Advertisement
_I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_
_KIBIYAR AJALI…..!_
_(sulke baya tare ta sai ta wuce)_
_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_
Advertisements
_PG:22_
_BOOK:2_
_Masu bukatar makeup.. Casual, special casual, simple glam, bridal makeup, fixing of lashes, gele and turban, modeling. Sai ya tuntubi BEELANAH BEAUTY.. Instagram handle: Beelanah_Beauty… Tana court road, Kusa da novomed, kano nigeria. 08034697302 Domin nemanta ko karin bayani sai a tuntubeta ta lambarta👈🏼Available to travel. #blush it up 🥂_
<><>
……Cizon lips dina da hakori na, shi kuma ya yi saurin tashi daga zaune ya karaso guri na dan ya bani taimako, nasa hannu na da karfi na riko nashi ina gwalalo ido, magana cike da tashin hankali.
“Salman please me yake faruwa dani? Me nake ji a jikina ka sanar dani dan Allah.”
Magana nake yi Ina kuka hawaye suna sharara akan kumatu na, zuciya ta tana zargin tabbas mun kasance abu daya da Salman wanda nake ta boyewa dan zuwa nan gaba. Girgiza kai kawai nake Ina addu’a Allah yasa ba tunani na bane, Ina son idan mafarki nake yi nai gaggawar tashi dan kuwa ya firgita ni matuka. Amman kuma me? Sai naga Salman yana kokarin rungume ni da son lallashi na, nai saurin ture shi Ina cewa.
Advertisements
“Me kayi min dan Allah? Ka sanar dani kace min babu abinda ya faru damu Salman please ka gaya min gaskiya.” Na karasa magana cikin fashewa da kuka.
Jikinsa yana rawa ya kuma nufo ni tare da kamo fuskata yana son mu hada ido amman na hana hakan faruwa idona a rufe so kawai nake naji dadin bayani a gurinsa. Zugin da nake ji a kasa na shine yake kuma razanani, gashi shi kuma ya kasa cewa komai sai son mu hada idanu da yake yi.
“Kiyi hakuri m…”
Ban bari ya kai karshe ba nai saurin cewa.
“Innallilahi wa’inna’ilaihir rajiun, wayyo Allah Salman ka takaita ni. Daman wannan shine dabararka a kai na? Dama shi yasa kace ka shirya mana wasanni?”
Kukan da ya kuma sarke ni shine yasa ni yin shiru Ina jin rai na yana zafi. Lallai kuwa ya raina min hankali fiye da tunani, sai yanzu na gama gane inda ya dosa amman a baya babu abinda nake ganewa sai shirme. Kamar zai yi kuka da alama yasan laifin da ya yi min, yace dani bayan ya durkusa guiwarsa a kasa ya dora ta hannayensa a gefen gadon yana faman dafe kai yace.
“Ina sonki ne Khadija, kuma banyi miki haka dan wata mafita ba sai dan kare mu daga sharrin da ake jifan mu dashi. Dan Allah ki saurare ni my love wallahi Ina kaunarki ban yi miki haka dan mugunta ko son zuciya ba, kuma wallahi da a lokacin kin nuna min bakya so ba za….”
Cikin jin haushin kalamansa, wadanda suke kuma sosa min zuciya na dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu tare da cewa.
“Kafi kowa sanin ina so ko bana so, tunda kasan ban shiryawa zama da kai ba cikin wannan masarautar mai cike da tashin hankali. Ni duk ba wannan ba, tunda ka yi abin da ranka yake so kazo ka mai dani sashe na Ina son zan yi wanka.”
“Dan Allah ki tsaya kiyi anan karki fita a haka.” Ya fada kamar zai fashe da kuka, haushinsa ya kamani nace.
“Bazan kuma yin minti goma a nan ba, idan ba zaka taimaka na tashi ba ka barni zan tashi da kai na.”
Ganin ina shirin tashi yasa shi saurin taimaka min na zauna, sannan ya kamo hannu na amman na kasa motsa kafafuwan. Amman da yake yan kafiyar suna nan sai da na yunkura na mike tsaye da taimakonshi, Ina ganin na tsaya akan kafafuwa na sai na ture masa hannun, na daga kafa zan yi tafiya na kasa yi saboda axaba da zugin da naji, ban san lokacin da nakai hannu na riko shi ba da yake yana tsaye a kusa dani.
