KIBIYAR AJALI 22

Advertisement

 

*2__2*

 

 

*SAS*

 

    *Yana* zaune a bayan mota driver yana janshi, gaban motar tashi motar yan sanda ce masu kula da lafiyar shi. Bayan kuma ta manyan yan fadarsa ne sai kuma ta dogarawan shi. Gabaki d’aya tunani ya

tsaya masa ganin yau ne ranar daurin auren shi, gashi babu wanda ya sanarwa zai yi, sannan be gayawa dangin yarinyar cewa zai yi tafiya mai nisa ba yau din, to wa zai yi masa wakilcin auran? Ya samu an bashi yarinyar cikin mutunci be dace ace ya nuna rashin damuwa da lamarin ba, kar suyi tunanin bashi da kirki. Tunanin tsayar da driver din yake a ransa, amman bakin shi ya gaza budewa dan ya sanar da shi cewa ya tsaya.

 

Advertisements

Da kyar da dauriya Salman ya bude d’an karamin bakin sa yace wa driver ya tsaya, ya kuwa sanya signalya koma bakin titi ya yi parking. Nan da nan sauran motocin ma suka tsaya, yan sanda suka yi saurin fitowa tare da zagaye motar da yake ciki. Waya ya dakko ya kirawo Turaki da suke dayar motar yace dashi.

 

“Ina son mu koma akwai wata magana da zan yi daku.”

 

“Ranka ya dade da mu karasa airport d’in, tunda a Abuja zamu sauka kafin lokacin tafiya Cyprus d’in sai a zauna in ba damuwa. Allah ya taimake ka.”

 

Da kyar sarki Salman ya sake bude bakin sa saboda yadda yake jin wahalar magana yace.

 

“Tana da muhimmanci ne.”

 

Turaki ya kalli Galadima dake gefen shi da alama ransu ya baci saboda so suke yi kawai ya yi tafiyar nan koda kuwa ba za ta yi masa dadi ba. Amman dan kar mutanan da suke tare wato dogarawa da yan sanda su fuskanci wani abu sai suka amsa masa. Nan Turakin ya sanar da yan sandan cewar zasu komai gida, mai martaba yana son ganawa da yan fada. Haka kuwa aka yi nan da nan akai convoy suka koma masarautar Basannabas. Daidai shiga fada suka yi parking saboda sun san zai kuma fitowa ya shiga motar shi yasa basu kai ta ma’adanar su ba.

 

Advertisements

Yana fitowa fadawa suka fara yi masa kirari irin wanda ake yiwa manyan sarakuna masu ji da mulki, yana taku day-daya kamar baya son yi a haka har suka karasa cikin fadar. Cikin wani amintaccen parlor da yake zaman sirri da yan majalisar sa, Bayan sarki Salman ya zauna akan kujerar shi, sai sauran ma da day-day suka dinga kai gaisuwa suna samun gurin zama kasan cewar kowa yasan a inda yake zaman shi yasa zaman fada yake kasancewa cikin ladabi da biyayya. Sai da kowa ya zauna sannan waziri ya gyara zama kansa a kasa yace.

 

“Na gaishe ka sarkin sarakuna, d’an sarki jikan sarki. Allah ya kara maka lafiya, munji kace a dawo gida Allah yasa dai lafiya, Allah kara maka lafiya.”

 

Sarki Salman ya kalle shi ta cikin bakin gilashin sa, tare da kallon kowa dake zaune. Murya can kasa kasa yace.

 

“Lafiya.”

 

“Allah ya karawa sarki lafiya.”

 

Duk suka hada baki wajan fada, Ya murza idanuwan shi, shi kansa yasan maganar da zai yi musu yanzu sai tasa sun rai na kan su. Amman duk da haka zai gaya musu saboda ya zama wajibi su sani, sannan a yau ne za’a kawo amarya kar yaje a yi musu rashin mutunci bayan an bashi yarinya a karramance. Kamar ba zai yi magana ba sai suka ji yace.

 

“Ina so na sanar daku wani abu.”

 

“Girmanka ne ranka ya dade, fadi duk abinda yazo bakin ka muna saurara ya sarkin mu na adalci, Allah kara maka lafiya.”

 

Ya kuma jan numfashi ya sauke tare da kawar da ido daga kallon da yake musu ta cikin bakin gilas din shi yace.

