da ni a cinyar sa, Na kalle shi ya kashe mun ido d’aya, Cikin kunnena ya radamun,

“Haba dai… Matsoraciya ce ke dama? Yanzu fa wasan zai fara.. Tun bamu soma ba yanaga kin fara karaya.. Uhm? My Love! Kiyi hak’uri kidena tsoron komai, Salman bn Aliy ibn Salman na tare dake..”

Yana magana yana shafa gadon bayana.. Ahankali na daga kai na ina maida duba na ga computer, Hijabi muka ga ta zura, Ta daura nikhaf, Can sai kuma na maida kallo na ga na’urar dake haska sashe na, Na lura ba dakaran tsaro ko d’aya, Sai ga shaheedan nan da hadimarta sun shiga har sashena, Wajen d’aya daga cikin shukata suka tsaya, Ta baya inda ba’a ganowa. Nan suka tono shukar suka zura kwadon, Wani tsoro ne ya shige ne na rirrike jikin Salman ina jujjuya kai na,

“Dena kallo kinji… Bara na karasa gani sai nasa acire.”

Juyawa nai na dena kalla, Saboda bazan iya jure kalla ba, Shi kuma Salman ya kara kallon komai, 

“Love… Ba ni wayana a gefe kinji.?”

Dakkowa nai na mika masa, Ya karba ya danna wata number ya kara a kunnen sa,

 “Falaki…… Zan turo maka wani shot clip yanzu, Kaje da kanka ka tono, Ka ajiye shi, Saboda nan gaba kadan Zan neme shi. Amma kafin sannan akwai wani laya aciki ka samu masana ilimin tsibbu su fassara maka ita, Wanda ya fassara dinma zamu neme shi idan lokaci yayi.. Yes! Nagode.”

Juyowa nai zan masa magana… Yai hanzarin saka harshen sa cikin baki na, 

“Say no more love….. Yanzu wasan zai fara..”

“Wasa kuma….?”

Na fada ina numfashi ahankali Saboda sunbar daya kaimun ta bazata…..

_Ahh sai zagin dije ake😂👩🏽‍🦯 fisabilillahi dole taja aji😒wayace ya aureta bada yarjewarta ba? Bayan sun gama tsara rayuwar auren su da Mahboub ne ko masoud😂💔 kawai ya aure yar mutane.. Koma dai menene kunfasan tawajen ku da halin nata..inde kafiya ce to oganniya A ce🤦🏼‍♀️ Tawan (billyn A) Inde kika kara zage dije to yasin sai an kusa Kai ruwa rana akan ta😂Sai Salman din da kike ji dashi ya jigata.. .. Muci gaba da bin labarin yar mutan durbun a sannu🏃🏽‍♀️… Na gaishe ku.. GAISUWA mai kima🥰❤️_

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 27

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 29

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…