“Kiyi hakuri na taimaka miki dan Allah.”
Ya zanyi dole na barshi idan ba haka ba ban san yadda zanyi na taimaki kai na ba, haka ya dauke ni gabaki daya ya kaini bathroom inda na fara tunanin abinda suka faru kafin na jini cikin yanayin da nake ciki. Already ya tarar min ruwa a bathtub hakan yasa muna shiga sakani kawai ya yi a ciki, zafin ruwan da naji a kasa na shine ya sani saurin riko masa wuya Ina sakin siririn ihu.
Ya rike ni sosai yana shhhhhh alamar nayi shiru, na dago cike da hawaye na galla masa harara yai saurin yin kasa da kai, be yi dariya ba saboda yasan shi din mai laifi ne. Sai da ya tabbar ruwan ya ratsani na rage jin radadin sannan ya bude gurin da ruwan yake wuce wa ya sake tarar min wani duk Ina kwance a cikin tub d’in.
“My love..In marriage, romance is the icing and love is the cake. Ina sonki kamar yadda na sha gaya miki a baya, The heart wants what it wants, and as it seems, my heart wants nothing more than to be with you. Ba kuma wai wani sashe nake so a jikin ki ba no. Ke d’in ke nake so khady, kuma wallahi lokacin da abubuwan suka faru kice kika dinga kamo hannuna kina kaiwa wasu sashen da dole muka kasa hakura da juna.”
“Wait…! Kana nufin ni yar iska ce kenan, ni na fara nemanka ko me kake nufi? Kuma Allah ni ba nice na fara ba me yasa ka dage Sai na kwana a dakin ka?” Nai magana Ina kuka mai cike da shagwaba wacce bamma san nayi ba.
Cikin lallashi ya rike min hannu ganin Ina shirin kai masa duka, ya sake matsowa da yake yana durkushe wajan tub d’in, yana shafa min gashi yana cewa.
“No… No.. No my baby, ta ya za ai nace miki haka? Abin da nake nufi shine, kece idan na kai hannu na kan ki kamar idan nayi haka…”
Ya dora hannunsa saman kirji na nai saurin bugewa Ina turo baki, shi kuma ya yi murmushi kasa-kasa yadda bazan ji ba dan yasan a harzuke nake yaci gaba da cewa.
“Toh shine ke kuma sai ki sake riko ni kina kara matsa min hannu alamar dai kema you need mo…”
Ihun da nai ne yasa shi saurin tashi tsaye yana dube-dube duk a tunaninsa wani abun tsoro na gani, ni kuma karshen zancen nasa ne bana so shi yasa na saki ihu mai hayani dan ya yi shiru kuma yayi d’in. Ya juyo yana bina da ido na murguda baki Ina cewa.
“Ni kazo ka fita.”
Ya koma inda ya taso yana fadin.
“Kin bani tsoro fa, wallahi nayi tunanin wani abun kika gani. Kuma idan na fita waye zai taimaka miki.”
“Allah ne.” Na fada cikin tsiwa.
Salman ya sauke numfashi ya kuma kokarin saka hannu a ruwan nace.
“Ni bana son taimakon ka yi tafiyarka.”
Babu yadda zai yi dole ya tashi ya fita tare da jan kofar, Sai dai be yi nisa ba a jikin kofar ya tsaya yana jiyo ta tana kuka tana mita har ta kammala sai dai duk da haka ta kasa fitowa daga tub d’in. Jiyo ta kawai ya yi na masifa tana Kiran shi.
“Wai kana Ina ne.?”
Dariya ce ta kufce masa, yayi saurin saka hannunsa ya toshe baki da kyar ya maidata. Ya gyara fuskarsa kamar baiyiba sannan ya bude ya shiga. na kawar da kai na gefe ina cewa.
“Toh kuma ba zaka zo ka fito dani ba?”
“Korata kika yi ne ai hajiya”
Yana maganar yana wani hade fuska. Cikin tura baki nace,
“To haushi kaji?”
“Sosaima kuwa”
Ya bani amsa yana zaro min sabuwar rigar wanka yazo ya nannade ni a ciki tare da daukata gabaki daya muka fito.
Zai kwantar dani akan gadon sa nai saurin riko masa wuya Ina faman hade rai nace.