 

“Yau da karfe goma sha d’aya za’a daura min aure.”

 

Galadima, Ciroma, Wambai da sauran tsirarrun mutanan gurin suka zaro idanuwa suna kallon sarki Salman, yau kam bakin gilashin sa yafi koda yaushe kona musu rai saboda sun so su kalli cikin idanunsa dan tabbatar da maganar da yake gaya musu a daidai wannan lokacin. Sai dai ina basu gani, haka kuma kanshi a sunkuye yake da alama jiran su yake suyi magana a kai. Waziri ne ya rissina yana fadada murmushin fuskar shi ya miƙa gaisuwa yace.

 

“Wannan duk damar ka ce ranka shi dade, sai dai wacece wannan wace tayi matukar da ce da samun ka a matsayin miji.?”

 

Daman sarki Salman yasan waziri ne zai yi farin ciki da duk abin da zai yi, sabanin sauran da basa iya bude bakin cikin su sai sun bayyana. Salman ya kuma yin kasa da murya yace.

 

“Khadija.”

 

“Masha Allah, yar wajan Wambai ko? Gaba salamun baya salamun sarkin sarakunan mu, wannan abu ya yi kyau.”

 

Wambai da yaji an kira sunan cewa yar shi sai ya fara washe baki duk da cewa yasan yarinyar ma ba ta wani isa aure ba, yanzu ta cika shekaru tara. Amman da yake son zuciya yana tattare da shi sai ya yi tunanin auren za’a yi sai ta kuma girma sai ta tare a gidan. Maganar sarki Salman ita ce ta dawo da tunanin da Wambai ya tafi, inda yaji yana cewa.

 

“Ba ita ba ce, wannan ba ta shafi jinin sarauta ba, yau da karfe goma sha daya na safe  za’a daura, idan an gama komai zan tafi airport sai kuma na dawo.”

 

Tashin hankali wanda ba’a sanya masa rana, duk irin sanyin a.c dake ratsa cikin fadar, su ciroma gumi kawai suke yi dan basu taba zato ko tsammanin haka daga wajan Salman ba. Shirya yin aure ba tare da ya sanar da kowa ba har sai a ranar da za’a daura, babu shakka wannan yaron ya fara raina su dole su kara tashi tsaye ta yadda ba zai kuma aiwatar da komai ba sai ya gaya musu.

 

“Ahh to ai sai a gaya mana wajan daurin auran dan muje mu halarta kar aga duk babu mu a wajan.”

 

Waziri ya fada yana nuna farin ciki da wannan auran. Salman yaji dadi da waziri yace za shi wajan daura auran har ma da karbar ragamar yi masa wakilci a maimakon shi da yace zai karbi abin shi da kanshi. A takure duk suka zauna har lokacin da dogaran sa suka shigo suka kakkare shi ya mike ya fice.Gashi waziri ya hana kowa tashi daga gurin sai da Salman ya kalli agogon hannunsa yace ya kamata su tafi dan kar iyalin su suyi ta ta jiran su. Galadima da Ciroma dai basu bisu ba saboda sam basu da nutsuwa, gashi suna so suyi magana tare da kamo hanyar da suke tunanin zata bulle musu.

 

°°°°°°°°    °°°°°°°°°

*KHADIJA (DIJE)*

 

Tun ana gobe daurin aure nake fama da wani irin zazzabi amman na kasa nunawa dan karma a bani magani saboda na san ba na shan magani bane zazzabin. Yadda naga rana haka naga dare, asubar fari na shiga nayi wanka nayi sallah sannan na koma kan gado na yi kwanciya ta ina tunanin rayuwar da zanyi a nan gaba. Yan matan da suka fara cika mana gidan ne suka shigo dakin sai ihu suke yi, nan da nan kai na ya fara ciwo na yi ta rintsa idanuwa.

 

“Ke Dije waye yace miki amarya tana bacci ranar daurin auran ta? Wallahi ba zaki bacci ba hauka ma ke nan.”

 

“Tashi kisha tsumi yarinya saboda karma angon ya raina mana ke.”

 

“Wai shi angon nan ba zai bayyana kanshi ba, sai kace wani mace yana ta boya kanshi.”