“To kayi hakuri tunda kaji haushi. Ai kai dinne da laifi. Kuma ni dai Sashe na zaka mai dani, daman ai har gorin riga kayi min”.
Kallo na yayi domin daukar jarirai ya yi min, na rufe ido Ina turo baki kawai naji ya sumbace ni akai na bude ido ina cewa.
“Ka bari dan Allah ina da alwala.”
“Ai naga ne duk kin zama me tsiwa, gwara nayi maganinta kafin sadakina ya gama hucewa”
“Okay, ashe da mugunta dama kayi? To Ka kai ni daki na ni”
Sosai ta bashi dariya. harya kasa dannewa sai da yayi kadan. Yace,
“Ina ni ina yima gimbiyata mugunta. ?kawai dai a cikin game ne. Kiyi hakuri kiyi sallah ki huta sai na kai ki.”
“A’a bana son nan.”
Babu yadda zai yi haka ya nufi sashe na Ina ta faman tsuke fuska, a kan bed ya kwantar dani sai faman cije baki nake saboda har yanzu Ina jin zugi. Wardrobe dina ya bude ya dinga karewa kayan nawa kallo kafin ya zaro guda, daya, yana warwarewa yaga doguwar riga ce Abaya, ya nuno min nayi kamar ban san me yake yi ba yace.
“A dako wannan.?” Cikin son kona masa rai nace.
“Bana so ka barshi zan dakko da kai na.”
Sai yaki jin haushin Sai ni da raina ya kuma sosuwa.
“Haba hajiya ai ba zaki Iya bani haushin ba, ki bari dai ni da na jangwalo nayi miki komai.”
Idanu na gwalalo waje. dan na fahimci a fili nai maganar ashe. Ganin ya kalloni nai saurin dauke kai na, na share shi kamar ban ganiba.
Shima watsar dani yayi ya juya ya ciro min riga da zani na atamfa, inda nake ya dawo fuska babu alamar wasa ya taimaka min nasa ya saukeni kan sallaya sannan yace min.
“Kafin ki idar bari naje na shirya sai nazo nayi jinya.”
“Ka barshi ni dai bana so.” Nai maganar a hankali kaina a kasa. dan inhar ya cuskule fuskarnan tsoron kai masa wargi nakeyi. kusa dani yazo dab da fuskata.
“Haba baki da lafiya fa, idan anzo ance meke damunki ai ni zan gaya musu. Kedai kawai kiyi sallah tare da addu’ar Allah yasa mufi haka kusanci, Allah kuma yasa yarima ya isa masaukinsa” ya kare maganar yana dora hannunsa a marata da wani kashemin ido cike da shakiyanci.
Harara na sake narka masa bance dashi komai ba na ture hannunsa na tayar da sallah.
Shi kuwa Salman dariya ya fita yanayi, ta dauka yana jin haushi idan ta harare shi ba tasan kyawunta yake sake gani ba, yana ganin tamkar shagwaba ce take masa ta soyayya. Juyawa yai ya koma sashen sa dan ya shirya kasan cewar yau yasan akwai bakin da zai ta gani a fada saboda taron bikin nan.
**
Ni kuma Ina idarwa na mike zan koma kan gado na kasa tafiya sosai, na saki kuka ganin babu mai taimaka min. bansan na furta sunansa ba ina hawaye. Babu yanda na iya dole sai na rarrafa na kama gadon sannan na dafa naje na kwanta ina tariyo duk abinda ya faru a daren jiya kamar a mafarki ko film. Tunawa na dinga yi wani abun inji haushin kai na saboda ai kamar yadda ya fada ne tana bashi gudun mawa wajan nuna son ayi, amman ita kanta ba tasan maganadisun da ya dinga janta ba har ta dinga biye masa.
Ina nan kwance cikin tunanin abinda ya faru, wani ya sakani haushi wani murmushi. Tabbas na sake yadda Sarki Salman yana so na. Sannan shi din na dabanne. Wai nice yau matsayin matar sarki salman, matsayin abu daya?. Wani iko sai Allah. Dije nan ta kauye mai dan karan jahilci da neman fada. Baiwar gajiyalle. Hawayen da suka cikamin ido nasa hannu na share. Samun kaina nai da dora hannuna saman marata saboda tuno maganar Yarima da yayi dazun. Lumshe idanuna nayi a hankali, sai naji knocking. ba damar na iya tashi hakan ya bawa mai bugun damar murdawa. Hadima tace kanta a kasa tai sallamar tare da durkusawa daga can bakin kofar tace min.
“Allah ya taimaki Gimbiya, munga baki sakko bane shine muke son ganin ko lafiya.?”
Gada sai na nemi na rikice, banda a kwance nake nasan tsab zan Iya faduwa. Yanzu me zan ce mata fisabilillahi? Na daure dai na ce mata.
“Karku damu kai na ne yake ciwo shi yasa. Kuje kuci gaba da hidimarku, yau biki kuma ku ci bikin ku.”
“Asha, sannu Gimbiya Allah ya baki lafiya ya yaye miki, ko maimarta ya sani? Idan be sani ba gwara a je a sanar dashi kar….” Na dakatar da ita.
“Karki damu na sanar dashi ta waya.”
“Toh shikenan ranki ya dade amman za’a kawo miki abinci ko?”
“No bana sha’awar komai idan anjima naji Ina bukata zan kira in sanar miki.”
“Toh ranki ya dade na barki cikin aminci da salama, Allah ya kara lafiya.”
Fita tayi na sauke ajiyar zuciya. A lokacin ne Salman ya shigo hannunsa rike da tea cup dayan kuma vanilla cake ne a cikin sosa. Lumshe ido nai tamkar mai bacci, har ya karaso kusa dani ya zauna ban motsa ba dan ko ido bana son mu hada.
Rankwafowa ya yi kai na tare da shafa min fuska idanuwana suka fara motsi still naki budewa.
“My love ki tashi kisha tea Kar Yarima na ya farajin yunwa”
Ko motsi naki yi.
“Okay bacci kike yi? Ba zai yiwu ba ki yi wannan abun kuma ki zauna da yunwa salon Kema ulcer ta kamaki Ko ta kama min yarima”
Yana kaiwa nan ya ajiye tea din a bedside ya fara Kokarin cire min hijabi nai saurin bude ido Ina turo baki.
“Ni dai gaskiya ka rabu dani.”
“Zan rabu dake amman Sai naga kinci wani abun sannan K da yarima”
“Na koshi ni. Wai waye yarima kabi ka isheni da zancensa”
“Zaki sanshi” yayi maganar yana wata munafukar dariya.
Fuska na sake ciskulewa nace
“To nama fasa cin”
“Ba zai yiwu ba my love. Dole kisha saboda yanzu da zan taho mukai waya da Ammi tace kina ina lafiya dai ko? Nace mata baki jin dadin jikin ki, tace to na tabbatar kinsha magani kuma kinci abinci kafin tazo dubaki. Dan na fada mata yau kin zam……..”
A mugun zabure na tashi zaune. Cikin rawar baki nace,
“Kace mata na zama me?”
Kwashewa yayi da dariya sosai.
Na zuba masa harara ina komawa na kwanta.
“Yi hakuri wasa nake miki bance mata hakaba fa”
Kin kallonsa nayi nasa hannu kawai na karbi cup d’in, a hankali na ke sha yana gutsuro cake d’in da fork ya samin a baki, ban ma san Ina jin yunwa ba sai da naga na shanye tea da cake d’in.
“Yauwa Good girl. Yanzu me kike ji? Akwai ciwo a gurin?”
Samun kai na nayi da daga kai still Ina ta turo baki gaba alamar har yanzu ban huce ba. Ya kwantar dani a hankali nayi rigingine kawai naga bawan Allah yana shirin daga min zani, da sauri na rike tsakiyar zanin Ina zaro ido cike da mamaki.
“Menene haka?”
Salman ya sosa habarsa ya kasa bari mu hada ido. Can kuma naga ya kalle ni tare da matsowa ya dafa kafadata yace.
“Duba miki zanyi ko wani abun ne a gurin, amman yaci ace kin mike tunda kin gasa dan nasan ba da karfi na….”
“Wai kai dan Allah meye haka? Kai yanzu Sai ka lek….” Na kasa karasawa saboda kunya, Sai kawai na ture masa hannun na juya tare da rufe ido.
Bakinsa ya kai kan hannu na ya sumbata sannan ya mike yana fadin.
“Sorry baby na tafi zan dawo na kuma ganin lafiyar ki, nasan lokacin kin huce ko cewa nai zan kuma zaki karba.”