 

Gabaki d’aya suka isheni da surutu na banza da na wofi da ba wani farin ciki yake sani ba sai bacin rai da damuwa. Ana cikin haka sai ga matar kawu Kabiru ta shigo hannunta dauke da boul ta tashe ni, sai da na zauna sannan ta miko min tace na cinye na kuma shanye roman kar na bawa kowa. Haushi ya cika ni na dinga hararar kazar da roman ina jin kamar zan yi amai saboda rashin son ci da ba nayi. Ina ma ace Mas’oud ne, wallahi tallahi da kai na zan fara gyara ba ma sai anyi min ba. Haka dai na caccakuna ban cinye ba suka je suka gaya mata tazo ta sani a gaba har sai da na sude boul d’in ta kyale ni.

 

Ruwan wanka aka sake had’a min na musamman wanda yasha turarukan yerwa, hawaye yana zubar min haka nayi wankan na fito aka yi min kwalliya. Nayi masifar yin kyau mutane sai yankawa suke yi, ni kuma ina ganin akuya ma ta fini kyau a wannan lokacin saboda yadda nake jin kuncin zuciya da rushi.

 

Gidan fa ya cika yadda bana tsammani, a kuma sannan ne na jiyo ihu da shewa a  parlorn kasa, wai ashe kayan lefe aka kawo akwatuna ashirin da biyu da mukullin mota. Mami kam da ta gani sai da ta kusa hadiye zuciyar ta, ba ta yi zaton zan samu akwati biyu bama bare ace fiye da haka, sai gashi an kawo wanda hankalinta ya ke kokarin gaza dauka.

 

“Dije dan Allah ki gaya mana waye wannan saurayin naki?” Ya Waleedah ta tambaye ni lokacin ina zaune a gefen gado.

 

“Ni ma ban san ko waye ba.”

 

“Karya ki ke yi munafuka, baki sani ba zaki yadda a aura miki shi ne. Kin san me azxiki ne shi yasa duk kika ki gaya mana sai munafincin kuka da kike yi a baya wai ke bakya son auran. Kin dai san mu mun gaji arziki dan a cikin shi kika zo kika same mu, ke kuwa taka haye ce kowa ya sani.”

 

Ya Shukrah ta karasa maganar tana bugar min kafada.

 

“Rabu da ita abin da yau karya ta kare, yau zamu ga ko wanene take boyewa.” Ya waheedah taja ta suka fita.

 

Ni kai na da naji uban yawan kayan sai da na girgiza na fara tunanin waye wannan zai siye ni? Kwarai kuwa siya ta zai yi, banda haka ya za’a yi a ce an kawo min akwatuna ashirin da biyu sai kace wata sarauniya? Kiran Mas’oud ne ya katse min mamakin da nake ciki, na dauki wayar nasa jikin kunne na, yadda naji muryar shi a wani iri shine ya sake tayar min da tsananin hankali, yace dani.

 

“Wannan shine kira na karshe da zan miki, sannan ina miki fatan alkairi a gidan da zaki shiga, naga sauran yan lokuta ki zama a karkashin wani. Amman dan Allah ki sanar dani waye zaki aura?”

 

Na fashe da kuka na kasa yin magana, nifa gani nake kamar karya ne ba za’a raba mu dashi ba, har yanzu ina ganin wannan al’amarin tamkar mafarki.

 

“Ki gaya min ko waye.”

 

“Wallahi ban san shi ba Mas’oud har yanzu, amman naga kowa yana jin haushi na akan cewa na sani kawai fada ne ba zan yi ba, kuma wallahi Allah ban san ko waye ba har yanzu ka yarda dani Mas’oud.”

 

“Shikenan na yarda dake. Ina miki fatan shiga gidan miji lafiya… Bye Khadija sai wata rana….”

 

Ya katse kiran naji kit, kawai sai na saki wani marayan kukan mai ban tausayi. Shigowar Aisha ta zauna gefena ta na lallashi muka ji ana cewa yan daurin aure sun zo har da ango. Dan gidan sarauta Dije zata aura, to waye a ciki? Me ne ne matsayin sa a cikin fadar masarautar Basannabas? Nan fa kowa ya kasa kunne dan sauraran jin waye angon Dije. Cikowar unguwar kuwa ba a magana, ashe Alhaji Isma’il gayya ya yi sosai ba tare da sun sani ba. A cikin masallacin jikin gidan aka tabbatar da auran Nana Khadija Basheer da Sarki Salman Aliyu Salmanu (SAS) akan sadaki mafi daraja…

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like