Hannu nasa tare da toshe kunne na alamar ko yayi ba zan ji ba. Ina jinsa ya juya ya tafi yana dariya, ni kuma na bude ido Ina bin hanyar da uwar harara. Lallai ma guy d’in nan, ashe haka yake daman? Anya kuwa ba kwanan nan ya zama haka ba, dan idan ka ganshi ko yana maka magana Sai ka rantsa da Allah ba zai Iya wadannan abubuwan ba. Amman dubi yadda ya yi min, duk da cewa ma ni ya yi ne cikin rainin hankali, da Ace babu wannan game d’in da yasa ban san abin da zai faru ba sai Allah.
Ina cikin wannan tunanin bacci ya dauke ni mai cike da mafarkai. Muryoyin da na dinga ji ne yasa na farka ina murza ido. Wasu manyan mata na gani kai da ka gansu kasan cewar ko wacce ji take da kanta. Na sake ware ido bayan na juyo yadda zan gansu sosai, manya ne da kowacce a cikin su tayi uku na saboda girman halitta.
“Kece amaryar Salman d’in?” Wata farar mata sanye cikin wani shegen lace take tambaya ta.
Na sunkuyar da kai Ina wasa da hijabi na, suka girgiza kai dayar tace.
“Kece kishiyar Shaheedah kenan?”
Nan na ban amsa ba kuma ban kallesu ba saboda ban san dangin waye a cikin masarautar ba. Zagaye suka farayi na dinga satar kallon su kasa-kasa zuciya ta na ta karanto addu’o’in neman tsari. Can na jiyo muryar daya daga ciki ba wacce tai tambayar farko ba sannan ba wacce tayi tambaya ta biyu ba.
“Me yake damunki baki fito gurin shagalin ba.?”
“Bana jin dadi ne.”
“Wane irin rashin jin dadi ne bakya ji?” Samun kai na nayi da cewa.
“Zuciya ta ce bata min dadi, komai duhu nake Jin sa ban san dalili ba.” Na karasa magana cikin jimami.
Murmushi suka yi dukannan su sannan ta farkon tace.
“Kin sanarwa da Salman.?”
Na shiga girgiza kai alamun A’a kamar zanyi kuka na kuma dora hannu na a kai na da alama ko sunan Salman bana son su furta, kuma ban san dalilin da yasa nake yi musu wannan acting d’in ba, ko kuma dan sun ambaci Shaheedah ne oho min. Kamar hadin baki duk suka fita Ina jiyo dariyar su har wata na cewa.
“Lallai wannan aikin na Shaheedah ya fara aiki.”
Na sauke numfashi da karfi tare da rufe ido Ina sake yiwa Allah godiya. Wato da na nuna musu cewa na sanarwa Salman zasu yi tunanin Muna manne, yanzu da na nuna ko sunan shi bana son ji shine suke tunanin aikin bokayan su sun yi tasiri a gare mu. Oh duniya Ina zaki damu wajan son zuciya da neman duniyar ba ta hanyar Allah ba? Lallai Sai na yi taka tsantsan idan ba haka ba kuma na shiga uku daga ni har ganye na.
…Ni dai gaba d’aya har aka kusa kammala bikin su Munaya dakyar naje event biyu, Shima sai da na gayyato su ya shukrah saboda kar ace ba wani a dangi na da yazo, Dakyar suka yadda suka zo, Amman dai sun fidda ni kunya domin sunyi ado na kece raini. Nima nasha kyau cikin wani dakakken lace da Ammi tabayar aka kawomin a dinke, Lemon green da dark army green. Na nada laffaya itama rantsattsiya ta cikin kayan lefe na. Ba karamin kyau nayi ba. Event biyu naje na walimah/Budan kai. Daganan sai hawan sukuwa da akai da dawakai, Shima dan Abdullah ya haune shysa na leka banjima ba na dawo sashe na, Ko sau d’aya ban hadu da shaheedah ba, Naji dai ana cewa tazo events din da akai na baya. Ita tasani.
Duk wani abu da zai Kara had’ani da Salman a inuwa daya na guje shi, Y’ar wasan buya nake dashi yanzu. Bana taba bari ya rabeni saboda azabar danasha a hannun sa rannan, Har yanzu fama nake da kai na, Na kuma tabbatar wannan wasan ba irin nawa bane na manya na ne. Haka aka kammala bikin aka kai amare gidajen su. Sai fatan Allah yasanya alkhairi.
*****Ina kwance akan kujera na idar da karatu kenan, Na shiga tunanin yadda zan tunkari Salman da zancen barina naje gidan Kawu Daddy, Domin Tunda akai aure na banje ba, Inason na zazzagaya dangi ma inda hali, Amma tayaya zan tambaye shi bayan wasan buya nake dashi? Karar waya tace ta katsemun tunanin da nake,
‘Zawj habibyy..!”
Shine sunan da ya fito akan screen din, Na ware idanu ina sake karantawa. Nide sam bangane wanene ba don ban saving sunan kowa da haka ba. Wata zuciar ta sanarmun da Salman ne ya rubutawa kansa haka. Gaba na na faduwa na dauka ina raba idanuwa tamkar yana gani na..
“Hello……!”
“Assalamu Alaikum… Ya zawjati aleaziza .. kayf halika? ahbuk waftaqadk kathirana.. Deeeja! Kina jina?”
Yadda yake magana ahankali cikin wata irin murya yasa na sauke ajiyar zuciar da ban shirya ba. So yake ta karfi da yaji ya sururuta ni wallahi. Shiru nayi har sai da ya maimata sau uku,
“Barka da rana…”
“Nace miki ina son ki kuma nayi kewar ki sosai.. Babe.. I love and miss you so much. Meyasa kike hana idanuna ganin ki ne? Shin Kinsan yadda kike azabtar dani kuwa…? Zuma naaaaa.”
“Ai ni ba Y’ar iska bace..”
Nayi subul da baka, Ashe ya jiyo. Dariya najiyo yayi mai sauti. Yadda yake wani rage murya yana lankwasa harshe kai ka rantse da Allah da budurwar sa yake magana.
“Naji.. Inde akan ki ne.. Ni dan iska ne number daya. Kina jina? Love! Kefa halaliya ta ce…. Anjima bayan isha’i kishirya zan fara zuwa zance. Duk acikin wasan ne. Karki kuskura kice a’ahh.. “
Kit ya katse Kiran, Nabi screen din wayar da kallo ina maimata kalmar ‘zancen’ daya ce. Wane zance kuma bayan ya auro ni gaba d’aya? Naja tsaki Ina mai wurgi da pillown kusa da ni. Tashi nai na shige bandaki ina jinjina al’amarin Salman…
*GIM. SHAHEEDAH*
Gaba d’aya a razane take, Ta tattare ta koma k’arshen gado ta kudundune da bargo, kwallin idanunta duk ya zazzago, Tamkar ta fece da gudu yadda take a dimauce. Sai rawa jikin ta yake tana mai toshe kunnuwanta, Tana mai nanata,
“Wayyo Allah hajjaju na.. Gasunan sun zagaye ni, kingan su Kowanne harshen sa ya zazzago. Wayyo zasu cinye ni hajjaju. Kinga kwaduna zasu cinye ni hajjaju…”
Wajen kofar dakin kuma hadiman tane Kowanne ya tsaya cirko cirko sun rasa yadda zasuyi. Cikin haka saiga jakadiya Abu (Zainab)ta shiga hankalin ta a tashe,
“Ina gimbiyar take…?”
“Tana ciki tahana kowa ya shiga..”
Cewar batula babbar hadimar ta.
Kutsa kai jakadiya tai tashiga ciki, Tana shiga shaheeda ta kurma wani ihu hade da lailayo lafiyayyen zagi ta maka mata, Da doriyar jefa mata wani babban matashin kai dake kan gado,
“Subhanallah! Asssha gimbiya, Ni ce abu, Jakadiyar mai martaba, Ki temaka na kaiki wajen su Mama Huwaila ko kyaji sassauci kinji.”
“Wayyo Allah hajjaju gasunan zasu kamani.. wayyo .”
Haka shaheeda taita fada, Dakyar jakadiya ta kamota ta shiga lallamata kamar karamar yarinya. Har saida tasamu tayi bacci tukun Sannan, Suka temaka suka kaita sashen su Mama Huwaila………….
*GIM. KHADEEJA….*
Ina kwance ina kallon Chinese drama din love 020 naga message d’insa ya shigo wayata,
“Ki sakko ina parlorn kasa…..”
Ajiyar zuciya na sauke, Na hadu da gamo na ni dije. Banyi wata kwalliya ba don banga abunyi ba, Na dai shafa turaruka Na koma goga man lebe. Na zura abaya baka na yane kai na da mayafi. Sai dana bata lokaci kafin na fita na sauka kasan, Tundaga bene na hango shi a kasa. Ya zauna akujera yana danna wayar sa. Sanye cikin shadda sky blue, Yasha wata hula damanga. Wallahi kamar wani saurayi. Saboda yadda kwantaccen gashin bakin sa yayi masa kyau. Bansan sanda na gurde ba garin kallon sa, Sai ji na nayi ajikin mutum ya tallabo kugu na yana bina da kallo…
Kallon juna muke yi tamkar yaune rana ta farko da muka taba haduwa. Shi nasa kallon mai cike da soyayya ne tare da kulawa, ni kuma ina kallonsa ne ganin irin taimakon da ya bani cikin gaggayawa dan da tuni naci kasa wallahi. Iskar bakinsa ya hura min mai cike da kamshin mint, na lumshe ido ina kara bude kofofin hanci na dan jiyo kamshin.
“Zaki janyo min asara.” Naji ya fada a hankali.
Waro ido nayi na kalleshi da son jin karin bayanin wacce irin asara kuma? Dagoni ya yi tare da saka ni cikin kirjin shi, bakinsa kusa da kunne na yake magana.
“Idan kika fadi kika ji ciwo ai kinga nayi asara tunda zaki ji zafi.”
Ina jin haka nayi saurin ture shi ina yatsina fuska, kai tsaye na nufi gurin kujera na zauna ina kikkifta idanuwa kamar wata marar gaskiya. Kusa dani yazo ya zauna, sai kawai na samu kai na da jin wata irin kunyarsa, na kawar da kai gefe ina wasa da hannun kujerar.
“My love babu gaisuwa?” Yayi maganar yana son ganin fuskata amman na hanashi.
“An yini lafiya.”
Ya shafa kwantaccen sajan shi.
“Saffa – saffa dai tunda kin boye Kwana da kwanaki kin hanani ganinki.”
Uhmmm lallai ma wannan mutumin ni zaka sake rainawa wayo bayan ganin nawa da kake yi kare min lissafi kake shine zan yadda na ringa ganinka. Ya kuma matsowa kusa dani tare da rungumo ni zuwa gefen jikinsa, na shiga tutture shi amman yaki saki na.
“Ya isa haka my love, zance fa nazo ko kin manta.?”
“Haka daman ake zancen duk ka nanike ni sai kace yar air.?”
Sake matse ni ya yi a jikinsa bakinsa kusa da gefen fuskata yana fadin.
“No… No… No my love! Zance zamu yi irin na turawa. Ya gida dasu Ammi?”
Ya fada cikin son bagarar da wancen maganar.
“Ni fa gaskiya bana son irin wannan, turawa ai ba namu bane mu koma larabawa tunda daman a can kafi yin rayuwarka.”
Kamar na zuga shi sai kawai naji ya dakko ni gabaki daya tare da dorani saman cinyarshi, na shiga zillewa ya hanani koda motsi yana cewa.
“Dai dai kenan baby na, kinsan shi balarabe akwai…Iya tattali da kulawa akan abinda yake so, musamman ma mace.”
Lallai wannan bawan Allah yasan takan rainin sense, kiri-kiri yasan abinda nake nufi amman sai ya dinga bagarar da lamarina yana yin nashi.
“Ina son na samu lokaci na ziyarci dangin ki my love.”
Da sauri na juya Ina kallonsa cike da mamaki, ya akai yasan abinda yake cikin zuciyata? Kodai na yi masa zancen ina son zuwa gida ba tare da na sani ba? Kai Anya wannan mutumin baya amfani da aljanu wajan sanin abinda yake rai na? Sumbatar da ya kai min a gefen kumatu na sune suka sani dawowa daga gajeran tunanin da na shiga….
_Masu bukatar makeup.. Casual, special casual, simple glam, bridal makeup, fixing of lashes, gele and turban, modeling. Sai ya tuntubi BEELANAH BEAUTY.. Instagram handle: Beelanah_Beauty… Tana court road, Kusa da novomed, kano nigeria. 08034697302 Domin nemanta ko karin bayani sai a tuntubeta ta lambarta👈🏼Available to travel. #blush it up 🥂_
<><>
Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma’ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
GIPHY App Key not set. Please check settings